Showing 114001 words to 117000 words out of 213309 words

Chapter 39 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5874

tsaye Ina kallonsa harsaida yafice a gate ɗin makarantar sannan nasauke wani wawan ajiyar zuciya Ina murmushi kamar wata wawiya sannan najuya nanufi garden ɗin don ɗaukan ledan dayace nawane. Aikuwa Allah yataimakeni ba'a ɗauke ledan ba,anan inda muka barta nasameta.

Buɗe ledar nayi senaga sponge cake ne me kala kala guda huɗu dayasaya a Oasis,sekuma roasted fish dake cikin foil paper,slice bread,se irin Babban kwalin exotic guda ɗaya aciki.

Mamakin Ina yasamu kuɗin dayamin sayayyarnan nashigayi dan senake ga kamar ɗan aikin dayacemin yanayi yanzu baikai yasamu wannan amount of kuɗin ba,anma danayi la'akari dazai iya yuyuwa yajima yana tara kuɗin ne seban yi mamaki ba because for sure nasan ba sata yayiba dan nasan Yaya Lamiɗo baiyi kama da wanda zaiyi sata ba and from the way he's so contented with what yakedashi sanda muke zuwa field tare a Babban Buli na tabbatar bazai taɓa yin sataba,besides i trust his intentions sekawai naɗauki ledar nanufi hostel abuna raina fess kamar banine nasha kuka kala kala ba yau.

***
Tunda nashiga gate ɗinda zai sadani da hostels ɗinmu nakejin hayaniya tako'ina unlike ɗazu darana dana shigo naji ko'ina shiru. Ma'ana yanzu kowa yadawo daga visiting ground ana hirarrakin abubuwan dasuka faru acan visiting ground ɗin. Ko waɗanda nike wucewa a hanya yawanci hirar dazakaji sunayi kenan,daga masu bada labarin yan gidansu semasu bada labarin sauranyinsu dayakawo musu ziyara yauɗin.

Nidai harna Isa hostel ɗinmu fuskana ɗauke yakeda murmushi hakanan duk wasu moments ɗina da Yaya Lamiɗo yau su kaɗai keta ringing a kwakwalwana. tunaninsu yabi ya mamaye duk wani takaici da bakin cikin da aka cusa min yau. Ɗakin mun ma danashiga surutu na tadda suke tayi ayayinda tundaga bakin kofa nadinga cin karo da empty kwalayen juices, biscuits, indomie su conflakes dadai sauransu,ma'ana dayawansu sunyi gyaran lockersu ayayinda wasunsu kuma yanzu suke kanyi.

Corner mu nida Sadiya nawuce na buɗe locker na na ajiye ledan da Yaya Lamiɗo yabani tareda kuɗin daya bani sannan narufe lockern nasake fita waje. Matrass ɗinda bazan iyacewa nawane kona Sadiya bane naɗauko nashigo dashi dankuwa haryanzu babu abunda yacanza a abunda takeyi min game da fitsarin kwancenta haryau.

katuwar blanket ɗinda na shimfida akan gadon yayi serving kamar katifa dayake yanada nauyi nacire sannan na ɗaura katifar akan gadona Ina tattaba inda na zuba masa ruwa ɗazu dasafe don jin koya bushe dakyau kobai busheba dayake yau ban fitarda katifar dawuriba kasancewar yau anyi inspection,seda aka gama sannan nafidda shi da Aziza tazo min dasafe. Kuma ita tanunamin dabarar shimfida blanket ɗina akan inbar gadon empty mutane suna gani,kuma dayake katone blanket ɗin seka saka Ido sosai zaka gane babu katifa akai.

Bayan nagyara gadon na shimfida bedsheet ɗina sena ɗauki buta nafita a ɗakin natafi can bakin tap ɗinda ke can wajen hostel ɗinmu nadibo ruwa sannan nadawo nan gaban kofar ɗakin mu nazauna nayi alwala dayake gaf ake da akira sallar maghriba. Ko bayan dana koma ɗaki bayan na'idar da alwalan kwanciya nayi akan gadona inajiran akira sallar maghriba ayayinda nake tunanin Yaya lamido. Tunani nakeyi ko yana Ina yanzu? Shin yasamu motar komawa ne kobai samuba? Inma yasamu motar tacikane kobata cikaba? Kokuma kilan suna kan hanya yanzu? Ni kaɗai dai haka nadinga sake sake cikin raina har aka ƙira sallah natashi na shimfida sallaya nahau darduma nayi.

