Showing 75001 words to 78000 words out of 213309 words

Chapter 26 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5871

sunce gaida me gaisheka and besides Shi Yaya Fahad ɗin wata magana ta taɓa shiga tsakanina dashine dazaiyi tsanmanin gaisuwa daga gareni? kokuma haryau yayimin gaisuwar rashin mahaifina? Yes yana da kirki kuma yana ɗaya daga cikin mutanen dabazan manta playing important role dasukayi acikin zamanmu na asibitin nan ba but one thing is for sure,komi yayi min nida Baba yayine under instructions ɗin Kawu Sani,biyayya yayima mahaifinsa bawai don yanason yibane ba. Wanda zance ya jajirce tsakanin sa da Allah yayimin abubuwa toh Yaya Salim ne,alokacin dayake gida hakanan zataho asibiti dan karan kanshi yazo yaduba Baba yayita kuma comforting ɗina anma Yaya Fahad kam sede in turo shi akayi kokuma in tare sukazo da Kawu Sani and moreover for once he never sympathize with me. Sabida haka tsakanin sa da Yaya Salim akwai huge difference.
Tunanin dana dingayi kenan ahanyar mu tazuwa gidan Kawu idrissa da Kawu Adamu hakanan inajin Yaya Salim nata zuba surutu shikadai amotar wanda gogan naku daga yayi murmushi se ya jinjina kai baka taɓa Jin muryarsa and I'm very sure Yaya Salim besan da existence dina a motarba danda yasani da dani za'ayi hiran tunda sarai yasan halin Yayan nasa.
Akofan gate ɗin gidansu Kawu idrissa Yaya Fahad yayi parking wanda hakan yasamin tsananin bugun zuciya hakanan inajin Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad ɗin mesukazo yi agidan.

Ahankali Yaya Fahad yace "we're here to drop Rukayya" ayayinda yake ƙoƙarin buɗe murfin motarsa not minding how Salim ɗin will react akan maganar tasa.

Cikeda mamaki Yaya Salim yace "wace Rukayya?" Ina gani yanuna masa bayan motar atakaice wanda hakan yasashi saurin juyowa yana kallona,cikeda mamaki yace "Rukayya daman kina cikin motar nan?" gyaɗa masa kai nayi ahankali ayayinda hawaye suka taru cikin idanuna sannan nace "Eh. Ina wuni Yaya Salim" Yaya Salim cikeda tausayina yace "Lafiya Lau Rukayya. Ya hakuri?" kasa amsamai nayi,se hawaye hakanan inajin mutuwar Baban nadawomin sabuwa azuci gakuma tunanin zaman dazanyi agidan Kawu idrissa. Shikanshi Yaya Salim ɗin nasan yayi regretting ta'aziyar dayayi min ɗin because daga ganin yanayin fuskarshi nagane hakan. Sekawai naga yabuɗe kofar motar yafita yazo yabuɗe kofar side ɗinda nake zaunen yakamo hannuna yafito dani sannan yatsuguna a gabana yashiga gogemin kwallana cikin sanyi yace "why are you crying? kukan na menene kuma yau Rukayya?" cikin gunjin kuka nace "Babaaaa..." jiki sanyaye Yaya Salim yace "kwanaki bana hanaki yimasa kuka ba? Kokin manta nace miki addu'a zakinayi masa?" Girgiza masakai nayi alamar "a'a" banmanta ba sannan nace "toh ai yanzu mutuwa yayi! yatafi yabarni,yatafi inda bazan sake ganin saba Yaya salim" dukyanda Yaya Salim yakai ga daurewa seda idanunshi suka cika da kwallah.

Dakyar yayi Mastering courage yace "Nasani Rukayya! I know he's gone,nasan yatafi yabarki,yatafi yabarmu duka a Inda muma bazama dauwamma anan ɗinba,dole wataran muma zamu bishi. Anma kokinsan ba'ason yima mamaci kuka? Anma ko kinsan babu addu'ar datakai na iyaye ga Ƴaƴan su hakanan babu wanda yakai na Ƴaƴa ga iyayensu?" Yaɗan numfasa sannan yace "Wa Uncle Umar yake dashi bayan Baffa Mallam dayake mahaifinshi inba keba? Inbakiyi masa addu'a ba wazai yi mishi? barema keda kikeda kankantar shekarunki. You're very innocent, Allah Yana karban addu'an yara kanana cikin gaggawa ko bakison ki haɗu da Uncle a aljanna?"

