Showing 180001 words to 183000 words out of 213309 words

Chapter 61 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5882

idanun dazanyi se suka sauka kan Yaya Zaheera da saurayinta a filin gidan. Ashe baitafi ba,lokacin ne yafito zaitafi tanayi masa rakiya,hannunsu sarke dana juna se hira sukeyi wanda bana iyajin komai se motsin bakinsu danake gani dakuma irin annurin dake fuskar sudayake akwai security light agidan. Bakomai yabani mamakiba illah irin closeness dinda ke tsakanin su ayayinda suke nufar motar tasa,kaman wanda zasu shige jikin junansu.

Ahaka suka Isa jikin motar tasa,yajingina da jikin motar suna kallon juna still baisaki hannuntaba. Sundan Jima suna magana ananma kafin suka rungumi juna yakama hannunta yamata kiss sannan yabude motar sa yayi shigewansa yatafi.

Seda zuciyata tayi wani rass ganin abunda sukayi din dankuwa dukda rashin wayauna sosai alokacin nasan abunda sukayi ba daidai baneba tunda ansha koyamana a islamiya cewa "taba wanda ba muharraminka baneba babu kyau a addinance harsai in aure yashiga tsakanin ku", sannan nasha karantawa a News paper dinda ake tanadar ma yan club dinmu na makaranta(press club) every week cewa rape cases yayi yawa sabida irin wannan huldan da Yan Mata da samarin yanzu keyi,nataba karanta wani labari akan wata Yarinya da Saurayi ya yaudareta yarabata da pride dinta with alkawarin zai aureta anagab da auren yace yafasa. Take sena tsinci bakina nayima Yaya Zaheera addu'ar Allah yasa saurayinta Uncle Abdul ba haka yakeba, Allah yasa baya daya daga cikin wadannan mazajen.

Washegari Sunday muna Isa islamiya Malamin mu nasamu nayi masa karyar banida lafiya ne shiyasa banzo islamiya jiyaba. Tambayana yayi yajiki nace masa dasauki kafin yacemin ai yanzukam anwuceni dankuwa jiya bayan ankarbi hadda anyi kari kuma har rubi'i guda akabayar kuma yau za'a karba asake bada wani. Hankalina tashi nayi sannan nashiga bashi hakuri akan yataimaka min yayi wani abu akai dankuwa tabbas indai akayi gaba aka barni toh akwai probability din in akazo exams inyi failing Qur'an amaidani baya dankuwa kullum aka karbi hadda se anbada scores iya dede kokarin ka gurin bada haddar. Seda Malamin mu yaga inashirin yi masa kuka sannan yajitausayina yabani sharadi,yace sede idan antashi a makaranta intsaya yakaramin karatun danayi missing jiya Inna bashi haddar da akabamu tun kan mutafi makaranta.

Sannan dole gobe zankawomai haddar jiyan danayau daza'a bayar agaba.

Aicikin sauri nace "Nayarda Mallam" dukda kuwa nasan it'll be difficult for me in iya haddacesu kafin gobe but still I'll try my best tunda nikeson cigabana and moreover alfarma yamin. Haka natafi ajinmu muka fara daukan darasi.

Anatashi daga islamiyar kuwa banzarce ko'ina ba se office din Malamin Qur'an dinmu danyamin Karin karatun. Banwani damu dasanar dasu Sadiya ba sabida nasan Kona fadama a banza ne bafada ma Wanda zaizo daukarmu uzurina zasuyiba while nikuma bazan yarda inyi loosing wannan opportunity dinba. Nasan indai Yaya Salim ne zezo daukar mu toh tabbas zetambayi Ina nake,insukace basusani bama ze iyacewa sudawo cikin islamiyar sudubani kokuma shidakanshi ma yazo nemana. Yaya Zunnurain kuwa ko tambayar inda nake bazaiyiba nasani hakanan bakaramin aikinshi bane dasun shige motar dukansu yatada mota yatafi yabarni anma sede koyayi hakan bazan damu ba tunda inada other alternative.
Inada hundred naira dinda zanyi kudin napep dashi dayake dasafe kudi Aunty taraba mana kasancewar Iya batazo aiki dawuri ba ta makara. In akace mujira tagama girki tabamu har mu taho dashi islamiya zamuyi latti shiyasa kawai Auntyn tace muci Tea and bread inyaso setabamu kudi musayi wani abu a makarantar.

