Showing 30001 words to 33000 words out of 213309 words
dasafennan ma benemi sanin ko anyi test ɗin ko ba'ayi ba. haka yaɗibi kafafunsa yatafi wurin aiki,nikuma banyi tunanin tura kaba alokacin kwata kwata sabida naga kuna tareda Rukayya babu daɗi abarta ita kaɗai kafin Gogoden ta ta'iso"
Harsuka Isa lab ɗin asibitin Kawu sani faɗa yakeyi sosai kan rashin nuna kulawar dasu Kawu Adamu kema Baba dagasu har iyalinsu.
Kawu Sani yace "I'm very disappointed by them wallahi. dan bantama tsanmanin zasuyi abukamar hakaba even though najima dasanin cewa Adamu da Yaya idrissa kansu kaɗai suka sani,Yan ɗakin su kaɗai suka damuda sabida irin hudubar kajin da mahaifiyar su tayimusu anma ai yanzu shekaru sunja. Kowa yayi hankali kuma cikinmu babu ƙaramin yaro bare ace yana following footsteps ɗin tane.
Inbanda abunsu ma surasa wazasu ma wannan rashin kulawar se Umar? Umar ɗinda baidamu dakansa kamar yanda yadamu damuba? Umar ɗinda komai nashi nakowane? Umar ɗinda damuwar kowa nasane? Umar ɗinda ke kokarin kyautatawa kowa even though bawani karfi gareshi ba zuciyar yine kawai Allah yabashi donkomu damuka fishi samu bamukaishi yin alheri ba,bamu kaishi taimakon marasa karfin cikin dangiba dakuma kyautata ma iyaye. Nannan sanda Adamu yayi rashin lafiya rai a hannun Allah ina Umar ɗin ne yazauna dashi na tsawon watanni uku a asibiti batareda ya gajiya ba anma duk sun manta wannan,sonkai da son abun duniya ya rufe musu idanu" Salim yace "Abba abunfa se du'a'i kawai. wani sa'in iyayen mu mata ke causing rarrabuwar kannan tsakanin Ƴaƴa,they always cause confusion,they always involve their children cikin faɗan su da kishinsu" Kawu Sani yace "that's the point my Son. kowa sotake Ɗanta ya bi bayanta,kowa sotake Ɗanta yashigar mata faɗa wanda inkuma hakan yafaru se afara samun sabani sabida babu Ɗan da zaiso araina uwarsa yayi shiru batareda yashigar mataba. Daganan kuma andinga samun rarrabuwar kai kenan. Women are just so hard to understand really" Salim yace "hakane but ni aganina Abba no matter how the differences between our mothers bekamata ace ana samun rabuwar kai tsakanin Ƴaƴa ba sabida sufa iyayen nan namu da wasunmu keson shige musu faɗan basanin juna sukayiba,zaman aurene yahaɗasu ayayinda sukuma ƴaƴan jini yariga ya haɗa, they're bearing thesame Father and identity. Then why always the fight?" dafa kafaɗunshi Abba yayi yace "da ace kowani Ɗa zaiyi tunani irin naka da polygamy house da dama sun rabu da irin matsalolinnan da Ƴaƴansu ke fama dashi. I just hope my other children think the way you do Son" murmushi Salim yayi batareda yace komaiba.
Littafin *QADR* na kudi ne don samun damar shiga paid group Amin magana ta whatapp for payment details 08147722806
Vote
Comment
Share!
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert* @wattpad
*Page Twelve*
Free page
Haka suka karbo robar da za'a dibi jinin Baba suka kaima Nurse on duty yazo yaɗiba sannan akamayar lab ɗin don carrying test ɗin inda akace daga baya aje akarbi report. Daddy yabar Yaya Salim da Kawu Hassan tareda ni inda yacemana zeje yadawo. ashe zuwa yayi ya sille Ƴan uwan nasa kan abunda sukayi. A makeken shagonsu dake makare da atamfofi,laces,shaddodi kala kala,kayan yara da manya dadai sauransu yasamesu. gakuma customers daketa kai kawo cikin shagon suna sayan kaya. Kawu Sani bayan sungaisa dasauran yaran shagon yaceda Yaya idrissa yanason magana dasu shida Kawu Adamu wanda hakan yasasu shigewa can cikin store room ɗinsu suka kebe.
