Showing 207001 words to 210000 words out of 213309 words
karatu every night dakeba. It's just that I've some work to cover for a few days,may be ma harkuyi resuming school,so bazai yuyu mudinga yin karatu dake kamar yanda muka saba ba. I'm really sorry kidage kinabin na Malamin ku kawai" gyadamasakai nayi ahankali jiki sanyaye sannan natashi nace "okay toshikenan Yaya Salim. Babu komai karka damu" sannan najuya nanufi kofar fita a parlourn. Ninasan babu aikin dazai hana Yaya Salim yimin karatu dankuwa ada kowani irin aiki yakeyi bari yakeyi indai lokacin karatun mu yayi harsai mungama sannan yaje yakarasa. Nadaifi zaton Ummine tahana shi yimin karatun tunda tun asali daman batasan muna karatu dashiba,se jiya da taji inafada ma Kawu Sani. haka nakoma sashin mu jiki sanyaye. tundaga ranar mukadaina karatu da Yaya Salim dukdama hakan besa yacanza minba,inya shigo mukanyi wasa da dariya dashi kokuma innaje sashin su kai musu abinci ranar girkin Aunty inmungama aikin abinci nida Iya mai aikinta wanda hakan yazame Mata duty dinta inda nikuma nake tayata.
Ranar girkin su Ummi kuwa bana aikin komai dansu sukeyin abunsu dakansu dukda nakanji suna mita korafi atsakaninsu. Inaso inatayasu har raina anma tsoron su gwasaleni yasa banama attempting.
Haka Yaya Lamido ze kirani kullum dare musha hirar mu babu wanda yasan Ina rike da waya a hannuna agidanmu dankuwa kullum dasafe innatashi kasheta nakeyi insah acikin akwatina se dare innatashi kwanciya in kunnata inda nanne yake kirana musha hira dashi and that was our first mistake nida Yaya Lamido.
Ranar Friday dadare muna waya da Yaya Lamido gabadaya senajishi wani iri dana tambayesa damuwarsa seyacemin ai tsoron abunda zai faru inyazo washegari yakeyi,kwarin gwiwar nadinga bashi sannan nace Masa komai zaitafi yanda yakamata insha Allah. Adaren ranar Yaya Fahad ya iso gida dukdama babu wanda yaganshi awannan daren kasancewar isowan dare yayi sosai,dankuwa wuraren Sha daya da rabi Ina waya da Yaya Lamido lokacin naji shigowar motar sa. se washegari dasafe daya shigo gaida Aunty muka ganshi. Senaga yakara kyau,yayi kiba yakuma kara manyanta compared to sauran lokutan dayake zuwa gida.
***
Fahad nafita a sashin su Aunty straight sashin Kawu Sani yawuce don su gaisa kasancewar babu wanda yahadu da adaren Jiyan dayake isowar dare yayi sosai,motarsace tabaci masa ahanya seda aka gyara sannan yakaraso Bauchin. A parlour yasamu Kawu Sanin Yana breakfast, sallama yayi Kawu Sanin ya amsa sannan yasamu guri yazauna yace "Abba Ina kwana" Kawu Sani yace "Lafiya Lau Son. Ya gajiyar hanya?" Fahad yace "Alhamdulillah Abba" Abbah yace "mota setayi maka tsiya jiya" Fahad yadan saki murmushi yace "wlhy kuwa Abba,Allah yataimakeni Ina kusa da shiga Zaria ba'a dokar daji tabaciba" jinjinakai Kawu Sani yayi sannan yace "it's a good thing and alhamdulillahi tunda ka iso gida lafiya" Fahad ya jinjinakai Yana murmushi, soyake yatambayi mahaifin nasa dalilin kiransa anma yakasa.
