Showing 54001 words to 57000 words out of 62407 words

Chapter 19 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

ce mai shafar aljanu, maganar zarar bunu ce yau na tabbatar da zan iya da na gogeta yanzu, sabida gaba daya ba ta kama ta ba.  Salma nagode. na ji ya fada, shiru na yi zuciyata tsinke ga ba daya.  Mai ya kai ki wanan maganar Salma?. nasan tabbas wanan magamganun ba daga cikin zuciyata suka fito, domin ni kai na nasan a yanzu wanan tsnar mus ab din babu fiye da rabi a zuciyata. To mai ya kai ni wanan maganat.  innullahi wa ina illahir raji un. na fada a cikin rai na, tare da dagowa sai dai babu Mus ab babu mai kamar shi cikin.  Ya hayyu ya ™ayyum. na maimaita ina jin hawaye na zuna a idona, wa yanda ban san na mene ba kuma ban tare su na hana su zuba, sai dai na yi masu isata sanan na ta shi na koma daki, maganganun da na fada masa na ta dawo mun a kai na, kamar yanzu na fade su, Salma kin sha ro™on Allah ya gama ni da Masifar duniya, to Salma Allah ya gamani da masifar kaunarki, wacce na san shine amsar addu arki.







 Mus ab& naji kuma na saurari kalaman ka. Amma ka tuna, ba duk kyawun magana ke tsinkewa cikin zuciyar da bata so ba. Na riga na saka wa zuciyata sakata. Na rufe ta da ruf da ™iyayya. Ban taba sonka ba, kuma banza taba sonka ba, na san dai na karSe ka a matsayin mijin kaddara, mijin da iyaye da  yan uwa su ka yimun, amma ba jagoran zuciyata ba na karbe ka a matsayin mijin da iyayena suka zaba. Amma ko yau a ce babu ran iyayenmu, babu wani abu da zai sa na kara zama ko na awa ne a tare da kai,So ba dole ba ne. Kuma ni ban zauna da kai saboda so ba. Na zauna da kai ne saboda biyayya ga iyaye, amma zuciyata ba ta son ka, kuma ba ta da wajenka. Maganganun da suka ta shi Mus ab kenan daga baccin da ya samu ya yi bayan sallar asuba, amma gaba daya daren jiya bai iya ko runtsawa ba, Salma ba ta son shi kuma ba zata ta ba son shi ba, anzo gejin da yake ji ya kamata ya sauwake ma ta kawai ya huta ta huta, yasan dai yana son ta amma ya zama dole ya bar ta sabida ba ta son shi kuma ba za ta so shi ba. Ban daki ya shiga ya watsa ruwa ya shirya, kallon agogo ya yi bayan ya kunna wayarsa, karfe 09:19 gida kawai zai je.





Nima jiya bacin rabi da rabi na yi, ban samu mai tsayi ba sai ba yan sallar asuba, nayi matukar mamakin rashin ta shi na da Mus ab ya yi, jikina ya yi san yi ya mutu gaba daya, na yi dana sanin wa yan can maganganun kuma a shirye na ke na yi zaman aure da shi, ko da ba na son sa zan zauna da shi. Wanka na yi na saka bakar doguwar riga na nufi kitchen hada breakfast. Ina kichen ina sa ka ran shigowarsa ya zo ya yi mun magana, amma babu shi babu alamun shi. Na ji ni gaba daya wata sukuku a kitchen din, haka har na kamalla na kai masa kan dinning, shiga ta daki na ji alamun ya fita da sauri na fito ko ya taba abincin amma bai ko kalleshi ba.





Kai tsaye gidan Galadima Mus ab ya nufa, byan sun gaisa da Hajja ya y bangarensu, nan ma su ka gaisa ya yi namu bangaren. Daki ya shiga ya jira Ummanah bayan sun gaisa sa Abbanah, shigowa Ummanah ta yi ta zauna tare da fadin. Mus ab lafiya dai ko?. ya dau mintuna kafin ya yi magana.  Ummah na zo wajen ki ne a matsayin uwa ba matsayin maman Salma ba, na zo wajen ki ne dan nasar da ke hukuncin da na yanke, ina tunanin zan sauwakewa Salma.



 Ya salam, Mus ab mai Salma ta sake yi, ina tunanin ka ce mun abubuwa sun yi sauki, nima kuma ina magana da kai ne a matsayin uwa ba matsayin uwat Salma ba.



