Showing 51001 words to 54000 words out of 62407 words

Chapter 18 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

amfani dashi, amma sai ya shigo.  Ki bari na yi wanke-wanken Gimbiyata.



 kabar shi dan Allah.



 A a ni gaskiyya na yi niya kawai ki bari.



 Mus ab ba na son yawan magana, dan Allah ka kyale ni.



 Nifa A a sai dai mu yi tare.



 Dan Allah ka bari, ka je ka yi wani abun mana. Cika mun ya yi ya fice, ni kuma na ci gaba da abinda nake. Yan mintuna kadan na kammala na fito falo, tsaye na gan shi rike da moper yana mopping, almun ya yi shara ya gama.  Kai duk rashin jin maganata Mus ab ya fini wallahi. Na fada a rai na, ina nufar wajen Tv na fara gogewa, sai ya zama kamar tare muke aikin yanayin can barin ina yin can barin.  Gimbiya kin gam mu kamar wasa best couples.



Ni a rayuwata ban san lokacin da Mus ab ya zama mai yawan surutu ba, kuma kowa na cewa Mus ab ya na da surutu ba zai ta ba yarda ba.  Gimbiya idan kana tare da wanda kake so, ka na zama mai yawan surutu ne ba tare da kai ma ka sa ni ba, kawai dadin soyayya ke di ban ka.



 To ni mai ka ji na ce maka?. Murmushi ya yi sanan ya ce.  Nasan a ran ki kina mamakin yadda na zama parrot haka.



 Ni ban yi ba, kawai sai na zauna na yi tunani ka?.



 Ko ba ki yi yanzu ba, wata rana za ki yi. Bude ba ki na yi da niyar yin tsakin da na sa ba, amma kuma sai na ji na kasa, mikewa na yi na shige daki na kwanta, can mintuna ina zaune daki na ji am shigo, da sauri na dago tare da janyu blanket na rufe jiki na, ina kallonsa ya na murmushi har ya zauna gefen gadon.  Barka da rana, ranki ya dade. Shiru na yi ban da niyar magana dan ban ma san me zan ce ma sa ba, wai  barka da rana.



 Ina neman wata alfarma ne Gimbiyatah. Shiru na kuma yi, amma kuma ya gane ina sauraron sa.  Ina so nu dan fita mu ga gari, zaman kwana biyu ya yi yawa. Har cikin rai na na ji dadi, ko ina zamu dan wallahi kamar a kan ™aya na ke a zaune. Kishirya nima bari na je na shirya. Ban ce komai ba dai har ya fice, na dau yan mintuna kafin na ta shi, shiryawa na yi cikin riga sa skert na wata atamfa, na yi kyau sosai da sosai ko abu daya ban dauka daga lefensa ba haka na yi shiri na, kuma har yanzu ko dan kunnen ban ta ba dauka daga lefensa ba.



Fitowa falo na yi na sami waje na zauna ina kallon Tv, ban fi minti biyar da zama ba ya fito cikin shirin shi, ba zance ya yi kyau ba ko bai yi kyau ba, sabida ni ba wani kallon arziki nake masa ba, amma dai na kwana na tashi da sanin Mus ab Wan wanka ne kuma dan gayu.  Yanzu wanan kwalliyan duk na mene, so kike mu fita maza su biki da ido?. kallon kai na yi, ni kwalliyar na yi ne, fuskata ko powder babu, multi lips ne kawai ke shinning, na san dai fuskar ta yi smooth sosai da sosai, sai kuma mai da kallona kan shi, shi uban kayan da ya saka da alama ma sababbi ne, amma ya zo ya ce wai wanan uwar kwalliyar.  Mus ab, zamu fita ne ko ba zamu fita ba?.



Legend's pen.





Page 38.



 Zamu fita ranki ya dade, amma kyanki ya yi yawa sosai da sosai. hanya na kama na fice, ban masan mai zance masa ba neman maganar kawai yake so, ni wallahi muryar Mus ab har cikin kwakwalwa ta nake jin ta, biyo ni ya yi a baya zuwa parking space, burki na ja na tsaya, sabida ban san wani mota zai shiga ba, tun da ga sunan burjik kaman na siyarwa. Ranki ya dade wanne zamu shiga?.



 Wai dan Allah kai ba ka iya rayuwa ne sai ka mun magana?. dagowa ya yi ya kalleni tare da yin murmushi.  Ranki ya dade idan ban kulaki ba wa zan kula?, yanzu ki zaba mana motar da zamu hau.



