Showing 6001 words to 9000 words out of 62407 words

Chapter 3 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

ya tafi, ni kuma na koma ciki.



Kamar wata Sarauniyar da tayi sata aka kamata haka na shiga cikin Wakin. Sai dai duk cikinsu babu wacce tace da ni ko uffan, hakan yasa nayi matuar damuwa. A hankali na ce."Umma, mai walida ta ce muku?." banza Umma tayi dani kamar ba taji ni ba, kuma nasan taji, hakan yasa na koma ga Mama. "Mama mai walida ta ce?."



"Mai kikaji wani yace miki?." Na girgiza kai na ce."Bakomai."



"To kuma, ko kinyi wani abun ne?." na girgiza kai kawai, can 'yan mintina na ce. "Walida ta so mu tafi." ba ta kai ga magana ba likita ya shigo Wakin. Bayan sun gaisa yace da su Ummah.



"Ban san wane likita ke duba Mus'ab ba, kuma ko ma wane akwai matsalal da ba daga likitan mu take ba, dagashi yaron ku take."



"Matsala kuma likita?." Mama da Ummanah suka tambaya, har wani hade baki sukeyi. Ni kam a raina na ce. "Allah yasa matsalal mutuwa ce." maganar likitan ce tasa na dago na kalleshi.



"Eyh matsala, domin gaskiyyya ba aina hin ciwon dake damunshi ake fada ba, kuma da masaniyar sa domin ko magungunan da ake bashi, na asalin ciwon sa ne. Kunga kuwa sun hada baki da likitan suna Soye muku.



Wani daWi naji a raina, domin nasan babban ciwon ne kadai ake boyewa iyaye ba'aso su ji sabida kadan hankalinsu ya tashi.



"To yanzu likita wane ciwo ne, na gaskiyya dan Allah." Ummanah ta fada kaman zatayi kuka, wani ululun abu ya tsayamun a ma oshi yanda matarnan ta damu da Mus'ab ko ni bata damu dani ba, ji yanda take magana kaman zatayi kuka.



Abban ciki ne yayi sallama, tare da Kawu mudi da kuma Yaya ilyasu. Shigowa sukayi baki dayansu, nida walida muka koma can gefe muka basu basu waje, kasancewar dakin babbane.



"Kai ka sa tsohuwar mutane cikin damuwa." Yaya ilyasu ya faWa. Likitane ya ci gaba da cewa."Kamar yanda na fada muku, matsalal shi ba ciwon kai bane kwata-kwata." da sauri Abban ciki yace. "To menene?."



"Matsala shi a ciki take."



"To amma mai yasa duk bayanan ku na baya yake nuna kai."



"A'ah ranka yadaWe, ko a file na asibiti cike ne, sanan magungunan da yake sha ma na ciwon ciki ne, kawai su na ambatar kai ne domin Soye muku."



Ina daga gefe na fara addu'ar, Allah yasa afendes ne yanda za'a yanka shi karshe a ce ya mutu.



"To yanzu likiti menene cutar?." Abban ciki ya ara tambaya, Likitan ne ya fara duba takardun hannusa, nikam hankali na kanshi.



" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba bace, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.



"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"





Legends pen.

(08165383931/ 08129553971).







Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, 500 kacal ne sai kuma masu buatar complete 1000.



Payment via.



8129553971

OpaY

Sani Muhammad lawan.



Shaidar biya.



08165383931.

*SAKATA*d'&



<;Stroy and written<;

By

Sayyid writer (Legend)
'





*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*



*(FUWA)=؋=*



SHAFI NA BIYAR

(P.05).



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE





" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba ba ce, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.



"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"





" He have been diagnosed with a rare condition called Hypersexual Hormonal Disorder HHD. It means His body produces an unusual level of sex hormones beyond control. That s why kake yawan jin wani irin zafi, idan kana ciwon cikin. Kuma irin wannan sha'awar ba irin wacce ake iya da ilewa ba ce,da ile ta da yayi na kwanakin baya yasa ta zama babba har haka."



