Showing 21001 words to 24000 words out of 62407 words

Chapter 8 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

yayi niya ba, sanan ba zata canja komai daga abinda ke rubuce a littafin addararku ba. Tun lokacin da naji ta ce banyi ko awa biyu da barin gida ba, aka Waura mun aure da Mus ab, ban sake tsintar ko kalma Waya daga maganganun ta ba, wani abu mai nauyi naji ya durga a kai na, zuciyata ta fara bugawa da wani irin arfi. Fat! fat!!, idanuwa su ka fara mun yaji, hawaye su ka Wauke, sai wani zugi da radaWi nake ji daga cikinsu, kalmar da na ara ji ita ce.  Yanzu Salma mene ribar abinda kikayi, banda Satawa kanki suna, ko kin san duk macen da ta taSa sa afa tabar gidan iyayenta, ta tashi daga matsayin mace mai daraja. BuWe baki nayi da niyar cewa.  Gwanda na dauwama a matsayin mara daraja, a kan na dauwama a matsayin matar Mus ab. sai dai jin baki na ya gagara buWuwa ya sa nayi shiru. Yanzu Salma ina zaki kai fushin iyayenki na kan ki?.



 Tana ina?. Muryar Abbanah ta kara We gidan, Wage labulen Wakin yayi, hannushi rie da bulala mai girma, take idanuna suka fara zubar da ruwa.  Kayi hauri dan Allah. Maman ciki ta faWa, Abbanah bai ko kalleta ba yayo kai na, ji kake zit, ya fara sauke mun bulala a jikina, ta na shiga ta da wani irin zafi, duka na yake kamar Allah ne ya aiko shi, babu tausayi babu imani, tun ina zubar da hawaye har hawayen ya are, na koma nishi kawai, sai dai zuciyata na ara tsanar Mus ab, shikenan ya shiga, ya fita ya rabani da iyayena, ko aina yake na san yana can yana farin ciki da jindaWi.  Yah Allah ka saka mun, kabi mun hainah a kan Mus ab, ka gama shi da masifar duniya ya Allah.





*Mus ab*



Kwata-kwata bai iya bacci ba, zuciyarshi tai bari ya runtsa, tai saurar masa da tunanin halin da nake ciki, ayyana masa take.  Yanzu ina Salma, tana wane hali, ta kwanta, ta ci abinci, ya zatayi da wanan sanyin da akeyi, sauro ba zai cije ta a inda take ba, idan ta haWo da Sata gari fa?. Shi kan shi ya rasa mai ya haifar masa da wanan damuwa da ni Win cikin ananin lokaci?.



Haka yayi kwanan zaune, yana ta faman tara da kwashewa, sai gab da asuba wani Sarowan bacci ya Wauke shi, kuma ba a samu wani ya tashe shi ba. Cikin bacci ya fara jin sautin kuka na, zuciyarsa na wani bugawa da arfi, runtse ido yayi sanan ya buWe su, rau yaji kukana.



Da sauri ya tashi ya buWe window Win Wakinshi, ni Win ce Abbanah ke duka, tabbas yaji daWin ganina da a kayi, amma kuma dukan da kukan nawa ya tsaya masa a rai, gani yake kamar shi yajamun komai, da bai yi rashin lafiyar ba, da ba za a auramun shi ba, shiru yayi yanajin saukar bulal a cikin su zuciyarsa. Mus ab, mene na damuwa da yarinyar nan haka?. yaji tambayar a cikin kunnuwansa, da sauri ya wai ga ko wani ne yayi masa maganar, amma ba kowa sabida ko ofar Wakin bai buWe ba. Ganin kamar Abbanah bai da niyar kyaleni ya sa shi buWe ofa ya fito waje da sauri.  Abba a yi hauri dan Allah. Wani maoon abu ne ya tsayamun a maoshi, tare da wata sabuwar tsanarshi da ta ninka ta baya, sau dubu da Wari biyar.  Munafuki, wutar Allah ta cika. Na faWa a zuciyata, tare da galla mai harara a fili.  Mus ab, ka karbe bulalal nan. Mamam ciki ta faWa, dan gaba d aya ta gama rud ewa da irin dukan da Abbanah ke mun, ni kam a yanzu zafin tsanar Mus ab, ya ninka zafin dukan da abbanah ke mun, hannu ya kai zai karb a Abbanah ya ce.  Karka kuskura, Anty ce ta shio ita da Alhaji k arami.  Kayi hak uri Yaya dukan babu abinda zai gyara, hukunci kuma ka ga ma yiwa Salma shi, tun da ka d aura ma ta aure. Alhaji k arami ya fad a.  Kyaleni kawai. Abbanah ya faWa, yana ci gaba da dakuna, ga mamakin kowa sai kawai ganin Mus ab a kayi ya faWu kaina, ya lulluSeni da jikinsa, ya kare ni baki Waya.



