Showing 51001 words to 54000 words out of 148964 words

Chapter 18 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

zai mata hukunci mai tsauri. Ta gama cin mutuncinsa na zarginsa da yarinya k'ank'anuwa sannan ta fice da y'arta ta bar masa nasa su kad'ai babu tunanin komai.
Ya hurar da hucin b'acin rai yana jin babu abin da yake susuta namiji irin rashin samun kwanciyar hankali a gidansa. Daga Bilkin har yaran cikin k'ank'anin lokaci sun firgita shi, wato mata babu mai iya musu sai Ubangijinsu.
A fili ya ce "Da suna da damar ja da hukuncin Ubangijin ma zasu ja bare kuma namiji da suka dauke shi abokin gaba kuma abokin adawa.
Daidai lokacin k'iran Faruku ya shigo wayarsa.
Ya dauka murya babu kuzari ya ce "Ranka ya dade masu k'asa".
Faruku ya yi murmushi ya ce "Kune da k'asa, kune ake yi muku jiniya"
Asad ya ce "Masu dala ai suen da k'asa ko na ce duniyar ma a hannunky take gabad'aya".
Faruku ya numfasa ya ce "Tun safe nake nemanka ban same ka ba".
Kaitsaye ya amsa da fad'in "Ayyuka suka sha kaina, ban jima da shigowa gida ba"
Faruku ya yi turus tare da tunanin har ya koma gida ashe ya ga Bilki bata nan amma bai neme shi ba?
Ya nisa ya ce "To bari na barka ka huta a gaida iyalin".
Kaitsaye Asad ya ce "Zasu ji tare da kashe wayarsa. Jikinsa na ba shi Farouku yasan bata gidan shiyasa ya k'ira shi a wannan lokacin. Shi kuma bikon ta ne ba zai je ba, tunda ta yi masa wannan wulakancin zai gwada masa kalar nasa.
Wayewar lahadi a gida ya yini bai fita ko ina ba, sannan ya ce da yaran su karya kada su jira shi. Ya dawo sallar la'asar yana ta tunanin ya kamata ya fara neman ta ko dan halin da take ciki, Allah bar shi idan ta dawo itama ya fara bata nata hukuncin don kuwa ba zai yarda ta dinga caba masa duk maganar da ta zo Mata ba da sunan kishi.
Daidai lokacin suna daki ita da Abida suna tattauna yadda bai biyo bayanta ba. Gabad'aya zullimi ya bayyana a jikin Abida ta ce "Bilki kada fa mutumin nan ya yi irin ta Yaya Sulaiman ni fa gabad'aya a tsorace nake, ban yi zaton zai iya kai wa wannan lokacin bai kawo kansa gidan nan, ko gidan Yaya Faruku a birkice ba".
Bilki da zuciyarta ta yi nauyi sosai a sanyaye ta ce "Ai zuciyarsa a bushe take sannan a kan ya'yansa ba ya ji, ba ya ga ni". Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:26]
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.

Abida ta ce "Bari na dauko jotter din da na rubuta wuridin da aka ba ni na kiranye mu fara doka masa kada bak'in cikin Baba ya zama biyu, kai maza na kan sharafinsu".
Duk da zuciyar Bilki a kuntace take matuƙa da gaske sai da kalaman Abida suka saka ta tuntsire da dariya don bilhakki Abida a firgice take da rashin zuwan Yaya Asad.
Ta gimtse dariyar ta ce "Dr Abida ba dai malamai kika fara bi ba?"
A sanyaye ta ce "A a sadakar kudi na bawa wani mutumi ya kawo mahaifiyarsa asibiti, k'arfinsa ya k'are sai na cika masa 1 million din da yake nema dan ayi mata aiki, shine ya ji dad'i yana ta mini addu'a. Ni kuma ganin Malamin addini ne da alamun tak'awa a tare da shi, shine na fad'a masa bala'in da nake ciki akan ya taya ni da addu'a, ya tausaya mini shine ya ba ni wuridin ya ce 'Ni da mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko y'aruwarsa shakikiya mu dinga yi babu kakkautawa, matuƙar yana da rai zai bayyana mana cikin gaggawa".
