Showing 39001 words to 42000 words out of 213309 words
sukuni,somewhere somehow zuciyarshi nabashi something is wrong. haka kawai Rukayya bazata ki neman sa ba.
Umma tace "babu wanda yaƙira ka Lamiɗo" gyaɗa kai Lamiɗo yayi ahankali sannan ya ajiye mata wayar agefenta yace "Ba inshiga inyi wanka Umma. Incase ankirani please kibama Jidda ko Basma wayar sumikomin wayar ɗaki na" Umma tace "to shikenan" ayayinda tabishi da idanu cikeda mamakin call ɗin waye yake expecting haka. acikin sati biyunnan kullum seyayi mata tambayarnan yafi a kirga kuma tana lura dashi tunsanda wayarsan ke aikima in su Jidda zasu karbi wayarsa suyi game seya musu kashedin da ankirashi sukawomai haka inya zo karbar wayarma seya tambayesu ko an kirashi da sabon number ko ba'a ƙira ba.
Lamiɗo tunda yashiga ɗaki yayi wanka yakwanta bacci bashi yatashi ba seda akafara kiraye kirayen sallar maghriba sannan Umma tatura Basma tatasheshi. yajima kwance kanshi na sara mishi sabida irin jimawan dayayi yana bacci,barekuma abunka da baccin yamma duk seyaji bayajin daɗin jikinshi gaba ɗaya. dakyar ya'iya ya tashi yashiga banɗaki ya dauro alwala yazo yatada sallah a ɗaki sabida lokacin har an idar da sallah a masallatai sede zancen isha'i kuma. tun kafin ya'idar da sallah Umma ta'aiko Jidda tace masa yafito parlour suci abinci sabida daman tare sukeci a tray ɗaya indai dukansu suna gida kuma lokacin cin abincin yayi. Jiddah seda tajira ya'idar da sallah sannan tace "Hamma Lamiɗo wai kafito muci abinci inji Umma" Lamiɗo tashi yayi yaninke sallayar dayayi akai ya ajiyeta gefen katifarsa sannan yace "Muje toh".
A parlour suka samu su Umma zaune gaban trayn biskin alkama da hadaddiyar miyar taushen da kamshinsa yagama gauraye parlourn baki ɗaya. Lamiɗo gefen Umma yazauna yana lumshe idanu yana shakar kamshin abincin yace "wannan sweet aroma ɗindai nasan girkin Umma ne banakowa ba" dariya sukayi dukansu Basma tace "toh ba Umma bace tayi. ninayi girkinnan Hamma Lamiɗo" Jidda riƙe haba tayi tana kallon Basma sannan tace "Kaiii Adda Basma bafa ke kikayi ba" hararanta Basma tayi jidda tadubi Umma tace "Umma inake kikayi girkinnan tunda ke kika haɗa komai da komai?" Umma dariya tayi tace "nibansan muku ba" Basmaaa tana hararar Jidda tace "bawani. wanda yahura wuta yaɗaura tukunya shine yayi abinci"
Lamiɗo dahar yafara zuba loma yace "kutsaya musu dai harsaina cinye abincin zakuyi bayani" Salma dake cin abincin itama tace "Kuma babu wani ba dan duka na foodflask ɗin na juyo" sa hannu sukayi suka fara cin abincin ayayinda sukeci suna hirarrakinsu gwanin ban sha'awa harsuka gama. tashi Lamiɗo yayi yaje waje yawanko hannunsa sannan yadawo parlourn yace "Umma Ina wayarki? ba'akirani ba?" Lamiɗo yajero ma Umma tambayoyi lokaci guda.