"Wannan wace irin cuta ce haka, nifa bangane komai ba?." Mama ta tambaya cike da ruWani. "Nima dai." Ummanah ma ta faWa.



Yaya Ilayasu ne, ya kallemu ni da Walida yace."Ku fita." Sim sim sim kamar munafukai muka fice, ni dai burina a ce mutuwa zaiyi.



Bayan munfita ne likitan ya kalli su Mama yace.



"Yana fama da wata irin cuta mai suna Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana jikinsa yana fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Wanan ne dalilin da yasa yakw yawan jin wani irin zafi, da kuma wata sha'awa mai arfi wacce har ta kan iya kayarda shi asa."



"Inullahi wa'inna illahir rajiun." su Mama suka shiga maimaitawa, likitan yakara da cewa."Tun farko bai bari anyi dogon bincike ba, a kan rashin lafiyar tashi, gashi har abun ya zama worst haka, ko kunyar ku yake ji oho."



"To amma fisabillillahi, ko da yanajin kunyar mu bashi da 'yan uwa maza. Kawai sabida rashin kula da lafiya." Ummanah ta fada cike da damuwa.



"To yanzu likita menene ai nayin maganin cutar?." Abban ciki ya tanbayeshi.



"There s no drug-based cure yet. But in most studied cases, emotional stability and natural intimacy especially within marriage. help the body regulate the hormones over time. Auren na iya zama magani a gareshi."



"Shikenan likita, insha Allahu za'ayi." Abban ciki ya faWa, likitan yakara da cewa."Yanzu za'a rubuta mishi drugs da zai na amfani dashi, zasu taimaka sosai da sosai."



"To mungode." Ummanah ta fada, likitan yasa kai ya fita, Mus'ab kam idonshi a kulle angama to na mai asiri yanzu kowa sai yasan halin da yake ciki.



"Yanzu fa Mus'ab da ka mutu d Wanan ciwon, baka da maraba da wanda yakashe kansa, kasani kuwa." Maman ciki ta fada murya a sanyaye, Ummanah ta dora da cewa. "Mus'ab, a duniyar nan babu kamar iyaye, ba'a Soye musu komai domin kowacce mafita tana daga garesu, ka bar ganin mun girma har mun haifi kamarku, duk wata matsala idan tataso mana, idan har mijinmu bazai iya magance mana ba, to iyayen mu muke nufa da ita." Tashi Abban ciki yayi ya fice, domin yasan duk abinda zai iya fada, Maman ciki da Ummanah zasu faWeshi. "Kuyi hauri..." ya faWa cikin sanyin murya, Ummanah ce tace. "Dan Allah ko dan gaba ku kiyaye baki Wayanku."



"Tom insha Allahu." Yaya Ilyasu ya faWa, sanan yace dasu Ummah. "Jiya masu neman auren Sadiya sun sake zuwa, a kace dasu sudawo yau."



"Lallai ne, Sadiya lokaci yayi." Maman ciki ta fada, inda Yaya ilyasu yace. "Saura Walida da kuma Salma, su kam kamar ma ba za su kai candy ba."



"Eyh kam, bazasu kai candy ba." Ummanah ta fada, Maman ciki tayi murmushi. Can sai ga Abban ciki ya shigo,rike da ledar magunguna.



" Gashinan, suma sai kayi wasa da shan su." Maman ciki ta amsa ba tare da ta cw komai ba.



"Ni zan koma gida, zan samu Hajja nayi mata bayani, Muji abinda zata ce."



"Tom shikenan."Maman ciki ta fada, shikuma yasa kai ya fice.



Muna zaune daga gefe ya fito, da sauri muka taso tare da cewa."Abba zamu tafi muma."



"A'ah ku xauna mana, ko za kuyi musu wani aikin."



"Ai Abba zamuyi girkin rana, sanan mu na da islamiya." na fada sabida ni hankali na, na kan na koma gida nayi sadakar alewa, zan kaWeWen saurayi kamar Masrur ya ce yana so na, shine sabida nice nafi kowa butulci ba xanyi sadaka ba.



