Showing 18001 words to 21000 words out of 62407 words

Chapter 7 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

zuciya ta sauke, sanan ta ce. Salma yimini bayani dan Allah.



 Wai wane bayani Yaya.



 Mai yaja auren, kuma mai ya kawo maganar. gani nai kamar tafi damuwa da shi, hakan yasa na ce.  Idan na mutu, kece zakifi kowa rashi. daga haka na kashe wayar, nayi wurgi da ita gefe, na shiga tunanarwa kai na mafita.



Ina zaune Sadiya da Walida suka shigo, ta shi nayi na nufi cikin Wakina, sabida banason ganin kowa cikinsu domin duk kansu munafukai ne, ba barin Walida ma.  Haba Salma, ko kowa yayi miki laifi, gani nake mu ba ma cikin masu wanan laifin Salma. Sadiya ta faWa, shiru nayi dan zan iya sauraron maganar Sadiya a kan ta Walida.  To menene?. na faWa, fuska fal da hawaye.  kiyi hauri Salma, ki zauna ki nemi mafita. Walida ta faWa, tana koarin matso ni.  Ku kyale ni kawai, gwanda na mutu domin rayuwata ba ta da amfani, da zama da Mus ab a matsayin mata da miji, gwanda zamana a gidan bariki. ina faWin haka na shige Wakina. Tabbas dole na bar gidan Galadima, domin zama a gidan ba nawa ba ne, barin gidan shine hanya ta farko, kuma mafi saui ta in auren Mus ab, amma idan na bar gidan Galadima ina zani, ina na nufa?, na san dai ba zan je gidan dake da alaa da Galadima ba na zauna, sai dai ko dangin Mamana.



Haka nai ta famam tunanuka kala-kala, a arshe na yanke shawarar haura da duk wani jindaWin duniya, na haura da komai, gida mai kyau, abinci mai kyau, suttura mai kyau, gwanda naje nayi rayuwa a matsayin mabaraciya mara komai, a kan na zauna na auri Mus ab. Kayan jikina na kalla, leshi ne mai kyan gaske, tashi nay na shiga Waki na cire, gwanda na fita a matsayin mara gata mara komai. Canja shi nayi da wani bakin material Win na, mara nauyi kuma mara kyau dan ya dad e, ni kaina na kwana biyu ban sa ka shi ba, haka Wan kunnen kunnena na cireshi, na saka wata aramar barima, dan tabbas na haura duk wani jin daWin duniya, gwamda na fita nayi bara, nayi sana a na samu kuWin kai na, wani silafas na Wauka na saka, na fito kamar wata almajira.



Sai da na lea sosai, na ga ba kowa sanan na fita a guje, dai-dai lokacin da Yaya Ilyasu ya fito daga Sangarensa, da sauri shima ya yo wajen amma ina, kamar nasan za abiyu ni na shige gidan ku sa damu, ganin ba kowa a wajen ya sa ya koma. Inda ya ci karo da Ummanah ta fito daga Sangaren Hajja.  Lafiya dai ko, naga ka shigo kana zare ido. Ummanah ta zolayeshi.  Wallahi gani nai kamar an fito daga Sangarenki, anyi waje kuma na lea ban ga kowa ba.



 angarena kuma?. Ummanah ta faWa tare da shiga ciki.  Salma, Salma. ta fara walamun kira, amma shiru.  Wai daman Salman na nan?. Yaya Ilyasu ya tambayeta.  Eyh, anan na barta.



 chaS, aikuwa ita ta fice. ya faWa tare da yowa waje, gidajen kusa da mu ya fara shiga, amma ko ina sai a ce bana nan, ko ban shigo ba.



A Sangarena kam, ina shiga gidan na Soya bayan ofa, ban fi minti biyu ba na fito, tunanin inda zani na fara, sai dai kuma dare ne.  Ina na nufa?. Na tambayi kai na, tuna wa nayi da wani Waki da ke zauren gidan Alhaji idi me mai, Waki ne da ke babban zaurensu, a rufe ma yake, amma mu da idan muna wasa mun san hanyar da muke shiga Wakin ta cikin ta ga, nan na yanke shawara zuwa na shiga zuwa da safe, babu wanda ya kula da ni, ya ga shi ga ta ko hucewa ta, dan ko mutum ma ya ganni banjin zai iya gane ni, dan nayi kala da mabarata.





