Showing 45001 words to 48000 words out of 62407 words

Chapter 16 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

ko da tun da ba ka sa ni ba?. Shiru ya yi, daman ya san a kan sa zata karar da komai.  Tambayr ka fa na yi?.



 Ina son sani ne.



 Tsanar da ka yi ma ta, da cin zalinta da ka yi a baya shi ya ja ta ce maka baka da kyan hali. Shirun ya sake yi, tare da mi™ewa ya yi al™warin ba zai ™ara zuwa wajen Mama da irin wanan tambayar, dariya ta yi sanan ta ce.  To ango Salame, kar dai amanta da amanar da a ka baka. shiru ya yi ya fice, Sangarenmu ya nufa kai tsaye, Abban mu ba ya na Ummanah ce kawai sai yaya Asma u, bayan sun gaisa kamar ko ina amma Ummanah ba ta tambayi ya na ke ba.  Ummah ba ki tambayi Salma ba. banza ta yi masa, sai Yaya Asma u ce ta ce.  Ya matar ta ka.



 Bansani ba.



 Eyh ka ce ba ka sani ba mana, sanda ina maka lefe gaishe ni ne kawai ba ka yi ba.



 Dan Allah ta shi k ba ni waje zan yi magana da Ummah. ta shi ta yi ta shege daki ta ci gaba da hade kayanta. Bayan ta ta shi ne Ummah ta ce. Lafiya dai ko Mus ab?.



 Lafiya kalau Ummah, daman tambaya zan yi miki dan Allah.



 Toh Mus ab,ina jinka. ta fada ta na gyara zamanta.  Umma menene nagarta, menene kyan hali?. Kallonshi Umma ta yi sanan ta gyara zama ta ce.



 Nagarta, ita ce yin abin da ya dace, koda babu mai kallo. Mutum mai nagarta yana aikata gaskiya da adalci, yana tausaya wa mutane, yana kiyaye alkawari, kuma baya cutar da wani ko da yana da dama. Nagarta kamar haske ce a zuciya tana haskaka rayuwar ka da rayuwar wasu.



 Na am Ummah kyan hali fa?.



 Kyan hali kuma, shi ne dabi ar kirki da ake gani a ayyukan ka da hulWarka da mutane. Yana nufin ka zama mai ladabi, hakuri, biyayya, girmama na gaba da kai, ka dinga magana da kyau, ka kuma daina zagi ko faWa da mutane. Idan mutum na da nagarta da kyawawan halaye, zaka fi kyau fiye da tufafi masu tsada ko kuWi masu yawa. Saboda mutane suna mantawa da abin da ka ce, amma ba za su manta da yadda ka sa su ji ba. Nagarta da kyan hali su ne ado na gaske da babu mai iya cire maka.



 Nagode Ummah, kuma insha Allah zan zama mai nagarta da kyan hali.



 Mus ab waya ce ba ka da nagarta da kyan hali?, duk misalan da na bayar na nagarta da kyan hali a kan halayen ka na dauka, ka na da nagarta, kyan hali, cika da kamala.



 Umma tun da Salma ta ce ban da su, da alamu na ga za ta wani Sangaren.



 Yanzu kai fisabillilahi Mus ab zancen Salma ka sa a ranka har ka zo ka na tambayata, kai wanan yarinya ba ta da hali kwata-kwata.



 A a ba haka ba ne Ummah.



 Mus ab idan har za ka saka haukan Salma a ran ka to za ta iya cewa kai din ba musulmi ba ne, lamarin Salma addu a yake bu™ata kawai, da kuma yi mata zuru.



 Shikenan Ummah ngde. daga haka ya tashi ya fice, Ummah ce ta kira Yaya Asma u da ke daki ta ce. Asma u ina so kije gidan Salma, ki ci mun ubanta sanan ki hada ni da ita a waya.



 Toh Umma, na ji duk yadda kuka yi da shi, ni ina mamakin yadda Yaya Mus ab ya faWa soyayyar Salma har haka.



 Asma u nima na yi mamaki, amma kuma ba a mamaki da lamarin ubangiji kuma isnha Allahu ita ma sai ta so shi, fiye da yadda ya so ta.



 Allah yasa.