Kawu Sani kuwa daman yasan halin abunsa Sarai,seyace "kashiga kun gaisa da iyayen ku Mata ne?" gyadakai Fahad yayi ahankali. Kawu Sani yace "toh abunda yasa nace kazo gida is because I'm receiving a very important visitor today and I want you and Salim to be there with me shiyasa na kiraka" gyadakai Fahad yayi cikeda gamsuwa sannan yace "Toh Abba" Kawu Sani yadaga kai yadubi wall clock din dake parlourn sannan yamaida dubansa ga Fahad. Yace "I don't know the time he's coming so just stay around karyazo bakwanan. inform Salim about it please" gyadakai Fahad yayi sannan yace "okay Abba. Allah yakawo shi lafiya" Kawu Sani yace "Amin" sannan yace "shikenan katashi kaje seyazo din"....
Haka Fahad yakoma sashin su yana mamakin wanene wannan bakon da Abba zaitaso dashi tundaga Abuja sabida kawai yaganshi. Koda yasanar da Salim sakon Abban seyaga Salim din ya yatsina fuska yace "Do we really have to meet the guy?" Fahad yaso yatambaya wani guy ne amma miskilancinshi bazai barshi ba danhaka sekawai ya warema Salim din hannayensa alamun shima baisaniba.
Dede lokacin Aisha tashigo parlourn nasu bakinta daukeda sallama. Salim ne kadai ya amsa Mata a fili,gaidasu tayi sannan tashiga tambayarsu kosun Gama da food flasks din abincin da ta kawo musu dasafe. Kallon shi Salim yayi sannan yace "you didn't have your breakfast Yaya" yatsina fuska Fahad yayi sannan yace "she should just take it" daganan yajuya yanufi dakinsa yana mamakin miyasa yau batazo kawo musu abinci da daukan kwanuka ba instead Aisha tazo? Komadai menene he just hope tasamu abincin dataci inkuma batasamu ba toh Allah yasa foodflasks din abincin da Aishan tafita dashi yashiga hannunta.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately on WhatsApp for payment details. 08147722806
*Page Sixty*
Nida nake bama Yaya Lamido kwarin gwiwar segashi yau nina tashi da matsanancin faduwar gaba,senakejin wani irin nervousness dana rasa dalininsa hakanan minti minti nake zuwa inleka filing gidan ko Allah zaisa Inga isowar Yaya Lamido anma shiru,haka wata zuciyar tadinga rayamin wayasani ma ko sanda baki leka dinba yashigo harya wuce baki saniba.
Wuraren shabiyun rana su Yaya Aisha suka fito daura abincin rana dayake girkin Ummi ne,dole na hakura da leke leken nakoma main parlour dankada suyi zargin wani abu anma fah dukda haka gabadaya hankalina baya jikina. Sonake kawai wani yazo yasanar dani isowan Yaya Lamidon kokuma azo asanar dani komai yatafi daidai tsakaninsa da Kawu Sani anma kuma nasani ko karen haukane yacijeni basamun irin mutuminnan zanyi acikin gidanba dankuwa Yaya Salim dinma danakeda hope akansa bason batun auren yakeyiba.
