Showing 174001 words to 177000 words out of 213309 words
take fushi da'ita itama.
Setace "Daman tambayarki zanyi Koh Yaya lamido yadawo? Inata Kiran layinshi baya picking" Jidda atakaice tace "Yadawo" Maimunatu tace "toshikenan thank you kilan yana bacci ne shiyasa baiyi picking ba" Jidda tace "may be" sekuma Maimunatu tayi mata sallama ganin bata samu fuskar dama zata iya neman taimakon tahada ta dashi tawayaba...
Jidda tsuka tasaki bayan sungama wayar sannan tayi wulli da wayar tana fadin "wallahi Yaya Basma dandai kince inyimata shiru ne dasaina amayar mata dana cikina yau" Basma tace "kidaiyi hakuri shida akama abun yadau mataki. Yanzu seke kidau zafi shibai daukaba yamaje susha soyayyarsu kisha kunya" Jidda wani kallo tama Basma sannan tace "Cabdi.... Yaya Lamidon? Wallahi ninasan yagama da Aunty Maimunatu kenan har abada. Kokin manta shi mutum ne dayatsani karya,yatsani aboye masa abu no matter how little it's barekuma maganar aure da bana wasa ba" jinjinakai Basma tayi cikeda gamsuwa sannan tace "Hakane Kuma. Allah dai yasa yakyaletan" Jidda tace "Amin. Aiko bai kyaleta ba mu zamu zugashi" dariya Basma tasaki sannan tace "kintashi a Team Maimunatu kenan" Jidda yar dariyar tasaki sannan tace "Daman can dinma kaddara ne yabarni acan"...
Girgizakai Basma tashigayi in desbelief tana fadin "Bakida dama wallahi Jidda".
Haka Maimunatu tacigaba da kiran Lamido babu kakkautawa ganin batada wani mafita daya wuce wannan,Lamido dafari yayi niyar shareta ne kawai harta gaji takyaleshi anma ganin taki barin kiran nashi yasa yagane baza fa takyaleshin ba inba nuna mata yayi yasan komaiba and moreover shiba ita baneba,he can't just be out of her life without unspoken words,bayason yayi holding grudge,abunda akayi zaifito yafada baiji dadinsaba.
Danhaka dakanshi seya kirata da dare,ko ringing din farko begama ba tadaga call din kamar wanda daman jiran kiran nasa takeyi.
Hankali tashe tace "Wai Ina ka shigane Yaya lamido? I've been trying to call you baka picking" batareda ya amsa tambayarta ba yace "Are you home?" jiki sanyaye tace "Eh" yace "Then I'm coming tonight. Akwai maganar dazamuyi" daganan baijira cewartaba ya katse call din ya wullar da'ita agefe.....
Ana idar da sallar isha'i ya yada zango akofar gidansu Maimunatu. yaukam agaban gidansu ma yatsaya bakamar da datakece mishi suje bayan layinsu ba sabida kada agansu agida ayimata fada ace tacika fita hira,shigabadaya seyau ma yagane ashe hakan datakeyi din dukdan kada ayi mata fada agidane tana kula wani bayan anbada ita kokuma dan kada wani yaganshi yafesa masa labarin daga baya. Shi kwata kwata be taba fassara abunba dayake tun farkon fara soyayyar tasu haka sukeyi wanda adadin sunayin hakan ne sabida sunyi kankanta alokacin anma yanzu fah? Shibai taba tambayar kansa miyasa basu canza dabi'a ba bayan shekaru sunja kuma yanzu lokacin sune seyau daya tsinci kansa a kofar gidan nasu komai yake dawo masa cikin kwanyarsa yana bashi explanation dede da tambayar sa. Da hijabi tafito as usual kamar kullum hakanan tadanyi simple makeup daya kayata fuskarta,Maimunatu kyakyawar budurwace da babu abunda tarasa a irin suffoffin da akeson mace maikyau ta kasance tanada shi. Bakaramin mamakin ganinshi a kofar gidan tayiba danyawanci inyazo can yake wucewa direct itakuma taje can tasameshi.