Magana yayi musu akan abunda sukayi anma memakon sununa regret ɗinsu sesuka daura ma Kawu Hassan laifi suka ce su bece musu komaiba,basu saniba.
Ran Kawu Sani baci yayi sosai dan yasan Hassan bazai taba yimasu sharri ba yace "Koh Hassan bai faɗa muku ba aganina yakamata ace kunayi kuna leka likitan kuna tambayarsa update gameda rashin lafiyar Umar ɗin. Kai koma bakujeba kwa tambayi shi Hassan ɗin me likitan yace anma cikinku babu wanda yataba tambayarsa bayan kunsan baiyi karatun dazai fahimci mema akecikiba ko anmai bayani,likitan ma baku taba nemansaba kwata kwata danyace Hassan kaɗai yasani" Kawu Sani yace "Why? sokuke kucemin aikinku yafi lafiyar Umar komi? couldn't you take few hours out of your work hours for your Brother? haba haba! kunbani mamaki wallahi" Kawu Sani yakarashe maganar cikeda disappointment.
Kawu idrissa dayake ganin Kawu Sanin raini yakeson yimai ba gyaraba yace "ya'isheka Sani,ya'isa haka. karka faɗa mana maganar banza. duk zuwan damukeyi muna dubashi baka ganiba,duk bata kuɗin transport da kuɗin mai ɗinda akayi akan iyalanmu dasukaje dubashi baka ganiba?sayan maganin danayi yauda safe nakawo shima duk baka ganiba se little mistakes ɗinmu koh? toh kai meya hanaka zuwa dakaga kafi kowa sonshi? yanda kakeson aikin ka haka mukeson namu muma hakanan yanda kakeson ciyarda iyalinka dede gwargwado haka muma mukeso muyi shiyasa muke faɗi tashi" cikeda bacin rai Kawu Sani yace "miye amfanin zuwanku dana iyalan naku tunda ba abunda yadace kukeyi ba? Kuma a shagon naku mekukeyi inbanda zama? ba yaranku ke aikin ba?" wannan Karan Kawu Adamu ne yayi magana yace "Dan yaranmu ke aiki se akace bazamuyi supervision ba?" Kawu Sani yace "gaskiya ce dai guda ɗaya kuma bakwa sonta sannan inason kusani rayuwarnan bakomai bane acikinta,inmutum yace zasa hassada da kyashi aransa toh he'll never succeed. Kuma in mutum yayi mai kyau zai gani a kwaryar sa,inbakayi maikyau dinbama duka mutum zai gani a kwaryarsa" daganan yajuya yafita rai bace yana mamakinsu.
Atunaninshi dukda suɗin se ahankali bazasu taba yin abunda sukayi yanzunba,aganinshi rashin lafiya tafi gaban komai,aganinshi ko makiyinka ne indai akazo tafarkin jinya dole ya sarara maka anma segashi nashi Ƴan uwan sunbashi mamaki lokaci guda,suncanza mai view dinshi gameda Ƴan uwan taka lokaci guda.
Dayanman ranar Gogode takoma Babban buli inda tayi tayi inbita anma naqi nace nida Baba zanzauna kuma har lokacin banbar zubda hawayeba hakanan naqi sakin hannun Baba koda kuwa na minti ɗaya ne. Da dare Kawu Hassan yafita yasiyo mana Koko da kosai yadawo,sanda yamin tayi kinci nayi nace naqoshi hakanan inaganinshi yazauna yaci abincin iyacinshi harsaida yakoshi sannan ya ajiyemin sauran.
