Showing 93001 words to 96000 words out of 148964 words

Chapter 32 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

ya rantsuwa.sai ta k'ure.
Ya numfasa ya ce "To Baba ko direba ya kawo Maigadon kawai Su gaisa don yanzu fita da Zan yi".
Baba ya ce "Sulaiman zai zo gidanka ya gaishe ka daga nan ya ga tagwaye duk da bai sna wacece ta haifa maka su ba".
"Amma baba..
Baba ya yi maza ya katse shi da fad'in "Shi da yake na isa da shi, ina yi masa fadan bai gaishe ka ba, ya ba ni hak'uri, a take na zartar masa da hukuncin ya biyo ka har gida ya gaishe ka, to kawai ya ce mini saboda giyar kud'i da mulki basu fara bude masa idanuwansa ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:09]
Hankalin oga Asad ya tashi ainun ya shiga ba shi hak'uri tare da fad'in "Ka yi hak'uri Baba zan zauna na jira shi. Ina maraba da mijin Abida".
Nan da nan dad'i ya kama Baban ya yi murmushi da ya isa har kunnen Asad din.
Ya ce "Yauwa oga Asad Allah ya tsare ka da tsarewarsa."
"A sanyaye ya ce "Ameen Baba". Don tausayi ya ba shi na yadda ya shiga tsakaninsa da Sulaiman da son ya yi musu sulhu. A fili ya ce "Allah ka karbi kyakkwar niyyar Baba akan zumunci. Allah ka shirya tsakaninmu gabad'aya."
Baban ne ya katse wayarsa yana jin tunda ya danne Asad to ya samu sauk'in matsalar. Don ba k'aramin aikinsa ba ne idan Sulaiman ya je gidansa ya saka a hana shi shiga duk da Bilki na cikin gidan kuwa. Da kansa Baba mamaki yake yi yadda y'ay'ansa uku halayyar kaninsa suka kwashe tsaf ta kar ta san kar. Asad Usman da Abida wadannan ukun idan aka taɓa su basu da d'adi ko kad'an.
Yayin da Faruku, Salaha da Munira idan ta sune kiyama ba zata tsyaa ba.
Haka nan yana mamakin yadda Bilki ta kwashe kammaninsu da halayyarsa, haka Sulaiman shi dazu da ya rike shi yana dukansa sai ya ga ma duk yafi su Faruku kama da shi sak sai dai halayyarsu tazarace mai yawa don kuwa yana rukunin su Asad da suka samo halin Baba K'arami. Baba k'arami kuma ance halin mahaifinsu ya yi har kama, yayin da shi Baba Babba ya yi kamar gyatumarsu shiyasa ba wani kama suke yi da baba K'arami ba. Amma ya'yansu an garwaya musu saboda tsananin tasirin jini. Shi ya haifi masu kama da Kaninsa, haka shima baba Karami ya haifi masu kama da shi.
Tunda suka dawo daga sallar laasar ya ce wa "Sulaiman zai aike su tare da Abida ya shirya zo.
Ya ajiye wayar ba jimawa Sulaiman din ya shigo cikin tsadaddiyar Farar jallabiya. K'amshin ya cika falon. Sosai ya yi kyau ya Dora farar hula irin Dai yadda suka.ga Baba Babba Yana sanya Farin tufafi. Da walwala Baba ya ce "Sulaiman ka ga yadda ka juye ka koma tamkar sadda nake cikin shekarun k'arfi irin naka?"
Sulaiman ya durkusa akan kafet din ya ce "Ai tunda na yi sa'a na yi kama da kai komai koyi nake yi da kai Baba ".
Farincikin Baba ya dada fad'ada ya ce "Amma fa ni bana gaba, da kullaci sosia kuka nake son zumunta da dabbaka shi ".
Zuciyar Sulaiman d'aya ya ce "Baba kullum Ina addu'ar na Zama irin Hakan, ina ji a jikina Kuma addu'ar ta karɓu jira nake yi Kawai na ji na gama sauyawa gabad'aya.
Dariya Baba ya yi ya ce "To bari mu ga ko kai a karan kanka kana son ka canja din. So nake.ka me gidan yayanku ka gaishe shi sannan ka yi masa murnar haihuwar tagwaye da aka yi.a gidansa kuma karon farko da aka haifa masa yara maza."
Zuciya Sulaiman ta harba baki mai yanka wuya.
Zuwa gidan Yaya Asad ba k'aramin takura ba ne.
Ya yi shiru. Nan da nan Baba ya gane baya son zuwa.
Ya numfasa ya ce "Ka ga shi da yake na isa da shi, ina fad'a masa zaka je gidansa da murnarsa ya ce da fita zai yi amma ya fasa fitar zai zauna ya yi dakon ka".
Kan dole Sulaiman ya ce "Ni ma ka isa da ni mana Baba. Zan je din"
"To Allah ya yi maka albarka sai ku tafi tare da iyalinka ta raka ka."
A kan tilas ya ce "To"
Don kada Baba ya ji da ya'yan cikinsa kad'ai ya isa ba dan haka ba, ba abin da zai saka ya fita unguwa tare da Abida a yanzu.

