Showing 183001 words to 186000 words out of 213309 words
ake tsintar suba" jinjina masakaina nayi ahankali cikeda gamsuwa,cikin sheshekar kuka nace "Nagane Allah ..." cikin gatse yace "Kadama kiganen. kifita kibarmin motana zantafi ni" araunane hakanan cikeda hope nace "Ka hakura kenan?" wannan Karan idanunsa dasukayi jazir yazubasu akaina sannan cikin tsawa yace "I said get out of my car......! kigode Allah ma daban fadama Abba abunda kikayi ba. I'm just giving you the taste of your medicine myself" daganan seya shiga kokarin tada motarsa wanda hakan yasani saurin bude motar na fita Ina kuka mai tsuma zuciya......
Bantaba sanin Yaya Salim yanada irin wannan zuciyar ba seyau. Haka nanufi hanyar hostel ina kuka nikadai ayayinda maganganun mu da Yaya Salim yadinga dawomin cikin kwanyana daya bayan daya. "Not everyone is to be trusted Rukayya. And Yayun bawai akan titi ake tsintarsu ba haka kawai" wadannan kalaman nasa su suka fi lingering a kwakwalwana ayayinda natuna cewa Yaya Lamido ma ba blood Brother na baneba. Haduwar hanyace kawai tasa muka shaku dashi harma nake ganin wasuma Inna hadu dasu they'll treat me as he does.
Sena tuna Yaya Sajeed ma ai tunda nahadu dashi he's done nothing to me than good,betaba min abunda zaisa inyi zarginsa ba kokuma inji tsoron yin alaka dashi. He's so nice and jovial like Yaya Lamido wanda hakanne yasa nima nasake dashi,toh anma kuma guduwar dayayi ranar shine yasamin ayan tambaya akansa harma nake ganin kamar Yaya Salim din might be right. Toh anma will Yaya Lamido actually do thesame idan situation irin haka yafaru?wannan shine tambayar dana shiga yimakaina inda take kuma sena shiga girgiza kaina nikadai ayayinda zuciyata ke rayamin "he'll never. Yaya Lamido bazai taba guduwa yabarni ba dan anganni dashi kamar yanda Yaya Sajeed yayi. Infact shida yakeson sanin family nama gabadaya dukda ma yasan few daga cikinsu,shida baiki yadinga zuwa Gidan Kawu Sani gurina ba dukda yasan halayensu nine kawai nake taka mishi birki. Koh kafin atafi hutun midterm break dinnan seda yacemin "Rukayya anya zan iya jira har kwanaki goma bangankiba? Kinsan yanzu munsaba sosai koh? I'm attached to you. Not seeing you for 10 days will be very hard on me. kozan kara kwanaki anan kafin inwuce Gombe inzo gidan Kawunki mugaisa sabida kwanakin dazanyi bangankiba ya ragu?"
Nikaina alokacin dayayi wannan furucin naso ace zan iya cemasa eh, because I'm also attached to him and I know I'll miss him more anma consequences dinda ke cikin yin hakan yasani yin fata fata da zancen atake. dukyanda yaso nayarda kinayi doledaga karshe ya hakura kan zamu hadu in andawo anma segashi nakara har kwanaki uku akan kwanakin hutun da aka bamu. Nasan babu irin nemana dabaiyiba and he must be missing me way too much kamar yanda nima nayi kewarsa. Take senayi fata fata da maganar Yaya Salim nacewa dayayi ba'a tsintar Yaya akan titi ayi claiming cewa shidin Yaya ne tunda gashi Allah yahada ni da Yaya Lamido kuma nagamsu dari bisa dari cewa yafiyemin wasu dubban Yayun ma dana hada dangi dasu.
