Showing 57001 words to 60000 words out of 62407 words

Chapter 20 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

na san ke kin san wanan maganar, amma su sauran ina tunanin ba su sani ba.



 Wace magana ce haka?. Hajja ta tambaya duk da ta san sun yi magana jiya, Abbanah ya ke ce mata Mus ab zai kara aure sun je su nema mai aure, ta yi fada sosai ta kuma ce ba zai yi ba, amma bisa wasu dalilai da ya fada mata ta amince.  Zancen auren Mus ab mana. da kallo duk suka bi Ummanah, Maman ciki ta ce.  Wane Mus ab din, kuma wane aure?.



 Yoo nima jiya Yunusa ke sanar da ni, wai sun je nemawa Mus ab auren yarinyar da ya so kwanakin baya kuma an ba shi, nayi fada kamar na ari baki amma sun ki ji na. Mikewa tsaye maman ciki ta yi sanam ta ce.  Nifa bangane ba ko kadan, wace yarinya zai aura, Salman fa?.



 Salma ta ki mai da hankali ta yi zaman aure, ku duba sakwan nin auren su yadda kowa ya nutsu, ita Sadiya ma har ta shiga watan haihuwa amma ita fa, ta zauna sai wahalal da bawan Allah ta ke, kun san yadda yake fama da rashin lafiyarsa, ko dan ku baya zuwa ya fada muku. Ummanah ta fada, tana fito da duk wani Sacin ran da ke zuciyarta.  Amma gaskiyya baki kyauta ba, Yaya wanan ba dai-dai ba ne, ranan tare da ke fa ya ce sun fita har park sun ne ai a hankali komai zai yi dai-dai. Anty ta fada cike da fushi. Ki fa da ma ta dai, to wanam auren gaskiyya ba zai yu ba. Maman ciki ta fada ranta a bace, ita dai matar Yaya ilyasu ba ta sa baki ba, tun ita ce karama cikinsu.  Ai kwai kuyi hakuri, Salma ta tsaya a matsayin uwar gida, amma kubar shi ya yi wanan auren. Ummanah ta fada kamar ba  yarta za ayiwa kishiya ba.  Ni kai na bana son auren, kuma nace indai har Salame ta canja kafin wanan lokacin za a fasa. Cewar Hajja.  Ni kawai Hajja a fasa, a karawa Salma lokaci.



 Lokaci fa kika ce, yanzu fa wata tara da auren su kenan. Ummanah ta fadawa Maman ciki da ta ce a karamun lokaci, shiru dakin ya yi an rasa mai magnar arziki. Cikin kwana daya maganar karin auren Mus ab ta zagaye ahalin Galadima, kowa ya ji sai ya ce.  Salma ba ta yi ba. zaton kowa da a ka ji mu shiru kwana biyu na yi hankali, ashe-ashe ba haka ba ne.



Ina can ina fama da rayuwa ban sani ba, ban san ta inda zan sani ba, kawai dai na daukar wa kaina masifar shiga dakin Mus ab Kullum, har kwanciya nake wasu lokutan a kan gadonsa, na yi kuka har na gaji na gode Allah, na fita hayyacina na rame sosai da sosai, damma yanzu ina samu na ci abinci shi yasa na dan rage kan jamewar nan.





Zaune naki cikin wani daki mai mugun duhu, kamar haske bai ta ba ratsa shi ba, ganin nan a zaune kamar andaure ni da igiya mai tauri, ina kuma jin azaba a jikina, kamar dai igiyar ta wuta ce ko karfe da ya sha huta ya yi ja a ka daure ni da shi, ciko cikon kwacewa nake amma na kasa ko kadan, wata kara mai firgitarwa ta karade kunnena, ji na yi ana jana kamar tsintsiya ko kayan wanki, dai-dai wani wajen dubu a ka tsaya sai ga wata tsohuwa ta fito daga cikin duhun, idanuwanta jajaye kamar wuta ko garwashi. Cikin wata muryar mara dadin ji kamar ihun gyare, tsohuwar ta ce."Ke ce 'yar da ta ki bin umarnin iyayenta? Ke ce wadda aka haWa aure, kika tozarta miji, kika hulakanta shi, kika nuna iyayenki ba su da daraja?. Tuni na ji cikina ya wani yi kuuuuu kamar zan yi kashin wuta, sabida yanda na ji kamar  ya yan hanjina na konewa, kokarin bude baki nake na karyata, amma murya ta ta makale, hannaye na na fara dagawa alamun roko. A take ™asan wajen ya Salle, na fada cikin wani ramin da yafi wanda nake zafi, zafin kamar wuta na tashi daga ™asan da na ke kai. Sanan ga jikina daure da wanan igiyar mai zafi, sai a lokacin na fara jin zuciyata ta fara magana.  Tabbas Allah ya bani uba, ya bani uwa amma na wulakanta su. Sanan ya ba ni miji, mai so na da kauna ta amma na raina shi, na hana masa soyayya, na ™untata masa, na sashi kuka."



