Showing 27001 words to 30000 words out of 213309 words
tsifa da dare.
Yanma lilis nadawo shima inashiga ɗaki nacire kayana nadaura zani nashige bayi donyin wanka. bayan nashirya maghriba tayi danhaka nayi sallah sannan mukazauna cin abinci da Indo inda daganan kuma muka tafi dandali wasa.
***
Bayan fitarmu Baffa yashigo gida sabida kiran da Gogode tayimai,agefen taburman datake zaune cikin rumfar kofar ɗakinta yazauna yana gaidata. Gogode ta'amsa inda yashiga tambayarta yanayin jikin Baba.
Sekawai tafara kuka,atake jikin Baffa yayi sanyi cikeda damuwa yace "Gogode kukan namenene kuma? Jikinnashi yayi tsanani ne komi?" cikin kuka Gogode tace "Umar najin jiki Idii,abun se addu'a kawai" jiki sanyaye Baffa yace "ikon Allah kuma shekaran jiya wancan danajeni jikin nashi dasauki sosai dan azaunema nasameshi harmukayita hira dashi yana tambayana Ru'eyya. Ashe bayan dawowana jikin yasake tashi?" gyaɗa kai Gogode tayi tana matsar kwallah sannan tace "mutumin da sai andaga ankwantar yanzu,komai yimashi akeyifah" Baffa Idiii yace "Ikon Allah. Toh Allah yatashi kafaɗunsa" Gogode tace "Amin ya Allah Idii. daman nakirakane batun Rukayya,inaganin zancen boye boyennan ya'isa hakanan,abunda yasa mukayi shiru ada ɗinma sabida munyi tunanin ciwon dazai warke yau ko gobene anma abuyakai ga har mutum baya iya tashi dakanshi se an daga ankwantar inaganin bekamata mucigaba da boyema yarinyarnan batun rashin lafiyar mahaifintaba gaskiya" Baffa yajinjina kai yanajin bayanan Gogode hartakai karshe sannan yace "kinada gaskiya Gogode anma batun alkawarin dana ɗaukar ma Umar fah? yanzu inyaga an ɗauki Yarsa ankaimasa bayan yace bayason tasani bazaiyi tunanin na kasa riƙe alkawarin dana ɗaukar mai ba? Bakya ganin zaiyi tunanin nakasa bama Yarsa farin cikin dayakeso asanda yake kwance kan gadon asibiti?" Gogode tace "nibansan wannan ba bankuma ɗaukeshi da mahimmanci kamar yanda nafi damuwa da Ƴar nan taje taga mahaifinta shima yaganta,koba komai intana taredashi shikanshi zaifijin dadi hakanan addu'an Yara karbabbiyace Insha Allah. Hali ne narayuwa Idiii babu wanda yasan abunda gobe zata haifar shiyasa kaga nayi wannan maganar" Baffa Idiii yadan numfasa sannan yace "duk shawarar dakika yanke yayi Gogode,inkince akaitan se akaitan mudai fatanmu Allah yabashi lafiya" Gogode tace "Amin ya Allah. Koni banason tashin hankalin Ru'eyya anma yazanyi? wayasan ranar daza'a sallameshi? Kuma dolefa tasani tunda hutunsu ma yakusa karewa sannan abumai mahimmanci ma shine yakamata ace tana tareda shiɗin donkoyau seda Kawunta Sani yatambayeni ita,yakuma nemi ba'asin miyasa ba'a kawota ba shine nasanar dashi abunda kacemin.
atake yacemin "wannan ba ƙwaƙwaran dalili baneba,Umar na'iya cewa kar akai Rukayya sabida kartaga yanayin jikinsa hankalinta ya tashi anma tabbas intana taredashi shikanshi zefi jin ɗadi" befito yacemin akawotaba anmadai yabani shawara kuma nidai maganarsa tayimin ma'ana fiyeda naka.
Baffa iddi yace "toshikenan se akaitan kawai" Gogode tace "hakan kam dazaifi. Ko gobe dasafema seka haɗa ta dasu Rahane sukaita taga yanayin jikinnashi daganan ma kaga su Rahanen swa dubashi. Baffa yace "toh Allah yakaimu" kafin yatashi yakoma kofarsu.