Daidai lokacin Abida ta fito cikin kwalliya ta burgewa.
Ta tsugunna a kusa da Baba.
Ta tausasa harshe ta ce "Baba ba Zan Ga ji da fad'a maka na yi kuskuren kin ji Umarnin da ka ba ni a baya ba. Ka ce na Koma dakin mijina na bijire, Sai Dai bijire maka da na yi ka zuba mini ido ka mayar da ni y'ancin yin Duk da abin da na so daidai ko ba daidai ba na matuƙar saka Ni tashin hankali. Ka yi hak'uri Baba nima ka dinga bani Umarni kan Duk abin da ya dace Konda ba na so dan Allah Baba ".
Idonta ya ciko da hawaye.
Tausayinta ya kama baba, sannan yadda take wanke shina idon Sulaiman da iyakacin gaskiyarta ya sanya kin ya huce da ita.
Ya tausasa harshe ya ce "Zan fara yi miki hakan idan Allah ya sake ara mini na ga kin koma dakinki kin nutsu kina zaune lafiya da mijinki ". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:13]
Sulaiman ya ji wani iri Baba Sai tula masa k'asa take yi cikin hikima.
Yayin da salama ta shigi Abida don har cikin zuciyarta take jin matsananciuar damuwa idan ta ga Baba na yin iko da y'an gidansu kaf dinsu amma ban da ita. Tun sadda ya yiwa Bilki kacakaca ya ce ta koma gidan mijinta ta gano tana cikin had'arin rayuwa don kuwa duk abin da zata yi a rayuwarta ido da to ne tsakaninta da Baba da Momi. Babu Mai ce mata a a , ko meyasa konba yanzu ba. Ashe ka samu mai saka da mai habaka ma ba k'aramin rahma ba ne?
Sannan yadda suke nan nan da ya'yansu Yaya Faruku da na Yaya Asad basa yi da junior. Farha kad'ai suke nunawa soyayya mai yawa ita kuwa tasan don tana hannun Bilki ne. Junior kam saffa saffa. Idan bata nan suna kula mata da shi amma akan idonta kam basa wani jansa a jiki illah kyara akan yana da fitina tare da fad'a mata ta samgarta shi. Wanda hakan na cikin dalilan da ya sanya kullum sai ta yi kuka, sannan zaman gidan ya yi matuƙar gundurarta. Shiyasa Idan ta yi sadaka sai ta ce a yi mata addu'a Allah ya bayyana mijinta.
Baba ya ce "Ku je ki raka shi gidan yayanku."
Da azama ta ce "To Baba bari je yamma na yi."
Ta mike tana fad'in "sai mun dawo tunda sai da ta shiga ta yiwa Momi sallama kafin ta fito falon.
Haka Sulaiman din ya mik'e tare da fad'in "mun tafi".
"A dawo lafiya ka gaida mini takwarorinmu".
"To".
Sulaiman ya amsa a nutse. Daga haka ya fita don tuni Abida ta fice.
Abida ta kalle shi ta ce "Za ka jamu ne?"
"Ba walwala ya ce "Nasan gidan ne?".
Bata ce komai ba, ta bude mass gaban motar. Ya shiga babu musu a ransa ya dinga tuna da shi yake yi mata irin haka. Ya rufe, sannan ta zagaya ta shiga ta ja motar aka bude musu gate ya fice.
Suna tafe Sulaiman na kallon yadda Abuja ta sake cigaba.
Cikin wata irin murya ta ce "Yaya Sule wai baka kewata ne?"
Cikin gatse ya ce "Ina yi mana dumudumu".
Ta murmusa Yaya Sule gatse ko wasa?"
Ya yi mata shiru. Ta nisa ta ce "Ba Zan iya zuwa guest room na kwana maka ba alhalin momi.da baba na nan, yanzu ya za'a yii taimaki kanmu".
Ya yi shiru tare da mamakinta. Bata da kumbiya kumbiya ko kad'an.
"Still cikin gatse ya ce "Ki kawo mana solution ".
Kaitsaye ta ce "To idan mun dawo daga gidan Dady kawai.mu samu lodge."
Ya ce "Mu kwana kenan?"
Ta ce "a a, zuwa magharib idan muka gama da gidan Yaya Asad. Ko 10 muka koma gida ya yi ai".
Ya ce bai yi ba. Idan zamu kwana na yarda mu je ki mana lodge Haj Abida. Idan kuwa Yan awowine to a bari kawai".
"Ya Sule akwai batun da nake so mu tattauna tsakanina da Allah!
Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi don bata maganarsa zummar wake. Amma ya cije ya ce "Zamu tattauna ai gaggawr me kike yi?".
Nan da nan ta ce "To gaskiya Yaya Sule zaka biya ni kudin kunyatar da na yi. Ta ya ya zan cire kunya na yi inviting ɗinka amma ka yi rejecting. Don haka Wallahi sai ka biya diyya".
Da mamaki ya juya yana kallonta, gabad'aya ta yi kicinkicin da fuskarta.
Ya kaurara murya ya ce "You are trying me ko Abida?"
Ta tura baki ta ce "Gaskiya ne fa, don haka zan saka shi cikin lissafin basukan da nake bin ka".
Da mamaki ya ce "Ni kike bi basuka ba ma bashi ba?"
Kaitsaye ta ce "Kai kuwa".
Ya yi shiru yana ayyana wai yaushe zata daina son kud'i ne"
Kaf y'ay'an gidansu mata babu mai kudin Abida. Amma kudinta nata ne ita kad'ai. Bata yarda ko bashi ya had'asu, amma yanzu ta kaikaice tana fad'a masa basuka take binsa. A yadda kuma ya ga yanayinta da gaske take yi, kuma duk yadda yake jin zafinta idan har ya mayar da ita d'akinta sai ya biya basukan nan.
Ya rasa me zata yi da kudade haka. Kud'insa nasu ne tare amma nata kam nata ne ita kad'ai.
Basu sake magana ba har suka isa inda suka nufa.
Oga Asad da kansa ya tarbe su a katafaren falon da yake ganawa da manyan mutane.
Gabansa ya fadi da ya ga Sulaiman da shigar da ya yi. Take ya tuno Baba Babba a shekarun baya da ya ke kai su makaranta shi da Faruku mussaman sadda suke sakandire a Rumfa college Kano. Sak haka yake tamkar Sulaiman a yanzu. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:16]
Bai san sadda ya daidaita ya yi saluting din Sulaiman tamkar yana saluting ogansu na koli I.G.
Dad'i ya kashe Abida don a tsorace take tundaa ta gane Dady yana jin haushin Sulaiman na jingine musu ita da ya yi. Haka a dazu ta fahimci shima Sulaiman din haushinsa yake ji da gasken gaske. Don haka ta shiga rud'anin zuciya tamkar yadda baba ya shiga idan basu jitu ba, tana cikin tashin hankali don kuwa Baba da Momi ne kad'ai suka zartasu a zuciyarta.