Kuka na fara mai ban tausayi ina fadin.  Allah Na tuba!, Allah na tuba, Allah ka karbi tuba na, Allah kasa mjina da iyayena su yafe ni. Ina cikin wanan kukan na ji ™arar saukar bulala mai zafin gaske a jikina, kuka na fara mai ta ba zuciya, sai naji kukan nawa na zama biyu daga ido na yi na ci karo da Ummanah tana kuka ta na cewa.



Legends pen.



Page 44.



 Salma, ke ce ™addara ta, amma me kika yi mun na sakkayya a rayuwa ? Mun miki aure da fatan zaman lafiya, da kuma biyayya a garemu, sai kika mayar da gidanki wuta, kika kuntaci mijinki, kika azabce shi, Salma duk abinda kika gani anan bai kai rabin kwatan azabar da ubangiji ya tana darwa miki da masu irin hilinki, idan har ku ka koma gareshi ba ku tuba ba, miji babban abu ne ba na rainwa ba ko hulakantaw, haka iyaye ma.

Hawaye ne ke zubo daga idanuwa na kamar ruwan sama. Na bude baki ina son na roki Ummanah gafara, amma sai na neme ta na rasa.



A daidai wannan lokacin na farka daga baccin da yau dauke ni a dakina bayan na dawo daga dakin Mus ab, ihu na saki jikina na rawa gumi yajikani sharkaf, zuciya ta kamar za ta faso kirjina ta fito, mikewa nayi ina kuka kamar zan shide.  Ya Allah! Na yi kuskure na yi kuskuren hada kiyayya da aure, auren da kai ka zaba mun, ya Allah ka gafarta mun, Na raina iyaye, na tauye hakkin mijina, ka ba ni damar gyara. Addu ar da na shiga yi kenan ina kuka. Ta shi na yi cikin sauri na shiga ban daki, na daura alwala na ta da sallar nafila, bayan na idar na daga hannu sama na fara addu a.



"Ya Allah, Ya Ubangijina, kai ne Mai gafara, kai ne Mai jin ™ai Wallahi na yi kuskure, na yi sakaci da ni imar da ka bani, na wulakanta iyaye da mijina, wanda bai cancanci hakan ba. Allah ka gafarta min, na gaza, na raina su, na tsaya akan girman kai da ™yama... amma yanzu na gane. Ya Allah ka wanke ni da hawayen tuba, ka tsarkake zuciyata daga hassada da ™yama, ka cire wannan ™iyayyar da ta hana ni ganin alkhairi. ka zaremun wanan Sakatar da ta rufemun ganin Alkhairan Mijina,Ka sake zuciyata kamar yadda kake sake shuke-shuke a lokacin damuna. Ka juyo da ni, ka ba ni damar yin gyara a kan barnar da na yi. Allah ka sa iyayena su yafe min, ka sa mijina ya ji tausayina, ya yafe min, ya nuna soyayya gareni, ka maida wannan auren daga tilas zuwa rahama, daga wula™anci zuwa soyayya. Ka bani ™arfi da hikima da ladabi na zama mace ta gari. Na gaji da yin girman kai, Allah na gaji da rashin biyayya, Wallahi na gaji.



Na fashe da kuka mai ™arfi daga cancikin kasan zuciyata, na jingina kai na da katakon gadona, zuciya ta na bugu da sauri, ina jin wani haki. Zuciya ta na ™una da tsoro da nadama, duk wani abu da na taSa yi na ke dauka bai komai ba ne, yanzu ya dawo mun da nauyi a zuciyata kamar dutse. "Ya Allah! Idan kana da hukunci a kaina, ka sauya mun ya zama rahama, Idan ni ce jarabawa ga mijina, ka mayar da ni salama gare shi. Ka juyo da ni Allah, kai ne Mai canza zukata, ka zaremun Sakatar ta wa zuciyar.



Na kara rushew da wani kukan kamar zan shide, sabida nauyi da na ji zuciyata ta yi mun, na rusunar da kaina ™asa, ina ci gaba da ro™on gafara a wajen sarki mai duka.



