Showing 45001 words to 48000 words out of 213309 words

Chapter 16 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5872

abunda yahaɗamu Umma. koyau tare muka zauna dashi a Islamiya" Umma na kallon Hafiz tace "kunyi sabbin abokanaine?" Hafiz yace "bamuyiba Umma" Umma tace "shifah? baka ganinsa da sabbin abokanai?" nanma Hafiz yace "kullum muna tare a both Boko da islamiya Umma. nidai bangayayi sabbin abokanaiba" wannan karan cikeda tuhuma Umma tace "tare kuke skipping classes da missing test ɗin kenan?" cikin sauri Hafiz yagirgiza kai alamar a'a.

Umma tace "shikaɗai yakeyi kenan?" shiru Hafiz yayi baice komai ba, Umma tace "kayi shiru Hafiz?" jiki sanyaye Hafiz yace "Umma kinsan Lamiɗo bayason karatu daman tuncan" Umma tace "Tara Ƴan mata dayakeyi kumafa? dama tuncan yanayine?" cikin sauri Hafiz yace "Tara ƴan mata kuma?" Umma tace "Eh haka principal ɗinku yace. wai yana skipping classes yaje yana soyayya da Ƴan Mata" Hafiz yace "nidai ban taɓajin Lamiɗo na soyayya ba Umma. nadaisan yanada friends mata sosai kuma duk su suke binshi wallahi bashi yake fara kulasuba. Umma kinkuma san shi bayida wulakanci kowa nashine and quite sure nasan yana missing classes amma bada zummar yaje yayi hira dasu baneba. sune dasuka gane hakan shine suke zuwa su sameshi suyita hira to which duk baiwuce akan normal life ɗinmu bane ba bawai dasunan soyayya ba" hararan Hafiz Umma tayi tace "Kare abokin ka kakeyi kenan?" Hafiz da iyakar gaskiyarsa yace "wallahi ba ƙarya nakeyi ba Umma" Umma tace "shine kuma ni yake zuwa yasameni yacemin Yayi budurwa?" dariya Hafiz yayi yace "Umma sekace bakisan Lamiɗo ba? Yana faɗa ne danyaji bakinki kawai and nothing else" Umma tace "naji nakuma yarda anma you as a friend yakamata ace kana faɗa masa gaskiya bawai kazuba masa idanu yana abubuwan dabai dace ba inbahaka ba toh miye amfanin abotar daman? Inka faɗa mai bai ɗauka ba gidannan wurin zuwan ka ne daman sekazo kafaɗamin ni zansan matakin dazan ɗauka akansa" Hafiz yace "kiyi hakuri Umma za'a gyara in Allah ya yarda" Umma tace "toshikenan taji kaje. nagode" Hafiz yace "toh Umma se anjima kafin yafice agidan yaje yasamu Lamiɗo dake zaune kan dakali yayi tsuru tsuru da idanu yana tunanin wani laifin yama Ummarsa da Hafiz yajima har haka" Lamiɗo na kallon Hafiz cikin sauri yatashi tsaye yace "menayi Hafiz?" Hafiz yayi dariya yace "wallahi Principal ya kulla maka kulalliya gwanda kaje ka warware kanka yanzunnan" Lamiɗo cikeda damuwa yace "toh ai baka faɗamin menayiba,ta'ina zan warware kaina toh?" Hafiz yace "mekake ci nabaka nazuba? yanzu zanfaɗa maka ai" Lamiɗo yace "toh faɗamin inaji" take Hafiz yazayyana masa yanda sukayi da Umma kafin daga karshe Hafiz yace "kajeciki kasameta kasan yanda zakayi ka warware kanka nikaga tafiyata kuma nan gaba in kasake wani laifin dakaina zanzo in faɗa ma Umma tunda tafara zargin I'm not a good friend to you. Ina tsoron ranar dazatace zata rabamu" Hafiz yakarashe maganar cikeda zolaya.