Ganin hakan yasa Abbanah ajiye bulal ya fice, ni kuma wani ululin takaici ya isheni, wai yau Mus ab ne ya ceceni, citon munafuncin, domin ko da ur ani a ka bani zan iya rantsewa da shi, zuciyar Mus ab fara take tas!



Abban na fita, Mama da Anty sukayo kai na.  Salma kinjawa kan ki fushi mai tsanani, kin san yadda mahaifinki da mahaifiyarki su ke, mai yasa kika buaci haka, yanzu Umman naki ke cewa, ba zaki sake zama wajenta ba, shima kuma tun jiya ya faWi haka, dan Allah salma menen ribarki anan?. Anty ta faWa, tabbas jikina yayi sanyi, a kan hukuncin da iyayena suka yanke, amma kuma koma menene Mus ab ne ya ja, kallonshi nayi yadda yayi wani tsuru-tsuru.  Ko menene ribarshi na haWa ni da iyayena oho?.



legend s pen



Page 14.





Kallona yake ta asan ido, yanda na daku naji jiki, abun ya matuar ta Sa shi, ga kuma hukuncin da iyayena suka yanke a kaina, duk wanan a kan shi, tabbas yana buatar neman shawara ko mafita a kan lamarin nan, amma kuma zuciyarsa ta addaba masa ta wani Sangaren, tunani da yawan damuwa da al amurana, tun daga jiya har yau, tunawa da yayi baiyi ko sallar asuba, ya sa shi ya tashi da sauri, duk da wai ba gari ne yawaye ba, dan wasu masallatan ma yanzu su ka idar.





Ficewa yayi zuwa Wakinshi, ya Waura alwala ya gabatar da sallah, sai dai ga matuar mamakinsa, sai ya tsinci kan sa da addu a gare ni.  Ya Allah, ka kawo saui a lamuran Salma, ka ba ta haske a rayuwa, ka sauaa zuciyar iyayenta da ta ta. Sai bayan ya idar yayi da addu ar ma, wani mamaki ya kamashi, sai kuma ya kaudar da tunanin ta hanyar cewa.  Tabbas yanzu Salma na cikin halin da take buatar addu a.





 Salma, ta shi ki je ki watsa ruwa, ko zaki ji daWin jikinki, sanan ki rama sallolin da ke kanki. Sai a lokacin na tuna ko Sallar magribar jiya ban yi ba, ga isha i da kuma asubar yau. Tasi nayi jikina babu wari kwata-kwata, afafuna sunyi tsami.



A hankali na nufi hanyar ban Wakin,dai-dai lokacin da a ka buWe kofa a ka shigo, Hajja ce, bayanta kuma Ummanah ce, kallo Waya na yiwa Hajja na Wauke kai, Ummanah ko kallo ban ishe ta ba.  Sannu. Naji muryar Hajja ta faWa, ji nayi kamar na shaota na tsinka ma ta mari, ko zan ji ni dai-dai.