Umma na kallonshi tace "Babu wanda yakiraka" Cewa tayi "toh" kafin yace "toh ni zan fita Umma" Umma dake kallonshi harlokacin tace "Zo zauna Lamiɗo" zuwa Lamiɗo yayi yazauna agaban Umma yana faɗin "Gani Umma,wani abun zava taho miki dashi inzan dawo?" Umma tace "A'a bana bukatar komai Lamiɗo. tambayarka zanyi daman. wai wayene zaikiraka da sabuwar lamba dakake ta tambaya kwanannan" wannan karan zama Lamiɗo yayi dakyau yana shafa sumar kansa sannan yace "Umma bakowafah" tunma kafin Lamiɗo yarufe bakinsa Umma tace "kamanya babu bayan kullum kanacikin tambayana ko ankira ka da sabuwar number ko ba'a kirabs sekace wanda kakebin wani bashi koyake binka" Lamiɗo ganin koya zai dojema maganar Umma bazata barshi ba kuma dole in one way or the other zatasani tunda seya nemi izininta kafin yatafi Babban bulin dayake tsumayin zuwa tunkan yagama exams yace "Kiran Mahaifin Nana nike expecting Umma" Umma cikeda mamaki tace "wace Nana kuma?" Lamiɗo yace "yarinyar dana baku labari farkon dawowa na daga field Umma" cikin saurin Umma tace "Yanzu daman baka hakura da batun yarinyarnan ba Lamiɗo? banace maka tunda basu kiraba kamanta da batunta kacigaba da harkokin gabanka ba? ita data damu kahadata damu miyasa bata kiraba?" Lamiɗo da tunda Umma tafara magana yayi ƙasa da kanshi hartakai aya yace "she's just a child Umma. bana tunanin haka kawai Nanah zataki kirana hartsawon wannan lokacin. Jikina yana bani something is wrong" Umma tace "ba abunda yasameta,bazai wuce tabatar da paper number daka bata baneba" cikin sauri Lamiɗo yace "Toh Umma kibarni inje kauyensu insake basu numberta su aikamata can gida" wannan karan wara idanu Umma tayi cikeda mamakin Lamiɗon tana rike haba tace "Anya Lamiɗo ba gamo kayi da aljana ba?" dukda irin pity face ɗinda yayi dan Umma tabarshi yaje Babban Buli seda yayi dariya yace "habadai aljanu Umma. Allah yakare. I'm perfectly fine,kawai tausayinta nikeji,jinakeyi inbanje naji dalilin rashin ƙiran nataba kamar banyi mata adalciba. Umma tace "nidai ban yarda mutum baceba,sabida haka babu inda zakaje" sosai Lamiɗo ke dariya ganin yanda ummar tadage wai Ƴar birni aljanace yace "Allah ba aljana bace Umma. Inbaki yarda ba kitambayi Hafiz toh. Kinsan shidai bazaimiki karyaba" Umma nanma tace "banyardaba babu inda zakaje,karufa mana asiri karufa ma kanka asiri. dabadan dare yayibama zuwa zanyi wurin Waziri yamaka rubutu inkawo maka kasha na kariya" dariya sosai Lamiɗo keyi ayayinda yatashi yace "toh nidai nafita sena dawo" ganin lallai fah bazai samu kan Umman ba inbawai ya lankaya da neman taimakon Hafiz ba.
Jiddah dake zaune gefen Basma ganin Lamiɗo yanufi kofa zai fita tace "Hamma karka manta tsarabata" Lamiɗo na dariya yace "Insha Allahu bazan mantaba" kafin yafice agidan yanajin Salma na mitar in ankawo tsarabar Itama saitaci yau,ai Jidda ba'ita kaɗai bane kanwar Lamiɗon.
****
kwana biyu kenan dacire oxygen ajikin Baba kuma alhamdulillahi jikinshi yayi sauki sosai fiyeda yanda kuke tsanmani,koda yaushe Ina tareda shi muna hira bana motsawa ko'ina. yau tun safe Baba yasa Kawu Hassan yaje gida yaɗauko masa wayarsa kan yanason yayi important call,da Kawu Hassan yakawo wayar seda akasakata a chargi tacika sannan akabama Baba amma da mamakina sebeyi kiran dayaketa zumuɗin zeyiba.
Da daredai dasu Kawu idrissa sukazo suna hira dashi naji yace musu duka yanason ganinsu gobe dasafe in Allah yakaimu kuma akwai mutumin dazaizo masa da sako duk a goben.