Ahankali takarasa inda yake tsaye tace "Ina wuni Yaya lamido?" Lamido yace "lafiya Lau" Maimunatu setadanyi murmushi tace "yau yanaga katsaya anan? Ko kewana kakeyi dayawa dabazaka iya jira har in isoba?" tayi maganar cikin sigar tsokana dukda kuwa tasan ba lokacin tsokanar bane yanzu.
Murmushin yake Lamido yasaki sannan yace "A'a kodaya. nanma ya Isa,yau anan nakeson muyi hirar" nervously Maimunatu tace "Kaman ta dalilin mu na rashin tsayuwa ananne wai?" dankuwa Allah yagani tsoro takeji wani agidansu yazo yaganta taredashi,barinma *Yaya khalipha(mijin dazata aura,cousin Brother dinta)* da takeda tabbacin yana iya zuwa kowani lokaci daga yanzu tunda yana gari. Lamido yace "Ganinayi mungirma,shekaru sunja so our relationship should be uplifted too. We can't keep going like this,doledai inson juna muke tsakani da Allah iyaye ma susan da alakar mu" take se jikin Maimunatun yafara trembling...
Duk kuma Lamidon na lura da yanayinta,yace "koya kika gani?" ahankali Maimunatu tace "Ina ganin kabari seka samu aiki kafara zama stable tukunnan mufara kai wannan gandun" wannan karan murmushin takaici Lamido yasaki,wato bazata fito tafada masa gaskiya ba, she'd rather continue giving him false hope? She'd rathe continue lying to him and leave him heartbroken in the end" Araunane yace "Atunanina badole sai ansamu aiki akefara neman aureba Maimunatu and besides baturowa gidan ku zanyiba,adai dinga ganina asan da zamana yana da amfani wanda wannan dinne kadai zai nuna seriousness dina akanki yazamanto bawai yaudaran juna kawai mukeyiba" Yadan numfasa sannan yace "Nibanga amfani kin barina Ina zuwa kofar gidanku hiraba ayanda nike yanzunnan tunda son tsakani da Allah mukewa junan mu. Sede indama can ba aurena ke kikeson yiba,sede indama can kinada wanda kikeso kunyi alkawarin aure dashine" Lamido yayi maganar cikin tune dinda ke nuna karaya.
wannan ran Maimunatu kuka tafashe da,kukan da itakanta tarasa na farin cikine kona bakin ciki,wai yau for the very first time Lamido yanuna yanason aurenta,yanuna yanason relationship dinsu tayi gaba kamar na kowani irin masoya anmu kuma sede itakanta tasan he's late,he's too late dankuwa baifito yafada alokacin da take tsananin bukatar irin wadannan kalaman daga gareshiba. Lokaci guda se taji bazata iya cigaba dayi masa karyaba,cikin rawar murya tace "Kayi hakuri don Allah" Lamido jiki sanyaye yace "it means my assumptions are right?" girgizamasakai Maimunatu tashigayi cikin sauri sannan tace "bahaka baneba" Lamido yace "toh menene?" Cikin kuka Maimunatu tace "Ina sonka wallahi... Kuma kana daya daga cikin mutanen dabazan taba mantawa a rayuwa naba koda kuwa awani hali na tsinci kaina hakanan mutuncinka da kimarka bazai taba gushewa a idanuna ba. Banki ace kazama mahadin Rayuwanaba Yaya Lamido anma sede dagani harkai bamu taba irin wannan maganarba,dagani harkai mundauki soyayyar mun bata wani ma'ana daban ne dukdani u wanted it further anma amatsayina na mace senake ganin kamar baikamata infara yimaka maganar aureba bayan kai baka taba yimin ba,na biyu tsawon shekarunnan karatu kakeyi baka ma gama ba bare ayi batun samun aikinka harma ka iya rike Mata while on the other hand kuma ni macece,iyayena sun matsamin da maganar