Yan awanin kadan naji wani sanyi ya na shiga zuciyata, naji wata nutsuwa wacce na dade ban ji irnta ba na shiga ta, wanan jire da hajijiyar ya dauke gaba daya, kai na kamar andauke dutsen da a ka doramun, haka zuciyata ma kamar an zare wanan babban karfe da ya tokare mun komai, wasayau haka naji kaina sa zuciyata. Mikewa na yina nufi sip di ta, wanan ledar da ya bani ranar da muka fita na dauka na bude, ga matukar mamakina sai naga wayar kirar iphone 17promax, wayar da ake ya yi a yanzu.  Mus ab ya cika mutumin arziki, ya cika miji na gari. Na fada ina murmushi da hawaye, kunnata na yi ta kama bayan na sata a chaji, da akwai layi airtel wanda da alama anyiyyi amfani da shi a ciki, shi ya kamata na fara kira, amma ban da lambar shi, lamabar Ummanah da Abbana ce a kaina kawai sai kuma ta Yaya Asma u, da sauri na shiga saka lambar nasan ita kadai ce za ta ba ni lambarsa kai tsaye a kan dai Ummanah ko Abbanah, bugu daya ta dauka tare da fadin.  Salamu alaikum. Amsawa na yi da fadin.  Wa alaiki Salam, Yaya ni ce.



 Salma.



 Na am. Na fada tare da fashew da kuka.  Salma lafiya mai ya faru, mai a ka yi miki?. Kukan na ci gaba da yi, sai da na yi sosai sanan na ce.  Yaya na tuba na bi Allah, na bi iyayena da mijina, na gane na yi babban laifi nayi kuskuren kin biyayya ga umarnin iyayena, da mijina, Yaya na tuba.



 Alhamdulillah Salma, Alhamdulillah addu ar mu ba ta fadi kasa banza ba Salma, Allah ya yi miki albarka Salma.



 Amin Yaya.



 Yaya ina son kiran Ummah, ina son kiran Abbah, ina son kiran Yaya Mus ab, amma ina jin tsoro.



 Salma karki ji tsoron kowa, mussaman Abba babu abinda zai miki, kowa zai ji dadi.



 Turumin da lambarsu har ta Yaya Mus ab din.



 Shikenan Salma. ta fada tare da kashe wayar, lambar Abba na danna tun da daman ina da ita a kai na, ina ni ta shiga hannuna ya fara karkarwa. Sai da ta ji ringi sau biyu kafin ya Waga.

"Assalamu Alaikum." Ya fada da Muryarsa mai sanyi, hawaye ne suka fara gangaro daga idona, baki na na rawa na ce. "Wa alaikum salam Abba..." Shiru ya biyo baya. Nasan ya gane wace a kan layin, kuka na ci gaba da yi, sai can ya ce. "Salma ke ce?. jan hanci na yi cike da kuka, na ce. "Ni ce Abba& Ni ce... Abba don Allah& Don Allah ka gafarce ni& na yi kuskure, na sabawa umarninka& na yi abin da bai kamata ba. Na raina shawararka& Na bijirewa zabinka, na kau da kai daga tsoronka..."

Sai kuma wani kuka ya ci karfina, cikin kukan na ci gaba da cewa.  Abba na gane kuskurena, Yanzu na fahimta, na fahimci cewa kai ka fi sanin alkhairi a gareni fiye da kai na. Duk da ba ka daWe da magana ba, zuciyarka ta fi nisan tunani na ka yi hakuri Abba.



 Salma. me ya sa kika yi haka? Me ya sa kika Wauka zan taSa maka wani zabi da zai cutar da ke? Ni mahaifinki ne kuma rayuwarki gaba Waya amana ce a gareni& " Shiru na yi ina sauraron muryar Abbanah, muryar da ita kan ta kam saukarmin da natsuwa.



 Salma na yafe miki, ban ta ba kwana da fushin ki ba, bake ka dai ba duk cikin  ya yana da na  yan uwana babu wanda na ta ba kwana da fushin sa, Rayuwa darasi ce, kuma idan kika koyi darasi, to kin gyara gaba. Allah Ya sa ki zama cikin masu tuba da gyara. Fahsewe na karaye da wani kukan sanan na ce. "Na gode Abba, na gode, Wallahi zan gyara. Zuciyata ba za ta sake bijire maka ba, zan zama 'yar da za ka yi alfahari da ita."*



 Ko a hakan ma na yi alfahari da ke Salma, sabida kin yi lafi kuma kin dawo kin tuba, ko ubanginjin mu yana son ba yi masu tuba, Allah yakarbi tuban mu ba ki daya.



 Amin ya Allah Abbanah. Na fada tare da sauke wayata a kunne. Kallon su Abban ciki da su Mama Abba ya yi, daman lokacin suna bangaren Hajja baki daya, kan maman ciki da dage ba za ayi wanan auren ba.  To kinga ni, kinga ni, yanzu a yanda kika ji muryar Salma kin san ta yi tuba na gaske. Shiru Ummanah ta yi wa Mama, zuciyarta fari sol da jin magana ta da kuma neman yafiar da na ke.