Lamiɗo yace "kaidai zamuyi magana gobe. principal ɗinnan kuwa seyasan ya taɓa Lamiɗo da mahaifiyarsa alqu'an" daganan Lamiɗo yayi kwafa yashige gida.

A parlour yasamu Umma zaune danhar lokacin bata tashi daga inda take zaune ba ko bayan dasuka gama magana da Hafiz. Umma naganin yashigo parlourn tayi maza ta tsuke fuskarta. karasawa inda take zaune Lamiɗo yayi yazauna shima sannan yace "Umma I'm sorry" amma ko kallonshi Amina batayiba bare yasa ran zata kulashi,kamar me shirin yin kuka yasa hannu yakamo hannunta yasaka cikin nashi yace "yanzu Umma shiru zakiyitayi bazakicemin komai ba? your silent is hurting me more. gwanda ki dakeni,gwanda kiyimin duka akan laifuffukan danayi than keeping quiet sabida hakan yafi azabtar dani" Umma kwace hannunta tayi still batace masa komaiba.

Lamiɗo yasauke kansa ƙasa jiki sanyaye yace "Hafiz yafaɗa min komai Umma and I'm sorry for causing you alot of troubles but you should've atleast ask me kiji ta bakina. nasandai bakiyi trusting malaman makarantar mu kamar yanda kika yarda daniba" Umma dasai yanzu taga daman yimasa magana tace "ada kenan ba anma yanzu I've no any other option than to trust them over my Son" Lamiɗo yace "akan wannan laifin dasukace nayi yasa kika yarda dasu over ni?" Umma dai batace masa komai ba Lamiɗo yace "nasan nayi laifi daban bi umarnin ki ba,banyi abunda kikeso ba amma aini bantaba ɓoye miki komaina ba Umma,tunbayau ba kinsan banason karatu,nasha faɗa miki acireni a makaranta anma kinki bin abunda nikeso shiyasa nayi taking wannan step ɗin. batun Ƴan mata kuma da akace inadashi wallahi ƙarya akayimin. niban taba budurwa ba inbanda friendship dake tsakanina dasu, shiɗinma su suka nema, maganar hira da akace inayi dasu inasasu suyi skipping classes niban taɓa cewa watarsu tazo tasameni a Inda nake zamaba suda kansu suka fara bina Umma anma insha Allahu tunda haryakai ga ana zuwa ana tadar miki da hankali bazan sake ba. Kiyi hakuri kiyafe mun don Allah,fushin ki wallahi azabtar dani yakeyi" Umma kallonshi tayi sannan tace "Uhmmm! nidama nace banyafe maka baneba? yana iya dakai daman inbanyi hakuriba tunda kanuna kafi karfina,kafi karfin in faɗa maka kayi,kafi karfin kataimakamin incika ma mahaifinka burinsa nason kazama mutum kamar kowa" Lamiɗo dayagama gane Umma faɗa masa magana takeyi a fakaice yasashi cewa "wallahi Umma bahaka baneba" Umma tace "Hakane mana Lamiɗo. kuma tunda kanuna kafi karfina semu tattara mukoma *Kwami* kawai gaba ɗaya,kannen naka ma dasun kara wayau duk aure zanyi musu tunda konace suyi karatun zasu iya kinyi tunda sunga Yayansu ma bai maida hankali ba sabida haka kafara shiri,kazuba ruwa akasa kasha zakabar karatun Boko kaje kayi abunda ranka yakeso,inkaga dama ma kaje kacigaba da haɗa temple kana tara mata suna zuwa kallon kyawun da Allah yayi maka" daganan Umma tatashi tabarshi zaune gurin kamar wani gunki.