"Shikenan ." ya fada tare da fita, Walida ce ta koma daki tayi musu sallama, nikam bayan Abba nabi sabida tsoron karma ya tafi ya barmu.





Muna arasawa gida na sauka nayi Sangaren mu, ban arasa ba naji muryarshi na cewa. "Ki cewa Abbanki ya same ni Sangaren Hajja."



"Thom." na ce sanan na ci gaba da tafiya, shi kuma ya juya ga walida. "Kira mun sauran kawunnanki." itama "Tho." ta ce, ta tafi kiransu. Ina shiga na tarar da Abbanah ya gama shiryawa. "Abba mun dawo."



"Toh sannu da dawowa, ya jikin na sa?."



"ya warke." na faWa a gajar ce, sai kuma na ara ce wa. "Abban ciki, ya ce ka same shi Sangaren Hajja."



"Ya dawo?."



"Eyh, shine ya dawo da mu."



"Okay." daga haka ya fice, ni kuma nayi cikin Waki. A Sangaren Hajja kam, gaba Wayansu ne zaune sun sa Hajja a gaba da kallo. "Ni wai lafiyan ku?, kun haWu kuma kun bini da idanu." Hajja ta faWa, sai kuma ta ce. "ko dai Mus'abu ne ya mutu?."



"A'ah Hajja, ba mutuwa yayi ba amma akwai matsala."



"Tsarin ubangiji muke nema a kan kowacce matsala." Hajja ta faWa, Abbanah kuma ya ce. "Yanzu Salma ke ce mun ya warke."



"Eyh hakane, su za su ga kamar ya warke. Amma a bayanin da likita ya yi mana, ya ce ba cutar ciwon kai ba ce ke damun Mus'ab tun farko, ya Soye mana ne."



"Waye ya Soye mana?." Abbanah ya faWa cike da fushi, dan shi a tunaninshi likitan ne yanzu ya je suyi Wauki ba daWi, dan duk gidan Galadima babu wanda ya kai Abbanah fushi, da zafin zuciya.



"Shi Mus'ab Win."



"Innullahi wa inna illahr rajiun, yanzu wace cuta ce haka zata kashemun jika na, Wan lele nah?."



"Mus'ab, na fama da wata cuta wai ita Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana dai jikinsa ya na fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Shi ke haifar masa da wanan ciwon cikin."



Kuka Hajja ta saki tare da faWin."Nashiga uku na, shiyasa nake ce wa yaron nan cike ke masa ciwo ba kai, sabida idan ciwon yayi zafi ciki ya ke riewa ba kai ba. Amma ya ce wai A'ah, yanzu idan ciwon ya kashe shi ina yake so na sa ka kaina."



"Kiyi hauri Hajja." kawu Mudi ya faWa. Abban ciki ya Wora da cewa. "A yanzu likita ya ce hanyar samun saui guda Waya ce, ayi masa aure." Abbanah ne ya ce. "Abinda ke raina kenan, dama ai akwai yarinyar da ya ke nema ko?." gyaWa kai Abban ciki ya yi, sanan ya ce. "Amma ya na da kyau idan anje neman auren a sanar da iyayen komai."



"Salan su hana shi, to wallahi ba da yawo na ba." Hajja ta faWa. "Yaya ba fa cewa sukayi ya na da Mentel disorder ba, kuma ba cewa su kayi ya na sa yawan buata ba. Dan haka wanan ai ba matsala ba ne." Abbanah ya faWa, Hajja ta cafeshi da ce wa."shine dai, yanzu ina so ku tashi daga nan kuyi gidan iyayenta a ba su komai da komai harda sadaki."



"Shikenan, amma ni ai babu ni za'a je ko?." Abban ciki ya faWa da alamun tambaya ga Hajja. "Uhmmm." ta faWa a gajarce, sai kuma ya ara cewa. "Su ma masu neman auren Sadiya fa?"



"Naga dangin Mahaifiyar ta ne, Wan gidan Yayar Mahaifiyarta uwa Waya uba Waya. Ba najin sun cancanci a hana su, duba da Mahaifinsa kowa yasan shi, tarbiyar gidansu ba Soyayye ya baci." Abbanah ya faWa.