Kawu idrissa da Kawu Adamu sukace Allah yakaimu goben yasa muji alkhairi.
Baba yayi murmushi yace "Amin" ayayinda Kawu Sani ke tambayar ko lafiya yace "wani abunne yafaru kakeson taramu Umar? dukkanmu ai munanan yanzuma why not kafaɗa. Kanada wani damuwarne?" murmushi Baba yayi sannan yace "Babu komai kudai bari se goben kawai" Kawu Sani yace "to shikenan Allah yasa munada rai" wannan karan dukansu suka amsa da "Amin".
***
Lamiɗo yana fita agida straight majalisarsu dake cikin unguwa yawuce dan yasan acanne kaɗai zaisamu Hafiz a irin wannan lokacin. Aikuwa yasameshi ɗin,suna zaune suna hirarsu tareda sauran abokanan su. Lamiɗo na'isa majalisar miƙama abokanan nasu hannu yayi sukayi musabaha kafin yadubi Hafiz yace "Mutumina Umma fah na nemanka" Hafiz yace "Umma dai Umma dai kokuma Umma ta?" Lamiɗo na dariya yace "tawa Ummar batakaba" tashi Hafiz yayi yace "mujetoh" haka suka jera tare inda suka nufi hanyar masarautar seda Hafiz yaga sunbar majalisarsu sannan yadubi Lamiɗo yace "yaukuma wace karyar kakeso in gindaya daka tsamoni daga majalisa ana tsakiyar hira" Lamiɗo dafa kafaɗun Hafiz yayi yace "yau babu zancen karya Hafiz se gaskiya tsantsa dazaka faɗa. koda danake saka kaje ka maramin bayan ai duk akan batun makaranta ne ko haka kawai nataba cewa kaje kama Umma karya akan abunda yashafi normal day to day lives activities ɗinmu?" Hafiz yace "nasani ko batun makarantar ne harynzu bata kare ba" Lamiɗo yayi dariya sannan yace "ba batun makaranta baneba. kaima kasan in ana hutu bana damunka dakaje kayi defending ɗina awurin Umma wannan ɗinma kamawa tayi" Hafiz yace "toh miyene abun?mezance ma Umma dan nasan ba haka kawai tasa kakiraniba" Lamiɗo yace "bama tace inkiraka ba ninedai nace haka sabida nasan inba hakan naceba bazaka ɗauki maganar da mahimmanci ba. batun Ƴar birni nakeso kayi mata Hafiz. Sonake ka tabbatar mata cewa she exists" Hafiz da mamaki yace "Wace Ƴar birnin?" danshikam yama manta da babin yarinyar kwata kwata inba yanzu da Lamiɗo yaɗauko maganarba.
Lamiɗo yace "Ƴar birni daya dai dakasani" Hafiz yace "kana nufin yarinyar damuka haɗu da'ita a Babban buli damukaje field work?" Lamiɗo yace "bayan ita kasan wata da ake kira da Ƴar birnin ne?" Hafiz yace "A'a kawaidai kabani mamakine danni gaskiya inbanda yanzu dakayi maganartama nama manta da shafinta" Lamiɗo yayi dariya yace "toh ni banmanta ba Hafiz. her memories are still lingering in my head" ware idanu Hafiz yayi yajuyo yana kallon Lamiɗo sannan yace "Maimuna kumafa? badai son Ƴar birnin kakeyiba?" wannan Karan Lamiɗo couldn't think of a better idea than to punch Hafiz head,yace "anmadai hankalinka kaɗan ne. wace kalma me dadi na soyayya Ƴar birni zata faɗamin inji daɗi? I don't love her,she's too small for me. kawai inason incika alkawarin dana ɗauka matane na cewa zan hadata da family na sabida ita batada su" Hafiz cikeda mamakin Lamiɗo yace "bangane ba? Kamarya batada family? akwai wanda bashida family ne arayuwarnan daman?"
