Showing 48001 words to 51000 words out of 62407 words

Chapter 17 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

kuduri ta shi ni duk asuba, duk asuba sai ya zo ya buga mun daki, yanzun ma bugunshi ne ya tashe ni sai dai na tashi da ciwon kai mao tsanani, ™ara rufe idon nawa na yi ko zan ji sau™i, amma babu alamun sauki. Hasbunallahu wani imal wakeel. na faWa ina daga kwancen.



Legends Pen.



Page 35





A Sangaren Mus ab ganin har ™arfe 7:30 babu motsi na a falo bare kuma kitchen ya sa shi sake zuwa bakin ™ofar Wakin.  Salma, kin ta shi kuwa. Kuka na fara, ina faWin  kai na.



 Salma me kike cewa?, ba na jinki.



 Kai na. na fada tare da fashewa da kuka.  Ina zuwa. ya fada tare da matsawa daga jikin kofar,  yan mintuna kadan na ji yana bude kofar, ashe yana da extra key a hannun shi amma bai ta ba budewa ba ko da wasa, shigowa ya yi tare da fadin mai kike cewa.  Kai na.



 Ya salam sannu kin ji. ya fada tare da ficewa, can ya dawo rike da ruwan zafi na tea. Salma ta shi ki sha, bari naje pharmacy na duba miki magani, kina da ulcer?.



 A a. ficewa ya yi, ni kuma na fara shan ruwan zafi, ina cikin sha ya dawo rike da ledan maganguna. Ajiye mun ya yi tare da fadin  Ga su ki sha. Wauka na yi na bude na sha da ruwan zafin sanan na kwanta shi kuma ya fice, sai ™arfe sha biyu da rabi na farko, lokacin ciwon ya Wan safafa mun, na mi™e na shiga ban Waki na daura alwala tare da yin wanka, sallar asuba na yi dan ban iya yi ba, na saka doguwar riga na fito falo dai-dai lokacin da ya fito.  Sannu Salma, ya jikin?.



 Da sau™i.



 Ga take away can a kan dinning zaki iya ci?. ban ce mai komai ba na nufi dining din, bayan na xauna na fara bude take away din, dankali ne da plantain, sai kum tea a plast da alamu shi ya dafa abunsa, sai da na fara zuba tea din na sha sanan na fara cin dankalin, ban wani ci sosai ba, na ta shi na dawo kan kujera na zauna.  Ya.™arfin jikin.



 na warke fa.



 To ai haka ake so Hajiya Salame.



 Wai kai Mus ab ba ka iya shiru ne a rayuwarka?. dariya ya yi, sanan ya ce.  Ai ke din ce ban so kiyi shiru kwata-kwata. Tsaki na ja tare da mikewa na shige daki, har da banko kofa. Tsayawa nayi cak, ganin dakin ba yadd na bar shi ba, angyara shi sosai har da gadon, ga magani na nan har da bottle water a kan centre table na cikin dakin. Karo na farko, abu na daya da Mus ab ya yi wanda na ji ya so ya burgeni, haka kwai abun ya tsaya mun a rai, amma kuma ban duba ba.



Har dare ban sake fitowa ba, sabida jikina babu kwari kuma bana jin wata yunwa. Washe gari ma haka ce ta kasance, ya yi mana order abin kare, ya gyara gidan gaba daya har daki na, a takaice dai sai da na yi sati ina wanan jinyar, Mus ab na mana aikin gida.



Ranan da na fara jin na warke da kaina na y duk wasu abubuwana, har na hada mana breakfast kamar yadda na saba, a kan dining na ajiye masa na shige daki na ci nawa. Ina zaune cikin dakin ya shigo, nesa da inda nake ya zauna tare da kiran sunana, yan mintuna bayan ya zauna.  Salma, a yanzu mun dauki wata da watanni cikin gidanan, amma ba kya yimun ko da maganar arziki ce, Salma ko gaisuwa wanan ba ta hadani da ke, ba ki da aiki sai yi mun tsaki kamar ba mijin ki ba, Salma na miki hakuri da sa ran gobe za ki canja amma kullum jiya iya yau.



Ban bari ya ™arasa ba na ce.  Idan Saki na zaka yi Mus ab ka sake ni, har yanzu ka sa ni ina zaune ne bisa umarnin mahaifna da kuma biyayyarsa, amma ba na ™aunar ka ko Wis. Shiru ya yi, ya kuma ra sa mai zai ce mun amma tabbas lamarin Salma bana kare ba ne, sa anin auren mu sunan kowacce na da juna biyu, amma shi ko kallom arziki bai sa mu. Mi kewa ya yi ya fice, ni kuma na ci gaba da abinda na ke.