infidda miji tunbayauba wanda hakan yasani fara kula wasu tunda banida tabbacin inda nawa da naka alakar suka dosa. Acikin wadanda nike kulawan ne Yaya Khalipha yakwanta min arai kuma yanada duk wasu qualities da kowace mace zata so ace Mijinta yanadashi arayuwa. Innace maka Banason Yaya Khalipha nayi maka karya Yaya Lamido dankuwa zuciya tanason me kyautata matane kumani babu abunda yarageni dashi kamar yanda kaima baka rageni da komaiba. We've been dating for two years with him kuma tun farkon fara soyayyar mu yaso yaturo gida anma nadinga delaying abun with the hope cewa wataran zakayi hobbasa,wataran zaka fara yimin maganar auren mu harma insamu courage din iya rejecting wanda yakeyi dagaske anma har rana maikaman tayau bakayimin ba wanda hakan yasa nabama Yaya Khalipha dama yaturo gida kuma yanzu har ansaka ranar auren mu dashi, January za ayi insha Allah" Maimunatu tadago a raunane takalli Lamido da idanunsa suka canza launi tace "Nasan bankyautaba na yaudareka,nasan bankyautaba naqi insanar dakai anbadani inacigaba da kulaka despite knowing that but believe I'm feeling guilty from within, tsoron kada kayi misunderstanding dina yasa naki nafada maka even though bawai inada niyar boyemakan bane har abada, I'm just trying to install some courage and moreover I'll miss you,rabuwa dakai will not be easy for me shiyasa zuciyata takasa aiwatar dakomai! Don Allah kayafemin" Maimunatu tayi maganar tana kuka maitsuma zuciya, Lamido duk seyaji jikinsa yayi sanyi,dukseyaji wani haushinta dayakeji yaragu because he can understand her pain,he can understand what she's going through and moreover shima da nashi aciki,he never make an effort which was why she's holding back too ..
Ahankali yace "kidaina kuka don Allah" batareda tabar kukan ba takumacewa "I'm sorry please...." Lamido yace "Yawuce... Kidaina kukan hakanan don Allah" dankuwa in akwai abunda yatsana a rayuwarsa toh yaga mace tana kuka. Sa hannu Maimunatu tayi tashiga goge hawayenta hartagama duk Lamido na kallonta.
Seda Lamido yaga tadaidaita kanta dakyau sannan yace "mucigaba da maganar ananne komu koma can?" ahankali Maimunatu tace "mujecan anytime Yaya Khalipha na iya zuwa" gyadamatakai yayi ahankali sannan yajuya yafara tafiya inda tayi sauri ta Isa inda yake suka shiga jerawa tare ahankali batareda kowa yace da dan uwansa wani abuba ahaka harsuka Isa inda suka saba hira acan bayan layinsu Maimunatun kan wani dakali. Zama sukayi dukansu sannan Lamido yace "Naji bayanan ki and I understand you Maimunatu. anma sede inason kisan cewa you've hurt my feelings by hiding things from me, Atunanina nidake munzama abu daya,Atunanina bamuda abunda zamu boyema juna amma still Kika boyemin maganar aurenki,sede naji labari awaje which is the worst part acikin komai. No matter how hard it's hakanan no matter what the problem is irin wannan news din ba'a boyeshi,you might think inkika fada min I'll be heartbroken shiyasa kike kin fada but believe me I'm more heartbroken now danaji abakin wani badaga bakin kiba. It's better kedin kifadamin koda kuwa raina zaibaci,explain yourself koda kuwa bazan gane mekike nufiba,Koda kuwa bazanyi miki uzuri ba aikeda kinfita a hakkina" gyadakai Maimunatu tayi cikeda gamsuwa.