Cikin sauri nace "inaso Yaya Salim" Yaya Salim yacigaba da gogemin kwallana yana faɗin "then karki sakeyi ma Uncle Umar kuka,gata ɗaya zakiyi mashi shine kiyi masa addu'a aduk sanda kika tuna dashi,kikumayi fatan Allah yahadaku a gidan aljanna"

Wannan Karan Nima saka hannayena nayi a idanuna Ina tayashi gogemin hawayena dukda kuwa acikin zuciyata bandaina kukan ba,seda ya tabbatar nagyara fuskana nadaina kukan sannan yatashi tsaye yakama hannuna muka shiga cikin gidan wanda alokacin tuni Yaya Fahad yariga mu shigewa cikin gidan.

Akofar Kawu idrissa muka sameshi,yana zaune cikin main parlour ɗinsu shikaɗai gakuma ruwa da aka kawomai akan tray aka ajiye ayayinda akwatunan kayana ke ajiye agefe. Tunda muka shigo parlourn hannun mu dake sarke dana juna kawai yakalla ya ɗauke kanshi wanda inaganin hakan ne yasa Yaya Salim sakin hannunawa sannan yanunamin kujera yace inzauna sannan yaje ɗayan kujerar yazauna shima.

Munfi mintuna biyar azaune cikin parlourn kafin mukaji anbude kofar ɗakin dake sashin gabar acikin parlourn wanda inada tabbacin ɗakin Maman Rabi'u ne and then my heart starts beating so fast tunma kafin in kalleta hakanan jikina yashiga rawa lokaci guda.
Aikuwa itanne tafito muna haɗa idanu ta watsamin wani uwar hararar dasaida nayi regretting kallon direction ɗin da take hakanan kan in akara naji ta dirar min wani uban tsawan da harsu Yaya Fahad seda suka tsorata.

Tace "Keee!!!!!" Dole seda na Kuma kallonta tsabar irin firgitani da tsawan nata yayi dukda kuwa har raina banso sake kallon nataba.

Tace "don Ubanki kujerar ubankine zaki wani hau kizauna min datsatsaman jiki? Kokuma Ubanki ne yake biyamin masu gogemin kujerun da gyaramin parlourn? Kuma wani gulman nema yazaunar dake kan kujerana yau bayan kinsan tunbayau ba na haneki dayin hakan inkikazomin gida?"

Nidai kasa cewa komai nayi inbanda zamewa danayi daga kan kujerar inakokarin zama akasa takuma sakarmin wata tsawar tace "Ai kasan ma banbaki izinin zama ba!fita zakiyi kibar parlourn kijirasu awaje tunda babu sa'anki anan gurin" gyada matakaina nayi cikin sauri kafin nafice a parlourn jikina na rawa.
Littafin Qadr na kudine. Duk maison shiga paid group ya tuntubi wannan layin *08147722806*

*Page Twenty Six*

Rukayya nafita a parlourn Maman Rabi'u takaraso cikin parlourn tasamu ɗaya daga cikin kujerun parlourn tazauna sannan tadubi su Salim da gaba ɗaya yanayinsu yagama nuna ransu a bace yake da abunda tayima Rukayyan. Anma se hakan baidametaba danko su ɗinma she's ready to hurt them indai akan batun Rukayya tazauna agidannan ne toh Babu wanda bazata iya bata ma raiba.

Salim ne kaɗai ya iya yagaida ta fuska ɗauke da ɗan fara'a dukda kuwa ransa a matukar bace yake inda Fahad kuwa ko kallon inda take yagaidata amma sebata amsaba,shima kuma sebe damuba dankuwa inda sabo yasaba darashin amsa gaisuwartasa. danne danne yakoma yi cikin wayar sa pretending as if bemasan abunda yake faruwa a parlourn ba anma dazaka buɗe zuciyarsa kagani kokuma ka kalli fuskarsa closely dole zaka gane ransa a matukar bace yake.