Har Malamin mu ya gamamin karin karatu babu wanda yazo nemana daga cikin yaran Kawu Sani wanda hakan yasani gane cewa ba Yaya Salim bane yazo daukarmu. Yaya Zunnurain ne.

Sanda nafita a harabar Islamiyar daidaikun dalibaine suka rage da ba'azo daukar suba,dayawa duk suntafi gidajen iyayensu. Tsaida masu acaba da napep dinda ke wucewa jefi jefi nadingayi agabsn gate din isIamiyar tamu Ina fada musu ga unguwar dazasu kaini anma duk sesuce banan suka nufaba wanda hakan yasani deciding intafi bakin babban titi kawai innemi abun hawa zaifiyemin. Taku nashigayi cikin sassarfa Ina nufan Babban titi,seda nayi nisa sosai da islamiyar nakusa Isa bakin titi kawai naci Karo da katoton Kare. Bakaramin tsorata nayiba,zuciyana yafara dukan uku uku take babu kakkautawa. In akwai abunda nake tsoro a duniyar nan a cikin dabbobi toh ya biyo bayan kare da mage. Ganin karen inda nake yake nufowa take idanuna suka tara kwallah Ina maimaita kalmar "lahaulaulakuwata illah billah" ayayinda jikina keta aikin rawa.

Gashi gurin shiru babu wulgawan mutane kasancewar babu wani gida akusa da gurin bare ince zan shige,daga uncompleted buildings sekuma fegi da aka zagaye sekuma juji daga daya bangaren. Tafiya da baya baya nafarayi harlokacin jikina baidaina rawa ba hakanan karen kanshi baidaina yowa inda nakeba. gashi bazaiyi inyi guduba sabida naji ance inkaga Kare ka gudu toshine zaibika da gudu yacijeka. Kai ranar naga tashin hankali,iya tsorata na tsorata danhar nariga nagama sadaukarwa karen nan cizona zaiyi. bullowar motar danaganine daga can Babban titin yashigo layin danakene yasani sakin wani irin nannauyar ajiyar zuciya dukda kuwa bandaina tafiya da baya bayan danakeyi dinba tunda Karen shima baidaina yowa inda nakeba. Dagama Mai motar hannu nashigayi a firgice ayayinda naga ya iso dab dani,nikaina bansan sanda nashiga motar ba ganin yatsaya.
Haka nadinga sauke numfashi Ina haki nikadai batareda nama damu da insan wanene Mai motar ba, alokacin damuwana shine intsere ma Karen nan shiyasa danaga na tsere mishin nakeji kamar na tsallake siradine. Nafi mintuna biyar Ina daidaita kaina,seda numfashi na yadawo daidai sannan najuya dan inkalli Mai motar. Hada idanun danayi da Mai motar ne yasani zare idanuna batareda na shirya ba.

Sekuma nayi sauri namaida idanuna wajen motar inadubawa kozanga Karen a wuraren gurin inkuwa babushi fita zanyi a motar anmasede harlokacin Karen bebar harabar gurinba,infact yawonshi yaketayi a gurin yana tsince tsincen abinci kan juji yanaci. "Hmmm take some water" shine abunda Mai motar yafada ayayinda yake mikomin bottle water Wanda hakan yasani maida dubana gareshi. girgiza masakai nayi alamar a'a bazan Sha ba Wanda hakan yasashi mayar da ruwan ya ajiye a ma'ajiyinsa sannan yatada motar yabar gurin.

Nidai fatana baiwuce muyi nesa da inda Karen yakeba ince masa yasaukeni inkama gabana dukda kuwa Ina mamakin meya kawo shi hanyar islamiyarmu yaudin?