Tunanin yau a misali Yaya Salim yasan da Yaya Lamido zai iya cewa zai rabani dashine yashigeni wanda hakan yasamin fear sosai. Hakanan nashiga godema Allah dakoh a subutar baki bantaba bama Yaya Salim din labarin Yaya Lamido ba anma kuma nadau alwashin Sena bama Yaya Lamido labarin fushin da Yaya Salim yayi dani sabida Yaya Sajeed dakuma abubuwan dasuka faru adan kwanakinnan din. Bawai don Ina shakku akansa ba sedan inaganin kamar zai iya bani shawarar yanda zansa Yaya Salim yasauko yadaina fushi dani inmun koma gida.
***
Lamido tunda yatafi Gombe Umma tatarashe da maganar kosun daidaita da Rukayya inda yace mata a'a aishifa ko maganar ma baiyimataba. Umma bakaramin baci ranta yayiba,yace "Akan wani dalili? Mekake jira da bakayi mata maganar ba?" Cikin sanyi Lamido yace "Umma naga kamar akwai sauran lokaci ne. kwata kwata yanzun hutun midterm break sukayi zamu koma akarashe term din and I'll get the opportunity to talk to her within that period of time" tabe baki Umma tayi tace "Kaine dai kake ganin akwai lokacin kuma inasonkasani muddin kakuskura kadawo mun gida karshen zango batareda kun daidai ta da Rukayya ba toh tabbas zancema Basma tama nata manemin magana yaturo gida dandama shi ita yake jira,Kuma dolenka kana gama service kafita harkar Rukayya tundakai baka daukan shawara" Lamido seyayi murmushi yana jaddada irin kaunar da Umman kema Rukayya farat daya daga jin irin halin rayuwar datashiga,yace "karki damu Umma. Insha Allah bazan watsa miki kasa a idanuba. Nikaina baki kaini son in tabbatar cewa Rukayya tawace kadaiba,baki kaini son incireta daga kungin gidancan indawo da'ita gurinmu yanda zata dinga samun walwala kullum ba. I'm just holding back sabida wani fear danake ji,I just want to have some courage ne kafin inyi confronting Rukayya" harara Umma ta watsa masa Jin kalaman nasa sannan tace "toh marar kunya Baban soyayya" dariya yasaki sannan yarungume Umman yana fadin "kefah nake fadama Umma bawaniba,Kuma inban fada Miki abunda keraina ba waye zanfada ma?" Umma na Yar dariyar tace "Bawani tunda bakaji kunyar fada agabana bama babu inda zakaji kunyar hidi" cikin nishadi yace "ohhh Ummana...yanzu daban fada dinbama cewa zakiyi bana nuna damuwata akan Rukayyan. Danna lura yanzu itace tagaban goshinki"
Umma tabe baki tayi tana dariya ayayinda tature shi daga jikinta tana fadin "Kaikasani dai. Nidaga ni godai godai kazo kawani shigemin jiki kamar jariri" tayi maganar ayayinda tayi nasarar tunbuke shi daga jikinta tatashi tanufi dakinta. Yajima yana tsaye yanabinta da kallo harta shige daki fuskarshi dauke da murmushi kafin shima yanufi nashi dakin. A saman katifarsa yakwanta bayan yashiga dakin yana sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya. Tunanin tayaya zaisamu karfin gwiwar tunkarar Rukayya da maganar soyayyar sa gareta yakeyi dakuma maganar aurenta dayakeson yi kwana kusa. Bawai bayason furtawa baneba shikawai tsoron sa wace irin amsace zata fito daga bakinta,bayason tayi misunderstanding dinsa wanda yake ganin kamar zata iya gudansa idan hakan tafaru. Sau.
tari kafin ataho midterm break dinnan yasha attempting yayi Mata maganar insuna hira anma seya kasa,se bakinsa yayi nauyi yakasa furta abunda keransa. Kuma duk wannan din bakomai bane face fear,fear din Rukayya ta kaurace Masa.