 Eyh Ummah sun yi sauki,amma Salma ta ki canjawa. nan ya bata labarin duk maganganun da ta fada masa daren jiya, sanan ya dora da cewa.  Na yi mamakin ganin breakfast yau, Sanam kuma tun ajiyan na ga alamun rashin jin dadin fadin maganar, amma kuma Ummah gsky ta fada.



 Mus ab, zan doraka a kan wani tsari guda daya, kuma zaki bishi insha Allahu za ka yi nasara, sanan ka yi addu oin da a ka ba ka?.



Shiru ya yi m, tare da girgixa kai.  Tabbas Ummah ban yi addu a ko daya ba, a rashin ganin dai-dai a al amuran Salma har da rashin kai kuka na ga ubangiji, na yi sake da addu a Ummah, kwata-kwata bana yin addu a, ba na ta shi cikin dare na kai kuka na ga ubangiji, na fada masa bukatu na na kuma rokeshi ya kawo mun sauki da mafita a cikin al amurana Ummah.



 To ka gani ko, amma duk da haka ka je ka rubuta takarda kar ka ba ta ka ajiye ma ta.



Legends pen



Page 41.



 Ummah ban gane ba? . Mus ab ya tambayi ummah. Ka rubuta takarda ka ajiye ma ta, nasan za ta ji tsoron bude takarda, sanan kar ta zama ta saki, ta zamna ka rubuta cewar ta yi hakuri ba zaka iya sakin ta ba, amma zaka je ka nemi wacce za ta so ka, ma ana dai zaka kara aure, sanan ka fita sabgarta gaba daya, ka hada kaya cikin sati biyu, kabar ma ta gidan. Zan maka matar da zaka aura ku bar gari da ita, wanan shine umarnina kuma duk ka bi su dole.



Dagowa ya yi ya kalli Ummah, sanan ya ce. Ummah aure kuma?.



 Aure Mus ab. ta fada tare da ta shi ta bar shi a wajen. Ta shi ya yi ya nufi gida cike da mamaki, mai Ummah ke nufi?. Ina zaunen na zuba uban ta gumi, gaba duniyar ba ta mun dadi jina ke kamar na rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwata, Sallama ya yi na miki da sauri tare sa fadin.  Sannu da zuwa. bai kalle ni ba bare ya amsa kawai ya shige dakin sa, da mamaki na ke bin bayan shi da kallo.  Ni Mus ab ke wa haka, laifi na ne ma da na yi mai sannu da zuwa. Na fada tare da shigewa daki, ina zaune ina faman bacin rai na ji ya shigo, wani sanyi na ji a rai na ina cewa.  Wallahi sai na rama wanan jan ajin da ya yi mun.



 Salma, ga wanan. na ji muryarshi a cikin kwakwalwa da kwanyata, dago kai na yi na kalleshi na ga abinda yake mikomun, takarda ce wacce tasa gabana ya yi mugun bugawa Durum.  Saki. na fada a zuciyata, na ce.  innullahi wa ina illahir rajiun. na fada ina kai na ™asa.  Salma ga shi.



 Wai mene?.



 ki karba ki ga duba mana.



 Ajiye a can. na fada ina kau da kai, ajiyewar ya ya juya ya fi ce.  Na shiga uku ni Salam, Mus ab zai ja mun tsinuwar iyaye, na shiga uku. na fada a fili ina zubar da hawaye.  Ai saki sai mace ta gani ko?, to ni bangani ba dan haka ban saku ba, babu inda zani wallahi. na fada ina rusa ihu, kuka na ci na gode Allah sanan wani wahalallan bacci ya yi gaba da ni, sai bayan la asar na ta shi, yau ko wankan ban yi ba na yi alwala na ta da sallar azhar da la asar, ko fito wa ban yi ba sabida ban ma jin yunwa ba bare na je kitchen, ni duk tunani na yana kan tsinuwar Abbanah, Ummanah kuwa kisan gilla ne za ta yi mun.  Mus ab ya cuceni ni Salma ya gama dani, ya gama da rayuwata. Abinda na ke ta maimaita wa kenan a cikin a raina, sai bayan magariba na iya shiga kitchen na dora ruwan zafi na sha na dawo daki, na zauna kamar mai yin takaba ko idda.