Agaban islamiyar mu yayi packing yabude motar yafita Wanda hakan yasani sa hannu daniyar inbude handle Nima infice anma senaji yadanna lock. Wara idanu nayi ayayinda nabisa da kallon mamaki. gurin sauran daliban dake zazzaune yadinga bi yanaduba fuskokinsu da alamaida wasu yakenema haryagama dube dubenshi yadawo motar. Yana shigowa Kuma yasake Danna ma motar lock,arude nace "Miye hakan Mallam? Don Allah ka budeni" kallona yayi ahankali yana murmushi sannan yace "Ashe harda mutane kike tsoro? Nina dauka dabbobin kike tsoro kadai" cikin son nuna bravity na nace "nibana tsoron kowa" seya saki Yar dariya yace "toh naji nayarda bakya tsoron kowa. but to prove me wrong you've stop panicking. Ba sace zanyiba Rukayya, I'm giving you a lift" cikin sauri nace "Banaso" idanunshi nakaina yace "Miyasa? Ba gida zakije bane?" Nace "Gida zani anma ai adaidaita nayi niyar Hawa" se yace "Nasani ai. Kuma bakikai ga hawan ba se Allah ya hankado mikini. hanyar unguwarku zani kibari inyi dropping dinki a gida se in wuce" ...

Daganan baijira cewana ba yatashi motar mukabar wurin ayayinda yake kokarin kiran wata number awayarsa. A handsfree yasaka wayar tana ajiye kan cinyarshi hakanan wanda yake kira din baijima Yana ringing ba tayi picking.

Shine yafara magana,yace "Aunty kinajina" wata sanyayyar murya naji daga daya bangaren tana fadin "inajinka Babanaaa? kana inane haka?" yace "Yanzu nabaro Islamiyar su *Ameera*,nazo natarar batanan anma friend dinta tacemin tabi yaran neighbors dinku suntaho gida tare shine nace barina kiraki nayi confirming" Matar daya kira da Aunty setace "ta'iso gida Babana. I'm very sorry natasoka daga gurin aikinka wallahi motata ce taki tashi, Baban su Kuma baya gari itakuma bata taba bin adaidaita sahu ba shiyasa naji tsoron cewa tabidin nayi maka magana kaje kadaukota" cikin sauri yace "No Aunty karki damu. I should be the one saying sorry banje daukota dawuri ba har tabi wasu. Wallahi abun slipping mind Dina yayi" Aunty tace "bakomai karka damu. Allah yabar zumunci" daganan Kuma seta shiga tambayarshi yaushe zaizo Mata ziyara. Dariya yayi sannan yace Mata seya samu lokaci inda itakuma tashiga korafin aikullum maganarshi kenan. Daga karshe dai seda tasashi yimata alkawarin washegari zeje gidanta yayi dinner tareda ita da Mijinta gabadaya shima zaidawo daga tafiya. Yace yayarda daganan Kuma sesukayi sallama.

Adede lokacin ne kuma muka iso titin dazai hau layin unguwarmu.
dasauri nace "ka tsaya please" tsayar da motar yayi sannan nadubeshi nace "Nagode zansauka anan inkarasa gida" nakarashe maganar ayayinda nake kokarin bude kofar motar anma arufe.

Juyowa nayi nakalleshi sannan nace "kabude kofar please" memakon yabude seyasaki murmushi yace "toh Rukayya matsoraciya zanbude miki kifita anma ko sunana bazaki tambaya ba?" da kamar zance mishi "mezanyi da sunanka Kuma" anma senaga kamar hakan baidace ba,namarairaice murya dukdan murabu lafiya nace "don Allah nidai kabude min intafi inbaso kake inmaka ihuba" dariya yasaki sosai hakanan baibude kofar ba yashiga fadamin sunansa da aikinsa. Yace "Sunana Sajeed. anan garin Bauchi nikeda zama, I'm a medical doctor by profession. tunranar dana ganki a shago naji hakurin ki da sanyin halinki dabaki mayarma Mai shagonnan magana ba ya burgeni. Shine nabi bayanki don innemi kulla abokantaka dake anma seke da Wanki kukayi shunning dina down harma na cire Rai da samun kawa kamarki. But here we're today, Allah yasake hadamu asanda nidake bamuyi tsanmani ba. So I feel like kaman Allah ne yasake bani wani opportunity din don insake neman alfarma gurinki. May be gamo na dake akwai alkhairi aciki. So can we be friends?"