Anma sede yasan yanzukam karyarsa takare,dole inya koma yasan nayi kafin ayi hutu tunda Umman tadage kuma haryanzu tanakan bakanta nafa sai antaimaki Rukayyan kwana kusa basai anbari yakai wani lokaci ba. Koda midterm break yakare zaikoma sede Umma tasake jaddada masa kan maganar Rukayyan yakuma ce insha Allah zaiyi Mata magana. Baigaji dazaman gidaba dankuwa yasan inya koma zaiyi kewarsu anma son ganin Rukayyan da irin kewarta dayayi bazai barshi yakara wasu kwanaki agaba ba don haka tunranar da Yara ke resuming yashirya yakoma shima.
Ko staffquarters baiwuce ba yadire kayansa a staffroom da zumar seyaga Rukayya sannan yatafi gabadaya. Haka yatafi inda Malamai ke checking dukda kuwa baya da ra'ayin yin checking din,baya kuma cikin committee din wadanda keyidin dukwai kawai danyaga dawowar Rukayya anma shiru baiganta ba bare yan uwanta har aka gama amsar dalibai ranar. Haka yatafi staff quarters da tunanin may be sunrigashi isowa suna hostel anma sede koda yadawo dadare ya aika hostel anemo masa ita se akace bata dawoba. Washegari ajinsu yaje inda yatabbatar dagaske bata dawo dinba kuma rashin ganin Sadiya seya tabbatar mishi cewa dukansu ne basu dawo ba ba ita kadaiba bare yayi tunanin tana cikin wani haline. Haka yinin ranar ma akayi checking dashi amma har aka sake tashi su Rukayya basu dawoba. Washegari ma haka,arana na ukun ne yagama sama ranshi indai Rukayya bata dawo ranar ba toh tabbas Sunday da sassafe zaikama hanyar Bauchi yaje yaji koh lafiya because yafara loosing mind dinsa, he's having weird thoughts dukda kuwa bawai itakadai dince bata dawoba harma da sauran Yayan kawu Sanin.
Gashi yatambayi Aziza Koh tanada wata masaniya akan rashin dawowan nata inda tace masa wallahi batasaniba,ita ai batama communication da Rukayya in anyi hutu sede in andawo makaranta su hadu tunda Rukayyan batada waya. Babban buli ne kadai tataba zuwa kuma Rukayyan batazuwa kauyensu hutu a midterm break se lokacin ainahin hutu so batajeba. Break dinda yatafi lokacin Sallar Azahar ne sebai dawo dawuri ba,yazauna jiran lokaci yayi yakoma se bacci yayi awun gaba dashi bashi yatashi ba se wuraren hudu na yanma. Toh awannan tsukukin lokacinne su Rukayya suka dawo harma baisamu sun haduba.
***
Sanda nagama kukan abunda yahadani da Yaya Salim dakuma tunane tunanena sena tashi nayi sallan la'asar nashiga kimtsa corner dinmu,nagyara gadona nayi masa shimfida,na gyara lockerna najera duka provision dina aciki sannan nafidda duka dattin cikin corner nashare shi fes. Alokacinne kuma Aziza tafado min arai,Sena fara tunanin kota dawo? dukdama nasan abu mai wuyane ace bata dawo dinba dankuwa ita mutum ce da batacika kara hutuba. Hijabina nadauka nasaka daman bancire uniform din jikinaba sannan nanufi hostel dinsu.
Sanda na'isa hostel dinsu da sallama nashiga dakinsu. Aikuwa da gudu tafito daga kwanarsu *Halima* class mate dinmu tayo kaina muka rungumi juna cikeda farin ciki. dagowa tayi baki sake kamar wanda akayimata albishir da kujerar makka haka fuskarta take nuna farin ciki sakamakon dawowan nawa. Nima kusan hakan nakeji because she's a friend da dole kowa yake zaune da'ita yayi kewarta insuka Jima basu haduba.
Kallona tashigayi daga sama harkasa tana dariya "Yan Mata yaushe agari?" Se nace "Dazunnan nadawo wallahi. kukam harkun tsufa a makaranta Koh?" Jan hannuna tayi muka nufi kwanarta tana fadin "kibari kawai,bakiga harmun fara furfuraba?" sekuma muka kwashe da dariya.