Tun a daren ranan bayan nadawo daga dandali Gogode tacemin gobe intashi da sassafe zamuje cikin gari taredasu Yadikko Rahane, daɗi kamar nayi yaya dankuwa tunda tafaɗa min nasama raina indai nashiga garin Bauchi gobe babu abunda zaihana ni zuwa gida ingano Baba kafin mudawo dukda kuwa ɗazu nama Gogode alƙawarin zama se hutuna yaƙare anma ai yanzu ita tace inshirya zamuje gari,kuma indai har zanje gari mezai hanani zuwa gurin Baba? tunda dalili yakaini. Tun adaren naciro kayan dazan saka na ajiyeshi saman akwatin Gogode kafin nakwanta bacci. washegari dawuri natashi nashirya kamar yanda su Yadikko Rahane suka tashi dawuri suma,takwas nayi mukatafi batareda nasan takamaimai inda zamujeba tsabar zumuɗin ance za'aje gari dani,nidai damuwana inje Inga Baba ba inda zasuje bane damuwata. Seda naga taxi driver na ƙoƙarin shiga general hospital na Bauchi sannan nafara tunanin "Daman asibiti zamuje? Toh waye babu lafiya?" and then my heart starts beating without a reason. Sonake intambaya waye babu lafiya anma bakina yayi nauyi,nauyin da nikaina bazan iyacewa ga dalilinsaba.
Ahakadai mai taxi ɗin yasamu guri yayi parking su Yadikko Rahane suka biyashi kuɗinshi sannan muka fara takawa cikin harabar asibitin. Mutane natakai kawo wanda kallo ɗaya zakayima kowannensu kasan ba daɗi yakawosu asibitin ba,jinyace takawosu danwasu zakaga tafiyarma daƙyar sukeyinta,wasu kuma turasu akema akan sickbay,wasu kuma gashidai suna tafiyar lafiya Lau amma kallo ɗaya zakayi musu kagane basuda isasshen lafiya. kawai kwantar dasune ciwon baiyiba,wasu kumada taimakon yan uwansu masu lafiya suke iya takawa. naga mata masu ciki,naga masu ciwon kafa,naga masu zazzabi,naga waɗanda sukayi accident(hatsari) dadai sauransu kuma duk seda suka bani tausayin dan by just a mere look zakagane how much they're suffering dukdama wasu sunfi wasu shan wahala and even though I was very young,deep down in my heart I sympathize with them. It was my first time going to the hospital dannidai bantaba rashin lafiyar datasa aka kwantar daniba,inkaga nayi zazzabi toh baiwuce kwana daya biyuba na warke sekuma mura dayazamo usual ciwona barinma lokacin sanyi,inada pneumonia dukdama baya tashi sosai sabida Baba namatukar ƙoƙari gurin ganin nakiyaye duk abubuwan dazai iyasawa yatashi.
Tafiya mukadinga yi harmuka isa wani ward,gaida security ɗin gurin Yadikko Deejah tayi sannan tashiga tambayarshi ɗakin da ake ajiye marasa lafiya awannan ward ɗin,kwatance yamana sannan muka mishi godiya muka shige cikin ward ɗin,a kofar dakin daya kwatanta mana muka tsaya. Yadikko Rahane tafara shiga sannan Yadikko Deejah tabi bayanta seni dake biye dasu abaya, ɗakine babba dayakeda tsayi sosai ga kuma gadaje sunfi dayawa,tundaga bakin kofa naga nake ganin duka gadajen ɗakin are all occupied by male patients wanda hakan yasa bugun zuciyana yatsananta batareda nasan dalili ba.
*Sorry for the short page please*
Littafin *QADR* na kudi ne don samun damar shiga paid group amin magana ta WhatsApp for payment details08147722806.