Lamido yace "anma bakomai yawuce,nayafe miki Allah ubangiji yayafe mana bakidaya and I want you to know that komai yafaru a rayuwarnan mukaddarine and everyone you meet has a role to play in your life. Yes we love each other but we're not destined to be together shiyasa dagani harke muka dinga yin nauyin baki har wani yarigani. And yes eventhough you're getting married and we're breaking up today inason kisan cewa bakarshen alakarmu ba kenan Maimunatu,we can continue being friends,you can also consider me your Brother if you want to and I promise to always be there for you. i just hope you find happiness in your marital home" Lamido yakarashe maganar sincerely.
Maimunatu bakaramin dadi kalamansa sukayi mataba,hakanan tana jinjina kyawun zuciya irin nashi,itakanta tasan tayi rashin namiji me halin kwarai dukda kuwa ko kadan bata danasanin auren Yayanta Khalipha dazatayi tunda shidinma ba bayaba. Ahankali tace "Nagode Yaya Lamido. Allah ubangiji yabar zumunci" ahankali Lamido yace "Amin Maimunatu" sekuma sukayi shiru dukansu harna kusan mintuna goma haka, Maimunatu Jin shirun yayi yawa setace "Ina Rukayya" take Lamido yaji wani irin dadi na musamman ya ziyarce na ambaton sunan Rukayya kawai da Maimunatun tayi,seyaji yana kewanta. Koyanzu tana Ina makaranta? Komi takeyi? Allah ne kadai masani dandai yasan yau ana hostel babu night prep bare yace tafita karatu. Daman dayana makarantar ne toh tabbas dayanzu suna tare suna hira ko tana game cikin wayarsa.
Seda Maimunatun takuma yi masa thesame tambaya sannan yadawo daga trance dinsa na tunanin Rukayyan dayashiga,fuska daukeda murmushi yace "She's fine. tabani sakon gaisuwa kinga nama manta banfada mikiba seyanzu da kika tambayeni ita natuna" Yar dariya Maimunatu tayi sannan tace "toh sakon gaisuwa ya iso. Ina amsawa,wannan karan batace akai mata tsaraba ba?" Yar dariya Lamido yayi sannan yace "Rukayya tana kin karban tsaraba ne? ai indai akwai kawai kibayar akaimata" Maimunatu tace "Babushi akasa yanzu amma insha Allahu gobe zantanada in aiko gida katafi mata dashi" Lamido yace "Allah yakaimu goben" sekuma yatashi yana duba agogon hannunsa,yace "bari in wuce kada inrike ki azo ana neman ki agida" tashi tayi tsaye itama,jiki sanyaye tace "toh shikenan" dankuwa the thought of this's the last day dazaizo hira gurinta just make her feel lonely,setaji tunyanzu tafara kewarshi hakanan memories dinsu suka shiga dawo Mata cikin kwanyarta daya bayan daya. Lamido lura da halin datake ciki yayi seyace "muje inraka ki kofar gida se inwuce nima" jinjina masakai Maimunatu tayi sannan suka shiga takawa ahankali.
Few steps to zasu Isa gida seta jefo mishi tambaya,tace "Kana Sonta Koh?" tsayawa Lamido yayi yana kallon Maimunatun, dukda kamar yagane watake nufi anma seyayi kamar baigane dinba,yace "Wa kenan?" Ahankali Maimunatu tace "Rukayya..." Lamido besan sanda wani irin lallausar murmushi ya subuce mishiba. Ahankali yace "Uhmmmm. anma ya akayi kikasani?" Maimunatu setayi murmushi tace "Hmmm yabazan sani ba" seyayi Yar dariya yace "shine kuma kika dinga nunawa kamar baki saniba?ko Yar kishinnan nawa baki taba nunawa kinayi ba" Lamido yayi Maganar cikin sigar zolaya.