Shigewa ban Wakin nayi, na gasa jikina da yayi tsami sosai, sanan na Waura Alwala na fito, Wakin Walida na shiga tana zaune ta rafka uban tagumi.  Bani kaya na sa. na faWa a daile, danni gaba daya gidan Galadima haushin kowa nake ji, gani nake gaba Waya sun tsane ni, tuno wa nayi da auren Mus ab da ke kai na. Hannu na Wora a ka tare da runtuma ihu na zube a asa.





Shigewa ban Wakin nayi, na gasa jikina da yayi tsami sosai, sanan na Waura Alwala na fito, Wakin Walida na shiga tana zaune ta rafka uban tagumi.  Bani kaya na sa. na faWa a daile, danni gaba daya gidan Galadima haushin kowa nake ji, gani nake gaba Waya sun tsane ni, tuno wa nayi da auren Mus ab da ke kai na. Hannu na Wora a ka tare da runtuma ihu na zube a asa.



Da sauri Walida ta watsar da kayanta, ta yo kai na tare da faWin.  Salma lafiya?. Banza nayi ma ta na ci gaba da kuka na, kuka wiwi kamar wacce a kayiwa mutuwa. Salma wai kukan mai kikeyi haka, sai ka ce wacce ta ga ranar mutuwarta.



 Ni da wanan mummunar ranar, ai gwanda naga ranar mutuwar Hajja. dariya walida tayi, sanan ta ce.  Salma Allah ya shirye ki, yanzu fa ke matar aure ce, mata a wajen Mus ab Galadima, matashin da kika daWe kina fatan zama matarsa.



 Allah ubangiji ya tsine miki albarka Walida, wallahi na tsani Mus ab, na tsaneshi fiye da yadda kike tunani, kuma wallahi ba zan taSa zama matar Mus ab ba.



 Matar Mus ab dai, kin gama zama, sai dai kuma idan ya ara auren ki zama uwar gida. Tashi nayi na shau wuyanta, ji nake kamar na kasheta ko na huta da wanan maganganun nata masu kamar sa saukar ruwan zafi a jikina.  Dalla cika ni, mahaukaciya. rufe idanuna nayi, abu kamar wasa ya zama babba, tun Walida na Waukan faWan arami, har ta fara mai da mun da martanin duka, ni kuwa na taarare arfina sai labtar ta nake, ita ma kuma ta fara ramawa.



arar hayaniyar da suka ji a Wakin ne yasa su shigowa, da mamaki suke ganin yanda muke faWa da junanmu, abinda ba mu taSa tun girman mu.  Walida!, Salma!, me kukeyi haka?. Maman ciki ta tambaye mu.  Wai kawai daga ina magana ta shaemun wuya.



 To na ce kiyi mun magana, kuma wacce magana kika zo kina mun, ina ce ba tsokanata kikeyi ba, wai matar Mus ab.





 To dan ta ce matar Mus ab shine ne, ba matar tasa ba ce, ko dan baki da ku bane, za ki zo kinawa mutane shirme anan. Ummanah ta faWa cike da fushi.  A ah, to ita Walidan mai ya kai ta yi mata wanan maganar.



 Duk ya isa haka, ke Salame ki shirya ki biyo ni Sangarena.



 A a, ni Hajja ba zanje Sangarenki ba.



 To gidan ubanwa zaki?. Ummanah ta faWa kamar zata dake ni.  angarenmu. na faWa tare da cuno baki.  To wallahi idan har kika ga kin dawo waje na da zama, to bana raye ne, Salma na sallamaki, na barwa duniya ke, tun da haka kika zaSa, kin zaSi dubiya a kan yi mana biyayya.



 A ah ya da haka, bana son ara jin wanan maganar. Hajja tari numfashin Ummanah.  Wai so kike sai kinyiwa yarnyar nan baki ne zakiji dadi?. Maman ciki ta tambayi Ummanah, sanan ta Wora da cewa. Idan fa rai yaSaci, hankali baya gushewa.