*Sabon littafin marubuciya Binta Abbale na Shirin riskarku*.
*Littafin da ya samu nazari da azanci yayin rubuta shi*.

*Gudun Aure*

*Sunan labarin, dafatan za'a bibiye Shi da zarar ya Fara sauka*.

*Na gode*.
Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:40]
*Surayya Dee*
08032773332.
*Littafin kud'i akan manhajar telegram*.
*1k*
*Via*
2384876855
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*


*Contact Bojuwa herbs*
08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*

Sulaiman ganin irin gaisuwar da Yaya Asad ya yi masa ta k'arshen koli a gidan tsaro sai kawai ya tsugunna a gabansa dan shima ya gaishe shi da k'ololuwar girmamawa.
Hakan da ya yi ya burge Abida da take ta faman yi musu hotuna da vedios don tana ganin oga Asad ya k'ame ta fara yiwa Baba recording.
Asad ya dago shi ya rungume Shi. Daga haka suka zauna a kujera. Gabad'aya Sulaiman ya ji yayansu ya kashe shi da kunya don baisan sadda ya zube masa tamkar mai neman gafara ba.
Yayin da oga Asad kuma har cikin zuciyarsa ya ji tsanar Sulaiman da ta darsu a dazu ta gushe daga zuciyarsa.
Cikin mintina k'alilan angela ta kewaye gabansu da cima kala kala.