A hankali na shiga gidan, na Wane tagar na shige cikin Wakin da sauri, ba tare da kowa ya ganni ba, duk urar dake d akin ba ta dame ni ba, haka na samu waje na kwanta ina faman tunanin makomata, gobe idan na tashi ina nufa?,





Tun Ummanah da Yaya Ilyasu na duba na asirrance, har abu ya fito gida kowa da kowa ya shiga nemana, abu har mawaftan mu. Hankali kowa ya tashi cike har da na Ummanah da Mamana ciki, dan ita Maman ciki har da hawayenta, Hajja kam salati tasaki tare da cewa. Kai amma wanan yarinya anyi  yar jakar uba, har tayi wayon da zata ce zata bar gida?. Walida da Sadiya suke yawo gida-gida nemana, fuskarsu sharkaf da hawaye. Ina jin sanda su ka shigo gidan, Alhaji idi me mai nemana, amma kasancewar babu wanda ya san na shigo, hakan yasa a ka ce da su ba na nan, Mama ce ta Wauki waya ta fara kiran mutane ita da Anty, ita kam Ummanah ta tsaya tsaye kamar gawar sababi, tunani take ina zan iya zuwa?.  Walida ina ne gidansu saurayin na ta. Ummanah ta tambaya.  Wallahi Umma ban sani ba, ita ma kan ta ba ta sani ba, domin ranar da mu ka zo asibiti ranar suka fara haWuwa.



 Haba, ya ma za ayi ta je gidansu sauray, dole tana gidajen  yan-uwa, kuma ina kyautata zataon arasawa ne ba tayi ba, shiyasa kowa yake cewa ba ta zo ba. Anty ta faWa, dan dai kowa yasan bazan iya bin saurayi ba.  Yanzu mai Salma take son ta zama?. Ummanah ta faWa kamar za ta yi kuka.  Babu wani abu sai Alheri, Allah ya riga da ya tsara komai tun kafin yanzu. Anty ta sake faWa, dan ita Maman ciki ta zabga ta gumi.



Abbanah ne ya shigo, kasancewar Yaya ilyasu ya kira su duka ya faWa musu, kana ganin Abbanah kasan ya je arshe a fusata, bayansa Abban ciki ne, shima ranshi ya Saci sosai. Hannun Abbanah rie da wata babbar leda wacce ba wanda yasan menene a ciki. Wai mutane da ka kira a waje na menene?. Abban ciki ya faWa yana tambayar Abbanah.  Yaya ka kyaleni, ba ita gani take ta isa ba, to wallahil azim cikin daren nan za a Waura musu aure, kuma ban laminci ko da an nemo ta ta dawo gidanan ba, sai dai ta huce can gidan mijinta.



legend s pen





Page 12





Duk yanda Ummanah ta kai ga son auren nan, sai da ta ji ya zo mata wani kala, ko ba komai ta so ta gyarani, tayimun abubuwa, sanan ga kayan kitchen da na gado, kar kuma abun ya zama shiga hai. Ko da yake, a farayin auren, sanan a sameni.



 Amma kana ganin hakan zai fi. Abban ciki ya tambaya, a fusace Abbanah ya juya.  Kaga Yaya, ban neme yardar ka ba, ko shawarar ka, da Mus ab da Salma babu wanda bani da iko a kansa, dan haka yanzu xanyi amfani da ikona, wallahi cikinsu babu wani da ya isa ya maidamu ananan mutane. Shiru Abban ciki yayi, domin fa tun suna anana daman tsoro Abbanah yake, sabida yana da fushi da zafin zuciya, sama da kowa a gidan.



Yaya Muhammadu yaya na ne ya shigo, ya kalli Abbanah sanan ya ce. Abba ga limamin. bai rufe baki ba, su Yaya Amira suka shigo, kowa da mamaki yake kallonta, an zaci Salman ce ta je gidan.  Asma u tana gidan ki ne?. Maman ciki ta tambayeta, girgiza kai tayi sanan ta ce.  Abbanah yayi mun waya lallai-lallai na zo yanzu, kuma ina jin bani kaWai bace, dan ina hanya yayar Abuja ta kira ni ta ce wai lafiya, Abba ya ce lallai gobe ta zo, shine na ce mata nima ina hanya, inaga gaba dayan mu ya ce mu zo.



 Salma ta jawa kanta. Anty ta faWa, dan ita tafi tausayin Salma.  Wai anganta ne?. Yaya Asma u ta ara tambaya, girgixa kai Maman ciki tayi, sanan ta ce.  Auren dai za a Waura.



 Ikon Allah, Ita kuwa Salma ina ta je haka?.



 Koma ina ta je zata dawo ta tarar da hukunci, duk wanda bai ji bari ba, ai yaji hoho. Ummanah ta faWa. A can waje kam, maota Abbanah ta taro, har da wasu cikin abokansa, inda limami ya Waura aurena da na Mus ab Galadima, kan sadaki naira dubu dari biyu, wanda Abbanah ne ya bayar da kansa. Cikin ananin lokaci, ahalin Galadima da ke kusa su ka hallara gabaki Wayansu, Yayar Abuja ce babu, sai kuma Yaya Amira ta zaria, sai ni da kuma Mus ab, wanda babu wanda ya nemeshi baki Waya.