Dana tambayeshi na Baba fah secemin yayi "ai anasamai drip bayama iya tashi bare ya iya cin abinci" wasu irin dummammun hawaye sukabi kan kuncina Ina tuno yanda Baba baya wasa da abinci,yana bama abinci ultimate respect,duk inda time ɗin three square meals ɗinnan sukayi zaibar komi yakeyi yadawo gida muci abinci,wataran innaki ci yayita lallashina yana rokona inci bayason ulcer takamani. Toh gashidai yauga abincin kuma lokacin cinta yayi anma babu halin tashi yaci.
Karfe takwas Yaya Salim yashigo ɗakin hannunshi riqe da ledan take awayn abinci dana fruits yasamu guri yazauna yana tambayar Kawu Hassan jikin Baba.
Kawu Hassan yace masa "Dasauki alhamdulillah" kafin yadubeni cikeda tausayawa yace "Rukayya kukan nandai bazakibarshi ba? do you want to hurt yourself by crying?" Jijjiga masakai nayi ahankali,daman tuncan shi mutumina ne akaf gidansu. bamusaba ba ko ada damuke gida ɗaya sabida boarding school yayi,hutu kawai muke haɗuwa shima ba sosai ba. Toh yanzu ma dayake jami'a bamu saba ba bakuma mutaba zama munyi hirar datakai na minti goma ba anma duksanda naje gidan indai yananan yaganni kuma toh zamu gaisa yatambayeni Baba fuska daukeda fara'a unlike the others shiyasa nake ganin darajarsa da girmansa sosai. Sauran Ƴan gidan kuwa,wasunsu inna samu hararama ingode Allah hakanan wasunsu ma ko kallo ban ishesuba,wasunsu kuma tsangwama da habaici kokuma azageni directly babu yanda na'iya. Shikaɗai yafita zakka, shikaɗai yake ganina da idon mutunci mugaisa lafiya lafiya.
Ledan abincin daya ajiye gefensa yashiga buɗewa tareda ciro take away ɗaya yamikama Kawu Hassan sannan yaciro ɗayan yafara buɗewa yana kallona yace "zokici abinci toh dukdama ba dahuwar gida bace,a restaurant Abba yabani nasiyo kinsan muna parking. Aunty da Ummi basuyi girkiba yau,abincin gidama duk a restaurant mukasaya. nasu yana mota inna tashi tafiya zanwuce musu dashi gida" nidai bancemasa komaiba dukda araina nagama raya yafaɗi hakanne just to make me feel better. Wata zuciyar tace "Shikuma miye nayimin karya bayan yafi kowa sanin nariga nasan halin yan gidansu,babu wanda yake kaunata dazaiyi min wannan hidimar,bandaisan mahaifina ba dukda mashi bacin abuncin yakeyi ba
****
Satina ɗaya a asibiti tareda Baba kuma haryau babu wani cigaba a rashin lafiyar tasa sema abunda yayi gaba. hakanan kullum cikin baƙi muke,wasu daga Giyaɗe,wasu daga Babban buli wasu kuma daga nan cikin gari. Kullum ɗakin baya rabuwa da masu zuwa dubiya hakanan kowannensu zaizo seya taho da ɗan fruits ko drinks haka. Baba mutum ne me mutane fiyeda yanda me karatu zai kwatanta, gakuma fara'a dason kyautata ma al'aumma dukda kuwa karamin karfi nedashi. dayawa cikin customers ɗinshi dasuka saba cinikayya a kasuwa sun zazzo sun dubashi dasuka samu labarin rashin lafiyar tasa.
Acikin sati ɗayannan konan da nan bana matsawa daga gefen Baba,koda yaushe ina makale da hannunsa,inkaga natashi to bandaki zani kokuma sallah zanyi. Akwai ranar da Kawu Adamu yayi yayi inbisu gida dasukazo da dare shida Kawu idrissa bayan suntaso a aiki anma naqi dole yabarni bayan Kawu Sani yace masa aishima yayimin tayin akaini gidansa anma naqi sukyaleni kawai.