110
Oga Asad ya ce "Je ki karɓa masa y'ay'ansa ya gansu".
Da hanzari Abida ta mik'e har tana tuntube da jakarta da ta ajiye a gefe. Ta hau saman farko.
Ta wuce zuwa saman yara sannan ta isa zuwa saman Bilki.
Ta tarar da ita a kwance lamo ga Alti na yiwa yara wanka.
Da murna Abida ta ce "To ki taso ga shi ya zo".
Bilki ta yunk'ura duk fuska ta yi ja.
Jikin Abida ya mutu ba zata so Sulaiman ya ganta a haka ba.
Ta ce "Akan ya hana ki zuwan ne kika zama haka ko dai wata matsalar ce?"
Kuka na sosai ya k'wacewa Bilki.
Ta dinga shesshekar ajiyar zuciya. Ta laluba ba hanata zuwa ganin Sulaiman ba ne matsalar kawai. Fishin da ya dauka da ita, ya shigo d'akinta ya duba y'ay'ansa ya fice na tare da ya ce mata uffan ba ne yake nik'arta. Sannan idan ya dawo da daddare ya k'ira Angela ta ba shi abinci na matuƙar nukurkusarta. Ga Alti ta tisa ta a gaba. Gabad'aya gidan ya yi mata tsauri komai zafinsa take ji. Magana sai ta k'ure da ya yi mata komai da y'ay'ansa yake yi ko da ma'aikatan gidan.
To ita a me take kenan?
Abida ta yi shiru ta ce "Hmm ke kuttunki yawa ne da shi Bilki. Saboda Allah menene matsalarki? Ki bude baki ki yi jawabi
Da kuka ta ce "Gaba fa yake yi da ni Abida kuma shi yake cin zalina".
Takaici ya mak'ure Abida ta ce "Kidahuma kawai har ki bari tasirin fishin miji ya bayyana miki haka baro baro?
Kin ga yadda kika zama tamkar mai fama da ciwon tsi da ha?"
Bilki ta kasa magana illah kuka marar sauti.
Abida ta numfasa ta ce "To idan ba ki d'auki matakin gyara ba ina miki rantsuwa da Allah kafin nan kafin wata shekarar sai Dady ya nukurkusa ki da bak'inciki kala kala. Ki yarda ko kada ki yarda shi din miji ne mai tsada. Kuma a halittarsa bai son gardama da musu. Na ga alama ke kuma su kike gwada masa su. Haka siddan Dady ba zai hanaki zuwa wajen Yaya Sulaiman ba ko da kuwa baya magana da shi. Baya yiwa wani hukunci da laifin waninsa. Hanaki zuwa da ya yi na gane raini kike yi masa shiyasa ya fara bude miki k'wanjinsa.!
Ta nisa ta zarce da fad'in "Anty Rukayya ma bata sha hannunsa ba bare ke."
Bilki ta rushe da kuka wiwi. Da kuka ta ce "Saboda ta fini a gunsa kenan ko kuwa me kike mufi?"
Bak'inciki ya sanya Abida fad'in "Na rantse da ace nice na baki watannin da kika bani sai na nada miki duka a d'akin nan idan ya so ki yi kukan jini."
Alti ta ce "Na gode miki Abidan Baba".
Bilki kuwa kuka take yi bilhakki don ita ji take yi tamkar an yi mata daurin huhum goro. Ga dai Sulaiman a cikin gidanta amma ta rasa sukunin zuciyar da zata marabce shi.
Yayin da Abida ta had'iye kuttun da Bilki take cusa mata tunda ta shigo d'akin.
Ta sanyaya murya ta ce "Ta shi ki shirya ba dadewa zamu yi ba. Yi hak'uri zan dawo mu tattauna kin ji Bilkisu yayar Abida".
Bilki aka saki ajiyar zuciya tabbacin ta ji dad'in tausasa harshen Abida. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:45]
Ta mike ta d'auki mayafinta.