Har wajen karfe goma babu Mus ab a cikin gida, kuka sosai da sosai nake yi a fili bama a zuci ba, ni ban san me ya dame ni ba, rashin sa ne ko kuma sakin da ya yi mun, ko tsoron tsinuwar Abbanah da dukan Ummanah.  Ni dai Salma na shiga uku na lalace. na fada a fili cikin Kuka, mai na yiwa mus ab da zai hade mun komai lokaci guda?, har wajen sha biyu na dare ban ji shi ba, lokacin kuma baccin dole ya dauke ni sabida gajiyar da idanuna suka yi da kuka. Shi ta shi Sallar asuba sabo ne, idan har ka saba to dole sai ka ta shi, hakan ce ta faru da ni domin tin ina gida na sa ba, ga kuma da na yi aure Mus ab ya sabar da ni, bayan na fito daga ban daki ina kokarin ta da Salla na ji alamun zai fita.  Ya dawo kenan, sai da ya bar ni ko barayi ne za su shigo sai su kashe ni ko?. na fada a rai na kafin na tayar da Sallan, ina idarwa na fito na shiga kitchen ko zai zo muyi sulhu, nasan ance idan miji ya kwana daya zuwa biyu zuwa uku yana sakkowa daha fushi kila ya janye sakin da ya yi mun. Ina jin shi ya shigo cikin falon yana zagaye,  yan mintina kadan bayan na fito na gan shi da jakkun kuna cike da kaya.  Ina zaka?. na fada ina zuwa inda yake.  Ina ruwanki. ya ban amsa ba tare da ya kalle ni ba.  Ni kuma ka bar ni aina?.



 Baki duba takarda da na baki ba?. shiru na yi tsuru-tsuru.  Mus ab idan na koma gida iyayena tsinemun za su yi, Ummanah kashe ni za ta yi, ka rufan asiri dan Allah.



 Kiyi hakuri Salma na gama yanke hukunci na, kintsane ni, bakya so na, zama da ni babu abinda zai miki, na gama yanke hukunci wanda shine zai fi alheri a gare ni har da ke.



 Yanzu ka yarda iyayena su tsine mun, kayarda?, za ka ji dadi idan ka ga an tsinemun Mus ab, menene ribarka idan haka ta faru da ni, wane dadi za ka ji?.



Legends pen.





Page 42.



 Salma nima biyayya na ke, amma tin da haka ne ki zauna a gidan ba sai kin koma gidan Galadima, ni na bar miki gidan halak malak ki yi ta rayuwa a ciki. Shiru na yi, mai kuma zan ce bayan wanan, ya bar ni na zauna a gidan ni ka dai, to ni ai har shi ina son gani a gidan ba wai gidan kawai ba, ya zan fada masa haka?. Ji na yi yana jan akwatin kayan na sa zai fice. Yanzu tafiya za ka yi?.



 Tafiya zan yi mana, ai na bar miki gidan ki yi zamanki kinga babu wanda zai tsine miki tin da kina cikin gidan. shiru na yi har ya fice, ina jin an bude masa gate ya fice na rotsa wani ihu mai karfi.  Na shiga uku na ni salame na lallace, ina zan sa kai na da rayuwata, Mus ab ya sake ni ya tafi ya bar ni, na shiga uku na, na lalace. Abinda nake fada kenan cikin ihun na wa, kuka nake babu mai jina babu mai kawo mun dauki sai Allah,  ina zan saka rayuwata a wanan gidan babu miji babu aure?. haka nai ta kukana bahu mai ji na, har lokuta su ka ja naji anfara kiran sallan azhar, ta shi na yi na shiga daki na kwanta kai na nayimun wani azababen ciwo, mai sa jira da juwa ko ka na kwance, rufe ido na ke ina son bacci ya dauke ni ko zan ji sauki amma ina babu bacci babu mai kamarsa, ina kwancen na ke jin ciwon kan da jiri dakin sai juyawa yake, kuka na fashe da shi amma fa hawaye ya dauke mun, domin nasan yau na karar da hawaye na har na gobe da jibi. Ina cikin wanan halin wani bacci mai cike da wahala ya kwashe ni.



Mus ab kam na fita gidan sa na gwari avenue ya huce, domin Ummanah ta ce masa jar ya nuna kowa ba ya gidan tare da ni, kawai sai dai kowa ya ji maganar aurensa, wanda nan da kwana biyi za ta fito a gidan galadima, ma ana sa rana da kuma shirye-shirye. Bikin wata biyu za a daga sa rana ba wani lokaci mai tsayi za a ja ba, ya bar komai a hannunta shi kuma ya shiga rokon Allah, da kai wa Allah kukan sa a kan lamaruna da wasu abubuwan na shi, ya san da yabar ibada ya yi sakaci wajen kai wa Allah kukansa, ayoyin da Hajja ta ba shi duk ya yi sake da su. Rabbi inni lima anzalta illaihi min khairil faqeer. da sauran ayoyin al Qur ani mai girma, cike da yakinin ubangiji zai duba lamuran sa.