Tunda naji faɗan da Kawu Sani keyi gameda abunda Kawu idrissa da Kawu Adamu sukayi ma Baba naji natsanesu,naji inajin haushin su gaba ɗaya and it makes me wonder miyasa suke min murmushi akodayaushe idan sukazo,miyasa suke comforting ɗina dacewa Baba zaisamu lafiya insha Allahu bayan suna ɗaya daga cikin mutanenda sukayi wasa da lafiyarsa har na wurin sati guda. sedaga baya nalura dakyau,idan idon Baba biyune suke nuna sympathy akaina,suke comforting ɗina hakanan idan sukazo idanunshi biyu sunfi jimawa a ɗakin hakanan sundinga tambayar Hassan meda me likitan yace kokuma suyita tambayar Baba koyana bukatan wani abu and he'll just smiled sannan yagirgiza kanshi akan baya bukatar komai. Se abun yazo yana damuna,nafara tunanin miyasa suke yima Baba *Fuska biyu*,why are they showing their care in yana gani inkuma yayi bacci they never care. Kawu Sanin daya damu da Baban ma sincerely baicika zuwa yana samun Baba idonshi biyuba hakanan duk wasu wahalhalu dayakeyi bana tunanin Baba yasani dansu Kawu Adamu nunawa suke tare sukeyi masa komai a idonsa to which ni bansan daliliba.
Yau dasafe Kawu Sani yayi sa'an samun idanun Baba biyu. karasawa yayi jikin gadon fuska ɗaukeda murmushi yace "Umar Ina kwana?" Dakai Baba ya amsa masa kafin ya tambayeshi "yajiki?" nanma yamasa signal dakai alamun dasauki sannan Kawu Sani yace "toh Masha Allah Allah ubangiji yakara lafiya" nida Kawu Hassan da Yaya Salim muka amsa da Amin.
Kallon jikin Baba yayi yace "Hassan yauya ba'ayi mishi wankanba?" Kawu Hassan yace "Yaya yau babu kayanda zan saka masane shiyasa ma banyimasaba nace barina bari sekunzo nafaɗa muku" Kawu Sani yace "tohh! Ina akwai kayansa agida?" Kawu Hassan yace "eh akwai. wancan satinma da Yaya Yusuf(another step brothern Baba dake zama a giyade) yazo muka kwana biyu naje can gidan nayi masa wanki" Kawu Sani yace "Toh ai shikenan tundama akwai bari aje a ɗauko masa daga can gidanna shi" Kawu Sani yadubi Salim yabashi makullin mota yace "gashi kaje can gidan kawunku kaɗauko masa kayansa" Yaya Salim yace "aibansan inda kayayyakin sukeba Abba" dubana Kawu Sani yayi sannan yace "tashi kuje Rukayya daganan kema seki ɗebo wasu kayanki kizo dasu dan sauyawa" cewa nayi "Toh Kawu" kafin natashi nabi bayan Yaya Salim dahar yafita ina tunanin rabona fa da wanka tunranar da zanzo garinnan hakanan bansauya kayaba bare inner wears dankuwa ninama manta dawani abu waishi wanka da tsafta tsabar irin damuwar danasaka ma raina.
Gida mukaje na tattari kayana dana Baba sannan muka rufe gidan muka kamo hanyar komawa asibitin sega kiran *Baba Hadiza* (Ummin su Yaya Salim) a wayarsa.
Ɗagawa yayi yasaka a hands free sabida driving ɗinda yakeyi,daga ɗaya bangaren Baba Hadiza tace "Salim wai kana inane ni?" Sa hannu yayi yaɗan shafa sumar kansa sannan yace "Ina hanyar asibiti Ummi,naje gidan Kawu Umar naɗauko masa kayan sawa zankai masa" take Ummi tafara faɗa tace "duka dangin nasa dake kai kawo a asibitin basu isa suje suɗauko masa kayan agidannasa ba sekai? wato anga ubanka yafara zama mutum shine za'a daura masa nauyin komai koh? toh muma munada bukatar motar anan. Yanzunnan kajuya kan motar nan kataho gida zan aikeka" Salim yace "Ummi nafa kusa Isa asibitin kiyi hakuri in miƙa musu kayan se intaho gida yanzu" cikeda bacin rai Ummi tace "banyarda ba kadawo gida yanzunnan inba kanason ganin bacin raina bane toh" asanyaye Salim yace "kiyi hakuri ganinan zuwa" daganan ta katse call ɗin,take yajuya kan motar muka nufi hanyar gidan kamar yanda tabukata batareda yacemin komaiba.