Lamiɗo yace "bazaka ganeba ba daman. She's only a Father, mahaifiyarta tun awurin haihuwarta tarasu,meaning she's no siblings. she's the only child to her parents shine takeson inhaɗa ta da Umma dasu jiddah,she want to experience the joy of having a Mother and siblings" wannan karan Hafiz dariya ya sheke da sannan yace "ikon Allah" Lamiɗo harara yabi Hafiz dashi sannan yace "Ohhh dariya ma magana ta yabaka kenan?" Hafiz yace "Dole inyi dariya Lamiɗo,the thing sounds childish to me. ta'ina zaka fara ɗaukar maganar Ƴar kankanuwar yarinya irin Ƴar birni harka sama kanka? koka taba Jin inda familyn wani yazama na wata dakecan wata uwa duniya? tukunnanma Ina nata family ɗin?apart from her Father dole akwai dangin mahaifinta dana mahaifiyarta damuka tarar a Babban buli. duk sukadai basu Isa subata love experience na sisters da mahaifiya ba sekai dakake dangin badalo? kaida bama zaman kanka kakeyiba bare ace zaka iya adopting dinta. amabar maganar adoption sabida it's out of option tunda ba'a ophanage kagantaba,tareda danginta kaganta. Uwa,kanni da yayu kawai tarasa danake da tabbacin cousins dinta can fill up that gap so stop feeling guilty for anything,maganace Ƴar birni tamaka Irinna yarinta bayan shi babukomai acikinsa" Hafiz yace "Aiko maganar gold datayi tadinga binmu tana wahalar dakanta akan unassured dreams ma kaɗai ya'isa yanuna maka yarintar Ƴar birni kararara wanda dakayi wannan tunanin you'll never take her words onto your heart" Lamiɗo dayayi shiru tun ɗazu yanajin bayanan Hafiz bawai don yana gamsuwa da maganar tasaba yace "I even gave her my number akan zata kirani kaga kuma haryanzu bata kiraba" Hafiz yace "toh kagani? duk cikin yarintarne. bazai wuce tayarda papern awani guriba tama manta da babinka kai kazonan kana tada hankalinka" Lamiɗo boldly yace "I don't believe cewa tamanta dani,I don't believe tayarda papern on purpose sede in bata yayi mistakenly kokuma something is wrong with her" Lamiɗo yakalli Hafiz yace "in her eyes naga how she desperately wanted to make my family her own,in her eyes I saw the truest sincererity ɗinta shiyasa kaga nadamu inkoma gareta. I don't want to cut her dreams as a young child,inma rasa number tayi I'll go there and give her the number again shiyasa nakeson inje Babban buli gobe. Innaje can nasan za'a haɗani dawanda zaikaini har gidansu shiyasa nake nemar taimakonka Hafiz. I told Umma about Nana tun dawowana wanda alokacin takarbi maganar wholeheartedly takuma ɗaukeshi amatsayin yarinta irinna yara kamar yanda kaima kaɗauko but still she didn't stopped my intentions,infact she was ready to talk to her tawaya sugaisa amma tunda Nana tazo bata kiraniba sanda tayi alkawari Umma tace kar insake maganarta agida ganin nadamesu. tace kilan tabatar da layinne kokuma tama manta da batuna so inbar maganar kawai Allah beyi zasu gaisan ba but I didn't listen,I kept expecting her call everyday batareda nasake yin maganarta agida ba harwayana yasamu matsala namaida simcard ɗina cikin wayar Umma sabida kawai kada takira taji layina akashe. toh yanzu sati biyu dayin hakan kenan,Kuma kullum sede inbanshiga gida ba sena tambayi Umma ko ankirani da sabon layi wanda hakan yasata zargin something is fishy,yau ta ritsa ni da tambayoyi wanda dole seda na amsa mata kasandai ni inba abunda yashafi makarantataba banayima Umma karya bana kuma boye mata komai. atakaice dai yanzu Umma kallon aljana takema Ƴar birni shiyasa nakeson kaje kafaɗa mata kaima kasanta please,daganan se insan yanda zanyi in lallabata tabarni inje Babban buli gobe" Hafiz yace "wallahi dabadan nasan yarinyar nanba nima cewa zanyi aljana ce. how can such a small child have so much impact on you Lamiɗo?" Lamiɗo dai dariya yayi sannan yace "wallahi nima bansaniba Haifiz. May be sabida irin sabon da mukayine na tsawon kwanaki" Hafiz yace "but still. That shouldn't be a genuine reason" Lamiɗo yace "nidai yanzu ba wannan ba,kataimaka mujemu gida kacema Umma kasan Ƴar birni nikuma daganan zansan yanda zanyi in lallabata tabarni inje kauyen Babban buli gobe" Hafiz yace "mujemu tunda ba karya zan gindayaba iyakar gaskiyata zanfada aida sauki" Dariya sukayi dukansu ayayinda suka cigaba da nufar kofar masauratar Gombe.