Kalamansa sunmin dadi kuma sunansa ma yamin dadi dankuwa farkon da nafara Jin sunan abakin Aziza (sunan Yayanta) nake yawan yabon sunan toh anma abunda yazo Raina alokacin shine daman ana abokan taka da mnyan mutane?kokuma Daman ana abokan taka tsakanin mace da namijine? Nidai bantaba jiba. Relationship dinda nasani tsakanin mace da namiji inya Yaya da Kanwa ba toh Saurayi da budurwa.

Don haka take senace Masa "aibazai yuyu inzama kawarka ba?" Da mamakina yace "Miyasa?" abunda yafito abakina shine "kamin Kato kazama abokina Kuma Kai namijine ni macece" wannan Karan dariya yake sosai harma Ina iya ganin hushiryarsa,seyau nasake ganin kyawunshi yafito sosai unlike ranar dana Masa kallon tsoro Kuma dayake yaudin manyan kayane ajikinsa se hakan yakara fidda haibarsa da kamalarsa.
Dakyar yatsagaita dariyar dayakeyi sannan yace "toh inba abokin ba wani gurbi za'a taimaka abani" akagare nace "Babu" seyayi fuskar tausayi yace "Babu kuma Hajiya Rukayya? Adai taimaka aduba" shiru nayi Ina nazari kafin can Kuma nadubeshi nace "Babufah. Kaga nibana Saurayi da budurwa tunda ni karamar yarinyace, Yaya Kuma banhada jini dakaiba bare kazama Yayana" wannan Karan ma seda yadara ma Yarintata.

Yace "waye yacemiki kinyi karama ayin Saurayi da budurwa?" Kai tsaye nace "bantaba gani sa'annina sunyiba Kuma Yaya Salim ma yace nayi kankanta" Sajeed yace "Yayanki danahadu dashi ranar?" Gyadamasakai na nayi ahankali.

Seyace "toh shikenan nayarda kinyi kankanta a Saurayi da budurwa,Kuma nayarda ba'a abokantaka da tsakanin mace da namiji injiki da fada anma ai Zan iya zama Yayanki koh?" Girgiza masakai nayi ahankali alamar a'a,fuskar tausayi yayi sannan yace "Miyasa?" cikin sauri nace "inada Yayu ai" seyace "Nasani. Nima inason inzama Yayanki ne dagayau sekisani cikinsu" shiru nayi Ina nazari,take kuma se Yaya lamido yafado min arai,sena tuno shimafa banhada jini dashiba anma kuma Yayana ne don haka Sena gyada masa kai nace "toh shikenan" irin murmushin dayasaki alokacin kadai yasanar dani dadin dayaji.

Seyace "Nagode Rukayya. Yanzu yaza'ayi mudinga haduwa? Za'abarni inazuwa gidanku kuwa?Naga kamar Yayanki is very strict ba lallai yabarni ba,karyace zanyi masa kwacen kanwa" yayi maganar cikin raha raha. Cikin sauri nace "bazakana zuwa gidanmu ba" Sajeed yace "toh a Ina zanna ganinki?" ware Masa hannu nayi alamar bansaniba.

Shiru yayi yana nazari sannan can yace "toh shikenan. Zanna zuwa islamiyar ku mudinga haduwa mu gaisa yayi?" gyada masakai nayi ahankali sannan nace "ai ranar larabama zamu koma makaranta. Makarantar kwana nakeyi" yace "anma ai gobe Zaki islamiyar Koh?" Cemasa nayi "Eh har jibima" seyayi murmushi yace "toh zamudinga haduwa kafin Kikoma makarantar Insha Allah"


Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately on WhatsApp for payment details.