Maman Rabi'u ko kaɗan batayi danasanin rashin amsa gaisuwar Fahad daba tayiba hasalima baya gabanta kamar yanda mahaifiyarsa bata gabanta. Koda can dasuke zaune gida ɗaya daman Ummi ce mutumiyarta dayake halinsu yazo ɗaya. Kwata kwata baswa jituwa da Aunty dukda kuwa she was the first wife. Ita tafara sani kafin Ummi anma dayake da'ita tayi kishin balbalinta shiyasa nasu baizo ɗaya ba,acewarta Aunty macece me shegen girman kai danuna tafi kowa shiyasa basu taɓa shiriba take kuma jin haushinta shiyasa Ummi nashigowa gidan tayi sauri suka haɗe kai suka zama kawaye suna harkokinsu tare suka juyama Auntyn baya.

Amsa gaisuwar Salim Maman Rabi'u tayi Jin yagaidata sannan ta tambayesa lafiyan kannensa sa da Umminsa inda yace duk lafiya Lau suke kafin kuma parlourn yaɗan ɗauki shiru nawasu daƙiƙu.

Salim Jin shirun yayi yawa gashi Allah Allah yake ya'isa gida sabida gajiyar daya kwaso a hanya dakuma dokin ganin iyayensa da su Zunnurain yasashi fara yunkurin tashi tsaye yana cewa "toh Aunty. Muzamu wuce gida,daman munkawo Rukayya ne" Maman Rabi'u zabura tayi kamarma tunda can batasan da zancen kawo Rukayya gidan ba.

Tace "wace Rukayyan? kuma awani gidan zata zauna?" Salim komawa yayi yazauna Jin abunda Maman Rabi'u tace cikeda mamankin ta,yes yaji haushin abunda tayi yanzu sannan yasan Rukayya ba ƙaramin wahala zatasha ba inzata zauna agidan anma bai taɓa tsanmanin Maman Rabi'u zatayi questioning ɗinsa akan hukuncin iyayen nasuba,atunaninsa tariga da takwana da sanin hakan anma Jin abunda tace yasashi cewa "Su Abba ne suka yanke shawarar tazauna anan" dankuwa dukda Fahad befito yafaɗa masa ba hakanan besan yasukayiba, he's very sure wannan ɗin decision ɗin iyayensune.

Maman Rabi'u tace "Cabdi jam! Toh nidai bansan da zancennan ba kuma Baban Rabi'u besanar dani ba inaganindai mahaifinka ne ya yanke shawarar sa shikaɗai shiyasa yace akawota nan" ahankali Salim yace "inaganin hakanne toh" Fahad dake zaune gefe yanajinsu tundazu yadago kansa yadubi both Salim da Maman Rabi'un sannan yace "it was not his decision. dukansu suka yanke shawarar Rukayya tazauna agidannan and even Kawu idrissa knows about it. Infact he was suppose to pick her up from her home rashin zuwansa ne yasa su Gwaggo Suwaiba sukace inkawotanan bayan na ajiyesu a tasha"

Maman Rabi'u data zubama Fahad idanu tun sanda yafara magana tanajin kaman taje tarufeshi da duka tace "komadai yasukayi can musu,atsakaninsu nidai babu ruwana tunda maigidana baisanar daniba sannan inbanda rashin adalci da rashin tausayi yakamata ace Rukayya tazauna agidannan nema? muma yaushe muka gama jida kanmu da namu ƴaƴan dahar za'ace za'akaro mana wani nauyin? Toh nidai ba'a gidanaba,kujecan kunema mata wani matsugunin anma banan ba. Shiɗinma inaga kawai kawaici yayi ma iyayen naku da akace yaɗauketa amatsayinshi na Babba anma ai Inza'a duba matsayi da status dakuma capability na mutum mahaifinnakune yakamata yariƙe Rukayya ba Baban Rabi'u ba,inkuma yaga shima bazai iyaba seya maida ta Giyaɗe wurin kakanninta ba shikenan ba? Anma se azo ace za'a ɗaurama wasu wahalanta bayan ubanta dayake raye babu wanda yataimaka ma inbanda kanshi da Ƴar sa daya sani"