Do you think Umma zatabar Lamido yaje Babban buli? will destiny unite them?
Wace magana ce Baba keson fadama Yan uwansa? waye Baba yakira awaya yakeson yazo suyi magana agaban kowa da kowa?
Wanene Dr Isma'il? lecturern daya tuna ma Rukayya past dinta,yadawo mata daduk wasu pains dinda ta adana acan kasan zuciyarta zuwa sabo?
Do you think Yaya Salim will play a role in Rukayyas life? kubiyoni cikin littafin Qadr dansamun amsoshinku.
*08147722806*
Vote
Comment
Share!
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
*Page Sixteen*
*Bonus page*
*ASALIN LAMIƊO*
Mallam Yusuf Kwami tilon Ɗa ne agurin iyayensa shiyasa suka ɗauki son duniyarnan suka ɗaura masa,dukwani abuna rayuwa dayake bukata yimashi sukeyi batareda suntaba tunanin yanda zaiyi building future ɗinshi ba,aganinsu he's their only child so babu abunda bazasu iyayi masa dakansu ba shiyasama basu taba damuwa da yaje yanemi abun kansa ba inbanda noma dayake taya mahaifinsa in lokacin damuna yayi har yakai shekaru ashirin aduniya wanda alokacin ne mahaifiyar sa tadage seyayi aure sabida tanason ganin jikokinta Itama tunda Allah bai azurtata dasamun Ƴaƴa dayawaba. Awannan lokacin Yusuf ko budurwa bayidashi danshi ba mutum bane me hayaniya da kalle kalle even though he was pampered by his parents,naturally shi mutum ne me sanyi dakuma rashin yawan magana shiyasa ma baka taba gane meyake so dawanda bayaso,shidai kawai se abunda iyayensa suka ɗaura sa akai yakeyi wanda wannan dalilin yasa mahaifiyar sa tayi deciding sunema masa auren Ƴar yayarta *Amina* wanda cikin lokaci kankani akayi biki Amina tatare agidan Mijinta Yusuf. Dukda auren haɗin gida akayi musu they accepted it wholeheartedly,cikin lokaci kankani suka fahimci juna kuma suke zaman lafiya cikeda so da kaunar juna. shekara biyu da aurensu anma Allah baibama Amina haihuwaba gakuma matsalar rashin abunyi da Yusuf ke fama dashi,indai ba lokacin Noma ba toh kullum yana kwance agida se abunda mahaifiyarsa Hauwa'u ta girka takawo musu gashi yanzu jikin Baban nasa dayake fita yanema musu abunda zasuci dinma babu daɗi sosai. Kusan kullum yanacikin rashin lafiya abunka da tsufa wanda hakan yatada hankalin Amina,tasan in one way or other dai dole wataran sesun nemi na gashin kansu bazaiyuyu suyita depending akan iyayensuba kullum kuma Yusuf ɗinma na iya bakin ƙoƙarin shi wurin ganin yanemi aiki anma abun yaci tura wanda wannan dalilin yasa Amina ma ta cigita masa cikin yayunta ko Allah zaisa yasamu abunyi daga bangarensu dake duk manyane kuma kowannensu nada abunyi. Alokacin cewa sukayi babu anma in ansamu zasuyi mata magana.