Akan bunk dinta muka baje,tace "Kullum senaje hostel dinku kozanga kindawo anma shiru. ga Yaya Lamidon kima duk yadamu,kullum muka hadu seya tambayeni Koh kindawo hakanan yakasa ya tsare agurin checking yana jiran isowar ki. Incedai kunhadu a bakin gate?" Aziza tayimin tambayar tana kallona. Girgiza mata kai nayi Ina blushing sannan nace "Haba? Aiikuwa bamu haduba" kallona tashigayi fuskarta cikeda mamaki tace "Dagaske kike baku haduba? Ko dazu dasafe naganshi agurin checking a admin fah kuma da bakinshi yacemin jiran dawowan ki yakeyi" nace "Allah bamu haduba. Kuma dayakema during break time na Malamai muka iso,seda muka dan jira suka dawo sannan akayi checking dinmu" Aziza tace "toh inaga baikai ga dawowa daga break ba akagama muku checking din shiyasa baku haduba" seta karada "kozaki koma kidubo inyana nan? nasan by now yanacan yana zuba idanu" dukda inason ganinsa kuma nayi kewarsa sosai senace "A'a kibari seda dare kawai" dangabadaya a gajiye nakejina bana tunanin Zan iya fita,moreover banason inkatse masa aikinsa.
Aziza tace "inkuma baishigo cikin makaranta dadaren bafah?" Nace "shikenan mwa hadu gobe" dukda kuwa jikina yana bani babu yanda za'ayi yaki zuwa nemana sanin cewa shima baidawo gurin checking din dawuri ba. Aganina yakamata yayi tsanmanin zan iya dawowa awannan dan tsukukin kafin yadawo tunda ai nama Jima agurin. Aziza setace "toh shikenan" haka muka cigaba da hiranmu wanda duk yawanci akan abubuwan damukayi engaging kanmu a hutun ne. Se dare nakoma hostel dinmu aikuwa banjima dashiga dakinmu ba Yaya lamidon ya aikoh a tambaya ko inanan.
Murmushi nasaki sannan nacema yarinyar taje tace "inanan Ina zuwa" dayake junior tace setace "toh Sister Rukayya" daganan tafice daga dakin namu inda nikuma nashiga shirin tafiya gurin Yaya Lamidon. Abakin masallaci nasameshi zaune yana jirana,Yana ganina yasauke wani nannauyar ajiyar zuciya tareda sakin lallausar murmushi.....
Tunma kafin inkara inda yake yashiga cewa "Yarinyar nan sokike ki kasheni daraina Koh? Meya hanaki dawowa dawuri?" Dariya nasaki ayayinda nakarasa gefenshi nazauna inajin wani irin sanyi araina na musamman sakamakon ganinshi danayi sannan nace "bagashi nadawo yauba" wara idanu yayi sannan yace "aww hakama zakice? Ke kinsan whalar danasha kuwa na rashin ganin ki dabanyi ba kwanakinnan?Wai tukunnan ma meya hanaku dawowa?" yasakeyimin tambayar dayamin dazu.
Ahankali nace "Ummi ce taroka mana Kawu Sani tace mubari seyau danko mundawoma ba lallai afara serious class ba se next week" Yaya Lamido yace "Aikuwa da baki dawo yauba sede kuganni a Bauchi gobe" dariya nasaki batareda nadau maganarsa seriously ba, nace "Habadai..." Baki sake yace "Awww kina ganin kamar wasane koh?" seyayi kasa da murya,yace "Yarinyar nan it seems like kamar nikadai nayi kewarki ke bakiyiba" cikin sauri nace "Allah nayi kewarka Yaya Lamido" yace "shine dakikazo baki nemeni ba saidani na nemeki" marairaice fuska nayi sannan nace "kayi hakuri. nasan zaka nemeni when you're free shiyasa banma fito dayanman ba" Yaya Lamido yace "toh don't do that again. Koyaushe kikeson ganina just look for me, I'll always be free indai akanki ne Naaanaa..." yanda yayi maganar kadai zainuna maka iyakar gaskiyarsa yake fada,sekawai nafara blushing.