Legends pen.



Page 45.





 To yanzu ina son a janye maganar auren nan na Mus ab. Hajja ta fada tana kallonsu, murmushi Ummanah ta yi sanan ta ce.  Hajja daman babu wani aure dai zai yi, kawai an yi hakan ne domin a sanya ma ta tsoro kuma da alamu hakkarmu ta cin mu ruwa. Dariya kowa ya yi daga haka su ka ci gaba da hira. Har zuwa lokacin da Abbanah ya fita sakamakon kiran da abokinsa ya yi masa.







Ji na yi zuciyata na gaya mun na bude wanan takardar a jikina nake jin ba za ta zama ta saki ba, na duba nagani. Ta shi na yi naje inda ya ajiye ta, gaba na na faduwa kirjina na dukan uku-uku na dauka, sai da na zauna kan gado sanan na budeta na ci karo da rubutu kamar haka.



 Amincin Allah ya tabbata a gareki ranki ya dade, ina rubuta miki wanan takardar da zuciya mai cike da soyayyarki, da kuma begen ki. Salma ban sake ki ba, kuma ba na jin zan sake ki, zan iya zama dake a duk irin kiyayyar da kika yi mun. Wani sanyi na ji a raina tare da fadin.  Na daina kin ka, nima zan so ka fiye da yadda kake so na. na ci gaba da karanta takardar.



 Sai dai Salma zan dauki wata hanya mafi sauki a gareni da ke, ita ce Zan kara aure. Salma zan kara aure, zan kuma tafi na barki na zauna tare da amaryata na gode sosai. Wani ihu na saki tare da yarda takardar, da sauri na lalubu wayata na kira Yaya Asma u, bugu daya ta dauka tun da ta gani lambar.  Hello Yaya. Na fada cikin kuka.  Salma ya a ka yi kuma, Abban bai hakura ba?.



 Wai aure Yaya Mus ab zai kara. Shiru ta yi kamar ba ta ji na.  Hello Yaya, magana na ke. Shirun da ta kara yi ne ya bani amsata cikakkiya.  Yaya dan Allah da gaske.



 Salma kin yi wasa da damarki. Kin yi wasa sosai, Mus ab na sonki kuma ya so ki, amma kin nuna masa zallan kiyayya mai zafi, wanda kalamanki sai da su ka nemi kashe shi, aure zai kara ina ga cikin satinan ne ma bakin,bai fada miki ba?. Kuka na fara wani sabo mai fitowa daga cancanki kasan zuciyata, na dama da na sani su ka cika ni, Sakata ba ta yi mun rana ba, Sakatar da na zurawa zuciyata ba amfane ni ba.  Ina son Mus ab, ina kaunar Mus ab, ina mugun kishin Mus ab. Lambar shi da Yaya Asma u ta turumun na shiga kira, sai dai gaba daya a kashe ba ta shiga, kamar layin na wa ne a ka yi blocking din shi daga kiran, sabida da na kira take faduwa, wani irin zafi na dinga ji a kirjina, kamar zafin wutar garwashi, kuka na fara da ban san lokacin tsayuwarsa ba, kuka ne daya ke ta ba kashin zuciyata.  Na yi wasa da dama ta, na kasance  ya mara biyayya, da a ce na zama mai biayyya da duk abun ba zai faru ba, da na samu alheri da ribar biyayya a duniya, kamar yadda su Walida su ka samu. Kuka na na ci gaba da yi, wazan kira na sa ya kira mun shi, na fadamai na yi na dama na yi da na sani, kuka na ci sosai da sosai, sai da na gaji sanan na nemi Yaya Asma u da ta turamun lambar Maman ciki, tana turumun na kira lambar, bugu daya a ka dauka naji sasanyar muryar Maman ciki ta na fadin.  Salamu alaikum. Kuka na fashe dashi ba tare da na iya amsawa ba.  Salma, Salma ke ce?.



 Ni ce Mama. Na fada cikin kuka.  Salma mai ya faru, dukan ki ya yi. Cikin kukan na ce.  A a Mamah, mamah ku yi hakuri dan Allah, na tuba ba zan sake bijire muku ba.



 Salma babu abinda ki ka yi mana, mun ya fe miki.



 Mama ki ce ya yafemun dan Allah, ko waya na kira shi ba ta shiga, Mama ki ce mai na tuba dan Allah, ina son shi wallahi. Murmushin jin dadi ta yi, sanan ta makawa Ummanah harara, su Anty su ka yi dariya.  Shikenan Salma, zan ce ya yafe miki shikenan ko?.



 A a Mamah.



 To menene kuma?.



 Mama ba ya gidan ku san sati biyu kenan.



 Salma ya gudu ne sabida tsoran kar ki mai wani abu.



 Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login