Mus ab daga bangaren mu, bangaren Anty ya nufa,nan ma sun gaisa sanan ya fice zuwa gida. Ina zaune a falo na cakare ado abuna, hankali na na kan Tv, daga kitchen kuma na Wora abincin, ™amshin abincin na ta shi a gidan. Sallama ya yi na amsa ciki-ciki, dan ba ma zai ji na amsa din ba.  Barka da gida Salame. ban kula shi ba, ban kuma juyo na kalle shi ba.  Tai ma ka mun da ruwa na sha. nan ma banzan na masa, ganin ba zan ba ya sa ya miki ya nufi fridge ya Wauki ruwan shi ya sha, ya dawo ya zauna.  Salma yau na sha rana, Mama da Hajja da Anty da Umma suna gaida ke. wani hawaye na ji na shirin tawo mun, ashe gidan Galadima ya je ya bar ni a wanan gidan na sa, mai kama da na fatalwa, wanan shine amfaninn auren kenan yazo ya turkeni kamar tikinya ko.  Kai da Allah. na fada a zuciyata.



Legends pen.



Page 33





 Salma mai kike so na yi, na kyan hali ko na nagarta, ki fadamun dan Allah.



 Wai Mus ab ina shiga sabgarka a gidanan ne, me yasa kai kake shiga tawa, ba ka da zuciya ne ko me.



 Salma a kan ki ba ni da zuciy kwata-kwata wallahi, Salma ba ni na Worawa rai na son ki ba, ubangiji da ya hallice ni ne. Banza na yi da shi, ni ban san me zan ce masa ba, kawai ya yi nesa da ni, amma tun da ba shi da zuciya ai shikenan ni dai ba zan kula shi ba.



Ta shi ya yi ya nufo inda na ke, ban aune ba na gan shi ya tsugunna a gaba na.  Salma ki yi wa Allah, ki yi wa ma aiki, ki sassauta mun wanan tsanar, ki yafe ni ki karbi tu ba na dan Allah.



 Ni ka ta shi daga inda na ke kawai.



 Salma, ki yi hakuri.



 Mus ab ba zan ta Sa yafe maka ba, ni kawai ka rabu da ni. shiru ya yi, ya rasa me zai mun, ya yi fushi ya kyale ni, ya sake gwadawa, ko me zai yi.



Ta shi na yi na nufi kitchen duba abincina, na bar shi wajen a durkushe, ina dalili zai zo ya yi mun makirci, ni akwai abin da zai sa na yafewa Mus ab a duniya kowa, ai ganin shi na yi yana masharsharar mutuwa ban jin zan ya fe masa, fito wa ta daga kitchen bayan na duba abincin ya yi dai-dai da fara knocking din kofar da a ka yi, shi ya ta shi ya nufi ™ofar ya bude, wa zan gani idan ba Yaya Asma u ba.





Ta shi na yi na nufi kitchen duba abincina, na bar shi wajen a durkushe, ina dalili zai zo ya yi mun makirci, ni akwai abin da zai sa na yafewa Mus ab a duniya kowa, ai ganin shi na yi yana masharsharar mutuwa ban jin zan ya fe masa, fito wa ta daga kitchen bayan na duba abincin ya yi dai-dai da fara knocking din kofar da a ka yi, shi ya ta shi ya nufi ™ofar ya bude, wa zan gani idan ba Yaya Asma u ba.



Yana ganin ta shigo ya sa kai ya fice, ni kuwa nayi cikin daki da sauri, yanda take zare idanu tana bina da wani kallo kamar sabuwar mayya ya sa nasan ba alheri ya kawo ta ba, da alama jibgata ta zo. Karki kulle dakin nan na gaya miki. tsayawa na yi ina kallonta sanan na ce.  Ya aka yi?.



 Ubanki a ka yi. ta fada bayan ta zo inda na ke.  Shige muje. dakin na shige a rai na ina mamakin munafunci irin na Mus ab, ya je ya kai gulma kuma ana zuwa ya gudu. Zama ta yi a kan gadon ni kuma na tsaya a kanta ™erere.  Zaki zauna ko sai na ci ubanki. zama na yi can nesa da ita, ina turu ba ki gaba.  Ni ba na ce ba zan kara neman ku ba har abada, to ku mai ya kawo ku waje na?.



 Ke dalla malama rufemun baki, shashasha da ba ta san me ke ma ta ciwo ba, ba ki san aure ba da darajarsa, to Wallahi Salma ki kula ki kama kan ki, aure ba abun hulakantawa ba ne, miji ba abin yarwa ko hulakanta wa ba ne, haka iyaye ba ababen wasa ba ne, ba kuma mutane da za a kiyiwa biyayya ba ne, dan wallahi muddin kika ci gaba da ba™anta musu, zaki ga wahala ne a rayuwarki wahala ta gaske. ™aurin da ke ta shi daga kitchen ne ya katse ma ta maganar da ta ke.  Me kika dora a huta, ta shi ki je ki kashe yana ™auri.