Tunawa danayi bangaidashi ba yasani cewa "Ina wuni?" Yaya Lamido yace "Lafiya Lau Nanaaa" nace "Ya kabaro su Umma, Yaya Basma,Yaya jdda da kawata?" Yana murmushi yace "Duk lafiyansu kalau sunce ingaida musu ke" fuska daukeda murmushi nace "Ina amsawa" ayayinda nakejin kaunar yan gidansu nakara samun guri cikin zuciyata..
Nace "tsaraba ta kuma fah? nasan sunbaka tsaraba kakawomin suna Ina?" Yar dariya Yaya Lamido yasaki "cab yarinya kin makaro. Aituni nacinyesu" tsuke fuska nayi lokaci guda tareda tura baki gaba sannan cikin sigar shagwaba nace "kut....nidai vazan yarda ba kabiyani kayana kawai" zubamin idanu yayi yana kallon yanda nake masa shagwaba,yana dariya yace "aifah sekiyi. hukuncinki nakin dawowa da wuri kenan" "aikuwa sena fadama Umma cinyewan dakayi" nayi maganar inasake kyabe baki.......
Yaya Lamido cikin sauri yace "Rufan asiri wasa nike miki inba so kike Umma tayi gunduwa gunduwa daniba intaji labarin nan. Tsarabar ki na staffquarters bani da tabbacin kindawo shiyasa ma bantaho dashiba. abincin da Umma tabani inkawo mikinedai tun ranar muka cinye nida Auwal sabida gudun karya baci"....
Cikin Jin dadi nace "Thank you. Na abincin kuma nayafe muku" seyayi dariya,yace "toh ya gidan Kawunki? Hope no one maltreated you during the break?" gyada masakai nayi ahankali.
Yana kallon cikin idanuna yace "Are you sure?" sena saki murmushi atake nace "Am very sure" seyasauke wani nannauyar ajiyar zuciya yace "toh bani labarin holiday dinki? How did it went? I want to know everything"......
Dazance masa nothing special sekuma labarin Yaya Salim da abunda yamin yafadomin arai. Cikin sauri nace "I've a gist Yaya Lamido" cikeda zumudi yace "I'm all ears" dariya nama yanda yadawo da gabadaya attention dinsa kaina sannan nafara basa labarin haduwata da Yaya Sajeed nafarko dakuma baci da ran Yaya Salim din yayi ranar,nafada masa second haduwar mu dakuma irin zuwa dayakeyi islamiya yana ganina harzuwa jiya da Yaya Salim yasake kamamu kafin daga karshe nayi fuskar tausayi,kamar wata meshirin fashewa da kuka nace "nasan nayi laifi nakuma gane kuskurena. Ni yanzu damuwana baiwuce fushin da Yaya Salim yakeyi dani ba. Bansan taya ya zanshawo kansa yasauko ba. Don Allah kabani shawara Yaya Lamido,mezanyi yasauko yadaina fushi dani? he's the only nice Brother i've in that house" nayima Yaya Lamido maganar cikeda hope anma maimakon insamu amsa maidadi daga bakinsa senaga fuskarsa tayi kicin kicin,idanunsa suncanza launi yace "Oho ......" "oho Kuma?" Nayi maganar jiki sanyaye ayayinda natsaya Ina kallonsa dankuwa bantaba tsanmanin irin feedback dinnan daga bakinsa ba....
Yaya Lamido seya dauke idanunsa daga gareni,cikin wata iriyar muryar datake nuna ransa abace yake yace "Toh mezance miki Nanaaaa? If I were in his place I'll do thesame....infact worst than this ma"
Take idanuna suka ciko da kwallah,araunane nace "Sabida miyasa?" Yaya Lamido dawo da dubansa yayi gareni wannan Karan yace "watoh haryanzu baki gane kurenki bakoh?" Nace "Nibanga laifin Yaya Sajeed ba Yaya lamido,he's nice to me just like you're. Aibunshi daya nagani guduwan dayayi sanda Yaya Salim ya cakumeshi baitsaya yayi defending dinaba"....