Da azama Bilki ta ce "To d'auko mu fara Abida idan mun ga fatahi akan wannan sai mu taru mu yi akan Yaya Sulaiman dan na lura mazan nan sai da addu'a mai zafi".

Abida ta ce "Sosai fa Allah dai ya sanya muna da zafin yawu Bilki".
Abida ta fice zuwa ɗakinta da hanzari yayin da Bilki ta sake tsorata idan har Abida yadda take cikakkiyar yar boko, mai kuma baudadden hali, sannan a bayyane yake Abida bata son maza, kusan ma feminist ce amma ta shiga tarkon namiji take karban kebra masu radadin gaske ai dole ita da take sonsu ta lallaba ta iya takunta tun kafin abin ya dawo kanta. Sai dai kuma tabbas ba zata bari ya dinga daukar hakkinta yana bawa yara ba, haka nan ba zata lamunci su dinga cin zarafinta yana kallo ba zai dauki matakin da ya dace ba.
Daidai lokacin Abida ta dawo d'auke da jotter da biro a hannunta. Ta zauna gefen gadon ta mikawa Bilki ta ce "duba ki ga ni."
Bilki ta karɓa tana karantawa. Ta kammala ta ce "Zamu iya yinsu ai babu wahalar yi. Kin ga kiranye yaya Asad ba zai yi wuya ba tunda kiran sunan nasa daga kansa ne zuwa kan kakanmu na biyu. Amma na Yaya Sulaiman fa zai bamu wahalar gaske ina muka san kakanmu na shida?"
Abida ta ce "Na rantse idan har na ga wannan ta ci zan gurfana gaban Baba ne ya fad'a mini sunan kakansa na biyar ".
Bilki ta gimtse dariyarta akan dole don idan ta tsananta yin dariya yanzun nan gayyar zata waste.
Sun yi alwallah zasu fara yin sallar daga nan su zarce da yin wuridin kafin junior ya tashi. Bilki ta ce "Idan na yi Ladifu d'ari ba d'aya cikon na d'arin ne zan ce "Asad ibn Musa ibn Garba ibn Bello ko?"
Cikin gasgatawa da yin imani Abida ta ce "Yauwa kin fahimta haka ma za ki yi idan kin yi iyaka na abudu 99 cikon na 100 din ki kamo sunansa har zuwa kan babansa na uku. Damu suke zancen".
Suka yi sallar la'asar suka dukufa wuridin Iyaka na abudu wa iyaka nasta'in da kuma ya Ladifu. Fiye da shud'ewar awa guda suna yi, tun Bilki na yi da cikin iyashege da dariya har ta gimtse take yi da gaske, tabbas tana son ya zo amma idan ya so din ba binsa zata yi ba, tare da an baje magana a faifai ba.
Suna daf da kammalawa wayar Bilki ta hau kuwwa alamun k'ira ne. Abida ta yi maza ta ce uhum uhum tare da girgiza kanta da k'arfi alamun kada ta katse wuridin.
Bilki ta fahimci manufarta dan haka bata katse ba ta bar wayar ta katse dan kanta. Sai dai k'iran cigaba ya yi da shigowa har sau uku sannan aka tsagaita.
Sai biyar da kwata suka kammala. Abida ta ce "Bari na dauko wayar mu ga ko shine aka fara tsikarin zuciyarsa, ai ba dan so nake ya ji jiki ba, da na tab'o shi na ji halin da yake ciki". Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:29]
Jikin Bilki ya yi sanyi da yadda ta ga Abida ta dage tana taya ta jin ciwon abin da ya yi mata duk kuwa da a bayyane yake Baba da Momi ne kawai suka sha gaban Yaya Asad a wajenta. Akwai kauna ta mussaman a tsakaninsu kamar dai ita da yaya Sulaiman. A zuciyarta take ayyana ko zata iya taya Abida dankwafe Yaya Sulaiman kamar yadda take yi mata akan Yaya Asad a yanzu?
