Showing 24001 words to 27000 words out of 62407 words

Chapter 9 - SAKATA COMPLETED WRITING BY SAYYID (LEGENDS PEN).txt

baki buWe Hajja take kallonshi, tun da ya fara magana, har ya dire.  Eyh Lallai ne, salau, sallamu, tun kafin a kai ta gidan naka, ka fara cewa baka son ka ga tana kuka?.



 Ni ba haka ba Hajja, gani nake kamar an shiga ha™™inta.



 Lallai ne Mus ab, to idan kamanta bari na tuna maka, yarinya fa an d aura muku aure, yanzu komai na ta yadawo ™ar™ashin ka, cin ta, shan ta, sutturarta, da duk wani sauran nauyinta, rashin yi mata duk wani abu na al adar aure shine shiga ha™™inta, dan haka tun wuri kaje ka fara shirya komai, wajen xama da kayan lefe. Shiru yayi, shi wajen zama ai sai dai ya bawa wani, sanan kayan lefe ma ba matsala ba ne, ko yanzu yayi waya kafin awa Waya sai an had a mai komai da komai, amma yanda za ayi zaman?, shi gani yake a ta bangarenshi babu matsala, tayi rayuwarta yayi ta sa, ko gaisuwa karta haWasu, ko abinci ba zai buk ata daga wajen ta ba.



 Kaji abinda na ce maka?. Gyad a kai yayi ya tashi ya fice, Yaya Asma u ya kira a waya, daman ita ce kawarsa a kaf Galadima. Tana zaune ta ga kiransa ya shigo, dariya tayi har sai da mijinta yak kalleta. Mus ab ne. ta faWa tana Waukan wayar.  Ango, Ango. Angon salame na Hajja, Yayana kuma mijin ™anwata. Tsaki yaja tare da cewa.  Asma u mai yasa ba zakiyi hankali ba. dariyar ta ™arayi sanan ta ce.  Hankali har ya huce na baka ™anwata ka aura?.



Legends pen





Page 16.





 Ba wanan maganar ba dan Allah, ki nutsu. zama ta gyara sanan ta ce.  Tom, na nutsu ina jinka.



 Idan za a haWa lefe, kamar nawa ce za tayi.



 Na talakawa ko na masu kuWi. ta tambaya tana dariya, a fusace ya ce.  Na dai-dai ahalin Galadima.



 A ah, mai yayi zafi bawan Allah da zaka gayamun ba suger.



 Zaki faWamun ko na kashe wayata.



 Yi ha™uri, idan za ayi ™arami 1.5million zata isa, idan kuma ana son matsaiakaci 2million, tsaka tsaiya kuma 3million, idan kana son wanda zai yi kyau ba ayi almubazaranci ba, amma kayan sunyi yadda za a faWa 5million, idan kuma ka na son mai yawa 10millon.



 Account dinki zai iya Waukan 7million?. ita kanta ta ji mamakin 7million Win da ya fada, amma sanin yana da kuWi, zai iya fin haka yasa ta ce.  Na wa kam bai Wauka, amma bari na baka namiji na.



 Okay, zan samiki 7millinon sai ku haWa yanda ya dace. daga haka ya kashe wayar.  Lallai salma anyi goshi,amma ta tsaya tana iskanchi. Yaya Asma u ta faWa, sanan ta kalli mijin ta ta ce.  Zan bawa Mus ab account dinka, zai sa mun kuWi zamu haWow Salma lefe.



 Okay badamuwa, sai na bar miki atm Win. wayarta ta Wauka ta kira Yaya ta Zaria, ta shaida mata komai. Eyh, Lallai Mus abun Hajja. Yaya ta Zaria ta faWa.  uhm bari ke dai, ran  yan maza yaSaci, yanzu goben kawai nan xaki shigo.



 Shikenan sai mu fita da huri. daga haka su kayi sallama.