Har Maman Rabi'u ta rufe baki idanun Fahad nakanta,girgiza Kai yayi in desbelief sannan yatashi tsaye yadubi bangaren da Salim yake zaune sannan yace "Salim let's go" Salim cikeda mamaki yace "let's go kuma? Toh a Ina zamubar Rukayyan bayan ba'a ƙira Kawu idrissa yamata confirming cewa anan gidan Rukayyan zata zaunan ba?" Fahad boldly yakumacewa "I said let's go" sannan yajuya yanufi inda kayan Rukayya yake ajiye yaɗauki wanda zai iya yabar sauran. Salim ganin abunda Yayan nashi yayi yasa yama Maman Rabi'u sallama ya ƙarasa yaɗauki sauran kayan yabi bayan Fahad yanajin Maman Rabi'u na faɗin "Allah yaraka taki gona"

Awaje yasamu Rukayya zaune jikin bango tanata shesshekar kuka tacusa kanta cikin cinyoyinta da alama ma batasan har Fahad yazo yawuce ba. Ajiye kayan hannunsa yayi sannan yakarasa inda take tsugune yashiga kiran sunanta.

Jin Ƙiran sunana da Yaya Salim yayi yasani ɗago dakaina na dubesa,ahankali yace "tashi mutafi Rukayya" banyi mamakin kalamansa ba dankuwa duk maganganun da Maman Rabi'u tayi aciki najisu karap acikin kunnena dakuma sanda Yaya Fahad yacema Yaya Salim yazo su tafi but I never thought tafiyar dani za'ayi seda yayi magana yanzu dukda kuwa naji Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad ɗin,atunanina tafiya zasuyi subarni inyaso su Maman Rabi'un susan yanda zasuyi dani itada Kawu idrissan inya dawo anma senaga sabanin hakan da Yaya Salim ɗin yace intashi mutafi.

Tashi nayi jiki sanyaye nabi bayansa Ina tunanin ko Ina zasu kaini dasukace mubar gidan Kawu idrissan?

Seda muka Shiga mota muka hau kan titi naji Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad inda zamuje.

Atakaice Yaya Fahad yace masa "we're going home" Yaya Salim yace "you mean she'll stay there with us?" Yaya Fahad yace "I don't know Salim. Wannan decision ɗinkuma Abba ne zeyanke shi" Yaya Salim sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "toh Allah yazabi abunda yafi alkhairi" sannan yakarada "anma banji daɗin abunda Aunty tayi  ba gaskiya. Aiko Uncle idrissa bece za'akawo Rukayya tazauna agidanan ba aibaikamata tayi mana abunda tamana ɗazunnan ba. I was very hurt by what she said ganin girmanta kawai yasa nadanne ɓacin raina ban tanka mataba" shidai Yaya Fahad bece komaiba haka Yaya Salim yadinga korafin abubuwan da Maman Rabi'un tayi harmuka Isa gidansu.

Nidai ko kaɗan banyi murnan canjin da akasamu ba tunda har lokacin ba'agama yanke decision ɗin inda zanzaunaba,sun ɗauko ni sunkawoni gidansu ne sabida anki karbana awancan gidan Kuma nan ɗinma babu mamaki aki karban nawa tunda daga nan ɗin harcan ɗin babu wani banbanci.

Yaya Salim da Yaya Fahad ne suka shigarmin da kayana cikin gidan inda suka ajiyeshi a main parlour wnda inada tabbacin rashin sanin sashin dazasu kaini ne yasa kowannensu ajiye kayan anan parlourn. Inaganin kowannensu yanufi kofar mahaifiyarsa inda aka barni tsaye nan parlourn kamar wata gunki. Nafi mintuna biyar zaune a parlourn banga wulgawan kowaba. Yes yaune zuwana na biyu gidan anma a zuwa biyun danayi gidannan nalura cewa wannan main parlourn ba gurin zaman ahalin gidan baneba,baswa zama kwata kwata kowa sede yazauna a kofarsa tareda Ƴaƴansa. Jinayi an buɗe kofa daga sashin arewa wanda hakan yasani kallon gurin. Yaya Siyama ce tafito  fuuuuu kamar an hankadota,sewani cika take tana batsewa ahakadai tawuce tanufi wata kofa dazata sadaka dacan bayan gidan inda Kitchen ɗinsu yake da alamadai wani aikin akasata ranta bayaso shine tafito cikin sauri rai abace. Wucewarta badajimawa ba sega Sadiya kuma tafito Itama ta kofar tasu anma memakon naga tabi bayan Yaya Siyaman senaga tanufo inda nake zaune.