Tunda yake arayuwarsa bai taɓa ganin tayi fushi irin haka ba hakanan bata taɓa furta magana mai zafi irin wannan agaresa ba,akullum albarka take saka masa wanda furucin ta nayau ɗin yasashi gane cewa yakaita bangone,tarasa yanda zatayi dashine shiyasa tayanke wannan decision ɗin. Shi mutum ne meyi mata biyayya akoda yaushe, maikuma son sata farin ciki kullum da ko kannensa ne suka sata yawan magana harhakan yaja bacin ranta he's always the one that cheers her up anma segashi yau for the very first time arayuwarsa shine sanadiyar ɓacin ran nata. damuwarsa ayanzu baiwuce yazaiyi yagyara laifin sa ba,atake wata zuciyar tace "Lamiɗo kayi abunda takeso,kayi mata biyayya wannan shine kaɗai abunda zaisa tasauko daga dokin fushin datakeyi dakai" ayayinda wata zuciyar kuma tashiga raya masa "toh zaka iyan ne? Kaida kaƙi jinin karatun boko tayaya zaka iya cika mata burinta?" and the other part immediately says "Uwace fah. kawai dole hakura zakayi kayi ɗin koda kuwa bakaso,kwana nawane ma yarage kagama karatun baki ɗaya?" dawa dannan tunanin Lamiɗo yayanke shawarar sauke duk wasu makamansa nason kinyi karatu tareda niyar washegari zaigyara halinsa.

Haka ya koma zuwa makaranta as a changed person,yamadaina skipping classes bare har yaje inda yake ɓuya Ƴan Mata da abokanan banza suzo suna tayashi zama. A ranar yaje yasamu malaman da yayi missing test ɗinsu sukayi mishi makeup,damuwarshi ɗaya dukyanda yaso yamaida hankalinshi a aji don yagane abunda akeyi he always end up sleeping kokuma yafaɗa wata duniyar tunani sabida tsabar ranshi bayason abun. Kullum inzai tafi makaranta seyaje yagaishe da Umma anma bazata amsa ba hakan kuma bazai hanashi sake gaisheta ba inya dawo. Lamiɗo yadaina zuwa koda football ɗinda akeyi kullum yanma a unguwarsu ne,ya tsiri tayasu Jidda yin assignment ɗinsu na makaranta dukdan Umma taga canzawarsa anma abanza wannan yasa hankalinsa yayi kololuwar tashi,yashiga damuwa hakanan yadaina cin abinci sosai,duk yabi yarame cikin sati biyu dayayi yana wannan ladabin amma Uwartasa taƙi ko kallon sa bare yayi tunanin samun sassauci daga gareta kwana kusa. Hankalinshi bai kara tashiba seda su Jidda sukazo sunamai kuka kan Umma tace zasu koma *Kwami* dazama karshen watannan kuma tace dasun koma aure zatayi musu dukansu dan Allah yaje yabata hakuri kilan taji tunda shine favorite ɗinta kuma shi ya mata laifin daya jaza musu wannan matsalar.

Adaren ranar Lamiɗo yaje ɗakin Umman nasa yazauna gefenta sekawai yafara kuka,kuka irin me tsuma zuciyarnan datasa zuciyarta karaya lokaci guda. dole tasauke duk wasu makaman yaƙinta cikeda damuwa tashiga tambayarshi dalilin kukan nasa tace "Kaikuma goɗai goɗai dakai kukan mekakeyi Lamiɗo?" yanda tayimasa maganar bazata taɓa cewa fushi takeyi dashiba,she act as if nothing happens(Uwa kenan) wanda hakan yakara bama Lamiɗo kwarin gwiwa hakanan bebar kukan dayakeyiba har lokacin yace "Umma kiyi hakuri kidaina fushi dani don Allah" and she couldn't help it but to hug her only male Son,rungumeta yayi tightly yanata maimaita faɗin "Umma kiyihakuri kidaina fushi dani. Umma kiyi hakuri kidaina fushi dani don Allah. namiki alkawarin bazan sake disappointing ɗinki ba,zanyi abunda kikeso ɗin" cikeda tausayinshi Umma tace "yawuce Lamiɗo. kadaina kukan nan ya'isa haka kada su Jidda suji Yaya babba yana kuka" and for the first time he smiled tun bayan data fara fushi dashi.
yashiga goge hawayensa yana faɗin "ai in suka ga hawayennan duk sesun biyani kayana dan nadinga zugaki mutattara mukoma Kwami kenan" dariya Amina tayi tana mai tayashi goge gunji gunjin hawayensa tace "watodai yarannan karata suka kaiwurinka koh?" yace "A'a Umma bawanda yakawo kararki jinayi kuna maganar" Umma na murmushi tace "yimin shiru sekace bansan halinkuba daga kai harsu ɗin" Lamiɗo yace "toh Umma tunda kinsan halin mu kiyi hakuri kibarmu a birni karki maidamu ƙauye" yakarashe maganar cikin sigar shagwaba Umma tace "duk wannan zancensu ne banaka ba ni nasani. Kai da ko acikin kogo akace kazauna so far as akwai abinci babu abunda zaihana ka zama Lamiɗo" Lamiɗo yace "toh adaiyimana afuwa abarmu anan ɗin Umma" Umma tayi murmushi tana satan kallon kofar ɗakinta dantasan yaran nanan gurin laɓe sunajinsu tace "zanyi maku afuwa amma sekasa kowacce ta ciko maka plate ɗai ɗai da abinci takawomin nayi feeding ɗinka" aikuwa dasauri suka fito daga laɓen dasukayi suna faɗin "Umma zamu kawo wallahi" daganan kuma suka ruga aguje sukayi kitchen daniyar zuwa ɗebo abincin inda suka bar Lamiɗo da Umman nasu namusu dariya.