Ban Jima da idar da sallah ba naji Sister Hafsat (Room Head) ɗinmu tana kwala kiran sunana,amsawa nayi sannan natashi natafi kwanarta,plate ɗin abinci da ledan fruit tamikamin.
karba nayi duk atunanina aikena zatayi wani guri anma da mamakina setacemin "jeki nakine" mayarmata nayi da sauri sannan nace "nagode anma a koshe nake Sister Hafsat" tsuke fuska tayi sannan tace "Anjima zakici ai,jeki dashi babukyau maida hannun kyauta baya" senayi murmushi nace "toh na gode" sannan najuya nanufi kwanana,senaga few daga cikin Yan ɗakinmu nata bina da kallo anma senayi kamar banganiba harna ƙarasa kwanana.

Banyi mamakin kyautar da Sister Hajara tayimin sosaiba don daman tanada kirki kuma she's very simple sannan duk tsanar da tsangwamana da sauran Ƴan ɗakin mu keyimin ita batayimin kwata kwata sannan bata taɓa zagina wai Ina fitsarin kwance ba infact sometimes intaji Ƴan ɗakin mu na gulma na har faɗa takeyi musu kotayi purnishing ɗinsu. Mates ɗinta nedai bata iya cemusu komai dayake batada righi ɗin hukunta su,cikinsu kuwa harda kawar Yaya Zaheera da Yaya Zaheeran tabama amanar Sadiya ranar da aka kawo mu dadare.

Dukda ba shiri mukeyiba gaisuwa kawai ke haɗamu and I respect her so much.

Na ajiye plate ɗin abincin kenan Ina neman wani plate ɗinda zan rufe abincin dashi kawai sega su Yaya Zaheera sunshigo corner mu dukansu huɗu,Sadiya,Yaya Zaheera,Yaya Aisha da Yaya Safiya.

Akan gadona Yaya Zaheera da Yaya Aisha suka zauna ayayinda Yaya Safiya tahau saman lockern Sadiya tazauna dayake babu wani bunk kusadamu,dagamu se kofar ɗakin,sauran bunks ɗin duk seka tsallaka ɗayan side din dakin zakasamesu. abunda ke gabana nacigaba dayi batareda na ɗagoba wato neman empty plate inrufe abincin da Sister Hafsat tabani.

Inaji Sadiya tatura ledojin kayan da aka kawomana daga gida,danasamo plate ɗin nima saina rufe abincin natura karkashin gadon mu kafin natashi tsaye daniyar infita inbasu guri inyaso daga baya insun tafi nadawo.

Anma sede ko steps uku banyiba naji Yaya Zaheera tace "Keee! Zonan!" wani irin rasss! Naji zuciyana yayi lokaci guda kafin najuya ahankali na karasa inda take zaune na tsuguna sannan nace "Gani Yaya Zaheera" harara ta watsamin ayayinda take taunar cingam sannan strictly tace "Wayene gayen dana ganki dashi a school garden yau?" aikuwa se bugun zuciyana yakaru,Sena fara tunanin kenan "taganni da Yaya Lamiɗo ɗazu komi take nufi?".

Wani tsawar data dakamin ne yafidda ni daga trance ɗina,tace "ba magana nakeyi miki banewai?" bakina narawa nace "Yayanaaa ne" wani kallo takuma watsamin sannan adakile tace "Yayanki ne?" gyadamata kaina nayi ahankali,tace "ta'ina yazama Yayanki?"


*ah toh Zaheera Nimadai tayani tambaya.😜 Fans ta'ina Lamiɗo yazama Yayan Rukayya?"