Ban ta shi daga wanan wahalalen baccin ba sai karfe biyar na yamma, lokacin ciwon kan ya ragu sai kuma yunwa dake kwazarzabar ciki na, amai nake ji amma ba na koshi ba na yunwa, ban samu sauki ba sai da na fara kwara aman nan, mai yawa na yi shi wani kore shar da shi, sanan na dawo na sa tea da bread a gaba na na fara sha, baki na babu dadi amma haka nake cusawa ko sabida yunwar cikina.



Haka rana ta daya ta zo ta huce babu Mus ab a gidan, na damu na kuma shiga wahala a kwana na biyu, na yi kuka har sai da idona ya fara zafi da yaji, kai na ya fara ciwo. Na yi nadamar kalamai na yi dana sani mai girma, nayi matsananciyar kewar Mus ab, muryar shi da nake cewa kamar ta gyare, yawan maganar shi da nake cewa yana damu na, kallonsa da yake yawan yi mun nake ce mai kamar maye, nayi matukar kewar su, a rana ta uku na gane cewa da ban yi kuka ba, ban damu ba domin kasan yin komai na yi, idan ka ga ni na rame na yi baki, kasan idanuna sunyi baki sosai kamar na zana kwalli, jikina duk ya fige babu wanan ado da gayun babu wanan kwaliarsa, na rame na fige kamar kazar mayu abincin ma sau daya nake ci a rana shima sai naji uwar azaba nake iya ci. Gidan ya yi kaca-kaca bana iya dauke ko tsinke domin da ciwon kai da jiri da nake yini nake kwana.



Haka rana ta hudu ma ta kasance, gaba daya Salma ta rame ta lalace kamar ba Galadima ba, naga rayuwa na yi na dama, na kuma tabbatar da zuciyata ta kamu da ™aunar Mus ab ko da karama ce. Ganin gidn na shirin zama bola ya sa na fara gyaran shi, ta kitchen na fara na yi kusan awa guda ko fi a cikin kitchen ina ta faman aiki kamar mara laka ajiki, haka na gama na dawo falo shima na kwashi kusan awa da motsi ina gyara shi, daga nan dakin da nake kwna na gyara akwai kusan Waku na biyar da ban ta Sa shiga ba bare na san mene a ciki, a iya ™asa kenan bare kuma sama wanda daga ni har shi ba ma rayuwa a ciki, dakin da naga yana shiga na nufa nasan na shi ne, kai tsaye na shiga nasan idan naga wani abu na shi zan rage wanan matsananciyar kewarsa da na ke.



Bude dakin na yi cikin sa a ya bude na tura kai, ™amshin turaerensa da nake cewa kamar na tumakai ya daki hanci na, sai dai yau jin shi na yi kamar yafi komai na duniya ™amshi mai dadi, dakin ya na da girma sosai da sosai, ya sha ado da gyara, frames din da na farfasa gaba dayansu an gyara su an manne su a dakin, zama na yi a kan katifar na ji zuciyata na wani iri bugawa da karfi, fiye da yadda nake ji lokacin da nake son Masrur.



Legends pen.



Page 43





Tabbas idan haka soyayya take a wancan lokacin ban so Masruru ba sai dai ko burgeni yake ko wani abu, amma yadda nake ji Mus ab har cikin Sargo da ™ashina ban ji masrur haka ba, hannu na sa na kai wajem frame din hotnan mu mai ni da shi guda daya na ciro, sanan na ciro mai hoton shi guda daya na hada nai waje da su zuwa da™in na sakale su, ko hoton na shi kadai nake kallo ai zan rage wani abu na kewarsa, amma tabbas ina son ganin Mus ab, ina son jin muryarsa, ina son jin motsinsa.





A Sangaren Mus ab kam ya dage sosai da sosai da sallolin dare da yawan na filfilo, ya mai da komai na shiga ubangiji. Yana jin kewata, ya na son ganina ya na son sanin halin da na ke ciki, amma yasan wanan hukunci da ya dauka shine dai-dai, ko bakomai zai gane idan ina son sa ko kuwa ba zan ta ba son sa ba. A cikin gidan Galadima kuwa, rana daya Ummanah ta fito sa zancen auren Mus ab, Maman ciki na zaune ita da Anty da matar Yaya ilyasu a bangaren Hajja, Ummanah ce ta ce. Hajja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login