 Ta farkon. Na fada dan san kawar da zancen, idan za a kasheni da wuka ma bansan wacce nake nufi ba, kawai dai na fada ne.  Angama Hajju. Ya fada tare da nufar motar, kawar da kai na na yi gefe ba na ma so naga wacce ya dakko din, sai da na ji alamu ya zo inda nake yasa na juya. Kai tsaye back seat na nufa da budewa, amma sai naji su a rufe, tsaki na yi na bude front seat fuska ta a hade na shiga.



 Ina muka nufa frist?.



 Kai ma ba kasan inda zaka kai mu ba?. Na bashi amsa kai na a kasa.  Nasani ko kina da inda kike son zuwa Gimbiyata.



 Muje park.



 Okay. Ya fada tare da saita motar zuwa hanyar park din, cikin mintuna kalilan mu ka isa duk da a hankali yake tukim cike da kwarewa. ˜ofar Gamji park mu ka je, park din da muke mafarkin zuwa nida su Walida, har cikin rai na ji dadi amma ban iya nuna masa hakan ba, bayan ya yi parking my ka fito sai ji nai ana ta Samun mayafi, kafin na karasa juyowa na ga ashe shine yake gyaran mun inda ya sauka bansani ba, duk inda muka yi a park din ya na manne da ni, kuma ranshi a hade kamar zai yi kuka ko zai daki wani, a raina na ce.  Ko uban mai a kayi masa oho?. Bayan mun gama zagayen mu ka samu wajen da ake zama muka zauna, yana faman danna wayarsa ni kuma ina wasa da wani game da ke wajen ina kuma kallon gefe da gefe, kamar nasan wancan mutumin da ke zaune, duk da ta baya yake amma tabbas ina ji kamar na san shi, ya so ya yi kama da masruru amma ba shi ba ne, sabida idan masruru ne akwai wani yanayin bugu da nake ji a zuciya ta mai nuna zallan so da kauna, mai nuna girma da zafin soyayya, kuma nasan har yanzu idan na gan shi haka zanji, duk da rabo na da tuna wani mutun wai shi masrur tun kafin na shiga gidan Mus ab, amma na san a yau na yi ido biyu da shi zan ji soyayyarshi a zuciyata, sabida shine mutum na farko da na fara so, kuma wa yancan da alama shaye-shaye suke, masrur kam na kwana da sanin mutumin kirki ne.  Salma me kike kallo, tunanin me kike?. ido na mayar kan sa sanan na ce.  Bakomai.



 Kin san wani a cikinsu ne?. da sauri na girgiz Kai na ce.  Ko Waya.



 Okay, mu tafi ko?.



 Uhm. na fada ina mikewa, daii-dai lokacin da suna samarin su ka ta shi, sakamakon zuwan wasu manyan karuwai, kana ganin yan matan nan kasan karuwai ne masu lasisi, duba da irin shigarsu, atamfa ce amma dinkin da ake kira.  Fan Warinka tsirara.  domin duk wani waje da yake bai kamata ya fita jikin mace ba ta su nasu a waje yake, sai gaisawa suke da mazan har da rike hannu, gaba na ne ya fadi amma bana soyayya ba, na tsoro sakamakon ganin masrur da na yi, hawaye na ji sun fara zubumin ban san na mene ba, amma kuma ban hanasu ba cikin sa a shima idanunsa suka sauka a kai na, bayan na juya inawa Mus ab magana. ˜amewa ya yi yana kallona, tabbas ni ce tare da wanda a ka bani a matsayin miji, gamu nan cike da so da kaunar juna, daman yaudararsa na yi ko kuma yau da gobe ce ta sa na fara son Mus ab din. Ji ya yi kamar yazo ya mun magana, sai dai kuma yanayin da ya ke, gashi kuma ni na juya na bi mijina, yana kallon lokacin da Mus ab ya budemun gidan gaba na shiga, ya rufe sanan ya juya ya bude nasa ya shiga muka tafi.