*Insha Allah I'll try and update tomorrow tunda banyi long page ba. thank you*

08147722806

*Page Fifty Four*

*Avoid typing errors please*

Cemasa nayi "Toh" sannan mukayi sallama natafi gida. Koda na'isa gida babu wanda yanemi ba'asin rashin dawowana da wuri barema har inyi tunanin koda ace wataran zan bata za'asamu mai nuna min irin wannan gatan.

Tundaga ranar kullum naje Islamiya sena hadu da Yaya Sajeed mungaisa,either alokacin break kokuma kafin inshiga islamiyar sabida naki yarda ma  muna haduwa bayan antashi kasancewar Ina tsoron kada azo daukarmu aganni dashi ko kar garin tsayawa gaisawa dashi Yaya Zunnurain yatafi yabarni.
Daman Wednesday yakamata muyi resuming school anma sai Ummi taroka mana Kawu Sani kan mubari se Friday koh Saturday kawai mu koma dan ballallai damun koma din ace za'ana mana serious lesson ba. Dole se wata satin tazagayo kafin akoma normal activities fully,dayake yan rashin strictness din Kawu Sanin suna kusa seya yarda wanda wannan dalilin yasa muka cigaba dazuwa islamiyar dandama sauran daliban dasuke boarding suma duk se cikin weekend dinne zasu koma makarantar su sannan dayake gajeren hutune har Thursdays and Fridays ma zuwa islamiyar mukeyi.

Ranar Friday nayi rashin sa'a asirina yatonu. during break naje mungaisa da Yaya Sajeed yabani ledar chocolates da kayan makulashe munyi sallama kenan nafita daga motarsa daniyar tafiya idanuna suka sauka kan motar Yaya Salim dayake kokarin parking motarsa agurin. Yakawo wa Sule lunch box dinsa daya manta agida,zare idanuna nayi atsorace sannan najuya nashiga tafiya dasauri zuciyana tana dukan uku anma abanza dankuwa Yaya Salim already yaganni,cikin sauri yafito daga cikin motar ransa a matukar bace yana kwala kiran sunana.

Dole natsaya sabida tsoron kada attention din masu gadin islamiyar daketa cikin makarantar yadawo kanmu harsu fito suce zasu hukunta ni. Juyawa nayi Ina kallonsa anma memakon inga yanufoni senaga yanufi motar Yaya Sajeed,baiyi wata wata ba yabude motar yacakuma wuyan Yaya Sajeed din dakarfi. Seda yayi Jim sanda yaganshi hakanan anger dinsa yakaru. Yana huci yace "What were you doing in the car with my sister? Banace karabu da'ita ba?" Yaya Sajeed dayagama rudewa yashiga cewa "Calm down Salim! Calm down please. It's not what you're thinking" bamu ankara ba kawai seji mukayi Yaya Salim din yakaiwa Yaya Sajeed punch a fuska.

Yace "Dan ubanka it's not what I'm thinking kakecewa? Tambayarka nakeyi mekayiwa kanwata!! why on Earth will you ask her to come and meet you outside islamiya?" Sekuma yasaki Yaya Sajeed din yayo kaina rai bace,jinadingayi kamar insaki fitsari a wando because bantaba ganin wannan side din Yaya Salim dinba.

Fizgana yayi yajuya dani daniyar zuwa gun Yaya Sajeed din anma da mamakinsa seyaga harya shige mota yayi reverse. Sakina yayi yashiga yabisa da gudu yana kwala masa kira tareda auna masa duk zagin dayazo bakinsa anma dayake bazaka hada gudun mota dana Mutum ba tuni Yaya Sajeed din yabar gurin bakidaya. Seda yabace masa dagani sannan yajuyo yanamin wani irin kallon tuhuma,idanun sa gabadaya sun canza launi harya iso inda nake.