***
Bin Rukayya da kallon tsana Aisha da Zaheera sukayi sanda tabar harabar backyard din harta shige parlour. tsaki Zaheera tasaki sannan tace "munafuka kawai! safa da Marwan merai takeyi tun dazu anan gurin" Aisha ne tace "dubawa takeyi kozata ga isowan masoyinta mana" harara Zaheera tawatsa ma Aisha sannan tace "Watoma ke fata kike yazama masoyin natane zezo neman aurenta Koh?" Aisha tayi dariya tace "bafata nikeyi ba Yaya Zaheera,it's just obvious,rashin damuwa da aurar da'ita daza'ayi da rawar jikin datakeyi tun safe kadai ya Isa ya tabbatar muku cewa Sir Isma'il ne meneman aurenta. Aike tareda ke muketa samata Ido tundazu so basai namiki dogon bayaniba" Zaheera tace "Komadai miyene you just can't be sure,kibari muganshi da idanun mu semu tabbatar" Aisha tace "toshikenan nayi shiru,Allah yakaimu anjiman sanda zai iso" Safiya dayanzu isowanta gurinsu taji last statement dinsu kuma tasan tabbas maganar bakon sukeyi seta samu guri agefen su tazauna tana fadin "toh inyazo din yaza'ayi musani? Kunsandai sashin Abba zashi direct kawai Koh?" Aisha tace "karki damu ai Yaya Zunnurain nanan kuma Ummi tace mishi daya iso yazo yasanar da'ita" Safiya tace "toh shikenan. Allah dai yasa ba Sir Isma'il din baneba dankuwa inshine inaga har zazzabi senayi wallahi. The girl can't be always lucky gaskiya" Zaheera tace "Kima bar maganarnan. Bashidin baneba dayardar Allah"
***
Karfe daya da Yan mintuna Auwal da lamido suka iso cikin garin Bauchi dankuwa Lamidon zuwa yayi ya ciccibo Auwal din a Azare,acewarsa bazai iya zuwa ganin Kawu Sanin shi kadai ba seya nemi dan rakiya. Dasuka baro tasha ganin lokacin sallar azahar yayi seda suka tsaya awani masallaci sukayi sallah sannan suka karaso gidan Kawu Sanin. Lamido baiwani sha wahalar gane gidan ba dayake yazo yafi sau biyuma shikadai.
Abakin kofa sukayi kicibis da Zunnurain yadawo daga masallaci ze shiga gida suma sun sauka a napep kenan,sallama Lamido yama Zunnurain din sukayi musabiha sannan Zunnurain yazuba ma Lamidon idanu yanason yatuna a Ina yasan fuskar(karku manta duk zuwan Lamido gidan da Zunnurain yake fara kicibis abakin kofah,sau dayane yahadu da Mai wanki har mai wanki ya je ciki yasanar ma Ummi zuwan shi zasu fita unguwa itada Zaheera) ganin irin kallon da Zunnurain din kema Lamido se Lamido yasaki murmushi yace "Baka ganeni bakoh?" murmushi Zunnurain yasaki yanadan shafa sumar kansa yace "wallahi nadai ga kamar nasan fuskar anma nakasa tuna a Ina nasan fuskar taka" Lamido yace "Allah sarki. I'm Isma'il,sau biyu muna haduwa dakai twice danazo gidannan kwanakin baya katuna yanzu?" take se abun yayi hitting kan Zunnurain,cikin sauri yace "yeah! natuna kaine kake zuwa neman Rukayya Koh?" Yar dariya Lamido yasaki yana gyada kai sannan playfully yace "but this time I'm here to your Dad,Allah dai yasa yana gida" Cewar lamidon. wani abune ya tsirga kirjin Zunnurain lokaci guda Jin abunda Lamidon yace,take se kwakwalwarsa tafara tuno masa hirarsu dasu Ummi da Aisha daren jiya,inda Aisha keta emphasising ita tasan Sir Isma'il ne ze nemi auren Rukayya ayayinda Ummi da Zaheera kemata fadan tadaina yimasu wannan fatan. Zunnurain besan sanda yadaga idanu yafara kallon Lamido daga sama har kasaba yana tuna sanda Lamidon yace masa sunan sa Isma'il. Cikin sauri zuciyar shi tafara raya mishi "this can't be...this can't be" because daga kallon yanayin yanda Lamido yayi dressing dakuma kyawunsa,nutsuwarsa dayanda yake magana kadai yasan indai Rukayya ta aureshi toh tabbas tayi musu nisa,zatayi musu nisan da bazasu iya taking revenge akanta ba.
Take kuma se wata zuciyar tashiga raya mishi toh kodai dayan bakon dasuka zo tarene,kodai rakoshi Lamidon yayi sabida baisan gidan ba tunda yaji ance lamidon cousin din Rukayyan ne. wannan tunanin dayayine yasashi Jin wani Dan relief anma sede daga idanu dayayi yakalli Auwal dan yasake assuring kansa seyaji tashin hankalin shi ya dada karuwa dankuwa Auwal dinma is perfect in everyway,shigace ta alfarma yayi,kayan jikinsa ma yafi na Lamidon tsada. Lamido kyau da charisma kawai zainuna mishi.