Kallona Mus ab ya yi sanan ya ce.  Wai kukan na mene haka?. Banza na yi masa, nasan duk shi ya ja rashin samu na ne ya sa Masrur shiga wanan halin, halin da ni kai na nai fatan na shiga a kan na zama matar Mus ab.  Kiyi hakuri idan na miki wani abun?. Goge hawaye na na yi, sakamakon parking da na ga munyi a bakin wani shago.  jirani. Kawai ya ce ya fice, bin bayan shi na yi da kallo na ga shagon da ya shiga an rubuta. Apple fix by Legend. Da alama shagon siyar da iphone, kau da kai na na yi, na shiga tunani da mamakin ganin masrur amma ban ji wa yanan yanayin da na yi imanin jin su ba mai hakan ke nufi, wai na daina son Masrur ko me, to idan na dai na son Masrur wa nake so, ko kuma wa zan fara so?.  Mus ab. Na ji zuciyata ta fada da karfi, nima cikin karfi da sauri na ce.  A a wallahi.



Legends pen.





Page 39.





Bude kofar na ji yanayi, da sauri na dauke kai da kallonshi haka kawai naji banson ganin sa ma, har ya shigo ya ja motar ban ce mai kala ba.  Dare ya yi amma ba sosai ba, zamu iya fita dinner?. Allah ya gani rai na a bace yake, kuma ba ma na son fita amma kuma ina tuna kalmar opportunity come once, ga shi kuma ni ban ma san ya a ka yi ba na ji ina son bin na shi.  Zuwa ina?.



 Do you have place in your mind?. Girgiza kai na yi sabida ba ni da wani waje, kuma ko ina da shi ma ba zan iya fada ba, dan na ga sakin fuskar da na masa kwana biyu ya samu sake a wajena, amma zan canja.  Okay mu shirya din sai muje inda Allah ya yi. Bance komai ba kawai na mai da hankali na kan titi, har mu ka isa gida ban ce komai ba. Yanayin parking na bude zan fita.  Ranki ya dade take this. Ya fada yana mikomun leda.  Mene a ciki?.



 Ki duba ki gani ma na.



 Ka bar shi kawai. Na fada zan fi ce.  Kiyi hakuri dan Allah ki kar ba. A yatsine na sa hannu na amsa na yi cikin daki, ina zuwa na dire leda kan gado na shiga toilet, wanka na sake na yi Sallah sanan na kwanta, wajen 30min na ji ya na mun knocking.  Ranki ya dade na shirya fa. Ya tsine fuska na yi, ni ba na son fitar ma ba ki daya. Sakkowa na yi daga kan gadon na shiga toilet na wanke baki na fito, doguwar rigar material na dauka na sa ban ko sa ka mai ba bare wani abu a jikina, ban san meyasa ba kawai na ji ba na son sakawa, ko dan ba na son ya na yawan yi mun magana ne oho.



A falo na sameshi yana tsaye cikin english wear, ya yi kyau sosai, tabbas yana kama da Aditiya roy kapur na india, ban ta ba gani ba sai yau.  Ranki ya dade na yi kyau kenan?. Tsaki na yi tare da kau da kai.  Nagode. Ban ce komai ba na fita shi ma ya biyo ni, front seat na zauna, bana son yawan jan maganarsa shiyasa nake kare komai, ban san me yasa ba kwata-kwata ba na jin dadin, kamar wani abu zai faru a can inda zamu.



Shiga ya yi ya fara jan motar, wacce mu ka fita da ita da zu ba ita ba ce wanan wata ce da ban. Country Hill Restaurant 21a Dan marna street unguwar rimi. Mu ka nufa, tabbas ko a da idan na zo hucewa ta wajen yana burgeni, amma ban ta ba ko mafarkin shiga ba sabida nasan sama ta yi wa yaro nesa, nasan a gida babu wanda zai bar mu zuwa wajen, sanan mijin da zan aura ba lallai mai irin wanan yawace-yawacen ba ne, amma Mus ab kwana biyu yana kokarin cikamun duk wasu buri ka na.



Vip mu ka shiga, komai aka kawo mana shi a mutumci da cafasity din mu, wajen a nutse a gyare ya yi masifar kyau da burgeni. Menu din wajen ya mikomun mai cike da jerin da WaWan girke-girken da ke wajen, komai mai tsada ne kuma mai dadi.  Ka zaba mana kawai. na fada sabida har yanzu ban jin wani kwarin jiki na ko dadi.  Mai yasa?, ki za Sa mana tare fa da mijinki kike ba saurayi ba. tsaki na ja cikin rai na, na kara dubawa. Haka na zabi abinda nasan zan iya ci da cinyewa na ba da,  yan mintina kalilan aka kawo mana.