Vote
Comment
Share
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
*Page Eleven*
Free page
A gaban wani gado naga su Yaddiko Rahane sun tsaya wanda hakan yasani tsayawan nima. kallon Kawu Hassan autan mazan gidansu Baba nayi zaune kan wata yar gujera wanda hakan yasani mamakin meyakawo shi asibiti kuma?waye ba Lafiya? sede tunma kafin nasamu damar tambayar wadanda nikejin zasubani amsa yanda yadace naji Yadikko Rahane nafaɗin "Mallam Umaru yajikin?" and if I'm right that's the only name da mutanen Babban buli ke ƙiran mahaifina dashi,afirgice na ƙarasa kusa dasu,nature Yadikko Rahane gefe ina kallon mutumin dake kwance kan sickbay ɗin helplessly. Babana ne,the only Father that everyone could ever ask for,mahaifina abunsona,mahaifina abun alfaharina,mahaifina danake ganin babu kamarshi acikin rayuta. Shine kwance agadon asibiti duk yatsomare,yayi wani iri,kallo ɗaya nayi mashi nasan yana tsananin shan wahala.
Wani irin ihu nasaki ina faɗin "Baba. Baba meyasameka? miyasa suka kawoka gurin marasa lafiya bayan Gogode jiya tacemin lafiyarka Lau? Baba meke damun ka" nayi maganar cikin gunjin kuka ayayinda nafaɗa jikinshi ina jijjiga shi ina faɗin "Baba kayimun magana dan Allah. Baba kacemin dagaske Gogode takeyi lafiyar ka lau"
Anma shiru baicemin komaiba sema jidanayi kamar ina jijjiga gunki wannan dalilin yasa naɗago dakaina cikin sauri nakalleshi. shima kallona yakeyi with so much emotions ayayinda naga hawaye yana zuba daga gefen idanunshi hakanan hannunshi yafara motsi wanda hakan yasani kallon hannayen nashi ina kokarin tabawa Nurses ɗin dake ɗakin sukazo suna ma su Yadikko Rahane magana kan sufitar dani inbazan yi shiruba sabida ina damun sauran patients ɗin dake ɗakin. Yadikko Deejah ne tazo tana ƙoƙarin kama hannuna anma senayi sauri nakama hannun Baba naƙi sakin hannun ina kuka metsuma zuciya. damuwata baiwuce yacemin wani abuba anma kalma ko guda ɗaya yakasa fita daga bakinsa,gashidai bakinshi na motsi alamun he desperately wants to talk anma maganar taki fitowa. ganin Yadikko Deejah takasa rabani da jikin Baba yasa Nurses ɗin dakansu suka zo suka jani daga jikinsa sunamin faɗa da indaina ihu,tayar masa da hankali zanyi dama sauran patients ɗinda ke ɗakin. cikin gunjin kuka nakalli Nurse ɗin nace "Meyesa baya magana? meyasamu Babana don Allah? yaushe zaisamu lafiya mukoma gida? bani da kamarsa, banida maisona irinsa don Allah kubashi maganin dazaisha yasamu sauki mukoma gida. Dan Allah kada kubari Babana ya wahala kamar yanda nake ganin sauran marasa lafiya suna wahala" duka Nurses ukun dasuka fitar dani waje seda suka zubda kwallah tsabar tausayina haka su Yadikko Rahane ma. ganin naƙi yin shiru ne yasa ɗaya daga cikin Nurses ɗin tajani zuwa jikinta ta rungumeni tana faɗin "Ƴan mata ba kuka zakima Baba ba,addu'ar samun sauƙi zakiyi masa kinji?" Ina sheshekar kuka nace "dagaske idan nayi masa addu'a Allah zaikarba yabashi lafiya?" gyaɗa min kai nurse ɗin tayi tana goge kwallarta tace "insha Allah,bareke da kikeda kankantar shekaru ma,Allah yafi karban addu'an yara kanana" jikina na bari nasaki jikinta,butan dana hango kusa da kofar shiga ɗakin nayi sauri naje naɗauka, Allah yataimakeni akwai ruwa aciki. Bantsaya tunanin gurin danake yadace nayi alwala kobai daceba kawai nahauyi agurin inayi ina hawaye,Ina sheshekar kuka....