*Littafin Qadr na kudine duk maison shiga paid group should talk to me privately via this number on WhatsApp 08147722806 for payment details*

*Page Thirty Seven*

Avoid typing errors Please.


Ta'ina yazama Yayanki? ya akayi kuka haɗa dangi dashi?" inajin tambayar da Yaya Zaheera yayimin amma senayi shiru bance mata komaiba dannikaina banida amsar dazan bata.

Yaya Safiya dake zaune akan locker ne tace "Tawurin mahaifiyarki kuka haɗa dangi dashi komi?" tsaki Yaya Zaheera tayi sannan tace "Babu wani dangin dasuka haɗa tawurin mahaifiya,ke baki taɓa ganin irin dangin mahaifiyar tata bane sanda muke zuwa asibiti duba Uncle Umar? they're typical villagers fa,Guy ɗin dana gani ɗazu kuma ko kusan haɗa kama da kauyawa ma baiyiba" Yaya Aisha tsaki tayi sannan tace "kyale Safiyar nan Yaya Zaheera,sekace bataji yanda su Rabia ke describing guy ɗin ba ɗazu" Yaya Safiya tace "naji mana,naji yanda suke describing ɗinshi anma ai that does not mean bazai iya haɗa dangi da Mahaifiyata ba. Take a look at us,muba Ƴan Uwan su Kawu Hassan dake Giyaɗe baneba? infact most of our relatives acan suke zama kuma babu wanda zaiganmu yace mana ga asalinmu so it can be thesame thing with the guy" sekuma maganar Yaya Safiyar tayi making sense agurinsu,se Yaya Zaheera takuma dubana dan tayi confirming tace "Dangin Maman kine?" rashin sanin abuncewa sekawai nace "Eh" tace "a Ina yake zama?" Nace "A Gombe suke" tace "toh ta'ina kuka haɗa dangi da mutanen Gombe kuma?" senayi shiru, Yaya Safiya dakejinmu tace "tace Yayanta ne kilan cousin Brother ɗinta ne"...

Se Yaya Zaheera tace "cousin ɗinki ne?" Kawai sena kuma cemata "Eh zamane yakai su can" tace "Awani makaranta yake?" nace "Gombe state University" dankuwa banmanta sunan makarantar tasuba.

"Wani course yakeyi kuma awani leven take?" Yaya Zaheera takuma jefomin wasu tambayoyin dayasa nafara tunanin anya ba Ƴar jarida baceba kuwa? wannan interrogation haka? And more over meyasa sukeson susan information akan shi? And miyasa naji suke zancen kawayensu suna describing ɗinshi anma ganin banida amsar tambayar danakema kaina gakuma dukansu sunzubamin idanu suna jiran ansar tambayarta daga gareni senace "Geology yakeyi kuma yagama aji uku yazu yana industrial training ɗinshi ne kafin suyi resuming yashiga final year"

Kallona juna naga suntsaya sunayi naɗan wasu daƙiƙu kafin suka dawo da dubansu gareni wanda hakan yasani sauke kaina ƙasa da sauri.

Yaya Zaheera tace "Keɗin ya akayi kikasan informations har haka agame dashi?" Yaya Safiya couldn't help it but laugh tace "mutum da Yayansu bazaisan abubuwa game dashiba?" Yaya Zaheera strictly tace "Bawani. Yayanta najinine? He's just a mere cousin Brother and anything can happen" sannan tamaida hankalinta gareni sosai tace "keh! ɗago kikalleni" ɗagowa nayi nakalleta kamar yanda tace sannan cikeda tuhuma tace "kodai Soyayya kukeyine?" Aibansan sanda na ware idanuna ba hakanan cikeda mamakin kalaman ta nace "Soyayya Kuma? Yayana nefah kawai" dannidai a iyakacin shekaruna I don't even think yakamata tayimin maganar soyayya.