Maimunatu tace "Waya gayamaka banayi? Kawaidai nasan kishin nawa bayida amfanine kona nunane shiyasa. And I know I'm leaving you toh maizaisa in hanaka kula wata? Innayi haka ai selfishness din nawa seyayi yawa shiyasa ma nadinga nuna kamar bansaniba" seta sauke ajiyar zuciya tace "she's a very sweet girl. I know you two will make a perfect couple" Lamido cire hannayensa yayi daga cikin aljihun wandonsa ayayinda yatsaida tafiyar dayakeyi din ganin sun iso kofar gidansu Maimunatu. Yana murmushi yace "Thank you" Maimunatu araunane tadan yi mishi bye bye da hannun sannan tace "Se watarana Yaya Lamido. Insha Allahu gobe zanturo sakon Rukayyan gida kafin katafi" gyada matakai yayi ayayinda yake daga mata hannun shima. Seda Lamido yabari Maimunatu tashige gida sannan yajuya yanufi hanyar majalisar su yana tuna rayuwarshi da Maimunatun shima,wani yayi dariya,wani yayi murmushi wani kuma ya girgiza kai kawai. Shikanshi yasan there're some special memories that can never fade away from his brains,Maimunatu might not be the woman but she's so many impact in his life da mantata dawuri will be very difficult.
Washegari Sunday Lamido yakoma Azare hakanan dazai tafi seda yahadama Rukayya tsarabobinta kamar yanda yasaba koda yaushe ciki kuwa hardana Maimunatu kamar yanda tayi alkawari.
***
Bayan visiting da sati daya da Yaya Lamido yaje gida yadawo segashi da tsarabobin dayasaba kawomin kowani lokaci inyaje gida. Dayanma ya aika aka kira masani a hostel inda nasameshi a varendern ajinmu acan classes area dayake weekend ne,wurin shiru babu dalibai duk suna hostel. Seda muka gaisa dashi natambayeshi mutanen gida yace duk ya barosu lafiya sannan yafara min presenting tsarabobin daya tahomin dasu. wannan karan tsarabar Umma daban ne dankuwa ba abun ci baneba,packaging dinshi ma daban akayi. Bayan nagama bude kowanne nagani sena janyo ledar dayace Umma ne tace yabani. Bakar ledace kuma tafi kowanne girma acikin sakonnin daya kawomin din.
Kiciniyar bude ledar nashigayi Ina mamakin miyene masu laushi aciki kamar kayan sakawa harna samu na bude,wara idanuna nayi excitedly sakamakon hango sleeping dress dinda nayi acikin ledar ta sama sama. cikin sauri nasa hannu naciro sleeping dress din ina fadin "Laaa kayan bacci masu kyau Umma ta aikomin" sekuma nashiga warewa,riga da wandone cotton mai laushi sosai pink ayayinda akayi zanen teddys ajikin kayan baccin. Rungume kayan nayi ajikina inajin sonsu araina dakuma son wanda ta aikomin kayan ayayinda fadin "sunyi kyau sosai wallahi. Inason su,Umma ta iya zabe Yaya lamido" shidai Yaya lamido zubamin idanu yayi yana murmushi. Seda nagama murnar sleeping wears din sannan na mika ma Yaya lamido kayan don yagani dandaga expression din fuskarsa kamar yanzu yafara ganin kayan shima and more over akwai wasu aciki,sonake incirosu Suma ingansu.
Hannuna namaida cikin ledar Ina ciro sauran kayan anma duk senaga ashe Bras ne har guda biyar masu shegen kyau sabbi. wara idanuna nayi da mamaki Ina dagasu daya bayan daya sannan nadubi Yaya lamido daketa kokarin kauda idanunsa tunbayan dana fara ciro brassieres din nace "Yaya Lamido Bras ne fa wadannan?" Cikin son kauda zancen batareda yakalleni ba yace "toh ni miye nawa aciki?" Tura baki nayi batareda wani damuwa ba nace "Ina ga mistake Umma tayi,inbahaka ba ni mezanyi da Brassiere?" danharga Allah da iyakar gaskiya ta nike maganar bankuma ji inajin nauyinshi ba kwata kwata alokacin seyanzu danake tuna abun.