"Auu hadani ma kikeyi da mahaukacin yaron can?" Yaya Lamido yayi maganar a hassale hakanan idanunsa nanuna wasu abubuwa dana kasa gane menene anma dukda hakan sebanyi kasa da gwiwaba, trying to defend myself nace "Bahada ka nakeyi dashiba Yaya Lamido. nagadai yanda muka hadu dakai akan titi haka shima muka hadu,I gave him a chance just because nayi tunanin he might be someone like you,someone that'll turn into my family kamar yanda kaikazama family na ayanzu" kawai senaga Yaya Lamidon yatashi daga zaunen dayake zaitafi cikin sauri nariko hannunshi ayayinda nasaki kuka mai sauti.....
Cikin karyayyar murya nace "Kaima guda na zakayi kadaina min magana don na kula Yaya Sajeed?" ture hannuna yayi daga cikin nasa wanda hakan yasa nayi tunanin tafiya zaiyi yabarni anma da mamakina senaji yadawo yazauna agefena. Munfi mintuna uku shiru kafin yajuyo yakalleni,araunane yace "toh kukan ya Isa haka Mana" dago da jajayen idanuna nayi nadaura akansa nace "miyasa dukanku bazakuyimin uzuri ba kuke hauhawa akaina kuna fushi? Tunda bakwaso inaganinsa nace bazan sake ganinsa ba tunda bakwaso ba shikenan ba?" Nakarashe maganar ayayinda nakuma fashewa dawani sabon kukan.
"It's okay.... Kidaina kukan toh don Allah ya Isa haka" Yaya Lamido yayi maganar araunane amma dukda haka bandaina kukan ba. Haka yashiga rarrashina Yana bani baki harsaida nadaina kukan sannan ahankali yace "Nanaaa bawai muna nuna bacin ranmu haka kawai baneba. We're trying to show you abunda kikayi bakiyima kanki adalciba baneba. Not everyone can be trusted this days..... bakowane zaice yanason alaka dakeba ki yarda farat daya, bakowane zece kishiga motar sa kishiga ba,bakowane zece yanason yazama Yayanki kiyarda ba. wasu will just use innocence dinki su yaudareki subar ki da tabon da bazaki iya goge ma kanki ba dukdama ba fata mukeyiba,anma ai bature yace "Prevention is better than cure Koh?".....
Gyada masakai nayi ahankali sannan cikeda curiosity nace "Amma toh yazanyi insan cewa mutum mutumin banzane bana kirkiba farat daya? Ba dole Sena Saba da mutum ba sannan zansan asalin halinsa kafin inyi deciding ko mutumin kirki ne koba na kirkiba,kozanyi alaka dashi ko bazanyiba" tambayana tadaure kan Yaya lamido seda yace "toh Naaanaaa miss curious..." Sannan yace "toh wai ma miye amfanin tara bare kice zakiyi alaka dasu? Is it a most? I mean someone like namiji mezai hadaki dashi a kankantar shekarun kinnan" cikin sauri nace "Ai cewa yayi yanason zama abokina shine nace masa ba a abokan taka tsakanin mace da namiji kuma soyayya ma nayi kankanta. Shine yace zaizama Yayana nikuma sena yarda" dafe Kai Yaya Lamido yayi cikeda desbelief sannan yace "toh waya gaya miki Yayun daga sama ake tsintarsu kawai? Wayagaya miki kowama Yaya ake daukanshi batareda anhada dangantaka dashi ba?" innocently nace "Gashi kaima bamu hada dangiba kuma Kai Yayana ne Yanzu" Yaya Lamido shiru yayi. Nadan wasu dakiku,inaga baiyi tsanmanin irin tambayar nan daga bakina ba.