Showing 39001 words to 42000 words out of 62407 words

Chapter 14 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

mutanen da zamuyi inviting amma ta ™i kulamu.





 To sai ku kyale shegiya, kuyi ba ita.



 Ai Yaya Mus ab ya ce lallai sai mun yi da ita, duka mazajen za su zo da abokansu, sanan shi y Kama wajen.



 To kawai ku faWawa Ummah, dan nasan ita kaWai za ta tursasata, Abbah ba zai ta kura ma ta ba tun da dai bidi a ne.



 Yanzu ku ba zaku iya ma ta magana ba, idan muka fadawa Ummah za ta iya dukan ta.



 To ai gwanda a dake ta tun da ta mai da kan ta jaka, ko shi Yaya Mus ab Win ya yi magana da ita, dan ni ba zan ™ara shiga shirgin yarinya ba ta zageni.











Ina zaune a Waki, bayan na gabatar da Sallar isha i na ya shigo, ban amsa sallamar sa ba, bare na Wago na kalleshi. Zama ya yi gefen gado na, kasancewar Wakin nawa daga gado sai sif, sai kuma dreesing mirrior ne kawai a ciki.  Salma, kin kammala?. banza na yi da shi.  Salma ki yi wa Allah, ki yi wa Annabi, ki tsaya muyi magana, dan darajar iyayenki. Wagowa na yi na kalleshi alamun ina jin shi.  Salma,  yan uwanki sun shirya muku event, mai yasa ba zaki hallarta ba?.



 Sabida ban da ra ayi.



 Bangane ba ki da ra ayi ba, Salma wanan abu ne da kin san ya zama kamar al ada ko?.



 Su ai  ya yan ga ta ne,  ya yan da ake so a ka basu wa yanda suke so, ni wanne a ka yimun a ciki, har wane haWe kai suka yi, su kai ma dai ni bare, to ba za ni ba. daga haka na mi™e daga kan daddumata na haye gadao.  wallahi babu abinda zai kai ni, kenan ma ina murna da auren?. haka ya gama xaman sa ya ta shi ya fice.



Abu kamar wasa baki na ta matsowa, shirye-shiye na ™ara gaba, sai dai har yau ban sa ko abu Waya na cikin lefenan a idona ba, ban san wane kalal abubuwa ba ne a ciki, haka kuma Ummah ba ta ta kuramun sai na ga ni ba.





Yau laraba, yau ne za a gabatar da cocktail Win da suka shirya, ni dai ina zaune Wakin mu ko lalle ban yi ba, babban daWin da na ji Ummanah da ta tarka ta ni ta watsar, ko uffan ba ta ce mun a kan lamarin bikinan. Ina zaune Waki bayan na gama cin uban kuka na, tunawar da na yi duk masifa ta nan da kwana uku, an dauke ni an kai ni gidan Mus ab, na kwana a gidansa na ce albarka cin sa. Sallama a ka yi, yayan Abuja ce da su Yaya Aleesha, haWe girar sama da ta ™asa na yi, ba na ma so wani cikin su ya yi mun magana a kan waccan shirmen.  Salma, wajen ki mu ka zo. Wagowa nayi na kalle su sanan na ce. Ina jin ku.



 Salma, mun zo mu faWa miki gskyr da kowa ya ka sa faWa miki.



 A matsayin ku na wa?. sororo su ka tsaya suna kallona, ni kam ko a jikina indai iskanci ne ai gidansu ka tarar.





Legends pen.



Page 28





 Salma yanzu abinda kike yi kina tunanin ya da ce. Yayar Abuja ta faWa, wanda ita sai ynzu ma ta yi magana tun da su ka shigo.  Wai ni me na yi ni yanzu, kuka ku ka ga Ina yi, ko ihu na ke ina cewa ba na son auren?.



 Ba mu ga kina haka ba, amma Salma kin nuna wa kowa ba kya son auren nan.



 To Yaya zan yi ™arya ne?, ba na so.



 Nifa ga ni nake magana da mara kunyar yarinyar nan ba shi da wani amfani, mu ta shi mu sami uwarta mu gaya mata. Yaya Aleesha ta faWa, na Wago na watsa ma ta uwar harara, damam su  ya yan Maman kwata-kwata ba su da kunya, sai raina  yan gidan Galadima, ko da muna dangin ubansu ne oho?.  Duk wanan bai ta so ba, Salma za a zo ayi miki lalle ja da ba™i, sanan zaki je cocktail din Anjima.