Maman ciki ce ta shigo ta ganni ina ta faman zubar da hawaye, ga kuma tulin kayana a gaba na. Zama tayi kusa dani tare da faWin.  Salma. a hankali na ce.  Na am.



 Ya kamata ki nemi yafiyar iyayenki, domin suna matu™ar fushi dake, hakan kuma ba ™aramin abu ba ne. Murya ta a hankali na fara magana. Amma Mama mai yasa ummanah ba ta so na,a kullum ta zaSi abinda bana so a kan wanda nake so, ba ta damuwa da farin cikina.



 A a, wanan maganar ba gaskiyya ba ce Salma, babu yanda xa ayi mahaifiyar da ta haifi mutum ya zamana ba ta son shi, kin san irin sadaukarwa da iyaye domin farin cikin  ya yansu, kin sam irin yanayin da iyaye ke shiga idan su kaji kukan  ya yansu?, tabbas kinyi wa mahaifiyarki fahimta ba dai-dai ba, kiyi gaggawar tuba wajen Allah, sanan ki cire wanan tunanin a ranki. Shiru nayi, zuciyata na ko™arin gano mun lokaci Waya da Ummanah ta taSa yin wani abu da yayi dai-dai da ra ayina, amma shaiWaniyar zuciyta ta kasa hango mun, bayan tulin abubuwan Alheri da mahaifiyata ta mun, da kuma wanda take shirin yi mun.  Ki tashi ki matsar da kayan naki, insha Allahu ba zaki ™ara sati biyu cikin gidannan ba, zaki tafi naki gidan.



 Lalai matar nan. na fada a rai na, ni ina mamakin yadda zasu ajiye ni gida Waya da Mus ab, kuma har washe gari su dawo sai su sameshi da rai, ko da cikkakiyar lafiya. Tashi tayi ta fice, tun da ta ga na shiga tunani, Allah yasa nayi tunanin abinda yake Alheri, buWe baki nayi da niyar cewa ta bani aron wayarta na kira Masrur, sai dai tuna wa da nayi da ™addarararen auren Mus ab a kaina ya sa nayi ™us. Magana kikayi Salma?. girgiza kai nayi alamun A h, ta sa kai ta fice.





Tana shiga Waki ta kira wayar Mus ab.  Kazo duk inda kake, ina son ganinka. ta faWa bayan ya Waga wayar.  Ina Wakina.



 To na ce dai kazo. Tashi yayi ya fito zuwa Wakin na ta, tana zaune kan kujera, shi kuma ya zauna ™asa.  Mama gani. Kallonshi tayi, kusan minti biyar sanan ta ce. Mus ab, ko kasan kai ne sanadiyar rashin fahimtar dake tsakanin Salma da iyayenta, musamman ma mahaifiyarta?. da sauri ya Wago kai, ya kalli Mama ta kuwa Waga masa kai alamar  Eyh sanan ta ce.  Ka san yadda mahaifiyar Salma ke son ka, ko ni irin son da zan maka kenan, kai ne ka cusa ™iyayyarka a zuciyar Salma, ka kuma raine ta, domin a farkon tashin Salma ta na son ka, amma bakin halin irin na ka ya ja ka haifar da tsana mai girma a zuciyarta, ka kawo rashin fahimta tsakaninta da iyayenta, Mus ab ha™™ine a kan ka, ka Winke Sarakar nan, ha™™ine a kan ka ka raini Salma, ka goge wanan tsanar, ka mayar da ita Soyayya, sanam ka kawo iyayenta ita a matsayin masoyiyarka,kuma wacce tayi biyayya ga iyayenta, shine kadai hanyar da zai sa su sakko daga wanan fushin da sukeyi a kan ta.





 Shikenam Mama, insha Allahu zanyi duk wanan abubuwan, zata tabbatar na kawo Salma a matsayin mai biyayya, zan yi ha™uri da duka halayenta, sanan zan goge duk wata ™iyayyata a zuciyarta, nayi miki wanan al™warin Mama.





 Allah yayi maka albarka, ya kuma da fa.