Ɗauke kaina nayi daga gareta sanin halinta sarai yayinda araina nake tunanin mekuma zatace min? Yau Sadiya ne hartake kusantar inda nake?eh lallai za'ayi ruwa da kankara yau. Sede tunma kafin ingama aune aunen danakeyi araina naji ansake buɗe wannan kofar still and then I look at that direction.

Yaya Fahad ne yafito wannan karan kuma nalura tunda Sadiya taji yabude kofar parlourn Aunty naga tayi sauri takaraso inda kayana suke tashiga kinkiman akwati sabanin ɗazu da dakyar take tafiyama wanda hakan yabani mamaki ba kaɗan ba anma seban ce komaiba.

Ban ƙara cika da mamaki ba seda naji Sadiya na ƙiran sunana tana faɗin "intashi mushiga ciki" dafari tsayawa nayi baki galala Ina kallonta harsaida tasakeyimin magana akaro na biyu sannan narufe bakina natashi nabi bayanta bayan na ɗauki sauran kayana dake ajiye nan parlourn wanda alokacinne kuma naga fitan Yaya Fahad daga main parlour ɗin hannunsa riƙe da bottle water wanda fitowarsa parlourn ne yaɗauka a wani fridge dakenan cikin parlourn.

Koda muka shiga parlourn su Ba
babu kowa acikinsa inbanda TV daketa aiki shikaɗai, ɗakin da tashiga nashiga nima,a tsakiyar ɗakin naga ta ajiyemin akwatina tareda sakin tsaki sannan tazube kan gado tana nishin gajiya da alamadai nauyin akwatina ne yagajiyar da'ita haryasata behaving this way. Rashin sanin abunyi yasa nasamu kasan carpet ɗin daga jikin gini nazauna ayayinda natakure kaina guri ɗaya ina karema akwatina dake tsakiyar ɗakin kallo.

Munanan zaune shiru babu wanda yacema ɗan uwansa cikanka har aka ƙira sallan la'asar. Ina gani Sadiya tatashi tashiga bathroom ɗinsu dake cikin dakin ta dauro alwala tazo tatada sallah sannan nima nashiga bayin nayi alwala nafito na jonata. Na sallame sallar kenan ina addu'a Yaya Siyama tashigo ɗakin. Turuuusss tatsaya abakin kofar ɗakin tana karema kayana dake tsakiyan ɗakin kallo kafin tadubi bangaren danake zaune kan carpet Ina addu'a sannan tamaida kanta kan Sadiya da ayanzu takoma kan katifa tayi kwanciyarta tace "meye nake gani haka a tsakiyar ɗakin nan?"

Sadiya tace "Uhmmm kayan Rukayya ne mana" Siyama akafule wannan karan tace "bangane kayan Rukayya ba? mekayan ta yakeyi a ɗakin mu kuma inbanda neman a kazanta ma mutane ɗaki yayi ta tsami". Ta harari Sadiya sannan taci gaba da magana,tace "Wai wani gwanin ne yashigo da kayanma tukun?" Sadiya tashi tayi daga kwancen datake ayanzu tazauna a tsakiyar gadon sannan tace "Nina shigo dawasu Itama tashigo dawasu kuma Yaya Fahad ne yace in ɗauko mata kayanta daga main parlour inkawo su ɗaki sannan ince mata tashigo nan tazauna"