Haka ya zauna gaba daya ya rasa mai ke ma sa dadi, ta ina zai fara lamura na, an ce kulawa na sa ka soyayya, amma ni kara mun kiyayya ta yi, an ce hakuri amma shi da alamu na shi ba riba, wani bari daga zuciyarsa ne ya ce.  Ka da ka sare Mus ab, akwai abubuwa da yawa da ba kayi ba, akwai hanyoyi da dama, ka yi ma ta kyautar da baza ta iya banza da ita ba, waya, ko wani abu, ka fita da ita ta ga gari, ka dinga bata nishadi.



 Salma ba bina za ta yi ba, nasan babu inda za ta bini muje, tama ki bani dama na nuna ma ta kulawar ko soyayya.



 Ka bi ta hanyar Mama da Ummah, kar ka nuna musu ta yi maka wani abu, amma ka sa su gane ba ta jin maganar ka.



 Amma ai haka zai ba ta ran ta, zai ja su yi ma ta fada.



 A a Mus ab, suma sun san gyara a ke so ba za su yi ma ta fadan da za su ji haushi ba.



 Shikenan bari zan gwada. Hirar da Mus ab ke yi kenan da zuciyarsa, haka ya yi ta kwashewa da debewa har ya samar da matsaya guda daya, wacce za ta bude ma sa hanyar samun sa a.



Mota ya shiga kai tsaye ya nufi gidan Galadima, kamar ko da yaushe bangaren Hajja ya nufa, bayan sun gaisa ta tambaye shi matar shi, ya ce.  Hajja a dai ci gaba da mana addu a kawai, amma lamarin ta sai hakuri.



 Wane sabon iskanci kuma ta tsuru da shi?.



 Hajja, Salma ba ta mun magana duk tsahon lokacin nan, sai dai ta dinga bani abinci kamar ya wane maye, amma babu ko kalma daya ta magana.

Dariya Hajja ta yi sanan ta ce.  Daman matarka gwana ce wanan fannin na gaba da mutane, ina kai ne ka ce wai ba matsala ba ne danna ta yi banza da ni, ina ga wanan ba abun damuwa ba ne Mus abu.



 Hajja ba za ki ga ne ba, Hajja lamarin na ta ya yi yawa fa.



 ka kara hakuri kawai. Mikewa ya yi ya fice kawai, bangaren Ummanah ya nufa, bayan sun gaisa ne ya ce.  Ummah dan Allah ina neman alfarma wajennku, ku tai maka kuje gidana, bawai fada ba ne ko matsala, amma ku yiwa Salma nasiha.



 Wane sabon abun kuma ta tsiro da shi.



 A ah Umma, kawai rashin maganar ta ta ya yi yawa, har yanzu ko gaisuwa fa ba ta hada mu.



 Duk wanan lokacin Mus ab. Gyada kai ya yi sanan ya ce.  Duka wallahi Ummah.



 Shikenan bari na yi magana da Yayan sai ka kai mu ko da daddare ne.



 Shikenan Ummah, amma dan Allah kar ku fadawa su Abba.



 Ba zamu fada musu ba Mus ab. Ta shi Ummaha ta yi ta nufi bangaren Maman ciki, bayan ta gama gaya ma ta komai ne Maman ciki ta ce.  To mene amfanin zuwan dan Allah, yarinyar nan ai ta yi kokari, tun ta na cewa ba za ta tare ba har ta tare, ta ce ba za ta zauna ba ta zo ta zauna, ta ce sai ya sake ta, yanzu ta daina maganar sakin, wanan din ma za ta dai na.



 Salma ba za ta dai na gaba ba, kin san da mitsiya cin riko, kamar yar zamanin kafirai, ba fada zamu yi ma ta ba ko duka, nasiha ce kawai.



 Shikenaan muyi sallan magariba ya zo ya kai mu. Komawa bangaren mu Ummanah ta yi ta same shi zaune.  Mus ab bari muyi sallah sai ka kai mu ko.



 Tom shikenan Ummah. Ya fada tare da mikewa ya fice.



Legends pen.





Page 36





Ina zaune a cikin daki na naji ana bude kofar main falo.  ko gidan ubanwa yaje oho?, sai yanzu ya dawo. Na fada a rai na, ina jiya ya shigo na cancare mai, kwana biyu ina dan jin dadin yi masa rashin mutunci, kofar dakin nawa ya bude tare da shigowa.  salma muna da baki?.