 Shiyasa na ce dole a raba ta da yarinyar nan, nasan nan ke zaki rieta, amma mugun halinta ba zai barta ta zauna ba. Hajja ta faWa. To ai wajen naki ma Hajja ba zama zata yi ba. Maman ciki ta faWa.  To ina za a kaita?. Zallan mamaki ne ya kusa kasheni, wai ni da gidan ubana a ke neman inda za a ajiye ni, kamar wata kayan wanki,  taya za ace bazan tsani Mus ab?. na tambayi kai na.  Ni ba zan tsoma muku baki ba, amma gidan mijinta shine inda ya dace ta zauna. maganar Ummanah ta dawo dani daga tunanin da nakeyi.  Ba fa yarinyar nan zata bar gidan nan ba, sai anmata duk duk wani abu da ya kamata, sanan haWe bikin nasu za ayi da Halima, sabida shi yaron yana son tafiya karatu asar waje.



 To yanzu Hajja ya za ayi?. Maman ciki ta tambayi Hajj, bayan ta gama magana. Ta ci gaba da zama nan, idan zaman nasu yai daWi, ko ita ko Walidan wata sai ta dawo Sangarena. Hawaye naji sun fara zubomun a fuskata, wani ni ce a ke yiwa haka, a kan wani ya shigo rayuwata, tabbas Mus ab ya zama annoba a rayuwata, ya zama fitana, Wakin Walida na koma na zauna, tare da zabga uban tagumi.





*Masrur*



Waye Masrur, mai ya kawo Masrur rayuwata?.



legends pen





Page 15.







*Masrur*



Waye Masrur, mai ya kawo Masrur rayuwata?.



Kamar yadda ya faWamun a farko, sunanshi Masrur, kuma wanan asibitin na mahiafinsa ne, kuma shi ke kula dashi. Masrur shine Wa, Waya tilo a wajen mahaifinsa, Wan-gata ne na arshe, mara kuma jin magana. Irin su Masrur ne matasan da kan shafe shekara da shekaru suna bautawa mace, a kan su sameta na rana Waya, lokaci Waya.



Masrur irin mazan nan ne mazinata, shi kan shi bai san adadin  yan matan da yayiwa fyaWe ba, wayanda kuwa yayi zina da su, sun fi cikin buhun hatsi, karuwai kuwa yana da su sunfi guda asirin, ya ware sosai a yaudara.





Wanan shine Mus ab. Mai ya kawoshi rayuwata.





Ranar Wata Asabar, mun dawo daga makarantar hadda ta safe ni da Walida, lokacin Sadiya tayi gaba sabida tana sauri zasu je gidan yayar Anty, gidansu saurayinta. Shi kuma dai-dai lokacin ya fito daga wani babban shagon aske da ke bakin titin mu.



Waya ce a hannunshi yana dannawa, amma idanunsa na sauka a kanta yaji ya kasa Wauke su, zallan kyau ne kawai ya Webeshi, sakamakon sauran  yan matan da jikinsu ne ke Wibarsa.  Wanan tayi yarinya. ya raya a ran sa, amma shaiWaniyar zuciyarsa ta ce masa.  Wanan ita ce dai-dai, ka rai ne ta da soyayyarka, yadda zaka juyata yadda ka so. Ba shiri ya fara bin mu a baya, har zuwa lokacin da mu ka shiga gida.



Tun daga wanan ranar Masrur yake sintirin bin bayana, har sai da ya gama fahimtar komai a kan rayuwata, ranar da muka fara magana, ranar ya tsara hakan, sanan layin da ya bani, ni kadai ke kiran shi da shi, shiyasa duk lokacin da na kira yake kama sunana kai tsaye, a kullum mugun kudurin shi a kaina ara girma yake, yau da gobe yana ara jin sabuwar sha awa a kai na, wacce bai san ta zama soyayya ba.





Matsalal shi da Mus ab kuma ita ce.