Seyaki kallona kwata kwata, yashiga danne danne cikin wayarsa wanda hakan baitaba faruwa ba in muna magana dashi anma duk bankawo komai araina ba,yace "Me akeyi dashi?" Kai tsaye nace "Sakawa. Anma ai seniors dinmu kesakawa ba Irina ba" senaga yasaki wani irin lallausar murmushi...
Daukan bras din nayi nashiga maidasu cikin leda Jin bece komaiba sannan nace "inaga mistake Umma tayi tahadomin dasu dukranda zakaje Gombe seka tafi mata dashi" Na karashe maganar ayayinda nadaura masa ledar kayan akan cinyarsa bayan nasaka sleeping wears dinnawa a dayan ledan tsarabana. Sauri yayi yadawomin dashi yana fadin "A'a ki ajiye agurinki dukranda kuka hadu seki bata dakanki" tsuke fuska nayi sannan cikin sigar shagwaba nace "Ni yanzu nasan ranar sake ganinta ne Yaya Lamido?" seya waremin hannayenshi alamar shima baisaniba kuma badamuwarsa baceba.
Kamar zanyi kuka nace "Dan Allah kamayar Mata" wannan Karan strictly Yaya Lamido yace "Allah bazan mayarba aicewa tayi nakine" akafule nace "toh ai nace maka mistake tayi" karon farko daya dago yakalleni tun bayan da muka fara maganar brassieres din hakanan besauke idanunsa akan ko Ina ba se setin kirjina,kallon gurin yayi nadan dakiku kafin kamar wanda yatuna wani abukuma se yayi sauri yadauke idanunshi daga gurin yamayar kaina,adan daburce yace "Mistake fah kikace?" memakon inbashi amsa sena tsinci kaina da kallon kirjina nima cikeda curiosity inason sanin meyakai idanun shi gurin,abunda idanuna suka ganemin ne yasani fasa ihu lokaci guda ayayinda nadaka tsalle natashi daga zaunen danake kan varendern nanufi hanyar hostel dagudu.........
Inaji Yaya Lamido na kiran sunana yana dariya kasa kasa anma ko juyowa banyiba bare yasaka ran ganina,ledojin tsarabar tawa ma duk anan gurinsa nabarsu. Sanda na'isa kwanarmu zubewa nayi kan gadona Ina sauke haki tareda sauke numfashi akai akai sakamakon irin gudun danayi. Seda numfashi na yadaidaitu dakyau sannan nadago kamar wata munafuka nashiga sake kallon kirjina kamar yanda nayi dazu.....dukda hijabin dake jikina kana iya ganin irgen dangina dasuka fara tasowa luf luf dasu,tunda nake bantaba lura haka suka kara girma ba kuma koma naluran bantaba tunanin har mutane zasu na lura dashiba innasaka kaya hakanan bantaba tunanin yakamata infara tare su dawani abuba. Tuno yanda Yaya Lamido yakalli gurin dazu nayi kafin cikin sauri nasa tafukan hannayena narufe fuska nikaina inajin kunyar kaina dakaina bareshi. Sena tuno maganar Brassiere danayi ta masa kamar wata wawiya duk yana kaucewa.....
Inacikin tunaninnan ne wata yarinya tayi sallama a bakin kwanarmu,amsa mata nayi ayayinda tashigo tamikomin ledar kayana tana fadin "Wai gashi inkawo miki inji Sir Isma'il" karban kayan nayi namata godiya kafin tayi tafiyarta. Bude ledar nakumayi naciro kayayyakin bakidaya,daya daga cikin bras din nadauka nacire rigar jikina nasaka senaga tayimin daidai,cip cip dani and then I realize cewa Bras din mani aka kawomawa and Umman may be talura da abubuwan ne yasatayi tunanin Ina bukatarsu. Buka tsalle nadanyi cikin sigar shagwaba