Seta cemin "tsakanin ki da Allah Yayanki ne ba soyayya kukeyi ba?" Cikin sauri nace "Allah Yayana ne kawai" tace "toh miyasa zaizo miki visiting shikaɗai?" senace "sabida muna shiri sosai kuma baiyimin ta'aziyar rashin Baba ba shiyasa yazonan" hararana tayi naɗan wasu daƙiƙu sekuma tatashi tsaye tanacema su Yaya Safiya sutafi, naɗauka sun rako Sadiyar ne su sukoma anma senaga Itama tabi bayansu.

Nidai harsuka fita a ɗakin mu mamaki nakeyi kamar mi, I'm so speechless and out of words gashi banida wanda zan tambaya insamu amsar dalilin wannan interrogation ɗin.

Fitarsu bada jimawaba sega Aziza niki niki da kaya tashigo cornern mu.

Cikeda mamaki nasaki baki Ina kallonta daga zaunen danake a bakin gadona sannan nace "kekuma niki niki da kaya inazaki kaisu?" hararana tayi sannan tace "nikitaso kitayani bazama zakiyi kina tambayana kamar wata Yar jarida ba" tashi nayi na karba ina dariya sannan nace "kene harzakicema wani Ɗan jarida? Har akwae wanda yakaiki iya tambaya ne daman?" Aziza samun guri tayi tazauna agefena bayan mun ajiye kayayyakin dake hannunmu tana faɗin "aigwanda ni inzanyi tambayar reasonable questions nike tambaya! Kekuma naqi tambayar harda silly one's kike haɗawa" hararanta nayi ina murmushi nace "Komadai menene bankaiki ba" sena canza maganar tahanyar nuna kayayyakin data shigo dasu nace "kekuma sakon Suwaye haka kikawani zomin dashi corner na?" Aziza tace "nawa kuwa inba naqiba? Mummy ne tace inbaki tunda kinki kikoma kuyi sallama" takarashe maganar ayayinda ta kama hannuna tasaka min kuɗi aciki tana karawa da "wannan ita tace Inbaki"

Ware idanuna nayi sannan nace "Keh lafiyarki Aziza? duk wannan uban kayan inazan kaisu? Anya bakayan ki Kika dibo Kika kawomin ba?" Aziza seriously tace "wallahi ba kayana baneba,kayana na hostel Mummy ne tace inbaki inkuma bakiyarda ba ranar Monday muje gurin Sir Buhari inkirata ki tambayeta" kawai sena rasa abun cewa, I'm so out of words and speechless...

Daƙyar na'iya uttering kayannan sunyi yawa Aziza,don Allah kiɗauko kikara akan naki toh. I've provision yauma kuma ankaromin daga gida" harara Aziza ta watsamin sannan tace "seki kara da wannan ɗinma kumani babu ɗiban dazanyi,nawama sun isheni kuma ainaki ne banawa ba" mikamata kuɗin nayi dasauri nace "kuɗin toh kirikeshi please! kikara akan naki inbaso kuke kuɗi sufara tsuro ajikina ba" dariya Aziza tatsaya yimun sannan tace "sufara tsuron mana,aini abun murnane agareni,duksanda nikeson kuɗi kawai sede inzo gurin ki in tsinka inje insayi abunda raina yakeso" hararanta nayi ganin tamaida abun wasa anma still sebata daina zolayar nawaba.

Daga karshe dai ganin taki yarda daduk wani kudirina senace "Nagode. Allah yasaka da alkhairi kuma don Allah ranar Mondayn zaki rakani muje ki kiramin Mummyn insakeyi mata godiya" Aziza gyaɗa min kai tayi sannan tace "Allah yakaimu" senace "Amin" ayayinda nakejin wani iri,duk senaji babu daɗi,ita iyayenta sunyi min abudayawa harda wahala dani anma ni banida abunda zanbata. Gashi Ƴar provision ɗinda nake takama dashima su Yaya Safiya sunkarbe.