In short shidai yasan kowaye Rukayya zata aura acikin zaratan maza biyunnan toh tabbas tayi sa'a kuma tayi musu nisa.
Auwal da Lamido ba karamin tsarguwa sukayi ba ganin irin kallon da Zunnurain din keyi musu,ganin abun bana karebane se Lamido yayi gyaran murya wanda hakan yafidda Zunnurain din daga trance dinsa,baki na rawa ayayinda zufa tafara keto masa yace "..ye..ss yananan,yanzunnan ma yadawo daga masallaci yashiga ciki. Bismillah muje inraka ku gurinshi" Zunnurain yayi maganar ayayinda yafara tafiya cikin sauri inda su Lamidon suka mara masa baya suna mamakin behaviors dinsa. Shi kwata kwata Lamido yana daukan Zunnurain amatsayin Salim ne tunda Rukayya take bashi labarin Salim,seeing how nice he's always been to him inyazo gidan koda yaushe seyasama ranshi cewa Zunnurain din shine Salim.
A parlourn Kawu Sani Zunnurain yasauki Lamido da Auwal sannan ya karasa ciki danyasanar da Kawu Sanin isowan su. Koda yasanar da Kawu Sanin cewa yayi yana zuwa sannan yace yakira masa Fahad da Salim yace suzo sashin sa susameshi yanzu.
Zunnurain cewa yayi "toh Abba" sannan yayi ficewarsa cikin sauri,bashida wani buri alokacin daya wuce yaganshi a dakin Umminsu shiyasa koda yafita a sashin Kawu Sanin bezarce koina ba se sashin su Ummin. Fahad da Salim da akace ya kira kuma kiransu yayi awaya yafada musu sakon mahaifin nasu.
A parlour yasamu su Zaheera suna kallo "Kai kutaso kuzo" shine abunda yace musu ayayinda yashige dakin Ummin. Dasauri suka tashi suka bi bayanshi jiki na bari dandama jiran zuwansa sukeyi tun dazu sanin cewa shine zai kawo musu wani rahoto gameda zuwan bakon Abban nasu. Koda suka shiga dakin Ummi na sallah don haka sesuka samu guri suka zauna suna jiran ta idar, Zunnurain dubansu Aisha yayi sannan yace "Wai daman wannan shine Sir Isma'il din naku?" dagowa sukayi dasauri suka dubeshi, Zaheera tace "kaganshi ne?" Zunnurain yace "nadawo daga masallaci zanshigo gida kenan wasu samari biyu suka sauka a napep. I don't know the other guy anma dayan nasanshi yasha zuwa gidannan neman Rukayya so when I didn't recognize him shine yatuna min Sanda yake zuwa yace kuma sunanshi Isma'il ne" Aisha tace "wallahi shidinne aidaman seda nafada muku" Ummi dayanzu ta sallame sallah ko addu'a batayi ba tawatsa ma Aisha harara tace "ke dallah yimin shiru" sannan tamaida dubanta ga Zunnurain tace "Kai yakamarsa take?" take Zunnurain yashiga yimasu describing Lamido haryagama.
Zaheera tatabe baki tace "shidinne kuwa" Ummi da ayanzu tafara zufar da Zunnurain keyi Itama tace "Zunnu ka tabbata haka kamanninsa yake" Zunnurain yace "Allah haka yake Ummi,mutumin da bayau nafara ganin saba" Ummi tace "Kuma shi yacemaka sunanshi Isma'il?" dankuwa she really don't want to believe it even though gashi tabbas shidinne.