 Abinci ne. na fada ina kokarin mikewa.  Ke sai yanzu kike yin abincin ranan sai yanzu, mijin na ki haka kike gana mai azaba, salma kiji tsoron Allah. shiru na yi kawai na tashi, a raina ina cewa  wa zai masa girkin ba dai ni ba wallhi. kamar ta san abinda nake fada ta ce.  Salma kina yin girki da shi?.







 Yaya ni zan masa girkin?.



 A a, ni zan zo na masa dan ubanki. ta fada tana danna wayarta, fita nayi zuwa kitchen din na kashe girkin na dawo. Tun kafin na kara shiga dakin na ji tana cewa.  To wallahi Umma ko girki ma iya cikinta ta ke yi, ba ta ba shi. ban ji mai Ummah ta ce ba, amma nasan fada ta ke.  Bari ta shigo.



 Innullahi wa inna illahir rajiun. na shiga maimai ta wa, jikina sai Sari yake na kasa shiga dakin gaba daya, sai da na dau kusan mintuna 10 a haka sanan na shiga dakin.  Sai yanzu kika gama tsayuwar? To ki zo ga Ummah. ta fada tare da mikamun wayar, karba na yi hannuna na rawa na fara magana.  Ummah ina kwana.



 Bansani ba Salma, bansani ba.



 Ummah kiyi hakuri dan Allah.



 Salma mai kike so ki zama, mai kike nema a rayuwa haka, mijinki kullum kina masa ra shin azirki, Salma kullum kina ba ta ran iyayenki, kina tunanin zaki samu riba a haka?.



 A a Ummah.



 Salma kin fusata mahaifinki, kin kai shi karshe ya sare da lamarinki, so kike nima na yi haka, mu barki da duniyar, mu barki da halinki?.



 A a Umma Wallahi bana masa fada, bana masa rashin kunya.





 Amma ai bakya ba sa abinci, bana jin ma ko gaishe shi kina yi?.



 A a Ummah.



 Salma ba zan ™ara ce miki ki gyara ba, ki yi komai da kika ga yada ce, amma ki sani Allah na ji kuma yana gani.



 Ummah ki yi hakuri dan Allah. Wif naji an kashe wayar ga baki daya, kuka na ci gaba da yi iya karfina babu mai rarrashe na babu mai ce mun dai na.  Salma idan kinga dama kin yi hankal kanki, idan ba ki yi ba ma kan ki, amma ki sani duk ranar da kika kashe auren ki, tsakanin Ummah da Abba babu mai karSar ki, kuma kin san duk duniya babu inda zaki ji dadin zama, kamar gaba iyayyenki. shiru na yi ina ci gaba da kuka na, a zuciyata ina cewa.  To yanzu me nake, ni ina son in rabu da iyayema lafiya, amma Mus ab ya na so ya ga haka ba ta faru ba.



Legends pen.



Page 34





 ki ta shi kije, ki dora wani abincin, kuma daga yanzu ki tabbatar kina kowanne girki da shi, safe rana dare, ki kai mai kan dinning ki ajiye masa.



 Tom. kawai na ce na ci gaba da kuka na, haka tai ta bani shawarwari, amma ciki ban ji wacce zan iya dauka ba, domin shwararwarin na ta sun tafi kan macen da ke so miji ya so ta, ni kam ban ga abinda zai sa na so Mus ab ya so ni ba, mai zan yi da soyayarsa, mai zan yi da ita. Har ta gama ta tafi ban dai na kukan ba, sai da na yi mai isa ta har na ji kai na ya fara mun ciwo sanan na yi shiru, wani wahalallen bacci ya yi gaba da ni.



Ban ta shi ba sai bayan biyar daman lokacin hudu ta yi, ta shi na na yi wanka, amma yanzu ban yi wanan azababben make up din ba, yunwa nake ji hakan yasa na nufi kitchen, yana fallon yana aikin latsa computer, ban kalli inda yake ba bare ma na san da zaman sa. Taliya na dora jollop na hada drinks, ina kitchen din komai ya kammala, na zuba mai a plate na dauka na fito falon, kan dinning na je na ajiye mai tun da can a ka ce na dinga ajiye mai, sanan na koma kitchen na dakko nawa na yi cikin daki.