 Amin ya Allah. Ta shi ya yi zuwa Wakinsa, bayan ya kwanta ya yi shiru, ya na so ya amsarwa zuciyarsa sabon yanayin da yake ji. Tabbas bai san so ba, amma yana jin kamar zuciyarsa ta faWa soyayya da Salma. Amma ai ance soyayya ba ta shiga sai wani abu ya Wauki hankalinka, to ni mai ya Wauki hankali na a tare da Salma?. Ya yi wa kansa Kan sa wanan Tambayar, amma sanin babu mai ba shi amsa ya sa shiru, domin ya san haka zai dauwama cikin shirun, ji ya yi zuciyarshi na azal zalal sa lallai sai ya je yaga Salma, ko ta dai na kukan, ko ba ta dai na ba?. Ba yan da ya iya, dole ya ta shi ya fita, a bakin taga ya tsaya yana kallon Salma, wacce ta baje kayan ta a ™asa tana kallon su tsaf, tana faman tunani kala kala.



 Way anan su ne  yan kayan da aka kawo mun, sauran kayana masu kyau fa, nufin su idan naje gidan mijin kwalliya zanyi masa ko me?. na tambayi kai na, a lokacin da na ke kallon kayan, ji nayi kamar mutum a kai na, hakan ya sa na Waga kai na, sai dai babu kowa, na ci gaba da kallon kayana, idona na kai wajen window kawai na ga mutum yana kallo na ™ir.



Legends pen.



Page 17







MurguWa masa baki nayi, tare da galla masa uwar harara, har da jan tsaki, dan nasan a cikin gidansu dai bai isa ya taSa lafiyata ba, ga matu™ar mamakina sai na ga yayi murmushi. Wani ™ululun abu ya tsaya mun a ma™oshi, ji nayi kamar na ta shi na fara dukan sa, har sai ya dai na motsi, ko zan ji wani abu ya ragu a zuciyatah. Šauke kai nayi, na mai da shi kan kayana, a zuciyata ina faWin.  Wai wanan ne mijina ni Salma, gaskiyya nayi asarar Kyakyawan matashin saurayi, mai kyau da jini a jiki, wato Masrur, an haWani da wanan lange langen. domin ni tabbas zuciyata rayamun take idan na kama Mus ab da duka, tsaf zan iya Sallashi, ban san ba ko tsanar da nayi masa ce ta sa nake ganin shi kamar tsinken kwa-kwa.



Juyowa nayi na sake kallon tigar, yana tsaye kamar an dasa shi, sai dai wanan lokacin wayarsa yake kallo ba ni ba, hararsa nayi, tare da murguWa masa baki, na mai da hankalina kan kayana.  Na tashi na je na amso kayana wajen Ummanah, ko kuma na bar su kawai, tun da ba ta son gani na?.



 Allah ya isa Mus ab, ko a haka ka cuceni, ka sa mahaifiyata da mahaifina na fushi da ni, ka raba ni da iyayena, ka haramtamun shiga Sangarenmu. Wasu ™anan hawaye na ga suna zubowa ta idona, da sauri na juyar da kai na, ba na son ya ga hawaye a idona, dan nayi al™wari Mus ab bai isa ya ga gazawa ta ba, ya™in yanzu ya fara, mu zu ba mu gani, shege ka fasa tsakani na da shi.



Bai ga hawayen da ke idona ba, amma yasa wayarsa ne yana recording Win na video, mussamman lokacin da na sake juyowa, na murguWa masa bako, tare da harara. Ta cikin wayar yake kallona, tare da yin murmushi, ya yanke iya wajen da nayi harar da murguWa baki, ya yi saving. Kiran Abdul ne ya shigo wayarsa, Abdul shi ne babban abokin Mus ab a duniyar nan, tun su na  yan ™anana suke yin abota, mai cike da so da ™aunar juna, suna raba duk wani sirri tsakaninsu, su magance damuwarsu, su bawa junansu shawara. Ba wai ba su da wasu abokan ba ne, amma su biyu ta su tafi zuwa Waya, ganin abubuwa na ™o™arin cunkushewa Mus ab ya sa ya kira Abdul, a iya sanin Abdul ya san an Waura mai aure daren jiya, amma ya ce zai ma sa bayanin komai.