Basma ce tafara kawo nata sannan Jidda sannan Salma, Lamiɗo na kallonsu duka yace "wato laɓe kukazo kuna mana nida Umma na koh?" Jidda tace "Yaya dolece tasamu yin laɓen nan wallahi" Lamiɗo yace "Aiko seku shirya komawa Kwami tunda dukanku kunga hawayena" Basma dasauri tace "nidai bangani ba Hamma" Salma tace "Nimadai banganiba Hamma" Jidda data rasa yanda zatayi ta kare kanta tace "oh so kuke kuce nikadai nagani kenan komi?" And they all laughed at her reaction.

Lamiɗo yace "uwar tsarguwa kwantar da hankalinki babu mai komawa Kwami dazama sede zuwa hutu" tuni jidda tashiga washare baki tana murna. Lamiɗo yamaida kallonsa kan plates har uku da duka ke makare da abinci yace "nashigesu inazankai duka wannan abincin?" Umma tace "duka meals ɗinka dakayita missing suka haɗo maka anan duk seka cinyesu yau" pity face Lamiɗo yayi yace "Umma Allah yamin yawa sede inci ɗaya yanzu, ɗaya anjima, ɗaya gobe" dariya Umma tayi sannan tadubi Basma tace "Basma tashi kiɗauko tray mujuye duka muci abincin tare" dasauri Basma tafice a ɗakin Lamiɗo nafaɗin "Daman nayi kewar cin abinci tareda ku wallahi".

Bayan sungama cin abincin ma seda yataimaka musu sukayi assignments ɗinsu sannan suka danyi kallo kafin kowa yatafi makwancisa daga baya.