Gaba Wayansu suna zaune a falon Hajja, bayan Abban ciki ya buWe taro da addu a, kasancewar ya saba hakan a duk wani taro da za ayi, Abbanah ne ya Wora da cewa.  A yau, Allah ya nufemu da Waura auren Mus ab da Salma, wanda mutane da dama su ka shaida hakan, to abinda yasa na tara ku a nan, kowa da kowa shine; ina so nayi amfani da wanan lokaci domin na sanar da ku cewa, in dai har Salma tai biyayya ga auren Mus ab, ko kuma tai zama a gidan Mus ab, to na sallamata, na cire ta lissafin  ya yana, wanan magana ce wacce na yanke ta, kuma babu canja magana dan duk kusan ba halina bane, sanan shima Mus ab ku sanar masa, idan har ya sake wanan yarinyar tafi arfinsa, ta kai ga har saSani ko saki ya shiga tsakani, to wallahi shima nida shi ne



 Toh, amma yanzu ita Salman ta ina?, kawai sai ayi wanan hukuncin ba tare da an nemi lafiyarta ba, sanan mai ya kawo maganar auren haka cikin gaggawa. Mami wacce take yaya a wajen Abbanah ta faWa.  Wanan su zasu iya yi miki bayani, amma abinda yasa na na Waura auren yanzu shine; daga Salma har Mus ab babu wanda ya isa, ya nuna bamu isa ba, babu wanda ya isa cikinsu, ya ma yar da mu ananan mutane.



 Yunusa, tambayarka nayi mene asalin abinda ya kawo auren?. ta sake maimaita masa, dan ita ma akwai zafin kai. Ni ce na haWa, nina haWasu auren. Hajja ta faWa, dan tasan a zafin kai irin na Mami, da ba a Waura auren ba tsaf zata iya hanawa. Shiru Mami tayi, tun da Hajja tayi magana kuma ai shikenan.  Amma kuma yana da kyau a nemi inda take dai. Ummah wacce take anwar Abbanah ta faWa.  Eyh, dole za a ba zama nemanta, amma ta kwana da sanin ba za ta sake zama a waje na ba. Ummanah ta faWa.  Ni a kawo ta waje na. Maman ciki ta tare Ummanah.  Amma ni cewa nayi cikin gidan ne ba zata ara zama ba. Abbanah ya faWa.  A ah Yaya, ba za ayi haka ba, dole Salma zata zauna da mu, kafin shi Mus ab Win ya haWa mata lefe, da sauran kayyaki, sanan kaima akwai hain kayan Waki da na gado a kanka, sanan duk wasu abubuwa da aka gudanar a bikin sauran ita ma za ayi a nata. Yaya ilyasu ya faWa, tun da ya fuskamci dai babu wanda zai iya faWawa Abbanah, shiru yayi sanan ya ce. Da komai da komai kar ya huce kwana goma. daga haka ya tashi ya fice, shi dai Abban ciki mamakin yadda ya wace mai girma kawai yake.







*Mus ab*



A Sangaren shi kam, tun da Maman ciki ta ce dashi, idan har ya sake ya fasa auren, ko ya musguna mun ba ta ya fe ma sa ba, ya samu waje ya zauna.  Shikenan wanan auren ya tabbata, ya zama na dole, domin yasan tun da a kazo wanan matakin, komai ya are. Ya zai yi da rayuwarsa, ya zai yi da auren addarar da a ka Waura masa, Zuciyar da ya sa wa SAKATA ya rufe, zai buWe da soyayyar wanan aramar yarinyar?.  Mai yasa to na damu da kukan da naga tana yi?. Yayi wa kan sa wanan tambayar.  Tabbaa naji kukan da take yi har cikin zuciyata, kuma naji babu da







 Amma Mus ab, mene laifin Salma a wajenka?. Wani Sari daga cikin zuciyarsa yayi masa wanan tambayar.  Yarinyar ba ta da kunya. ya bawa kan sa amsa, shi ba ma wanan ba. Mai yasa yake jin kukan da take yi har cikin zuciyarsa, shin shi Win ba mutumin arzii bane, da zai ji ma ta tausayin aurenta ko me?. Tabbas ya damu da wanan kukan na ta.





*Salma*



Ina zaune cikin Wakin, naji shigowar su Walida da fitarsu amma ko a jikina, domin ina zaune na gama tsara yanda zanyi da rayuwata, bara ne zanyi na  yan kwanaki kafin na samu miji nayi aure, shima Masrur Win duk naji ya ficemun a rai, garin zan bari baki Waya ya fiyemun. Ina nan zaune naji suna koarin kulle gidan, alamun sha biyu ta gota, sai a lokacin naji wani mugun tsoro ya ka mani, yanzu idan sukayi bacci Sarawo ya shigo fa?, ni ce a farko ni zai fara Waukewa, hakan yasa na rufe idona tare da yin addu a, idona a rufe har bacci ya Waukeni.