Take kuma se abunda Yaya  Lamiɗo yakawomin yafaɗo min araina,daman na ajiyene akan setazo muci tare dasauri nasauka daga kan gadona nanufi lockerna na buɗe sannan naciro ledan na ajiye agabanta sannan excitedly  nace "ban faɗa mikibadai, Yayana yazoshi ɗazu bayan su Aunty sun tafi" sekawai naga Aziza tasauko daga kan katifana cikin sauri tadawo ƙasa kusa dani tazauna sannan cikeda zumuɗi tace "Daman Yayan kine yazo ɗazu dagaske?" gyaɗa matakai nayi sannan cikeda mamaki sannan nace "Anma Ya'akayi ke kika sani?" Aziza tace "Ai talk of the town kika zama yau a hostel yarinya" cikeda mamaki nace "kamar Yaya?" Aziza tagyara zama tace "kekam tun ina hanyar dawowa daga visiting ground bayan su Mummy sun tafi da yanman nan naji wasu suna hira ahanya,wai yau wata yarinya Brothern ta yazo mata surprise visit, tundaga nesa dakika ganshi kika kwala kiran sunanshi excitedly kikaje da gudu kika rungumeshi kika fara kukan murna,wai su murnar dakikayi da zuwa da kikayi kika rungumeshi dakuma haɗuwar gayen ne yabirgesu,kinji yanda suketa maganar kuwa? wai he's so caring,sewani rarrashin ki yakeyi duk inajinsu dayake agabana suke tafiya ahaka dai har muka iso wurin hostel dina nina shige inda su sukayi gaba anma me dana ƙarasa ɗakinmu sena tarar da Yan ɗakin mu ma Thesame hira sukeyi. Ashe tunkan nashiga ɗakin Khalisat ɗin ɗakinmu tasanar dasu kece dayake tana gurin abun yafaru kuma taganki shine dataji suna hirar seta sanar dasu cewa aikece dakike zuwa gurina kullum mufita tare"

Shine fa Su Sister Salma ɗakin mu dasuka ga nashiga ɗakin sukayita tambayana kona san Yayan naki ko mun haɗu,nace nidai bamu haɗu ba kumadai bansanshiba gaskiya,shine Sister Salma tace gobe inkaiki gurinta wai itadai Allah yagani tafara crushing akanshi dukda bata taɓa ganinshi ba.

Tunda Aziza kebani labarin nayi shiru Ina saurarenta ayayinda nake analyzing kowani maganarta Ina assimilating ɗinsa,Sena tuna kallona da Yan ɗakinmu sukayi tayi dana karbo abinci a wurin Sister Hafsat,natuna interrogation ɗinda su Yaya Zaheera sukazo sukamin ɗazu,natuna cewa dasukayi wata tace yahaɗu and then I got it cewa Ashe har samana ido akayi a gurin mu bamuna saniba.

Araina senashiga ayyana "ikon Allah! Wai daman haka boarding ɗin yake?asamu magana ɗaya aita yadashi? Masu exxageration suyi masu karyama duk sukara akai.

Maganar da Aziza tayimin ne yafidda daga trance dina bayan tagama bani labarin,tace "ashedai dagaske Yayan naki ne? anma cousin Brother ɗinkin from maternal side koh? Because as far as I know bakida blood Yaya,you're the only child to your parents dangin Babanki kuma ai ɗazu sukazo" murmushi nayi sannan nace "Eh Aziza. Munsaba dashi sosaine kuma baiyimin ta'aziyan rashin Baba ba shine yazo nan makarantar yau" tsuke fuska Aziza tayi sannan tace "Shine baki taɓa bani labarin shiba koh?Ni kullum sede inyita baki labarin close one's ɗina anma ke kwata kwata bakya bani labarin waɗanda kukasaba wanda har hakan yakesani tunanin you're always tortured at home ne" cikin sauri nace "waya faɗamin I don't have loved one's? I've so many of them anma the most dear ones to me bayan Babana are three in number" na ɗaga fingers ɗina nashiga mata counting nace "Kinga Gogede Grandmother nane and she's my role model,se Gwaggo Suwaiba,she's my Aunt but more like a Mother,i always have her back and lastly Yaya Lamiɗo,he's one in a million,he's my smile,my happiness and my ultimate emotional support. banjima da sabawa dashiba anma zan iyacemiki yafimin mutane dubbai danasaba dasu kafin shi"