Tundaga nan Lamiɗo yake kokari gurin ganin baisake ɓata ma Ummarsa raiba,daman akan karatune kuma yadaina laifuffukan daduk akace yanayi a daɗin. Karatunne dai haryau bayason sa kuma baya tunanin zai taɓa sonsa arayuwarsa,yanayine kawai don ya faranta ma Umman nasa rai dukda kuwa bayamaida hankali yagane ɗin,yanadai copying note da dictation in malami nayi sabida shine kaɗai Savior ɗinshi dankuwa inzasuyi test aranar dazasuyin yake ɗaukan note ɗinshi yakaranta yashiga yayi test ɗin, inkuma exams ne se ana gobe za'ayi exams ɗin ze ɗauki littafinsa ya kakkaranta yaje yarubuta and luckily he always pass with average scores ahaka yasamu yagama secondary school ɗin. Sanda Umma tamai maganar jamb kuwa baitada hankalin shiba dan ya ɗauka jami'ar ma kamar secondary school ne,zaiyi mata yanda yakeyi a secondary school ayi awuce gun kawai anma seyaga abun yasha banban da yanda yake tunani daya samu admission,yayi registration ya fara zuwa lectures. Lecture se ayini anayi,dawannan malamin yafita wani zai shiga hakanan kowanne yazo ze dibga musu uban handout yakuma ce sukaranta unlike secondary school dabai wuce amusu dictation ɗin pages huɗu ba arana na gaba ɗaya courses ɗin. tun Lamiɗo naganin abun kamar wasane daga baya zasu samu sauki anma sema abunda yayi gaba wanda hakan yasa yafara gajiya,yaji bazai iya jurewa ba. Seyaje wannan lecture ɗin yaƙi zuwa next one hakadai,daga bayama yazo yadaina zuwa sosai,seyayi kwana biyu bai shiga ajiba sede dayashigo makaranta yawuce hostel ɗakin wani abokin shi dake zaman hostel ya sharara barcinsa in lokacin tashi yayi yatafi gida abunsa har akazo aka fara continues assessment wanda se alokacin yaje yasayi handouts ɗinda akayita jibga musu. In za'ayi test se ranar daza'ayi zaikaranta kuma baya taɓa iya gama karantawan sabida yawanshi ba iri ɗaya bane dana secondary school anma ahakan zeshiga rubuta test ɗin with the hope za'ayi tambaya a Inda ya karan ta ɗin anma seyaga abunfa bahaka baneba. haka yayi tayi har aka gama test aka fara kawo scripts duk seyaga yayi failing gashi lokacin exams yariga yazo babu lokacin yin karatu na haikan mani'in kuma ko akwai ma Lamiɗo baya tunanin zai iya,na secondary school da da yake kaɗan ma kawai kuke zuciyar sa yakeyi yayi ahaka barekuma yanzu da abun yafi karfin tunaninsa dole ahaka yarubuta exams ɗin sukayi hutu.

Da akadawo kuwa aka manna result segashi a probation. hankalinshi ya matukar tashi alokacin bawaidan damuwarshi Umma anma ahaka dole yaje yafada mata halin da ake ciki anma sebata masa faɗa ba tace yadage kawai next time dan daman tunda yasamu admission ɗin Hajiya Hadiza tacemata course ɗin nada wahala kuma ana faɗi sosai shiyasa koda yayi failing tayi masa uzuri,bata taɓa kawowa ranta Lamiɗo yakoma gidan jiya baneba tunda tana ganin effort ɗinshi akullum,yana zuwa makaranta,yana kuma tsayawa karatu har dare. wannan rashin damuwar da Umma tanuna yasa second semester ɗinma yacigaba dayin abunda yakeyi,acewarsa tunda Ummarsa ma tasan makarantar da wahala zata cigaba dayi masa uzuri harzuwa lokacin dataga yakasa ta haƙura tacireshi.

Suna gama session ɗin farko da result yafito yaga anyi masa step down bewani damuba sabida yasan Umma zata sake yimasa uzuri,ahaka aka dawo next session wanda alokacin yama dena attending lectures kwata kwata,sede yashigo yagama yawonsa in lokacin komawa gida yayi yakoma gida,haka in lokacin Test da exams yagabato seyace ma Umma kwana zaiyi a school yayi karatu and she'll allow him wanda inyazo ɗin bewuce yayita yawace yawace da friends ba sekuma duk inda dare yayi yaje hostel yakwana wataran kuma yagudo gida ya tsallako ta katanga yashige ɗakinsa ta window yayi baccinshi peacefully,assusuba nayi kuma zai sake ficewa batare da kowa ya sani ba yakoma makaranta wanda ananne zeshiga neman gurayen ajinsu yaroƙi alfarmar su shiga jarabawar tare dan ya zauna a bayansu su goyashi,inkuma baisamu ba haka zai rubuta paper yafito abunsa with the believe cewa definitely cewa course ɗin zata dawo masa.