 Ango! Ango. Abdul ya faWa bayan Mus ab ya Wau wayar, haka kawai Mus ab ya tsinci kansa da yin murmushi jin an kira shi da Ango.  Man how far?. Mus ab ya faWa, har lokacin da murmushi a fuskarsa, amma ya matsa daga jikin window Win, ya nufi Wakinsa.  Normal ango, ya kwanan angon ci.



 Me yasa kake da matsala har haka ne. Dariya Abdul ya yi sanan ya ce.  Yanzu fa nake ™o™arin ™arasowa, motan da nake son fita da ita ne ba a wanke ba, sai da na jira.



 Kai kuma da ke an ce dole sai ita zaka hau?. Mus ab ya ba shi amsa.  No ba haka ba ne, na kwana biyu ban hauta ba, anyway gani na ™ara so.



 Okay, kar ka shigo, bari na fito ni.



 Okay. Abdul ya faWa tare da kashe wayar, shi har yanzu so yake ya gasgata cewar an Waurawa Mus ab aure, gaba Waya jiya ya dawo daga cafoniya, wayar da ya kira Mus ab ya faWa masa ya dawo, shine yake sanar mai wai an Waura mai aure.



Mus ab Win ne ya buWe motar ya shigo, kallonshi Abdul ya yi sanan ya ce.  Ya na ga karame, kai da kake ango, na mayi tunanin zaka ce gidanka na G.R.A zan zo?.



 You think am joking ko?, kayi tunanin wasa nake ko?.



 To Mus ab ba dole nayi tunanin wasa kake ba, dan ma ban ce ka hauka ce ba. Zama Mus ab ya gyara sanan ya ce.  Man, harkar asibitin nan ce ta tashi.



 Garin ya haka?.



 Ciwon ya tashi sosai, har na shiga critical condition, ban san inda ya ke ba, sanan asalin doctor Win shi ya duba ni, ya faWa musu komai da komai, sanan ciwon ya zama very worst, sabida daWewa da ya yi a jikina.



 Yaushe abun ya faru, kuma shi likitan ya ce ayi maka aure?. Abdul ya je fa mai tambayar.





 Yes, last week. Ciwon ya matu™ar tsorata Mama da Umma, Abba ne ya tambayi likitan maganin ciwon, sai ya ce best solution shine aure.



 Yanzu samiran ka aura?. Girgiza kai ya yi sanan ya ce. Iyayenta sun sami labarin wai inda cuta, sai su ka ce sun fasa ba ni.



 What!, how comes.



 Wallahi i don't know Abdul, kawai haka su ka ce. Kwantar da muryar Abdul ya sa ke yi, sanan ya ce. Mai yasa duk ba ka faWamun ba, yanzu kuma wa ka aura?.



 Abdul ka na calfoniya, sanan contract Win da kake aiki a kan sa babban contract ne, yanzu ba ga shi ina faWa maka ba.



 Yanzu wa ka aura?. Abdul ya sake dawo masa da tambayar. Wa aka auran dai, Salma ™anwata. wata irin juyowa Abdul ya yi, tabbas ya girgiza da jin sunan Salma a matsayin wacce Mus ab ke aure, domin ko ™udajen da ke yawo gidan Galadima zasu iya shaida tsantsanar tsanar dake tsakanin Mus ab Galadima da Salma Galadima.  Wa ka ce wai. Abdul ya sa ke tambayarsa.  Salma Galadima, ™anwata.



 When a kayi auren?.