Masrur ya taSa yiwa wata yarinya fyaWe, wacce take  yar aikin gidan su abokin Mus ab, to a lokacin da aka yi case Win, Mus ab baya asar, sai da yadawo ya samu labari, kuma gayen da aka nuna masa yayi masa kama da Masrur, kasancewar an Wauki shekaru, Mus ab ya manta asalin kamar gayen, shiyasa kawai ya watsar da lamarin masrur, ko dan irin shigar kamalan da ya gani a tare da shi.





*Wanan kenan*





Zaune nake kan doguwar kujera, na kafa uban tagumi, tambayar zuciyata nake.  Ina Mafita?. sai dai zuciya tayi banza dani, kamar ba da ita nasaba neman shawara a kan komai ba, so nake nayi tunani amma na kasa, abu Waya ke dawowa zuciyata, shine: na zama matar Mus ab. Ji nake kamar na cire kayana, nai ta ihu kamar mahaukaciya, ko kuma na kama gini nai ta duka, ko zanji saui a zuciyata.



Ikram ce ta shigo, janye da atuwar akwati wacce nasan ta kayana ce.  Ke wanan fa?.



 Ummah ce ta ce a kawo miki, wai kayanki ne?.



 To ina sauran?.



 Wai an haWe miki su, da su za a haWa da lefenki a kai gidan mijinki. Ji nayi kamar ta watsa mun huta, na kai hannu na Waka ma ta duka, ta fice da gudu tana faWin.  Ke da Allah. Ni kai nasan kwana biyu na koyi saurin hannu, wanda da ba haka nake ba.  Uhm, bawanan ne ga ba na ba. Na faWa a fili, domin nasan ba shi bane a gabana, tunani nake son yi amma na kasa.





 Salma ya kama ta ki rage wanan mummunar addu ar ga Yaya Mus ab, domin ance idan kayi addu a ga wani bawan, mala iku suna amsa da cewa Walaka, idan macece Walaki. Tuno lokacin da Sadiya ta faWamun wanan maganar nayi.  Ke ni Wallahi indai Mus ab zai ga mu da masifar duniya, to ba wani abu ba ne, dan nima na gamu da ita, Sadiya ba zaki gane yadda natsani Mus ab ba. Amsar da na bata a lokacin kenan.



Tabbas addu a ta ta amso amma a kai na, domin tabbas Mus ab ya kasance masifar da aka gama ni da ita.



Wanan wace irin rayuwace, nayi masa addu a ta faWa kai na, nayi masa mugunta sabida ya mutu da ciwo, ya juye kai na.





Tabbas addu a ta ta amso amma a kai na, domin tabbas Mus ab ya kasance masifar da aka gama ni da ita.



Wanan wace irin rayuwace, nayi masa addu a ta faWa kai na, nayi masa mugunta sabida ya mutu da ciwo, ya juye kai na.



Kuka na fara, hawaye suna bin kunci na, ga tilin kayana da aka kawomun daga gidan ubana a gaba na, duk wanda ya ganni dole ya tausayamun. Yana tsaye bakin taga yana kallon yadda nake zubda hawaye, yana jin zubar hawayen a cikin zuciyarsa.



Tabbas ya kamu da tausayina mai girma, domin duk wani kuka na, ko zubar hawaye na, yana jinsa a zuciyarsa, ji yake kamar ya je ya kamani ya gogemun hawayen, ji yake kamar ya je ya bawa Abbanah hakuri kan su janye auren nan, in dai hakan zai sa na daina wanan kukan.



Ficewa yayi zuwa bangaren Hajja, tana zaune daki tana faman lisssfin bikin Mus ab, wai zata gayyato awayenta na uruciya, suyi ashobe abunsu, kuma so take Abban ciki ya kawo mata atamfar turmi ashirin tarabawa kawayen na ta. Kallon shi tayi, yadda ya shigo sim-sim kamar mara gaskiyya.  Mus abunah mene ya kuma faruwa?, dan nasan wanan fitinanniyar matar taka batta bari mu zauna kalau. Zama yayi kusa da ita, sanan ya ce.  Bakomai Hajja, kawai gani nake dan Allah a fasa wanam auren Hajja, bana son naga yarinyar nan ta na kuka.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login