Zunnurain yace "shiya fadamin" Ummi tace "toh mekacemishi? Wayasani ma neman Rukayyan yazoyi like all times bawai abunda muke zato bane" Ummi tayi maganar tanama Zunnurain hararar Allah yasabai kwafsa musuba. Dukda halin da Zunnurain keciki seda yayi Yar dariya yace "hmmm Ummi kenan" Ummi tace "tambayarka fah nakeyi kanacemin Hmmm" Zunnurain yace "toh ai Ummi naga kinki karbar gaskiya ne kuma innace zanfada miki abunda yafada min toh tabbas sekinji abunda naji" Rai bace Ummi tace "Ina ruwanka da abunda zanji? Kaidai kafadamin mana" Zunnurain yace "toshikenan Ummi. Cemin yayi Abba yazo gani" tashi Ummi tayi daga zaunen datake sannan tafara safa da Marwa cikin dakin tana tunane tunane itakadai,can tadago takalli Zunnurain tace "dayace maka Abbanku yazo gani seme yafaru?" Zunnurain yace "of course I escorted them to his apartment" tsaki Ummi tasaki tana hararar Zunnurain tace "miyasa bakace Masa bayanan ba?" Zunnurain yace "Akan mi zanmasa karya bayan shi Abban dakansa yace yazo yasameshi yau" Ummi rai tace "bade kakyauta manaba gaskiya inbahaka ba miye amfanin gane shidinne?Aida tun alokacin daka ganeshi cemasa zakayi urgent tafiya tasameshi tunda babu wanda yaga zuwansa saikai" Aisha tace "yanzudai Ummi kwafsi anriga anyishi kiyi hakuri" Zunnurain yace "Koda nahanashi ganin Abbah yau wataran dole zasu hadu" Ummi tace "anma ai da kafinnan zamusan abunyi" sekuma tadafe kai tace "ninama kasa yarda shidinne gaskiya" tadago kai tadubi Aisha da Zaheera tace "dayarku tatashi tadauki tray takai musu ruwa da drinks daganan seku tabbatar min inshi dinne" cikin sauri Aisha da Zaheera suka tashi harsuna rige rige,daga karshe dai Zaheera ne tace ita zatakai dayake tagirmi Aisha dole Aishan tahakura takoma tayi zamanta.
***
Su Lamido basuwani Jima zaune a parlourn Kawu Sani ba yafito, bakaramin mamaki Kawu Sani yayi ba da ganinsu dankuwa basu yayi tsanmanin gani ba,their appearance wasn't what he realy expected anma daya tuna Zunnurain din Koda yazo yasanar dashi yayi baki ai bai Yi specifying ga bakin daga Ina baneba sannan bakon Rukayya aishikadai zaizo may be Basu biyuba,shine kawai yayi assuming manemin auren Rukayya ne don haka seyayi tunanin may be wadannan din bakin daya sabayi koda yaushe ne dasuke zuwa neman alfarma gurinsa a gida kokuma suna neman yayi guiding dinsu akan wani Abu. Seya karasa cikin parlourn fuska daukeda fara'a,akan three seater yazauna ayayinda Lamido da Auwal suka sake russunawa suka gaida Kawu Sani dukda kuwa daman akasa suke zaune.
Amsawa yayi yatambayesu ya hanya suka amsa da alhamdulillahi inda daganan kuma parlourn yadauki shiru dankuwa su Lamido suna tunanin Kawu Sanin ne yakamata yafara raising conversation din ayayinda shima yake jiran su sufara anma ganin sunyi shiru harnawasu dakiku seyasaki murmushi Yana dubansu,yace "Sede bangane bakin daga Ina baneba" Auwal ne yace "Daga Gombe muke" dankuwa Lamido tunda Kawu Sanin yashigo kanshi ke sunne a kasa,gabadaya yakasa kallon Kawu Sanin,wani irin nauyin mutumin yakeji.
Auwal yadan numfasa sannan yamaida dubansa ga Lamido yace "Na rako abokina gurinka ne Alhaji,shike neman auren Yarka Rukayya" ba Kawu Sani kadaiba har Fahad da Salim dayanzu shigowarsu parlourn were very shocked Jin abunda Auwal din yace,haka suka tsaya suka kasa zama sunabin both Auwal da lamidon dakalloh.