 Daren jiya, an saka auren, in the next two weeks amma yarinyar ta fara ™o™arin barin gida, kasa Abbansu da zafin zuciya, ya sa aka Waura auren daren jiya. Shiru Abdul ya yi, ya san Mus ab bai ™aunar Salma, Salma ba ta ™aunar Mus ab, zallan ™iyayya ce mai zafi, sai dai kuma Wumin ™addara ya haWa su, ya haWa su waje guda bayan Sakata da su ka gar™amawa zuciyoyinsu.



Legends pen.



Page 18





 Kasan wani abu?. Mus ab ya tambayi Abdul.  Sai ka faWa. Abdul ya bashi amsa.  Ni kake tausayi ko Salma?. Kallon Mus ab Abdul ya yi sanan ya ce.  Dukkan ku, amma kai ne babban abun tausayi, domin kai babbane, kasan aure ka san ta zama matarka, dole zaka saurara a wani abun, amma ita fa, she will still behave as how she is before, babu wani abu da zata canja.



 Kasan wani abu?. Mus ab ya sa ke yin tambayar. Wane abu?.



 Ban san so ba, amma tabbas zuciyata ta kamu da son Salma, tun daren jiya.



 Mai ka ke ji game da ita.



 Komai nawa ita, tunani ita, bacci ita, zuciyata za tai ta azalzalta a kan na je na ganta, idan na ga tana hawaye har cikin zuciyata nake jin su, idan ta kalleni ta harareni, ta murguWamun baki daWi nake ji, nayi mata video a waya ta, a yanzu shi nake son sake gani ko zanci sau™i a raina, ji nake kamar nayi ni sa da ita, ina jin zan iya dauwama ina kallonta.



 Ka faWa soyayya, mai shiga lokaci Waya, mai kuma ™arfi abokina, sai dai ko a mafarki ban ta Sa tunanin ™iyayyarka ga Salma za ta zama ™auna haka.



 Nima hakan, har yanzu na kasa gasgata zuciyata, na kasa yarda da hakan.



 Tun da har ka fara son Salma, komai zai zo da sau™i, ita macece ™iyayyarta ™arama ce, daga lokacin da ka Wauke, ™auna da kulawa ko Wora ma ta, shikenan yau da gobe za ta gane, za ta so ka, fiye da yadda kake son ta. Shiru Mus ab ya yi, zuciyarshi ta shiga tuno masa lokacin da ya dake Salma, lokacin da yayi mata targaWe a hannu, lokacin da ya tsige mata kitson kanta guda Waya, kawai sabida ya ga tayi kuka, tabbas ya san Allah ya jarabce shi da son ganin Kukan Salma, yana mugun jindaWi idan ya ga tana kuka, sai dai a jiya da yau, kukan ya zama abu mafi azabtar da shi, abu mafi soya zuciyarsa, a hankali ya bude baki ya ce. Salma na da ri™o, ta ri™e ni a kan abubuwan da nayi ma ta, ka na ganin Salma za ta so ni?.



Shiru Abdul ya yi, tabbas Mus ab ya azabatar da Salma, ya ci zalin Salma, ya na tuna lokuta da dama, da yake hana shi hakan, amma Mus ab ya™e ™ashi ™asa ya ce sai ya yi, yanzu gashi Allah ya jarabce shi da son Salman.



 Allah ya gama ka da Masifar duniya. Sautin muryar Salma ya shiga kunnensa.



Shiru Abdul ya yi, tabbas Mus ab ya azabatar da Salma, ya ci zalin Salma, ya na tuna lokuta da dama, da yake hana shi hakan, amma Mus ab ya™e ™ashi ™asa ya ce sai ya yi, yanzu gashi Allah ya jarabce shi da son Salman.



 Allah ya gama ka da Masifar duniya. Sautin muryar Salma ya shiga kunnensa, kamar yanzu ta ke faWa, wanan addu ar ta ta  yar kullum gare sa lokacin da yake dukanta ko cin zalinta.



 Yanzu, a ce Salma ce masifar duniyar da take ro™on Allah ya gama ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login