Suma Nurses ɗin se suka kasa cemin komai,suka kasa hanani dukda kuwa zubda ruwa agurin is out of bound harna idar da alwalan nacire ɗankwalin kaina nasamu gefen da mutane baswa bi nafuskanci gabar nashimfiɗa ɗankwali sannan natada sallah still hawaye basubar bin kuncina ba. Bazan iya faɗa muku mintunan dana ɗauka akowaci sujjadar raka'a biyun danayiba,sallah nake Ina kuka Ina addu'ar Allah yabama Baba lafiya harda shikewa. ganin na galabaita anma still naqi barin sallan har Ina neman faɗuwa sabida irin gajiyar da kafata tayi yasa ina sallamewa tareda niyar tashi insakeyin wata Yadikko Rahane tazo tarungumeni tana faɗin "ya'isa haka Ru'eyya am. zauna kihuta tukunnan" da idanuna dasukayi luhu luhu nadubeta cikin muryar tausayi nace "Baban yasamu lafiya ne?Yatashi ne Yadikko?" kawai se yadikko Rahanen tafara hawayen itama wannan dalilin yasana zame jikina daga nata ina ƙoƙarin tashi ayayinda idanuna ke zubda hawaye nonstop, ƙoƙarin sake riƙoni take amma nakauce ina faɗin "Baba baisamu lafiyaba Yadikko. Kibarni inyi masa addu'a tunda likitancan tace Allah zaikarbi addu'a na inni nayimasa" Yadikko Rahanen seta kasa cemin komai. haka tabarni nacigaba da sallah Ina sheshekar kuka. Bayan azahar Kawu Sani da Yaya Salim sukazo asibitin kuma sanda suka shigo ward ɗin yayi dede da lokacin da karfina yakare, immunity system ɗina yakasa jure tsayuwar danakeyi as a 11 year old child harna yanki jiki nafaɗi nasuma. Yaya Salim ne yafara ganina yana niyar nuna ma Kawu Sani ni nafaɗi na suma wanda hakan yasashi kiran sunana dakarfi "Rukayya!" Ayayinda ya ƙaraso inda nake kwance da gudu. ɗaukana yayi inda akakaini wani ɗaki akasama min bed akafara bani taimakon gaggawa. bantashi sanin inda kaina yakeba se bayan sallar isha'i dana farka naganni kwance kan gadon asibiti,irin gadon da naga Baba akai ɗazu yana kwance helplessly.
Juyawa nayi ina karewa ɗakin kallo ko Allah zaisa inga Baba anma babushi babu alamarsa,infact nan ɗakine dake ɗaukeda Mata zallah kamar yanda nasu ɗakin ke ɗauke da Maza zallah. tunanin halin da Baba yakeciki dakuma inda yake yasani saurin tashi zaune Ina ƙoƙarin sauka akan gadon Gogode tayi saurin zuwa tamayar dani ta kwantar tana faɗin "Ina zakije kuma?" hawaye nafarayi sannan nace "zanje gurin Baba ne incigaba dayimasa addu'a. koya samu lafiya ne?" Naqarashe maganar cikeda hope Ina kallon Gogode anma hawayen dana gani idanunta irinna Yadikko Rahane yasa gwiwata tasage,nasake fara kokarin sauka daga kan gadon ina faɗin "Gogode kikaini gurin Baba,Gogode kikaini inyi masa addu'a, Gogode kikaini gurinsa inzauna kusa dashi don Allah" hakuri tadinga bani anma naqi sararawa hardai Kawu Sani da Yaya Salim suka shigo ɗakin.
Ina ganinsu suma nafara rokonsu Ina kuka nace "Yaya Salim Ina Baba?don Allah kakaini gurin Baba" namatsa daga jikin Gogode nakarasa bakin gadon ina kuka nariƙo hannun Yaya Salim ina kuka tareda marairaice murya nace "kana yiwa Baba addu'a kaima?" seyakasa amsamin yajani zuwa jikinshi yakwantar dani akan kafaɗunshi yana comforting ɗina yace "it's okay Rukayya. Stop crying pleaseee" amma senaki daina kukan,nadago Ina kallon Kawu Sani kamar wata tababbiya nace "Kawu Sani Yaya Salim ma yarone ko? Kuma inyama Baba addu'a Allah zaikarbakoh?" Kawu Sani yace "insha Allah nakowa ma Allah zaikarba Rukayya" folding hannuna nayi alamar roko Ina kallonshi nace "tokuma kuna saka shi a addu'a don Allah. kawu karoki su Yaya Salim su Yaya Rabi'u, Yaya Fahad,su Yaya Zaheera dasu Yaya kaltum duk suna sashi a addu'a kilan yasamu sauki anjima ko gobe"
Gyaɗa kai Kawu Sani yayi yana shafa kaina yace "it's okay zan faɗa musu. Just stop crying kinji?" sa hannuna nayi nashiga share hawayena dukda kuwa haryanzu wasu suna bin wasu nace "nadaina. Sallahma zanje incigaba dayi inyi masa addu'a" nakarashe magana Ina kokarin sake tashi daga kan gadon.