Murmushi ya yi, sanan ya ta shi ya nufi dining din yana ci yana santi abun sa, lallai Salame ta iya girki abunta, shi kam ya ji dadi sosai ko iya girkinan zam dinga ba shi kullum, haka ya ci ya gatse sanan ya kai plate din kitchen ya dawo kan system din shi.



Ni kam ina shiga daki na sa abinci na a gaba na ci na sha drinks dina, hankali na kwance na gama na fito kitchen na wanke kwanika na, na gyara kitchen dina, tabbas wanan xaman ya ishe ni na gaji iya gajiya, ko makatanta ko wani abun, amma kuma ai ko waec da neco ba muyi ba, ina zancen zuwa makaranta?, ko ance na je ma ba zan je ba, dan ba zan iya shiga cikin  yan ajinmu ba a matsayin matar aure, matar auren ma ta mus ab wanda kowa yasan yadda na tsane shi.



A bangaren Mus ab kuma bayan ya gama ci Abdul ya kira shi a waya, bayan sun gaisa ne Abdul ya ce.  Boss yaushe xa ka koma aiki?.



 Ba ku sa ba fa, sai na samu soyayyar gimbiya ta ko zai dauke ni shekaru, nine mai gidan kai na babu wanda zai neme ni ko ya hukunta ni. Dariya Abdul ya yi, sanan ya ce.  Sai an nemo soyayyar gimbiya, akwai hanyoyi da dama na neman soyaya, ka yi amfani dasu mana.



 Wane irin hanyoyi Abdul?.



 Akwai kyautatawa, nuna so, nuna kula, ka dinga bauta mata, i mean ka dinga nuna mata so, dan baitin nan na waka ka yi mata, ka dinga daukan ta kuna fita dinner, da sauran abubuwa.



Shiru Mus ab ya yi, tabbas wanan shawarwarin idan ya gwada su za a iya da cewa





Amma ya san Salma na da matsla, ba lallai wa yanan abubuwan su burge ta ba, ya santa da tsatsauran ra ayi, amma ba a ™in ta mutum zai gwada hakan, godiya ya yi wa Abdul tukunna su kayi Sallama.





Fito wa na yi falon ba yan na idar da Sallar isha, nasan dai-dai lokacin MBC Bollywoood ke saka fina-finan indiya masu kyau, jikin sa a na ga sun daka jodha akbar na Ashwarriya da hrithick roshan, film Win da har yau ban ta Sa ganin karshen sa ba, godiya na yi wa Allah na sa a rai na yau kam sai na ga karshen film dinan, tin da dai nan ba dauke huta a ke ba, ina zaune hankali na na ka ya shigo ya zauna ne sa da ni, can ™asa na fara jin muryar shi kamar mai wa™a, dan mai da hankali na yi, sai ji nai ya na cewa.  Na ™yasa kalal ki, drees da tsarin zubinki sun ka tsuma ni. sai a lokacin na fahimci wa™a ya ke yi, dariya na so na yi amma na maze, na ci gaba da kallona.  Bege na son ki na ri™e, ki zare Sakata ki na bayyana miki ™auna. a rai na na ce.  Sakata na zura ta kenan ba zan ta Sa zare ta ba har abada. na faWa a cikin rai na, dan ban na ma nuna mai ina sauraron shi ba. Ke na hango jiki a take ya hau Wari, sai na rugo ™afafuwana cikin sauri, ungo-ungo kyauta gareki mai alkhairi, bude ki duba zuciya ta kamu da kauna. ya ™arashe tare da mi™o mun wata lead, kallo daya na yi mishi shida ledar na watsar, dan a ganina ban da lokacin shirmen sa.  Salma ki kar Sa mana is for you.



 Mus ab ba na bukatar komai da ga gareka, sabida ba a tsiya ce ka ganni ba.



 Nima ai ban ce a tsiyace na gan ki ba, ranki ya dade, kyauta ce wacce ba a tsammani na yi miki.



Ta shi na yi na shige cikin daki, dan ba ni da lokacin biyewa shirmen Mus ab, na so kallon ™arshen jodha akbhar amma bai bar ni ba.



Tun da shiga ban ™ara fito wa ba, gado na haye na kwanta tare da yin addu a, shima Mus ab din a bangaren shi dakin shi ya huce, ya na ™udurtawa a zuciyar shi ba zai sare ba, ba zai ha™ura ba.



Bud e idona nake ™o™arin yi, amma na ji idanu na sun yi mun nauyi, kaina ya na mun wani irin zugi, da alama da matsanan cin ciwon kai na ta shi, ina lissafe yau sati na biyu a gidan Mus ab, tun ranar da na fara girki da shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login