Ta kasa bawa kanta amsa don ita kanta bata sani ba a yanzu sai zuwa gaba tukun.
Abida ta yi shewar murna tare da fad'in "Wallahi shine! Ta jijjiga kai cikin gamsuwa ta ce "Yanzu muka fara har sai ka kawo kanka gaban Baba."
Daidai lokacin k'iransa ya sake faɗowa wayar.
Abida ta dauka ta gaishe shi ta ce masa barci take yi.
Ya numfasa ya ce "Autar Momi wai mun bata ne?"
A sanyaye ta ce "Me ka ga ni Dady?"
Ya ce "Tun shekaranjiya yarinyar nan ta baro gida ban sa ni ba, amma ko ki k'ira ni Abida?"
Ta numfasa ta ce "Ai da yake ni mace ce, kasan duk haka muke bama son a taka mu".
Jikinsa ya yi sanyi don Abida bata fadan rashin gaskiya, duk anincin da kusancinta da mutum bata bin bayan k'arya. Hakan ya sanya suka yi ta samun sabani na gaske shi da Rukayya don zai iya ce wa duk rikicin da zasu da ita mai tsanani akan Abida ne. Bisa hujjar Rukayya na yana fifita Abida fiye da ita, sannan ba dama Abida ta ganta da zani ko gold sai ta ce tana so, shi kuma sai ya siya mata fiye ma da nata. Bayan haka ta ce Abidan ce take b'ata ta a wajen Momi, shiyasa Momi tafi son matar Faruku da ta Usman a kanta. Shi kuma ya gane Abidan gaskiya ta fita, itace take k'yashin hidimar da yake yiwa kanwarsa, ta kuma yi kuskuren da ta bari Abida ta gane tana kishi da ita shiyasa ita kuma take baje mata kalolin shegantaka kalakala tare da yin shagulatin bangaro da ita, tana kanbabama sauran surukan gidan fiye da ita. Jikinsa ya yi sanyi don ya lura itama fishi take taya Bilki.
Ya numfasa ya ce "Siyar mini jarida Abida! Me ta fad'a miki na yi mata da ya sanya ta yi mini yaji?"
Ta murmusa a dalilin ya ce ta siyar masa da jarida tabbacin tuna mata da k'uruciyarta ya yi.
Ta ce "Yara na zaginta har kuma da yar sakabu tsabar samun wuri, kai kuma ba zaka tsawatar ba, ba gara ta gusa ba".
Ya yi turus don kamar camfi Idan Abida bata baka support ba, baka yin tasiri.
A sanyaye ya ce "Yanzu tsakaninki da Allah ya kamata ta banbanta y'a'yana da nata?"
Kaitsaye ta ce Bai kamata ba".
Yauwa autar momi ita Maigado wata irice, kullum tana mak'ale da Farha Amal da Noor a ware da k'yar na banbare wariyar da take nunawa, yanzu da zata yi yaji sai ta dauke Farha ta watsar da sauran indai don Allah ne mai zai saka ta bar su tunda sun saba da ita sun Kuma Saba da Farha. Na fita Sai kawai na dawo na tarar Babu ita babu Alti da Farha, zan ji dad'i? "
Jikin Abida ya yi sanyi ta ce "Ta yi kuskure amma fa bai kai naka ba gaskiyar magana. Ko rashin zuwanka nasan daga Yaya Faruku da ya baka ita har baba sai sun diga maka ayar tambaya".
Ya nisa ya ce "Gobe zan zo in sha Allah bana jin dad'i ne yanzu. Bata wayar".
Nan da nan Abida ta ce "A a barci take yi, zuwa bayan magariba ka sake k'ira, sannan ta tashi."
"To"
Ya fad'a a sanyaye.
Yayin da Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk taurin kanka Sai mun lausasashi da wuridin nan ".
Ta kalli bilki6da take zaune ta ce "Maigado this very powerful du'a. Zamu fara yiwa yayanki".