Awanni kadan muka dauka a can mu ka kama hanya mu ka dawo.  Ranki ya dade mai yasa bakya son sakik jiki da ni ne, ba dukan ki zan yi ba, ba zagi ba, ba harara ba. Shiru na yi ban ce komai ba har mu ka shiga gida, haka na fito daga motar na yi cikin falo.  Dan Allah ki tsaya na yi magana da ke, ba danni ba ba dan halina ba, dam darajar iyayenmu. tsyawa na yi cikim falon bayan na sami waje na zauna.  Salma, zan fada miki abinda ke zuciyatah, zan gaya miki girman Soyayyarki a zuciyata, ko da ba zaki so ni ba zan so ki rage wata kiyayya ta da ke cikin zuciyarki.



Ya yi shiru na  yan mintuna sanan ya ce.  Salma... akwai kalmomi da ba su da sauki a furtawa, amma yau zan furta su. A baya na sakawa zuciyata Sakata, na rufe ta ruf ba wai cike da ™iyayyarki ba, sai dai na san ban ta ba sonki ba, kamar yadda ban ta ba ™in ki ba... Na gina katanga tsakanin ni da ke saboda ganin Hajja na nuna miki Soyayya irin tawa, Salma ba ki ta ba yimun komai ba na ™i, ban ta Sa kai ™arar ki dan na tsane ki ba, sai dan ki gyara, ina so ya zaman gaba daya cikin gidan Galadima kin fi kowa nutsuwa da hankali, sai dai naga kinfi kowa rashin ji da taurin kai, duk lokacin da a ka dake ki ina jin babu dadi, sai dai ina saka ran zaki gyara. Salma ban ta ba jin sonki ba, kamar yadda ban ta ba jim tsanar ki ba, zance masrur kuma ba mutumin arziki ba ne tun ranar da na ganku tare ma gane shi, shine wanda ya yi rapping mai aikin gidansu Abokin, shiyasa na dage wajen kai karar ki tare da biayyarku a ko yaushe, Salma ban ga ba jin zan iya zare Sakatar da ke cikin zuciyata a kan ki ba, amma daga ranar da na ji iyayenmu sun yanke hukunci ha Wa aurenmu... sakatar zuciyata ta zare da kanta.



Legend's pen.



Page 40



 Na fara jin ki a cikin kowanne sashi na rayuwata. Muryarki na karade kunnena ko da ba kya kusa da ni. Abincina baya daWi sai na tunaki, Fuskar ki ce nake gani ko da idona na a rufe, kece kike zuwar mun cikin mafarki, ke ce yanzu ke ce har ibada a zuciyata. Salma, wallahi bana miki so na yau da kullum bana miki so irin wanda ke ™arewa da jiki. Ina miki so mai tsarki, irin wanda idan na mutu, ya kamata a rubuta a kabarina:  Ya mutu yana sonta! 



Ya juyo ya kalle ni kai tsaye, idonsa a cike da hawaye masu zafi, amma yana dariya da kuma murmishi, sanan ya ci gaba da cewa. Idan har ana iya so har fuska ta canza kama, to Salma ni na kai nan. Ina rokonki kada ki saka ni cikin duhun da ba zan iya fita daga cikinsa ba, ki bani dama daya, ko da karama ce, domin zan kashe raina wajen nuna miki ™imar ki a wurina.



Dago ido na yi na kalleshi, zuciyta na mun wani abu da na kasa banbance mene, kawai na dauke shi a matsayin tsana mai girma, baki na na rawa amma zuciyata ta bude ta na kokarin yin maganar da ni kai na ban san me zan ce ba.



 Mus ab& naji kuma na saurari kalaman ka. Amma ka tuna, ba duk kyawun magana ke tsinkewa cikin zuciyar da bata so ba. Na riga na saka wa zuciyata sakata. Na rufe ta da ruf da ™iyayya. Ban taba sonka ba, kuma banza taba sonka ba, na san dai na karSe ka a matsayin mijin kaddara, mijin da iyaye da  yan uwa su ka yimun, amma ba jagoran zuciyata ba na karbe ka a matsayin mijin da iyayena suka zaba. Amma ko yau a ce babu ran iyayenmu, babu wani abu da zai sa na kara zama ko na awa ne a tare da kai,So ba dole ba ne. Kuma ni ban zauna da kai saboda so ba. Na zauna da kai ne saboda biyayya ga iyaye, amma zuciyata ba ta son ka, kuma ba ta da wajenka.



Shiru dakin ya yi,ba ka jin komai sai numfashin Mus ab, ni kuwa mamakin kai na ya cika nibda nayi wa yanan furucin sai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login