Kiran sallar farko na buWe idona, dake ba wani dogon bacci na samu nayi ba, ina jin matasan gidan sun fita sallah na mie, gwanda na fita da duhun nan, sabida idan gari ya waye kowa zai ganni, kuma nasan zancen Sata na ya yaWu ko ina, tagar na ara kamawa na Wage tare da dirga asa na bi ofa na fice, sai dai ban fito a sa a ba, domin dai-dai lokacin Yaya Muhammadu da ya fito a makare ya nufa massallacin, tun fitowa ta na ganeshi, oarin komawa na fara shi kuma ya ce.  Wace anan?. da sauri na koma zan shige, amma yayi saurin sa hannu ya rie ni, kuka na fara tare da faWin.  Yaya dan Allah ka cika ni. a fusace ya ce.  Salma!. shiru nayi bance komai ba. Ba magana nake miki ba, ina kika je, kin san halin da kika sa iyayyen mu?, gaba Waya gidan Galadima jiya babu wanda ya runtsa, kowa yaja carbi yana ja, wasu kuma sai sallah suke suna roon Allah ya bayyanaki.



 Ni babu inda naje, a Wakin shirgi na gidan Alhaji idi na shiga, kuma ka cika ni na tafi, na bar muku gidanku, na bar muku ahalinku&



Legend s pen



Page 13.







Saukar marin da naji a fuskata ya sani haWiye yawon baki na babu shiri, jana ya farayi ni kuma ina turjewa tare da faWin. Wallahi bazan koma ba, idan na koma Allah yatsinemun, ka cika ni. Shi kam kawai jana yake ta arfinsa, domin nima nasa arfina ina neman fusgewa, na kwasa da gudu. Dai-dai ofar gidan mu na saka arfi na fusge tare da kwasa da gwado, shi kuma ya rufamun baya, ji nai a rino hannuna; ina juyowa aka kifeni da mari, tun daga saukar marin nasan Kawu Mudi ne.  Dan ubanki baki da hankali ko?. takaici ya isheni, na fara jan hannuna zan ci gaba da tafiya, cika ni yayi tare da faWin.  Je ki. aikuwa nasa afa na fara tafiya, danni gaba Waya gidan Galadima sun fitar mun a rai, bana son kowa, kowa baya burgeni, dan Wallahi a kan na auri Mus ab gwanda naje nayi bara, ara rieni yayi tare da kifamun wani marin, daman haushin Kawu Mudi nake ji, dan shine kullum cikin dukana yake, shima ja na ya farayi ina turjewa, da sani na na kama hannunsa na gantsara masa wani mugun cizo.



Duk zafi cizon baisa Kawu Mudi ya cika ni ba, sai da ya dangana ni da cikin gida. Gani na a harabar gidan ya sa na kurma wani mugun ihu wanda ya ratsa gidan gaba Waya. Ummanah na zaune kan dadduma ta jiyo ihun nawa, da mugun gudu ta taso zuwa harabar gidan, fitowar dai-dai da fitowar Maman ciki da Anty, gaba dayansu su ka zo kai na,Maman ciki na faWin.  Ina a ka gan ta?. Banza Kawu Mudu yayi musu ya shige ciki, Yaya Muhammadu ne ya ce.  akin shirgi na gidan Alhaji idi me mai ta shiga. nan suka hau salati da salallami, Ummanah ba ta ara cewa komai ba ta huce, Maman ciki ce ta kama hannuna zuwa Sangarenta, Anty kuma ta koma ciki, Allah ya gani ita Anty ba ta son auren nan, ba wai dan wani abu ba, kawai tasan yadda muka tsani juna nida Mus ab, da ace shi yana so na to da saui, amma duka ba ma son junan mu, amma addu ar ta ita ce.  Allah yatabbatar da abinda yake Alheri.





aki Maman ciki ta huce dani Walida na bin bayanmu, sai da mu ka shiga ta zaunar da ni kan kujera ta fara magana cike da hikima da dabara.  Salma! Salma!! Salma!!!, sau nawa na kira sunanki?. Kai na a asa na ce.  Uku.



 Salma mai kika aika ta haka, kin san fushin da kika Waukar wa kan ki, kin san adadin tsinuwar da mala ikun Allah suka yi miki a kan Sata ran iyayenki da kika yi, Yanzu mene amfanin gudun da kikayi, sabida ka da ki auri Mus ab?, to idan hakane kinyi a banza, domin ko awa biyu ba kiyi da tafiyar ba a ka Waura miki aure da shi Mus ab Win, kinga kuwa auren ku haWin Allah ne, wata SAKATA da kuka sakawa zuciyoyinku, ba zata hana Allah aiwatar da abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login