 Yaya, dan Allah a bar zancen Cocktail din nan, ba na so wallahi, suyi abun su kawai.



 Shikenan, bari a turo mai lallen. shiru na yi ban ce komai ba, hakam ya nuna kenan a turo. Ta shi suka yi suka fice, ni kuma na kwanta.



³an mintina kaWan mai lallen ta shigo, ban nuna wani Sacin rai ba na mi™a mata hannun ta fara zana mun ja da ba™in, cikin  yan awanin ta gama zana mun ta fice. Su Yayan Abuja kuwa suna fita Mus ab ya tare su, daman shi ne ya turo su.  Ya kuka yi da ita?.



 Ta ce ba zata je ko event Waya ba, amma yanzu za ayi ma ta lallen. Bai ji dadin haka ba kwata-kwata, duba da yanda abokan su dayawa za su zo, haka za su ga Abdul da amaryarshi, shi kuma ko oho.  Ka kyale ta, tun da a ka samu nasara za tayi lalle to saura ma za ta yi.



 Bari na je kawai. daga haka ya fice, ita kan ta ta yi mamakin yadda Mus ab ya rikiWe ya koma masoyi ga Salma, bayan kowa ya san ba sa ga maciji.  Allah kenen. ta faWa tare da hucewa

Wajen karfe hudu na fire lallen nawa, ban ko tsaya na kalleshi sosai ba, sabida kar ma na ga ya yi kyau na ji daWi, gado na ™ara komawa na kwanta, amare da kam sun ta fi make-up.



Ummanah ce ta shigo Wakin, da sauri na ta shi daga kwancinyar da na ke, rabonta da shigowa Wakina ai an kwana biyu, sai dai kawai ta kirani ta ba ni magani na sha, tasan idan wani ne ya kawo ba sha zan yi ba. Zama ta yi kan gadon sanan ta kira suna na.  Salma. Wagowa na yi na kalleta, sanan na ce.  Na am.



 Salma, ki na son kullum ki dinga ba™anta mun, ki na son na zauna da Sacin ranki ko?. da sauri na girgiza kai, ina zubar da hawaye.  A ah Ummah.



 Salma a yanzu zamana da ke ya zo ™arshe, zaki ta fi gidan mijinki, amma kina so ki tafi ki barni da Sacin ranki ko?.



 A ah Umma.



 Na miki shiru ko za ki yi hankali, amma Salma kin ™i ko?, kowa sai ya yi magana a kan ki za ki ji daWi ko?. 



 A ah Umma.



 Salma a yanzu ni ka Wai na san yadda nake ji a jikina, kuma na tabbatar miki idan na je asibiti cewa za ayi jinina ya hau, Salma kin san Sacin ranki ne ya haifarmun ko?, Salma ko mutuwa na yi a yanzu wallahi kece. da sauri na Wago idanu na masu cike da hawaye na ce.  A ah Ummah, dan Alah ki yi ha™uri.



 Salma kin fi son duk lokacin da na tuna ki maimakon na ji sanyi a rai na sai dai na ji a kasin haka, Salma kin fi son duk inda za ayi magnar ki a aibata ki?.



 A a Umma ki yi ha™uri.



 kin san ai abinda ya kama ta, ki ta shi ki halallarci abubuwan biki.



 Tom Umma wallahi zani komai, kiyi ha™uri amma banda na yau, wallahi da na mi™i jiri ya ke Wi ba na.



 Salma ke kika jawa kan ki komai, bari na kira likita ya duba ki.



 To. kawai na ce na kwanta tare da rufe idona, ita kuma ta ta shi ta fice, na kudire a raina tabbas zan hallarci komai na bakin, ko dan na cika umarnin mahaifiyata ta yi farin ciki da ni, amma wallahi babu murmushi daya ko fara a a fuskata.





Mintuna kadan likitan ya zo, duba ni ya yi ya bani magunguna har da yimun allura bacci, sabida kwata-kwata ba na iya bacci, mintuna kadan kuwa bacci ya dauke ni.



Sai wajen karfe 12 na dare na farka, mi™ewa na yi na shiga toilet na Waura alwala, na biya ba shi salloli uku da ke kai na, ban nemi abInci ba na sake kwantawa.





Washe gari.