Abida ta yi maza ta karbe ta ce "Dan Allah wanko fuskarki na gyara miki ita. A hakan kike so ya ganki?"
Ba musu ta yi bayi ta wanko fuskarta. Abida ta bata mai ta shafa. Ita kuma ta ɗauko powder ta shiga gyara mata fuskarta.
Ta goga mata wet lips sannan ta bude wadrof ta ciro mata dankareren leshin da ya cinye makudan kudi.
Ta ce "Saka wannan mana Bilki. Bai san fa ke ce matar Dady ba. Gara ai ya ganki a babbar mace cikin walwala da wadata sai ya tafi da farincikin ganinki a kyakkwan yanayi".
Ba musu ta karɓa ta saka. Abida ta daura mata dankali ta fito ta yi fes da ita.
Cikin shakiyanci Abida ta ce "Kin yi kyau Maigado. Kada fa Dady ya kasa mallakar kansa a gaban k'annensa."
Bilki aka cuna baki aka ce "Da dai yana ta tawa ne".
Abida ta ce "Iyawa ne baki yi ba Maigado. Ke gabad'aya kin fi nuna jarumta a inda kike so ba inda ake sonki ba".
Ta ji zuciyarta harba don kuwa ta san Abida shagube ta yi mata.
Ta kasa cewa komai.
Abida ta k'i barin batun ta ce "Tun a Saudi wanccan bawan Allah yake shagulatin bangaro da ni. Amma na cije nake ta bibiyarsa tunda nasan na yi masa ba daidai ba. Ke kanki idan aka ce zan yi wuridin kiranye akan rijalu za ki ce ba dai Abida k'anwar Bilkisu ba. Amma a yanzu da ruwa ya daki babban zakara na gamsu duk gatan mace dakin mijinta shine suturarta. Ni kad'ai nasan kuttun da nake shaka a zaman gidan nan da nake yi."
Idanuwanta ya cika da k'walla.
Jikin Bilki ya yi sanyi idan Abida da uwa da ubanta basa iya boye soyayyar da suke yi mata take fad'in zaman gida babu dad'i to wacece zata k'i zaman aure babu hujjar ana cutar da ita ta ji dad'in zaman gida? Kai ko tana da hujjar fa yadda take ganin hak'uri take yi a gidan mijinta to ko gidansu ma ta koma hak'urin za ta yi. Don haka idan ba tura ce ta kai bango ba, akwia yiyuwar zaman zai yiwu, to a yi hak'uri kada a fito, sai idan cin mutuncin namiji da keta haddinsa ne ya yi yawa.
Bilki ta nisa ta ce "Abida to ya zan yi masa ne?
Gaba fa yake yi sosai ya'yansa kawai yake dubawa. Idan zai tambayi lafiyarsu fa ga ni yana kallona sai ya tambayi Alti, haka siddan ya gindaya gaba mai tsananin gaske a tsakaninmu!
Abida ta ce "Tunda kika haihu ba ki koma masa ba period".
Alti ta ce kanki na ja Abidan Baba".
Abida ta ce "Na yi zaman gidansa fa. Bayan haihuwar junior na kusan shekara tare da su a port. Sai da na samu aiki anan na dawo. Yanzu dai zo mu je zan dawo mu tattauna sosai.".
Alti da ta kammala shirya yaran ta ce "Bari ki ji babbar matsalarta kishin kushewa ta ɗorawa kanta. Wai ba zata je d'akinsa ba tunda da hotunan marigayiyar matarsa."
Abida ta ce "Eh cin fuskarsu ya yi ai gabad'aya. Anti Rukayyan ma ai ba'a yi mata adalci ba. Balle kuma sarauniyar shaiba yayar Abida ".
Idon Bilki ya sake cikowa da k'walla.
Abida ta ce "Allah ne ya yi mini sakayya. Ban da ba'a son a fad'i aibun matacce da na ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login