Bilki ta murmusa ta ce "Bayan kin k'wace mini shi Abida!
Murmushi Kawai Abidan ta yi.

Washegari sassafe zai fita a motarsa ya d'auki Bilkisu da Laura, suka kai ta har makaranta shi da tawagarsa ya k'i daukan Hafcy ya ce direba ya kai ta wanda hakan ba k'aramin damuwa ya jefa ta ba, karon farko da ya fita a harkarta don kuwa kowa ga ni yake yafi sonta.
Har cikin gate din makarantar suka shiga da ita. Sosai Bilkisu ta ji dad'in wannan k'aramcin da Dady ya yi mata don ba zata iya tuna rabon da ya kawo su makaranta da kansa ba. Dan haka zata sake kamewa daga shiga rikicin da ba zai amfane ta da komai ba, tunda ta yi ba dawo da Momi zai yi duniya ba, ba kuma shine dalilin da zai saka ya auri anty Laura ba. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:32]
Kaitsaye Kaduna suka nufa suka kai Laura har gidan gaban Hajiya, kaitsaye ya mata bayanin rikici suke yi da matar gidan tunda itama yarinyace zaman nasu ba zai yiwu tare ba. Dan haka a yi hak'uri amma har gobe shi ne ubanta dan haka ba abin da ba zai yi mata na hidima ba, komai ya shafe ta yana kansa zai yi, kada kuma a ji nauyin fad'a masa dukkan al'amarinta. Sannan idan maneminta da gaske yake yi to ya turo a yi maganar aure.
Ya ajiye mata bandir din y'an dubu dubu sabbi k'al guda uku. Bayan kayan abinci da aka ta shigowa da su masu yawan gaske.
Ba kuzari Hajiyar ta yi masa godiya.
Ya yi sallama ya tafi. Hajiya ta ja dogon tsaki ta ce "Namijin hotiho sallamamme na namamajo ko yaushe Bilkin ta zama yarinya? Abu da tana da budurwar yarinya. Kawai ita ta saka ya koro ki tunda tana ganin da aure a tsakaninku, don babu yadda zata yi da su Aysha. Zaman lafiya kuwa babu shi a gidansa".

Laura cikin kuka ta ce "Wallahi Hajiya "A kanta ne, dama ta fad'a mini "Sai ta saka ya yi mini korar kare ga shi kuwa don da asubar yau din nan da ya dawo daga masallaci ya ce mini na shirya zai zo Kaduna ta'aziya zai sauke ni a gida, su Ayshan ma gabad'aya ya fita a harkarsu cikin kuka na barta ita da Hafcy. Bilkisu da su Amal kawai yake kulawa."
Hajiya ta sake jan dogon tsaki ta ce "Dama Bilkisu ba tamu ba ce tunda ya saka mata sunan shegiyar ai dole ta zama munafuka don kuwa suna na tasiri! Ta fad'a cikin k'unan rai.
Ta sake zabura ta ce "Irin kuttun da Rukayya ta sha akan yaran nan ba dama ta doke su ko ta hana su cin abin da suke so ita da ta haife su ma, amma wannan ja'irar harbta samu lasisin karya Hafcynsa amma ta kwashe kalau, sannan har tana da kuzarin hana a yi musu girkin da suke so Duk yana kallo? Tabbas ita ta biyo sawun uwarta na dibar albarka, ban da ta fita ta shiga ta ga gidan daula ta karkato da hankalinsa da na ubansa har ya kalle ta mabare aure ya gitta a tsakaninsu? Ai ko Alhaji Musa ba haka ta bar shi ba, tunda kotu suka maka shi Allah ne yasa bai kanannade ba saboda tsananin bak'incikinsu da na shedaniyar uwarsu, ta ta baza mugun iri."
Da kuka Laura ta ce "To Hajiya kawai ke ma ki shiga, ki fita ki wasko mini kansa dan Wallahi sonsa nake yi!
Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali.