Wasai na ta shi babu inda ke mun ciwo, dama na Wauki aniyar gyara, zan hallarci komai na bikin da su ka tsara, ai hallarta ba ita ke nuna cewa ina son Mus ab. Ina cikin gyaran gado na ya shigo bakin sa dauke da Sallama, ban amsa ma sa ba,na ci gaba da abinda na ke. Ya jikin na ki?. kallon shi na yi kamar ya san tambayar shi na ke son yi aina ya san ban da lafiya.  Jiya Ummah ta sa ni na kira likita, bayan ya fito ne yakw cemun rashin ™warin jiki ne da kuma rashin bacci su ka haifar miki da ciwon kai. ci gaba na yi da aiki na ban ce ma sa komai ba.  Jiya anyi cocktail, kin san wacce ta zauna amadadinki?. ji nai rai na ne neman Saci, ina ruwana da wacce ta zauna amadadina?.  ™awarki ce. A fusace na ce.  To ina ruwana da wacce ta zauna amadadina, mene ya dameni dama aurenta ka yi zai fi ma. dariya ya yi sanan ya ce.  Salame ashe ana kishi. wani abu naji ya ma™alen mu a ma™oshi, ni Salma na gamu da alheri, Mus ab dole sai ya sa ni magana.  Dan Allah Mus ab ka fita sabgata, ka fita a harkata dan Allah. ta shi ya yi ya fice, na ci gaba da abinda na ke,  yan mintuna kaWan sai gashi ya shigo da abun breakfast.  Yau tare da matata zamuyi karin kumallo.



 Dole sai ya sa na zage shi zai ji dadi. amma Ummanah ta mun Allah ya isa, duk ranar da na ™ara zagin Mus ab, ko na yi masa Allah ya isa.  Habibty ki zo muyi breakfast. fi cewa na yi daga Wakin na fito falo, mutane ne a falon ta cikinsu na ratsa nayi kitchen.  Ummah ina abin brealfast dina?.



Legends pen.



Page 29





 Wanda Mus ab ya shiga da shi ciki na uban waye. shiru na yi kawai na kama hanya na fice, ko ina na gidan a cike yake da mutane, Sangaren Maman ciki na shiga, shima cike da mutane har ya so ya fi namu cika, da kyar na kutsa inda ta ke na ce.  Amma a bani abin karyawa.



 Yanzu fa Mus ab ya fita da abincin ya ce ke zai kai wa. shiru na yi a raina ina cewa.  Shi dai wanan ina ga ko ina sai da yabi ya ce zai karSaemun abinci. fi cewa na yi na nufi Sangaren Hajja.  ina ma™il. na faWa a raina ganim inda ya cika ya cike da mutane, ta dole na koma Sangaren mu. Yana cikin dakin inda na bar shi zau ne, zama nayi daga gefe na fara cin ™osan da ke cikin plate din, fuskata a daure kamar zan kai mai duka. Haka na ci na sha tea din, da magani na na kwanta.



Sai wajen karfe hudu na shiga wanka, mai kawai ma shafa sai powder ita ma sama-sama, kayan da zan sa ma kawon mun a ka yi, na dauka na saka ko abun na din kan ma da kaina na nada, sanan normal naWi na yi ba kalal na amare ba.



Da kan shi ya zo ya fita ni, yau ko ina sai yabona ake ni dai na hade rai kamar wacce a ka yiwa mutuwa.



Haka mu ka je wajen event din, ban yi murmushi ko na secon daya ba, har a ka ta shi, washe gari kuma a ka yi daurij auren su Walida da Abdul, Sadiya da Umar, da yamma kuma a ka yi kamu wanda iyayn mu su ka shirya. Harabar gidan mu a ka yi uban decoration. Yu dai dole sai da a kayimum make-up sabida anfi karfina, amma gaba daya kamar ko yaushe banyi wata dariya ko murmushi ba.





Haka a ka gama event wajen karfe 07:30 a ka watse, amare suka shirya kowacce za a huce da ia gidan mijinta, zo kaga kuka wajen Salma Galadima, ihu nake kuka nake kamar wacce ta ra sa iyayenta duka biyu. Duk kukan nawa haka a ka fice da ni daga gidan Galadima mu ka nufi Malali G.R.A. Kuka na ke kuma duk  yan cikin motar sun yi mun banza, babu mai ce mun ci kan ki, a haka mu ka shiga makeken gidan malali. Kowa sai yabo da santin gidan ya ke, amma ni ban ko kalli waje daya cikin gidan ba.



Haka suka gama abun su su ka barni ni ka Wai, kuka na nake yi hankali na kwance, hankali na ya koma yadda za ayi Mus ab ya sake ni, na san babu wani abu da zai sa Mus ab ya sake ni, sai dai idan na takura, amma idan ya sake ni na je ina, nasan Abbanah ba zai karSe ni ba, amma dai dole ya sake ni.