Anma kallo ɗaya zakayi masa kagane ransa a matukar bace yake. mamakine yakamani danaga munwuce layin unguwarsu kallonshi nayi jiki sanyaye nace "Yaya Salim kawuce layin gidan fah" danduk atunanina bacin raine yasashi wucewa batareda ya saniba sekawai yasaki murmushi yace "ban wuceba Rukayya. banace miki munyi parking zuwa sabuwar unguwaba" nace "aina ɗauka wasa kakeyi" Ƴar dariya yayi ayayinda yayi parking kofar gidan sannan yace "yanzukam dai zaki yarda ai tunda gaki akofar sabon gidannamu" kallon katuwar gate ɗin nayi inajin zuciyata na aikin bugawa,tabbas gidan yamin kyau anma bana tunanin zan iya shiga cikin gidan sabida hali irinna mutanen gidan. buɗe motar yayi yana shirin fita yace "mushiga koh?" jijjiga masakai nayi alamar "a'a" nibazan jeniba sannan nace "kaje kadawo inajiranka anan" hararan daya watsamin ne yasani buɗe kofar motar nafice babu shiri yace "sokike inbarki acikin mota a layinmunnan da kafin kaga wucewar mutum se kajima?in gidannan bakonki ne ai mutanen ciki ba bakon ki bane Rukayya" daganan yasa key a motar yayi gaba ina biye dashi a baya Ina tunanin "inama babukowa agidan, inama barene acikin gidan da babu abunda zaihanani binshi ciki batareda nayi korafi ba anma ayanzukam nafi son ganin sabon gidan akan mutanen dake cikinsa. sabida koba komai innazaga nagani,the beauty of the of the house might lighten up my mood than suda nakeda tabbacin sedema sukaramin pain akan wanda nakeji yanzu"
Knocking kofar dake gefen gate ɗin yayi,maigadi yazo yabuɗe sannan muka shiga compound ɗin gidan. Kallon compound din gidan nashigayi bayan munshiga, compound ɗin kamar na tsohon gidan sune sede shi wannan sashi biyu ne aciki se boys quarters da ɗakin maigadi,kuma sashin ma ɗaya yafi ɗayan girma.
Babban sashin muka nufa inda yakwankwasa kofar Sadiya tazo tabuɗe takoma ciki batareda tace mana komaiba,shima baibi takantaba muka shiga katuwar parlourn sannan ya nufi wata kofa datake facing wanda naga Sadiya tashiga daga ɗaya bangaren. wani karamin parlour madaidaicin dabaikai wanda muka baro ba mukashiga, ko'ina a parlour fes dashi gwanin ban sha'awa gakuma su Yays Zaheera, yaya Aisha dakuma Yaya Zunnurain dake zaune suna kallon tashar *Zeeaflam*.
Kallon Yaya Zunnurain dake zaune kan kujerar dake kusa da bakin kofar parlourn yayi sannan yace "Zunnu ina Ummi?" Yaya Zunnurain yace "tana cikin ɗakinta" daganan yashige ciki yabarni tsaye gurin inajin su Yaya Zaheera namasa sannu da zuwa da alama ko lura dani basuyiba.