 Baki kuma?, ka na da baki dai, ni wa nake da shi da zai zo ko gidana ne?.



 Salma wa yanan bakin manya ne, ki zo karki jawa kanki fada, ni ba ruwana. Yana fadin haka ya fice.  Na shiga uku, su waya ya kwasa mana?. Na fada tare da mikewa, kofa na nufa zan fita sai kuma na tuna ko maza ne, hakan yasa na dawo na zura hijabi na fita. Da gudu nayi inda suke ina dariya da fadin.  Ummah. Hade rai Ummanah ta yi, na koma wajen Mama ina fadin.  Mama ku ne, mai makon ku shigo sai ku zauna anan?.



 Ai Salma ba zama ya kawo mu ba, gaisawa da ku mu ka zo yi kawai.



 Bari na kawo muku ruwa. Na fada tare da kokarin ta shi.  Ga ki a haka kamar mai hankali da nutsuwa, ko kuma wacce ke zaune kamar matar auren gaske. Zama na yi tare da cewa.  mai kuma ya ce na yi, shi shikenan idan bai hadani da ku ba ya jin dadi?.



 Ni a kace miki na ce wani abu?. Ya fada da saurin baki.  Wai Mus ab tsoron yarinyar nan kake ko me?, kai ka fada ta kashe ka, Salma abinda kike yi kina ganin dai-dai ne?.



 Mama dan Allah me na yi, me nake ma sa wallahi tun da Abba ya zo gidanan ko magana ban kara masa ba, bare na ba ta mai rai, Abba ya yi fushi da ni, ina masa girki, ina ajiye mai a kan dinning, ina share-share.



 Amma ai abincin a kan dinning kike ajiye ko da yaushe, ko da bana gidan kuma cikin plate, ba wai food plast ba, kina hadawa da ruwa?.



 To ance indinga baka ruwa ne, ai abinci kawai a kace, kuma Yaya Asma u cewa ta yi indinga maka girki ina ajiye maka a kan dinning.



 yanzu Salma dan ance ki dinga ajiye masa a kan dinning sai a ka ce ki zuba a faranti ki ajiye masa, kuma dan baki da hankali ruwa sai ance ki ba shi, yarinya ce ke?. Ummanah ta fada kamar za ta da ke ni.



 Yanzu kai Mus ab wanan ai kukan dadi kake, tana baka abinci, ba ta zagin ka, ba ta ma rashin kunya, mai kake bukata?.



 Haba Yaya ita ba ta da hankali, dan ance ta kai abinci kan dinning sai ta dinga kaiwa, dan ba a ce ba a ce ma ta ruwa ba sai ta ki kai wa?.



 To yanzu da ta na bar ma sa a kitchen fa?.



 Ba fa da kika zo ba, wani abun dai ya kawo ki. Ummanah ta fada tana harara Maman ciki.



 Yanzu Ummah ni ba wanan ba, ko kallo na ba tayi ba gaisuwa, babu wani hakkina da ta ke saukewa, idan zan kwana ina mata magana to ba za ta kulani ba, karshen amsar da zan samu ita ce ta yi mun tsaki ta bar mun wajen.



Da dukkan alamu ran Mus ab ya kai karshen ba ci, har ya yi wanan furucin bai sa ni ba.  Salma!, Salma!!, sau nawa na kira sunanki. Ummanah ta fada fuskarta a hade.  Sau biyu.



 To kar ki ba ri na kira na uku, dan ba zan kira sh da alheri ba, na fada miki.



 Yanzu Ummah me zan yi?.



 Kinga Salma ki kwantar da hankalinki, ki yi iya abinda kika ga za ki iya, wanda ba za ki iya ba ki barshi, yau da gobe za ta sa ki iya, ba kwa ganin Zuwa yanzu kiyayyar da ke tsakanin ta da shi ta sauka fiye da rabi, komai ma a haka zai zama tarihi. Cewar Maman ciki kenan.  Salma ba irin yaran da ake cewa yau da gobe za ta sauya ba, ya zuwa yanzu watansu nawa da aure, amma ace har yanzu ba ta san ta bawa mijinta ruwa ba, ruwa dai wanan abun banza.



 Dan Allah kar ku ta kura ma ta, Salma ki yi abinda za ki iya, ki yi kokari ki canja Allah ya yi miki albarka.