Cikin sauri Yaya Salim yariƙo ni yamayar dani yazaunar tareda sake kwantar dani jikinsa,Kawu Sani zama yayi gefena yakama hannuna yana min massage ahankali ayayinda Yaya Salim yafara magana yace
"Allah zai karbi addu'an ki insha Allahu Rukayya,kuma badole se a tsaye ake addu'a ba ko akwance mutum zaiyi kuma insha Allahu Allah zaikarba indai da tsarkakkar niya akayishi,baki ganin condition ɗinki ne? you're very sick sabida irin tsayuwar dakikayi yau. towai inkika fara rashin lafiya irinna Uncle Umar tayaya zakiyi masa addu'ar? koshi Uncle ɗin an faɗa miki zaiji daɗi inyaji kinfara ciwo sabida shi? get hold of yourself my Dearest Sis,pray for him yanda yakamata. Stressing yourself isn't a solution. you're just making the matter even worst than before. Rukayya you've to take very good care of yourself if not for your self then for Uncle Umar kinajina?" Jijjiga masakai nayi ahankali still ina hawaye sannan nace "toh ina Baba Yaya Salim? kukaini gurinshi" wannan karan Kawu Sani ne yace "liedown first,kwanta kihuta Rukayya. za'akaiki daga baya kiganshi" Ina hawaye nace "Toh yaushe zaka kaini gunshi Kawu Sani?" Kawu Sani yace "inkika kwantar da hankalinki kika samu lafiya dawuri aka sallameki" lumshe idanuna nayi hawaye nazuba kamar famfo hakanan duk addu'ar datazo bakina yinakeyi, inayi inahadawa da "Ya Allah kabama Baba lafiya,ya Allah kaji tausayina banida kamarsa" har nannauyar bacci yayi awun gaba dani.
Washegari darana akayi discharging ɗina kuma babu wanda ya ziyarceni a dangin mahaifina face *Kawu Sani* da
*Yaya Salim* anma ni duk wannan baidameni ba sabida basune agabana ba wannan lokacin. Wani guri daban da inda naga Baba jiya su kawu Sani suka kaini naga Baba kuma ɗakin na single patient ne(VIP) bakamar wancan da8kin dake daukeda marasa lafiya sunfi talatinba. ɗakine mekyau harda Ac,Tv,fridge dadai sauran kayan bukatu dasuka zamana necessary ayi amfani dasu a day to day life activities ɗinmu. yanzuma Baba baiyimin magana ba kuma still Kawu Hassan ke jinyarsa danshi kaɗai mukasamu a ɗakin,karasawa nayi gaban gadon nazauna ina kallonshi hawaye nabin kuncina,motsin hannunshi danaji akusa da cinyoyina ne yasani kallon hannun nashi,Ina kuka nasa hannu nakamo nashi hannun nasaka cikin nasa ina faɗin "Sannu Baba" damamakina Sena ga ya lumshe min idanu ayayinda ya matse hannuna cikin nashi. wani irin feeling naji,the feeling of belongingness, feeling irin wanda ke kara tabbatarmin cewa Yes. This's my Father and he's the most lovable and the important person in my life.