Tabbas kalaman Sadiya yabani mamaki because ko a wildest dream ɗina bantaba tsammannin Yaya Fahad could say something like this ba. Kai bama ani kaɗai ba,ama kowa ban taɓa tunanin zai damu da al'amarin wani haryasaka baki yayi magana irin haka ba anma seban nuna tsananin mamakina ba sabida wutar dake gabana ma ta'isa tahanani yin wannan tunanin.
Sadiya nagama jawabinta Yaya Siyama tace "lallai kam. Toh wallahi badai adakinnan ba. Ɗakinsa ne koshi zaizauna mana da'ita dazai wani ce ashigo da kayanta,intaimako yakeson yimata meyasa be ɗauketa yakaita ɗakinsa ba? dandai besan kazantar yarinyar nan baneba shiyasa ya faɗi haka"

Sannan tadubeni fuska ɗaure tace "kima tattara kayanki kinemi inda dare yamiki dannidai bazan zauna ɗaki ɗaya dakeba Allah yagani hakanan kuma bazan iya tafiya inbar miki ɗakin ba" daganan tayi shigewarta bathroom tana kunkuni da mitar akan hukuncin da Yaya Fahad ɗin ya yanke.

Share hawayena nayi da bayan hannuna sannan natashi daga kan carpet ɗinda nake zaune. Nakarasa inda akwatina yake naɗaukeshi na fidda daga ɗakin,nakoma naɗauko sauran kayanma nafitar dasu yazamantoh yanzu suna ainahin parlourn Aunty,ma'ana parlourn bangaren su Yaya Siyaman. Najima tsaye kusa da kayan nawa batareda nikaina nasan yazanyi dasuba hakanan harlokacin banji motsin wani ko wurgawan wani a parlourn nataba wanda hakan yasani fara tunanin ko Ina Aunty da *Safiya*( yayar Sadiya,itake bin bayan Siyama) sukaje. Inanan tsaye har Yaya Siyama tafito daga ɗakinsu zata fita waje taganni.

Rai bace "auuuuu baki fitar da kayan ba?" kamar zanyi kuka nace "inazankaisu?" dankuwa harga Allah nikaina bansan inda zankai kayan ba shiyasa natsaya agurin,rashin mafita ne yasani tsaye gurin kamar wata dogara sannan aikoda tace infidda kayan ai a ɗakinsu ne tace batason ganina da kayan nawa bawai a sauran guraren gidan ba shiyasa nayi mata wannan tambayar anma sena ga ranta yakuma ɓaci,a hassale tace "bansani ba. Kidurasu a hanci na tunda ke dakikiyace" daganan tayi ficewarta a parlourn tabarni tsaye.

This time I couldn't resist my tears,kobata sake faɗa min ba nasan bakar magana tafaɗa min and she mean I should take my things out daga sashinsu baki ɗaya shiyasa kawai nashiga ɗiban kayan nawa nadinga fitar dasu harna dawo dasu ainahin main parlour. wani wawan ajiyan zuciya nasauke sakamakon gajiyar danaji nayi sabida jigilar kayana danayi tayi hakanan so nake inzauna inhuta anma se wata zuciyar tashiga rayamin "dakika bar kayan naki anan tsakiyar parlourn bakya tunanin nan ɗinma ana iya cewa kizo kikwashe su? bagwanda kifitar dasu gaba ɗaya kihuta ba" dawannan tunanin nakuma kinkimar kayan nawa nanufi backdoor ɗinda naga Yaya Siyama tabi ɗazu dankuwa shine kaɗai hanyar danake tunanin zanbi safely da kayana batareda wani yayi min korafin na ajiye masa a kofar Saba.

Kusa da kofar fita backdoor ɗin nahangi wata yar kusurwa acikin parlourn kuma an lullube gurin da labule wanda hakan yasani ƙarasawa gurin dasauri naɗaga labule senaga babu komai agurin. Hamdala nayi cikin raina sannan nasaka duka kayana agurin namaida labulen narufe ina addu'ar Allah yasa kada wani
yagani yace indaukesu sannan nakoma can cikin parlourn nazauna kasan carpet natakure kaina guri ɗaya Ina mamakin miye dalilin dayasa banji duriyarsu Yaya Zaheeera da Yaya Aisha ba tunda nazo ni gidan.

***
Tunda motarsu Lamiɗo yabaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login