Cikin ikon Allah kuwa ba'ajima ba watarana sega yayanta *isiyaku* yazo hargida yakawo ma Mallam Yusuf tayin aiki inyana sonyi anma da sharaɗin bafa acikin Kwami bane aikin acan masarautar Gombe ne wanda kuma dole zaikoma can dindin din dazama. Without thinking twice Mallam Yusuf ya karbi aikin hannu bibbiyu dankuwa yajima yana neman aikin ruwa a jallo yanzu kuma dayasamu bazai bari ya kubuce masaba so far as akwai goyin bayan iyayensa. Cikin wata guda yatattara shida Amina suka koma cikin masarautar Gombe inda akabashi *Sarkin Dawakai* wato mekula da duk wata harka data shafi dokunan masarautar inda yake zuwa Kwami akai akai yana duba iyayensa dakai musu ɗan abunda ba'a rasaba in aka biyashi hakkinsa. shekaransu biyu a Gombe Allah yakarbi ran mahaifinsa inda bayan anyi zaman makoki angama Yusuf yaso mahaifiyarsa tadawo cikin garin Gombe suzauna tare anma taƙi fir wai ita bazata bar asalintaba,a Kwami aka haifeta kuma acan za'a binneta in lokacinta yayi. dole Yusuf yahakura yacigaba da zuwa ganinta akai akai kuma alokacin Amina nada tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe.
wani irin shakuwa ne me tsafta tsakanin Sarki da Mallam Yusuf dankuwa Mallam Yusuf is very loyal and simple kowa nayimasa wannan yabon a masarautar,bazaka tabajin anyi aikin algus taredashiba wanda hakan yasa Sarki ya yarda dashi sosai harma wani sa'in yakansa Mallam Yusuf aikin dabai shafi dawakan masarautarba. anacikin haka Amina tafara naquda agida wanda Sarki dakanshi yabada mota aka kaita asibiti. tafi twelve ours tana wahala bata haihu ba wanda hakan yasa likitocin sukayi deciding ayimata aiki,haka Mallam Yusuf yasaka hannu aka shigada Amina ɗakin tiyata. Cikin awanni biyu segashi tahaifi Ɗanta namiji kyakyawa son kowa ƙin wanda yarasa. Kwanansu biyu a asibiti aka sallammeta suka dawo gida. Sarki har asibiti yazo yaduba Amina kafin a sallamesu hakanan sanda suke asibitin abinci ma daga cikin nasa yasa ake diba ana kawo musu asibitin hakanan duk wasu expenses na asibitin shiya biya. ana gobe suna ma yasayi rago yasa akai har kofar Mallam Yusuf yace ace masa gudumawarsa ta bikin sunane wannan wanda hakan yasa Mallam Yusuf Jin nauyin saka sunan wani bana Sarkin ba dankuwa he's done alot for him da bakowane zai iyayin wannan ba. Abunda baisani ba shi Sarki arayuwarsa yanason mutum mai Amana, riƙon gaskiya dakuma sanin yakamata wanda tunda suka fara aiki da Mallam Yusuf Sarki yalura Mallam Yusuf nada waɗannan qualities ɗin yaji yana sonshi haka kawai shiyasa yake masa waɗannan hidindimun bawai don wani abuba. Ranar suna akasakama yaro sunan Sarki *Isma'il* inda ake kiranshi da *Lamiɗo* sabida a sakaya sunan.
Tun bayan haihuwar Lamiɗo Amina batasake haihuwaba harseda Lamiɗo yayi shakaru shida cip aduniya sannan tahaifi Ƴa mace akasaka mata suna *Basma* daganan kuma setacigaga da haihuwar ƴaƴa mata ajere,bayan shekara biyu ta haifi Jidda sekuma bayan wani shekara biyun tahaifi autarta Salma daganan kuma tace zata huta tukunnan dayake kuma batada rabon