Ina wanan tunanin naji alamun shigowarsa, da alamu shi kadai ne tin da babu hayaniyar abokai, tun da zu na ke som rufe dakin amma na jira ya zo muyi magana, dan wallahi ba zan kwana da auren sa ba. Ina zaunen ya shigo, bai ™arasa zama ba na yaye mayafi na, na dago na kalleshi.  Mus ab, ka ga ka ci nasara an kawo ni gidanka, babu abinda ya yi saura, dan haka ka taimake ni ka sake ni. kallo na ya ke yi sosai, bai ta Sa tunanin zan kawo maganar saki a duk tashin hankalin zaman da zamuyi ba, ya zama dole ya ja mun kunne a kan maganar sakin nan.  Salma, Saki kike magana?, to ki cire wanan a ranki domin auren mu aure na har abada, babu abinda xai rabamu.



Washe gari.



BuWe ido na yi, na ™arewa Wakin Kallo.  Yau dai na kwana a gidan Mus ab, matsayin matarsa. Kuka na fara yi ina kwancen, sai da na Wauki kusan minti 30 ina kwance ina hawaye, sanan na ta shi, kallon ™ofar Wakin na yi, na tuna kulle ™ofar da na yi bayan ya ta shi zuwa waje, toilet na shiga na watsa ruwa, sanan na Wora alwala, na fito na ta da Salla, zama na yi gefen gado ina kallon Wakin, yanda ya ke da girma kuma ya tsaru, an kashe zallan dukiya a Wakin.  Salma, mene mafita?. na yi wa kai na wanan tambayar, shiru na yi ina son na sami mafita, nasan dai wanan ™addararen auren yanzu a ka fara shi, duk da cewar idan na ta da har gitsi zai mutu.  To me zai hana na ta da har gitsin, ko zan tayar a sa a auren ya mutu. Ta shi na yi na buWe kofar Wakin na fito falo, falon kam ya tsaru shima, ya sha ado sosai da sosai, ga wasu hotona nan da na shi da a ka yi musu frame na gaske mai kyau da Waukan ido, duk da dai ni ba su Wauki na wa idon ba. Zama na yi kan kujerun Wakin, na Wora ™afa Waya kan Waya, ina jiran ya fito mu kwashe uwar sabada, ko Allah zai sa na da ce.  Ina kwana Salame. mi™ewa na yi tsaye, tare da juyawa na kalleshi.  Mus ab, kar ka ™ara so inda nake. Tsayawa ya yi yana kallona sosai, cike da mamaki, da™yar ya iya tambaya ta.  Me ya sa.



 Mus ab kar ka zo ku sa da ni, na tsane ka. Murmushi ya yi, snn ya ce. Kiyi ha™uri Salma, ba ni na jaranci kai na da son ki ba,Allah ne ya jarabce ni, kuma ba ki isa ki canja nufin ubagijia ba.





 Ni ma kuma shi ya jarabci ni da ™in ka, da tsanarka. Mus ab ka saki ni, ka sake ni na tafi gidanmu ko da iyaye na za su kashe ni, sai dai su kashe ni,amma bazan zauna a matsayi matarka ba. Matsowa inda nake ya yi, tare da kama hannuna. Da sauri na fincike hannuna tare da faWin. Kar ka kuskura ka ™ara ta Sa ni Mus ab, idan ba haka ba wallahi zan yi maka abinda ba ka yi tunani ba. Dariya ya yi, sanan ya ce.  Me za ki iya yi mun Salma?. Tsaki na ja sanan na ce.  Natsane ka Mus ab, kuma wallahi sai ka sake ni.



 Salma ki dai na yawan rantsuwar nan, kuma kalmar tsana da na ce tana mun zafi ki dai na faWa, dan Allah kar ki dai na faWa, ki mayar da ita lazimi. wani malolon abu ne ya sakko mun zuwa ma™oshi, na kai hannu na jawo da ™arfi tare da faWin.  Wallahi babu inda zaka sai ka sake ni.



 Wallahi Salma banga wani abu da zai sa na sake ki ba, ko da ba na sonki, zan yi biyayya ga iyayena tun da sun ba ni ke, bare kuma ina son ki. Hannu na kai na ™ara jawo shi baya, tare da faWin. Ka sake ni. shima hannun ya sa ya fin ciki jikin shi, kawai na kai hannu na sha™e shi.  Wai Salma ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login