Strictly yace "Meya miki?" Kawai sejikina yacigaba da rawa nakasa furta komai. Cikin wata irin tsawa dahar seda jijiyoyin wuyar satatashi yace "ba tammbayar ki nakeyi ba Rukayya?meya miki?" bakina narawa cikin kuka nace "Allah Babu abunda yamin" Yaya Salim yace "meyakaiki cikin motarsa toh?" cikin firgici nace "gaisawa mukayi Allah" Yaya Salim yace "Anma menace miki ranar? Banace Kar insake ganinki tareda shiba?yama akayi yasan islamiyar dakike?" harlokacin jikina baibar rawa ba nashiga bashi labarin yanda yasan islamiyar mu dakuma taimakona dayayi ranar da Kare yabiyoni harnakai aya sekuma nafashe da kuka maisauti...

Nace "Wallahi Yaya Salim cewa yayi yanason yazama Yayana and nothing else" Rai bace Yaya Salim yace "Dan bakida hankali Yayun tsintar su ake akan titi? Duk yayundakike dasu basu ishekiba sekin jajubo wani?" Yafurzar da wani iska mai zafi yace "Rukayya miyasa wani sa'in kike abu kamar ba mai ilimi ba? why are you trusting people so easily? Kinsan halin wasu mazan kuwa? bama mazaba harda Matan ma you can't just meet someone and trust him out of blue for goodness sake!!!! inkika cigaba da yin hakan you'll only ruin your life....." Yayi maganar murya a raunane dayake nuna tsantsar damuwarsa akaina.

Nidai inbanda kuka babu abunda nakeyi.

Cikin rawar murya nace "Kayi hakuri don Allah"

Zubamin idanu yayi batareda yasan abun yiba harna dan wasu dakiku kafin can murya akarye yace "Wuce muje mota" gyadamasakai nayi ahankali sannan sumui sumui nayi gaba yabini abaya harmuka shige motar. Lunch dinda ba'a bama Suleba kenan....hakanan Islamiyar daba'a karasata daniba ranar....

Muna Isa gida kuma becemin uffan ba yayi wucewarsa sashin su wanda hakan yasani nufan Kitchen nima....

Wunin ranar gabadaya Yaya Salim yacanza min fuska,ko lekoni baiyi a backyard ba kamar yanda yakeyi kullum inya shigo sashin namu. Dankuwa baya taba shigowa bai faki idanun Yan gidan yadan zagayo munyi hira Koda sama samaneba. Hakanan koda yaganni acikin parlourn ma yiyayi kamar baiganniba..

Danakai masu lunch da dinner ma duk yananan amma ko gaisuwata bai amsaba.

Hakan ba karamin tayarmin da hankali yayiba ganin cewa shine mutum daya danake samun sassauci agurin shi,gashi washegari zamu koma makaranta bare ince inada lokacin dazan iya making up with him. Shiya kaimu makarantar washegari hakanan ana gama mana checking bayan antafi da kayayyakin mu hostel zai tafi nayi sauri nabi bayanshi nashige motar nasaki kuka mai sauti. Sanda yashigo motar fuska babu yabo babu fallasa yace "kekuma mekika dawo yimin cikin mota?" cikin sautin kuka nace "Don Allah Yaya Salim kayihakuri Allah bazan sakeyin irin abunda nayiba. Shirunka is Killing me" harara ya watsamin sannan yace "wancan karan dinma ai haka kikace anma hakan baihana ki sake kula shiiba. So kalaman ki da pretense dinki bazasu shigeni ba. Nikifitar min a mota kinga akan hanya nike kar inyi dare" na marairaice fuska nakuma cewa "don Allah Yaya Salim kayi hakuri..." girgizakai Yaya Salim yayi sannan yace "Noo! you should be sorry for yourself and not me girl....guduwa dayayi baitsaya yacece ba sanda nayo kanki kadai ya Isa yanuna miki cewa he's not a person that deserve to be your Brother. And Yayun bawai akan titi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login