Aziza data riƙe Chin ɗinta da hannunta tana kallona tace "it seems like this Yaya Lamiɗo dakike magana shine yazo yau?" gyaɗa matakai nayi Ina murmushi sannan nace "Shine,naso ku haɗu anma Allah beyiba dannima bansan da zuwan nasaba,it was a surprise visit but next time I'll surely look for you inyazomin visit insha Allahu" Aziza setace "Allah yakaimu" dayake banagajiya da bada labari indai na Lamiɗo ne, because it gives me so much joy senace mata "aiyama sanki! na taɓa bashi labarin ki kwanaki" wara idanu Aziza tayi sannan tace "nikuma?nida da bamwa wani shiri ada labarina name kika bashi kuma?" senayi dariya nace "cewa yayi inada yawan tambaya, I'm always curious akan koda abunda baikamata insani baneba shine nace mishi aibankaikiba. Kema gwanace when it comes to asking questions in the class,nace mishi har haushin ki mukeji in zakiyi tambaya a aji" dariya Aziza tayi sannan tace "kema ai haka kike,ke kawai bakya tambaya a ajine se an fita kike damuna da tambayoyi. dariya nayi sekuma na buɗe ledan naciro roasted fish dinda yakawo mani.

Nasamana akan plate mukaci da bread,muka karada abincin da Sister Hafsat tabani duk muna hira,hiran da yawanci akan makaranta ne sekuma damuna da Aziza tayi incigaba dabata labarin dangina wanda nasan duk bugan cikina takeso tayi,tana son tasan halin danake cikine anma senaki bata wannan side of my story ɗin,sena dinga bata labarin mutanen Babban buli da Giyaɗe dasuke Sona. agidan Kawu Sani kuma sena bata labarin Kawu sani,Yaya Salim da irin mutuncinshi,sekuma miskilancin Yaya Fahad. ranardai atakaice Aziza a hostel ɗinmu ta kwana dayake weekend ne kuma Sadiya ma ba'a ɗakin mu takwana ba shiyasa nina dale bunk ɗinta nabar ma Aziza nawa gadon tayi bacci akai. washegari ma seda mukayi wanka mukaci abinci sannan na rakata hostel ɗinsu.

Ananne na haɗu dasu Sister Salman ɗakinsu,har kwananta tajani tana min tambayoyi akan Lamiɗo inda daga karshe ta cemin ingaishe shi innakoma gida danta tambayeni numbersa nace mata niban riqe ba.

Nidai harna bar ɗakinsu Aziza nakoma ɗaki mamakin wannan zubar da class har haka nakeyi dukda kankantar shekaru na,ganinake ita Sister Salman harnawa take dazata fara maganar Soyayya? nida duk a mentality na naɗauka a birni se angama karatu gaba ɗaya ake fara kula saurayi anma danazo boarding school senake ganin abun differently,senake ganin kamar banbancinsu dasu Kwaidum ma kaɗan ne tunda su auren akeyi musu at their young she while anan kuma yan mata kula samari sukeyi at their young age. Natuna jiya naga Yaya Zaheera na hira,yau ance ana crushing akan Yaya Lamiɗo kuma wani sa'in ma nakanji Ƴan ɗakinmu na hirar samarinsu atsakaninsu and this always got me wondering.

Koda nakoma hostel kayan da Mummyn Aziza ta bata ta kawomin na buɗe ina gani ɗaya bayan ɗaya. madara ne peack medium size na gwangwami se Milo karamin gwamgwami,se conflakes guda biyu na kwali da golden morn ɗaya,se sugar cube biyu,se packet na detol,sabulun wanki guda huɗu,toothpaste,body spray,body lotion,hair cream,se biscuits da juice half half carton se kuɗi 2k ɗinda Azizan tabani daren jiya,ba ƙaramin mamakin mutuncinsu nayiba ayayinda nasaka musu albarka inakuma addu'ar Allah yakawo ranar dazanyi musu wani abun alherin nima.

Jera kayan nayi cikin locker na sannan na haɗa 2k ɗinda Yaya Lamiɗo yabani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login