nidai tsaye nayi kamar wata gunki a bakin kofar parlourn kuma har haɗa idanu da Zunnu mukayi amma ko kala baiceminba sema kyabe baki dayayi yacigaba da kallonsa. Yaya Salim baijima dashiga ɗakin ba segashinan yafito yana faɗin "ashe Ummin na wanka shine bakufada minba?" Zaheera data tashi daga kwancen datake akan two seater tamatsa ma Yaya Salim yazauna tace "bamu masan tashiga ba inba yanzu dakake faɗa ba Yaya" Aisha tace "kumafa tun ɗazu kai take jira kazo kakai niqan wake inaga tagaji dajira shiyasa tashige wankan dandaman naji tana cewa zata fita unguwa" Yaya Salim yana wasa da makullin mota a hannunsa yace "niqa kuma?" Aisha tace "Eh Yaya,niqan wakene za'ayi alala dashi" Yaya Salim yace "yanzu niqan ne harsai ankirani ku bazaku iya kaiwaba?" Zaheera tace "Yaya babu injin niqa a unguwarnan wallahi,bakaga wahalar damukasha ba yaushiyasa" Aisha tace "niseda na gwammace bamuyi zancen muna kwadayin alala ba jiya da duk bamusha wahalar damukashaba yau" Zunnurain dariya yayi yana faɗin "maganinku ai. seku shirya missing kallon kabhi kush kabhi Gam dan ankusa farawa" Zaheera tace "Yaya Zunnu inamu kake ma bakin ciki to wallahi se inyi addu'ar Allah yasa adauke wutanma gaba ɗaya" Zunnurain yace "kiyi mana aini nataba kallon Film ɗin daman kune daman baku kallah ba" tura baki Zaheera tayi tana faɗin "koma miyene dai" and Yaya Salim couldn't stop laughing at them.
Nima bansan sanda nasaki murmushi ba ayayinda hawaye suka fara bin kunci na Ina tunanin inama nima inada yayu da kanne kamarsu,Ina ma inada wanda zan tsokana suji haushina kosuma su tsokaneni akan silly things kamar yanda sukeyi yanzu and carap idanuna suka sauka cikin na Yaya Salim dasauri nasa bayan hannuna nashiga goge kwallata sabida alkawarin dana masa bazan sake kukaba kwana uku dasuka wuce.
Littafin *QADR* na kudi ne don samun damar shiga paid group magana ta WhatsApp for payment details 08147722806
Vote!
Comment
Share!
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert* @wattpad
*Page Thirteen*
Free page
Ware idanu yayi yace "Rukayya daman baki zaunaba? Why are you standing over there?" dukansu suka juyo suna kallona banda Yaya Zunnurain da already yaganni tun ɗazu. Yaya Salim yace "zonan?" Ƙarasawa nayi inda yake sannan yace "zauna" nazauna agefenshi yace "kukan me kikeyi haka?" cikin sauri nace "Babu" yace "nikam bana hanaki kukannanba? banace addu'a kawai zakinama Uncle Umar ba?' gyaɗa masakai nayi ahankali yace "then why are you crying now?" Cikin gunjin kuka nace "ba sabida Baba nike kukaba Allah" yace "toh sabida menene?" Ummi datafito a ɗaki yanzu tanajinmu rai bace tace "sabida sakalalliyace,ubanta yashagwabata kamar yanda yashagwaba uwarta. komaima yimashi kuka sukeyi sabida suna damai biyema iskancinsu. kuma ma Ina ruwanka da kukanta Salim? meya kawota gidannan badai da'ita kake yawo a motarba?" Yaya Salim yakalli Ummi yace "Ummi Abba ne yace muje gidan tareda ita sabida ita tasan inda kayan Uncle Umar suke" Ummi tace "Kuma se akace dole a motar gidannan zakuje da'ita? motar da Babanku yamaidata kamar wani gwal,komu babu wanda yataba shiga cikinta inbanda kai dashi se ita da tsabar bakin hali Babanta ƙin sayan babur yayi sanda muke gida ɗaya dashi harsaida yasama musu gida su biyu sannan yasaya dukdan kar Kawunanka da ubanka wataran suce yayi mana lift. Mulokacin namu mazajen sunƙi siye sabida responsibilities ɗin gida da iyali yamasu yawa, ɗan gwanda Adamu daga baya yazo yasayi golf inda idrissa yasayi machine daga baya wanda alokacin mukuma muka zama abin tausayi sabida namu mijin yadage Boko zaiyi,yadage seyaga karshen biro wanda gashi yanzu tayi masa amfani. babu irin gorin da ba'ayi manaba hakanan