Abangaren Salim appearance dinsune yayi shocking dinshi kamar yanda yayi shocking Kawu Sani because this's what they've never expected inda Fahad kuma shi baima gane inda maganar ta dosaba,he just can't comprehend what's going on tunda bayida labarin batun auren. Hada one plus one yakeyi kawai a kwakwalwarsa danyagane wace Rukayya ce ake magana. Kawu Sani ne yayi karfin halin boye mamakinsa ganin yanda Salim da Fahad sukayi tsayen kan bakin nasu,yayi murmushi sannan yace "Allah sarki. aibanganekuba dayake nakanyi baki suzo gida ganina senayi tunanin sune kasancewar nayi tunanin shidin shikadai zaizo" Auwal da lamido murmushi kawai suka saki Jin abunda Kawu Sanin yace.
Yadubi Lamido fuska daukeda murmushi yace "toh ya sunan Dan nawa?" akunyace Lamido yace "Isma'il" Dede lokacin Fahad da Salim suka samu guri suka zauna wanda ganin yanda Auwal ketayi musu murmushi yasa Salim mika masa hannu suka fara musabiha,bayan sungaisa da Auwal din suka gaisa da lamido..
Kawu Sani yace "they're my two Sons" dubansu Lamido yayi yana murmushi yace "I'm Isma'il" Salim ne kadai ya iya maida masa murmushin sannan yace "and I'm Salim" take se Lamido yafara mamakin if this's Salim then who's the other guy? ganin bayida amsar tambayar seyayi saurin kawar da tunanin aransa. Fahad dai baiyi niyar cewa komaiba anma ganin gabadaya idanu yadawo kanshi bayan Salim da Lamidon sungama introduction sekawai yace "Fahad" yanayin yanda yayi maganar dakuma yanayin fuskarsa kadai zai nuna maka cewa shida Salim din mutane biyune mabanbanta a hali and definitely something is bothering him at the moment.
"And then he's Isma'il,shikeneman auren kanwarku Rukayya" Kawu Sani yayi maganar yana duban Ya'yan nasa maza biyun sannan yamayar da dubansa kan Lamido yace "Isma'il naji abokinka yace daga Gombe kuke,ku mutanen Gombe ne kenan?" Lamido yace "A'a ninedai Dan Gombe shi asalinshi Dan Bauchi ne,a Azarai ma yakeda zama rakoni yayi" cikin sigar zolaya Kawu Sani yace "Kace nan duk Yan gidane kai kadaine bare" dariya sukayi su ukun Auwal yace "shima yakusa zama dan gida insha Allahu ai" Kawu Sani yace "hakane. Allah ubangiji yazabi abunda yafi alkhairi" suka amsa da "Amin" duka,se yamaida dubansa ga Lamidon yace "Acikin Gombe kuke da zama?" Lamido ya gyadakai yace "Eh anma asalin mu Yan Kwami ne,aikine yakawo mahaifina zama cikin garin Gombe" jinjinakai Kawu Sani yana yar dariya yace "kace duk yamu yamu nedai kawai" dariya Auwal da Lamido sukayi ayayinda Salim kejin haushin how nice his father is being to the guest. Bangaren Fahad kuwa baisamasan mesuke cewa ba because yafita a duniyar su yashiga wata duniyar daban.
Kawu Sani yace "Iyi mana,mungudo daga kauyukanmu munfito birni neman kudi" Auwal na murmushi yace "ai in mutum yace zai zauna a kauyenne akwai matsala" Kawu Sani yace "matsala daya ko biyu. Allah dai yadafa mana kawai" duka suka amsa da Amin.
Lamido bakaramin dadin yanda Kawu Sanin yakemusu yayiba,it makes him feel relaxed,it gives him hope cewa everything will be alright insha Allah.
Kawu Sani yakuma kallon Lamido yace "a Ina mahaifin naka yake aiki Isma'il?" Lamido yace "a masarautar Gombe yayi aiki,he was the sarkin dawakai but he's late now" Lamido yakarashe maganar araunane wanda hakan yasa gabadaya Yan parlourn jikinsu yayi sanyi. Cikeda tausayi Kawu Sani yace