Gogode ma zuwa tayi tamasa yajiki inda yalumshe mata idanu tareda sakin murmushin karfin hali kamar yanda yamin. Gogede tace "Allah yabaka lafiya Umaru, Allah yasa garkuwan jikine" duka Ƴan ɗakin suka amsa da Amin daganan kuma yarufe idanu wani nannsuyar bacci yayi awun gaba dashi. Kawu Sani dake tsaye harlokacin yadubi Kawu Hassan yace "Adamu da Yaya idriss sunzo da safennan ne?" Kawu Hassan yace "Eh sunzo basujima ba suka wuce kasuwa shago" Kawu Sani da mamaki yace "basumaka maganar test ɗinda akace ayiba?" Kawu Hassan yajijiga kai alamar a'a sannan yace "basuyimin ba gaskiya. Yaya idrissa dai yakawo magungunan da likitan yarubuta shekaranjiya" Kawu Sani yace "yau yakawo maganin?" gyaɗa kai kawu Hassan yayi. cikeda mamaki Kawu Sani yace "Kuma kace tun shekaranjiya aka rubuta drugs ɗin?" nanma Kawu Hassan yagyada kai alamar "eh".
Daganan Kawu Sani besake cewa komai game dasuba sema tambayar cards ɗinda likitocin suka bama Kawu Hassan dayayi. nan Kawu Hassan yaɗauko duka yabashi,atake Kawu Sani yashiga dubawa yaɗauki wanda zai ɗauka ya mayarmai da sauran yace "this card has been with you guys for almost a week now but no body cares to do what was instructed in the card" Hassan dabai gane me kawu Sani ke faɗa ba anmadai yasan faɗa akan cards ɗin yakeyi kuma bazai wuce narashin siyo maganin dawuri bane yasashi cewa "Yaya ni likitan na bani takardunnan na danka ma Yaya idrissa tun adaren ranar daganan shima baice komai ba,nasandai kullum in likitoci sunzo sukan tambayi sakamakon gwaji kuma insunzo nakan sanardasu baswa cewa komai. Shekaran jiya da likitan yazo yaga jikin Yaya Umar ɗin yayi tsanani shine yarubuta magungunar nan yace asaya na ulcer da typhoid ɗinda suka tabbatar yana dashi ne kwanaki kafin musamu muyi test ɗinda sukace ayi dan tabattar da ɗayan cutar da ake tunanin yana dashi. Kuma su Yaya idrissa nazuwa naɗauki katin nabasu wanda seyau dasafen nan suka kawo maganin" tsaki Kawu Sani yayi sannan yafice a ɗakin inda Yaya Salim yabishi abaya.
Faɗa Kawu Sani yadingayi bayan fitarsu da Yaya Salim yace "people are so heartless wallahi. Ɗan uwanka ma bazaka tsaya kabashi time ɗinda yakamataba adede lokacin daya fi bukatarka for goodness sake? Everyone is just so selfish. People nowadays value money more than relationships. Bana gari Umar yafara rashin lafiyarnan Salim,I was in Lagos idriss yaƙirani yake faɗamin anyi admitting ɗinsa a asibiti. Atake nace masa acikinsu wani yazauna dashi,koshi ko Adamu kafin indawo kokuma anemi wani babba daga Giyaɗe yazo inma su bazasu zauna ba dan banma yi maganar kuba sabida nasan abunda Babba zai iya ba lallai ku ku iya ba but to my very own surprise jiya ina dawowa da mukazo na tadda Hassan ne zaune gunshi,shiyake jinyar Umar fisabilillahi. me Hassan yasani banda kwaba? bagwanda kubama akanshi dukda yagirmeku amma ai kukunfishi wayewa. tundaga expression ɗin likitan dakuma yanda yake mayar min da magana jiya bayan naje amayar dashi side room(VIP) nagane something is fishy,I asked about the health and his answer was anbamu test muje muyi munkiyi fiyeda sati me mukeso yayi mana?
Hakuri nabashi kancewa za'ayi ajiyan insha Allahu. fitowana daga gunsa nasamoka adakin da aka kwantar da Rukayya daniyar innasake dubata zankoma can ɗakin inkarbi card ɗin test ɗin inkai lab suzo suɗauki sample suyi Auntyn ku takirani wai *IYA* taƙi tasha drugs ɗin ta kuma kafafunta nadamunta shine natafi gida bayan naƙira Adam nafaɗa masa dalilaina nace atake yazo yaje yakai lab ɗin but it turns out baizoba tunda gashi haryazo