 Amin. Na fada tare da ta shi na huce ciki, bayan ita ma ta miki tana fadin.  idan ka ga dama ka zo ka mayar da mu. Kofa mu ka nufa tare da ita, ina iya lissafa lokutan da na fito wajen compund dinan, domin kullum ina ciki ba na fita, a ciki kuwa Ummanah ce ta kalli Mus ab ta ce.  Ka bata  yan kwanaki, idan ba ta canja ba akwai shirin da zan yi maka, wanda zai ka ci riba insha Allah.



 Shikenan Ummaha ngde. Ya fada yana ta shi, a ranshi yana mamakin Ummanah wacce irin mata ce, wacce ba ta dauki na ta a na ta ba, wacce ba ta fifita farin cikin dan ta a kan na wani ba. Sai da suka shiga mota na koma cikin daki na.  Me zan yi yanzu ni Salma, me zan yi?, na dinga gaishe shi da zuba masa abinci a plast na hada mai da ruwa, amma ai hakan ba zai rage tsanar da na masa ba, yana nan a kan wanan matsayin na Mus ab, mutumin da na tsana kamar mutuwa ta.



Kitchen na shiga bayan na dauke abincin shi da ke plate a kan dinning, plast na sakko da shi wanda ina ga banta ba amfani da su ba, na zuba abincin a ciki na gyara na kai kan dinning tare da ruwa da cup, sanan na shige daki na na kwanta.



Ya ji dadin ganin wanan, da alama za a samu canji yanzu lokaci ne da zai nunawa Salma mene so, lokaci ne da zai zubawa Salma ruwan soyayya a zuciya, lokaci ne da zai koyawa Salma soyayyarsa, lokaci ne da zai yi yakin ganin ya kuri duk wata kiyayay ta zuciyar Salma ta dawo soyayya, shima ya fara ji a jikinsa da gaske Salma za ta so shi, ko da bai kai rabin wanda yake ma ta ba, yana fatan ko da rana daya Salma ta bude ba ki ta ce.  Ina son ka Mus ab. Ranar bai san irin farin ciki da zai yi ba, bai san irin sadakar da zai yi ba, bai san irin sallolin godiyar Allah da zai yi ba.





37.



Washe gari.



Kamar yanda nake ta shi ko yaushe haka na tashi, bayan na yi wanka na, na caba ado kamar yadda nake ma fito falo, nasan bayanan bai dawo daga gudu da yake ba, daman ko da yaushe na saba sai ina cikin kitchen zai dawo ya zo ya tsaya a kaina ya na ta zuba mun surutu ina ja mai tsaki, har na gama. Ina shiga kitchen din kamar an hankadomun abu haka naji  yan uwana sun fadomin a rai, Walida da Sadiya, Yaya Asma u da yayar Abuja su Iki da sauran, tabbas na yi kewarsu kima na yi butulci na watsar da su baki daya, duk da nima sun watsar da ni amma hali na ne, ina tuna farkon aure na da su ka dinga kiran Mus ab su na cewa a bani waya ina kin amsa, ciki har da Walida kuwa. Amma nima ai bana cikin tawa nutsuwar kuma suma duk makiya na ne, suna farin ciki da auren Mus ab auren kaddarar mummuna da a ka yi mun. Haka nai ta aiki na ina faman tunani, ga kuma Mus ab dai bai shigo da huri ba, koma ya shigo bai zo kitchen din ba, haka kawai na ji na matsu ya zo.



Tsaki na ja tare sa cewa.  Uban mene na wa, da zuwan na shi. Ina fadin haka na ci gaba da aikina ina yaki ce zuciyata da tunanin shi, ina gab da kammalwa ya shigo kitchen.  Salame mai ake dafa ma na?. Kamar ko yaushe din banza na yi da shi, na ci gaba da aikina.  Salame ina jin yunwa ayi sauri.



 Ina kwana?. Na fada ba tare da na juyo ba, murmushi ya yi har ina jiyo sautin shi, sanan ya ce.  lafiya kalau gimbiyata, kin ta shi lafiya?.



 Cewa a ka yi na gaishe ka, ba na biye maka ai ta surutu ba. Na fada a rai na, a fili kuma dai na masa banza ban tan ka mai ba. Yana tsaye yana ta zuba har na kammala girki na, na zuba na shi plast da tea na zuba nawa a plate, juyowa na yi na gan shi tsaye, matsamun hanya ya yi tare da cewa.  Bari na fita da plast din. Ajiye ma sa na sa na yi, na dauki na wa dake ni a cup na zuba nawa, sai na dauki cup da plate na fice, dakina na koma na zauna na fara cin abincina, bayan na kammala na dawo kitchen na fara kokarin wanke kwanin ka da na yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login