"Sanan yaron yana zuwa nan sosai da sosai, haka mahaifiyarsa." Itama Hajja ta faWa.



"Shikenan, sai a ba su watanni. Amma kuna ganin za' a haWe dana yaron nan."



"A'ah kar ku fara, banason auren sa ya huce wata biyu fa." Hajja ta faWa cike da damuwa. "Shikenan." kawai suka ce sanan suka fice, dole sai sunyi tasu shawarar a waje.







Ina shiga cikin Wakin mu, nayi Sangaren Ummanah. asan kayanta na shiga du bawa, nasan nanne wajen ajiyar kuWinta. Cikin sa' a na gano su, naira dubu daya na dauka na ara da Wari biyar cikin canji mota na, na fita siyo alewa sadaka. Shagon bayan gidanmu na je, na siyo lolipop mai tsinke, har leda biyu a cewa ta "idan zaka gode wa Allah, ka gode ma sa da babban masaki sai ya ara ma ka da wanda ya fi wanan girma."



Ina dawowa harabar gidan mu, na fara walawa yara kira ina faWin."Sadaka, sadaka." cikin an anin lokaci yara su ka fara ta ruwa cikin gidan mu. Daga na cikin gida har na waje, ni kuwa faWi nake. "Duk wanda ya karSa ya ce Allah yabar auna." ai kuwa da sun amsa za kiji suna cewa. "An gode, Allah ya bar auna." na cafe da. "Amin." abuna, zuciyata shar, Allah ya bani zankaWeWen saurayi da ga sama.



Walida ce ta fito wajen da na ke sadakar, ta kalli ne ta ce. "Sadakar mecece haka kuma?." Jin wani yaro ya ce. "Allah ya bar auna, yasa ta bi ni da idanu, ni kuwa na murje na ce. "Menene a ciki?."



"Ce wa yayi yana sonki?." ta tambaye ni. "Ba ke uwar munafukai ba, a faWa miki kije ki ya Wa mutum."



"Ya za'ayi na ya Wa ki?."



"Walida da ban san halinki ba." na faWa ina ci gaba da sadaka ta. "Wallahi ba zan fada ba."



"To ce wa yayi ya na so na, har da ba ni lambarsa." na faWa hankali kwance.



"Lallai ne, ki na cikin Alheri. Kin san Sadiya ma an ba da ita?."



"Naji ishin-ishin dai." Na faWa, ni dai hankali na na kan 'yan sadaka. Ganin kamar ta ji babu daWi ya sa na ce. "Yanzu ke ma sai ki yi wa, Haidar magana kawai a kwashe mu."



"kina ganin Haidar zai yi aure yanzu?." ta tambayeni cike da damuwa.



"Mai zai hana shi tun da ya na sonki, ko ma ba za yi ba menene a ciki. Sai ki bawa wasu dama."



"Ni kam na fi sonshi."



"Sai ki zauna ki jirashi, ni dai wallahi ko yanzu a ka ce za'a Waurawa Masrur ne bin shi zanyi, na zauna na yi uban me a gidan?." Na faWa ina murguWa baki, kamar gaban iyayen nawa nake.



arar tsayawar Napep ya samu Wagowa tare, Su Ummah mu ka gani. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zangaye ni su na faWin."Allah ya bar auna."









Legends pen.

(08165383931/ 08129553971).







Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, 500 kacal ne sai kuma masu buatar complete 1000.



Payment via.



8129553971

OpaY

Sani Muhammad lawan.



Shaidar biya.



08165383931.

*SAKATA*d'&



<;Stroy and written<;

By

Sayyid writer (Legend)
'





*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*



*(FUWA)=؋=*



SHAFI NA SHIDA

(P.06).



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE







arar tsayawar Napep ya samu Wagowa tare, Su Ummah mu ka ga ni. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zagaye ni, su na faWin."Allah ya bar auna."