Jikin uwar ya yi sanyi tub'us. A sanyaye ta ce "A a Laura ba ni da halin da zan yi shiga da fita irin nasu, kinsan an ce kudi ne da ita, sannan gadonsu da aka raba ai ba k'aramin kuɗade da kadara suka samu ba. Irin wnanan don su kashe milyoyin kudi akan buk'atarsu ba komai ba ne. Ki dai yi hak'uri tunda Har ya kawo ki gabana da kansa ai kinsan tafi k'arfinsa Idan ma kin shiga ke ce a ciki. Ni kuwa da ki yi zmaan boranci a gun miji gara ki hakura, ki auri Wanda kike so ba Wanda ke kike so ba. Mu duk zuri'armu Bama boranci ba kuwa zan yarda ke ki fara ba, shi din ma AI kwallon shege ne wacce wuyar ce Rukayya bata sha a hannunsa ba? Kawai idan mace tana auren mai wadata sai a yi ta mata kallon jin dad'i. Amma yadda ya fifita ahalinsa akanta da yadda yana ganin ibilishiyar Abida take mata isgili kala kala, take wareta tana son sauran matan y'anuwanta amma ita tana kallonta kamar kashi kinsan dama ya bayar a taka Rukayya ai. Tunda ya ce kallon diya yake yi miki, to ki yi hak'uri ki yi kwance kwance ki ta tatsar ja'iri.

Wurin azahar ya isa Abuja sai dai ba samu zarafin isa gida ba sai wajen azahar saboda a dalilin matsanancin goslow.
Kaitsaye gidansu ya zarce. Cikin sa'a ya tarar da baba da Faruku suna zaune a babban falon dawowarsu daga masallaci kenan, ruwa ya goce. Jira suke yi jiran ruwan ya dauke Faruku ya raga Baban tattakin da yake yi da yammaci don sosia tlyake jin dad'in jikinsa idan ya yi atisaye din.
A cikin motar ya bar yaransa a dalilin ruwa zai jikasu.
Kaitsaye ya shiga cikin falon ya yi sallama suka amsa masa babu wani walwala.
Jikinsa ya yi sanyi ya isa gaban Baba ya cire hularsa ya yi saluting d'insa sannan ya tsugunna yana gaishe shi. Baban ya amsa ciki ciki fuska a daure. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:35]
Faruku ya mik'a masa hannu ba wani karsashi.a
Nan da nan ya fahimci fishi suke yi da shi. Bai zauna ba yana durk'ushe Kan k'afafuwansa tamkar mai zaman tahiyya. Murya ba amo ya ce "Baba ya jiki dafatan baka cikin damuwa?"
Baba ya harzuk'a matuƙa da gaske.
"Cikin kunar rai ya ce "Kusunuwarka Asad!
Ba Asad din da aka zaga ba, hatta Farouku zabura ya yi don kuwa basu taɓa jin ya yi zagi irin haka ba, duk kuwa da yadda ransa zai baci dama Baba k'arami ne ainihin Bakatsine shine yake danna musu ashariya kala kala. Hankalin Asad ya yi mugun tashi wannee irin abu ya yi mai muni haka da ya saka mahaifinsu fusata ya yi masa zagin da bai taba yiwa wani sun ji ba.
A gigice ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, a gafarce ni!
Baba ya ce "Ni zaka yiwa wulakanci irin haka? Me kake da shi, waye kai?"
Murya na rawa ya ce "Dan Allah a yafe mini Wallahi ban san me na yi ba".
Ran Baba ya ce "Oh baka san me ka yi ba kake fad'a mini? Na d'auki yarinyar nan na baka bayan an sha dogon fama da ita kafin ta amince da kai shine da ka cimma manufarka sai ka mayar da ita banza da wofi a cikin gidan, ka k'ure hak'urinta ta taho wajena, shine ka yi zamanka idan na matsu zan neme ka da kaina saboda kana ganin kai wanine ko?"
Murya ba amo "Ya ce "Ko kad'an ba haka bane Baba, amma na gamsu na yi laifi a duba Allah a yi mini afuwa, fishinka irin haka a kaina guba ce dan Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login