Atakaice dai Lamiɗo saubiyu yayi 100 level,200level ma haka wanda seda yazo sakeyin na biyun ne suka haɗu dasu Auwal suka kulla abokantaka ta dalilin Hafiz dashi daman baisamu admission dawuri ba sabida failing jamb dayayi tayi abaya. haɗuwa dasune yasa perception ɗinsa na akore a makarantar yafara canzawa,yaji shima bayason asake barin shi abaya yanason gamawa tareda su yahuta da wahalar bokon tunda haryau Umman ma batada niyar cewa yahakura da karatun. Inda kuma Allah yataimakeshi Ƴan clique ɗin su Hafiz ɗin duk sunada ƙoƙari,basu kuma da baƙin hali sesuke goyashi subashi amsa a hall yayi passing kamar su.

Bangaren Umma kuwa dukda shekarun da Lamiɗo ya ɓata a makaranta yana fama bata taɓa nuna masa damuwarta ba dukda kuwa abun na matukar damunta arai,seeing his efforts, perseverance and dedication yasa takeyi mishi uzuri akullum,she fully believe cewa Lamiɗo yana karatun haikan mani'an tunda yana nuna efforts ɗinsa a fili shiyasa kawai takeyi mishi addu'a kawai,akullum yama ta korafin wahalar jami'a setayi ta encouraging ɗinshi dacewa wataran zaizama labari in Allah yayarda shikuma Lamiɗo tsoron ya ɓata matarai tayi fushi dashi irinna da yasa yakeyi mata wannan karyayyakin batareda tasaniba. Umma a gabadaya rayuwarta flaws biyu tasani a tattare da Lamiɗo wanda takeda yakinin ta magance ɗaya ayanzu saura ɗaya. ma'ana ta magance matsalar rashin son karatun sa saura taurin kansa dakuma rashin hakurin sa akan abunda yakeso. Lamiɗo inyana son abu he always go for it,he can take any risk for what his heart desires,babu ruwanshi da consequences ɗinda ke cikin abunda yakeso ɗin,babu ruwanshi da abunda mutane zasu ce,hakanan baya hana kanshi abunda yakeso wai don yana tsoron wani. Lamiɗo bayabin abu a saru saru,baya neman shawarar kowa inyana son abu he just go for it,a believe ɗinshi babu wanda zai iya yimashi abu inba shiba,a believe ɗinshi if you want something now just give it your efforts and get it right instant without thinking about the negativity. yakanyi mamaki inyaga mutane na haƙurar ma zuciyarsu abunda takeso sabida maganar mutane, sabida consequences ɗinda ke cikin samun abun,sabida negativity ɗinda ke cikin samun abun,sabida risk ɗin dake cikin samun abun but to him waɗannan duk baswa cikin agender ɗinshi. Indai yanason abu bayama tunanin wasu risk da consequences sema achievement ɗinda zaisamu indai ya mallaki wannan abun hakanan indai yaƙi abu toh yakishine. His only weakness is his love for his Mother shiyass yake mata karya akan abubuwa guda biyu,akan karatu dakuma *Maimunatu*. His only girl friend,yarinyar da'ita kaɗai ce taciri tuta cikin Mata dukda kuwa irin crushing dinda Yan mata masu aji,kudi dasauransu keyi akasa,ita kadai yagani yaji tayimasa. Kawar Basma ce,ajinsu daya a Islamiya kuma tana yawan zuwa gidansu gurin Basma wanda ananne yaganta,shi babu abunda yaburgeshi a ita irin kamun kanta dakuma zakin muryarta,mata da dama suka kalleshi susake kallo amma banda Maimunatu wanda tunranar farko dayaganta agidansu yaji taburgeshi,bugu da Kari yazo yaji zakin muryarta topha daganan yadaura aniyar seyayi dating dinta amma bazai taba bari Basma tasaniba sabida yasan gulmarta da iyawarta, bakaramin aikinta bane tafada ma Ummansu Kuma shi bayason Umma tasani tunbayan incident dincan dakuma lura dayayi bataso yanayi mata hirar budurwa,tafison seyagama karatu shiyasa yabi tahanyaar Yar hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login