Sakkowa su ka fara yi daga cikin Napep Win, idanu na suka sauka a kan sa, a raina na furta. "Ya dawo bai mutu ba." na ja tsakin da ya fito fili, har Walida ta kalle ni, sai kuma na sake ce wa. "Kai ka Wai dai za ka ci tsiyarka, ni kam lokacin ta shi na daga gidan Galadima ya yi."





"Sadakar me a ke yi kuma?." Umnanah ta tambaya, bayan sun araso inda muke tsaye. BuWe baki nayi zan fara wa'in- wa'in yaron da yake gaba na ya ce. "An gode, Allah ya bar auna." da sauri nayi asa da kai na, ban san da wane ido ne zan kalli Ummanah ba, Maman ciki kam ce wa tayi."aunar wa?." Shiru mu kayi nida Walida, nasan dai Walida ganin ina wajen yasa ba ta faWi komai ba, amma da ba na wajen tuni ta shai da musu. Ummanah ce ta ce."Ku shigo da kayan." sanan ta huce, Maman ciiki ma ta huce. Ido nasa na kalleshi, wata irin tsanarshi mai nauyi ta durga a irjina, ni ke nan ba zanyi masa mugun fa ta ya kama shi ba, duk da haka ba zan gaji ba."Allah ka gama shi da masifar duniya da ta lahira." na sake faWa ina daukan kayan. angaren Hajja suka nufa, mu kuma mu kayi bangarensu. A raina naji dadin dawowar Ummanah, ko ba komai zan Wauki wayarta na kira Masrur.







Ban daddara ba, na mai da lolipop Wita jakar islamiya ta, a ce wa ta idan na fita nayi sadakar a bata, dan wallahi sai na nunawa Allah godiyata da yabani kyakyawan saurayin kamar Masrur.





arfe Waya da rabi nayi shirin Islamiyya, bayan na Wau jaka ta na fito falo na ce da Ummanah. "Na huce." tsaya ki mika wa Mus'ab doyar nan. TurSune fuska nayi sanan na ce. " Na ma kara fa."



"To sai kin kai, ko abinda ya fi makara kika yi. Wai ni Salma yaushe ne zaki dai na yi wa Mus'ab wanan iyayyar ne?."



"Au ni ce nake insa?." Na faWa a raina, a fili kuma na ce. "Ni ba insa na ke ba, kawai ba na son kowacce kalal alaa ta haWa ni da shi."





"Sabida ba Wan-uwanki ba ne ko me?."



"Umma kawo na kai."Na faWa domin son tsayar da waccan maganar. "Salma ba fa ke ce kika haife ni ba, kin san da haka?." shiru nayi, ni ba na son a ci gaba da maganar, domin har cikin rai na ba na son wani abu da ya shafi Mus'ab a rayuwata.



Ina tsaye ta gama soyawa ta mio mun."Sa a plast ki mia mai." ban ce uffan ba, na Wau plast Win na zuba. Ga ba daya na juye a plast din na kama hanya na fice, na fito daga Sangarn mu zan nufi Sangaren su na ga Sadiya ta dawo. Washe baki nayi da faWin. "Ka ga amarya, shine kika kwashe afa ki ka tafi, wato sai da a ka ce an basu shine ki ka dawo." Dariya tayi sanan ta ce. "Wallahi dazu Amina ta ce mun, Mal isah ya ce sai ya Sallani, shine ki ka ga na kwaso afa na dawo."



Dariya nayi sanan na ce."Ba kunya ki ka tafi gidan su saurayi ki ka zauna."



"Yoo kunyar wa zanji, ina shan zumar auna." ta fada ta na fari da ido."Uhm bari na mika wanan Sangaren Hajja, amma kafin nan tsaya ki amshi sadakar ki." na fada ina a jiye plast Win a asa. "Sadakar me?." ta tambaya ne da mamaki. "Allah ya kawo mun masoyi, na kece rai ni." Na faWa ina mia mata alewan."Ki ce mun kusa barin gidan Galadima."



"Mun kusa fa." na fada ina hucewa, ita ma tayi bangarensu. A hankali nayi sallama, amma ba'a amsa ba hakan yasa na shigo ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login