Showing 105001 words to 108000 words out of 148964 words
Chapter 36 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt
zan kasa samun alfarma a wajenki ba. Ina son yara. Ina son ya'ya da yawa. Ubangiji ya wadata ni da lafiya, ya yi mini arzikin da ban san adadinsa ba. Dan haka ba zan yarda a tare mini haihuwa babu dalili gamshasshe ba. Don Allah Maigado ki fahimce ni ".
Kanta na kasa ta ce "To ai ni Baban Bilkisu idan ina goyo ina yin period ka ga kenan zan iya samun ciki da wuri. Saboda Allah yanzu idan na samu ciki na yi ya ya da waɗannan jariran?"
Ya sake rik'eta ya ce "Zan kula da su da k'arfina, lokacina da kuma aljihuna. Zan sake dibar miki masu rainosu. Ga Alti kuma, ke fa nono kawai za ki dinga basu. Dan Allah Maigado ban son planning idan Allah ne bai kawo ba shikenan. Amma ban son a tare mini haihuwa tsakanina da Allah ". ,,
To Baban Bilkisu zuwa yaushe zan gama kenan?"
Ya yi shiru ya ce "yanzu 32 ku ke ko?"
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.
Ta zuba masa ido tana ganin da iyakacin gaskiyarsa yake tambayarta.
Ta ce "Lallai ma Baban Bilkisu wato dai kallo yarinya ainun kake yi mini. To 38 zan n cike next month."
Ya zare ido kai Maigado duka duka yaushe aka haife kune ke da Abida? Muna fa Rumfa college ne."
Cikin son ya gane ta girma ta ce "Wallahi 38 zan yi , ko Ansari ma ai 36 yake bare mu".
Ya jijjiga kai ya ce "Gaskiya shekaru na gudu."
"To Idan ba ki tare ta ba. Na miki alak'awarin idan kika yi 43 kin gama haihuwa sai kawai mu ta cin duniyarmu da tsinke".
Ta yi dariya. Ta ce Baban Bilkisu cin duniya fa da tsinke?"
"To tunda na auri yarinya ai reviving ɗina zata dinga yi".
Wani dad'i ya dinga ratsata ashe mijinka ya dinga maka kallon yarinta ba k'aramin alfarma ba ce. K'uruciya dad'i ne a gun miji da ya kere maka shekaru.🥰🥰
Allah ya k'arawa irin wadannan mazan lafiya a cigaba da lallaba mu.
Muna godiya da niimar Ubangiji. 😄😄😄
Ya rungume ta ya ce "To me kika ce?"
"A hankali ta ce "Allah ya bamu masu albarka ".
Dad'i ya kama shi. Ya rungume ta sosai yana bata kisses ta ko ina.
Cikin k'ank'anin lokaci suka yamutsa junansu. Daga nan aka shiga cin uwar sabada.
Basu rabu ba sai azahar sannan suka yi wanka ya tafi masallaci, ya barta tana busar da gashinta.
Haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Alti.
Amma ba zuciyarta Kawai ba gangar jikinta ma na cikin farinciki da annushuwa. Mararta kuma ta yi mata sakau don a an zubar da ruwa iya ruwa.
Da wani irin murmushi ta ce "Oh oh Baban Bilkisu duniya ne".
Da kanta ta sanya hannuwanta ta rufe fuskarta don ita kad'ai ma kunya ce ta mamayeta da ta abubuwan da suka wakana a d'azu. Shi da kansa ya gane itama kuntatawa kanta ta yi da ta kaurace masa.
A d'akin ya dawo ya sameta.
Ya zauna bakin gado.
Ya kalleta ta mayar da lingerie din.
Ya murmusa ya ce "Maigado danja. Ashe sosai kika yi kewata?"
Ta yi k'asa da kanta, tana murmushin kunya.
Ya numfasa ya ce "Yunwa fa nake ji me zan ci ne?"
Ta d'ago da fuskarta ta harari gefe daya tare da fad'in "Angela d'in bata nan ne?"
Murya a tausashe ya ce "Ai mun shirya nasan za ki ba ni abin da zanci".
Ta tura baki ta ce "Baban Bilkisu dama bana hanaka kawai don kana son musguna mini ne ya sanya kake bata order ta yi maka abin da zaka ci. Kuma Wallahi bana so". Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:37]
Da azama ya ce"Ai kinsan a kwanakin nan ne kawai na yi hakan amma daga yanzu ba zan sake ba. Yanzu samo mini d'an wani abu na ci, kafin ki kammala mini abin da zanci. Amma ki fara zuwa ki shayar da yaran nan, na ji sun farka Alti na fama da su. Bansan me ya hana ni shiga na karbo su ba".
Ta yi dariya ta ce "Kunya ce ai tasan abin da kake yi da ni tsawon lokacin nan da nake d'akinka.
Ya yi murmushi tare da fad'in "Ina jin haka ne. Yi maza ki je ban son su rikice".
Ta dora abayar ta fice ya bita da ido yana jin duk wani zullimi.da takurar da yake ciki sun warware masa. Yarinya k'ank'anuwa ta saka shi tashin hankali. Mata da tsiya suke Ga su da wuyar sha'ani, idan basu so na kai da gidanka na zaka samu nutsuwar zuciya a cikinsa ba. Ban da wuyar Zama ta ya ya abinci ma sai ana controlling d'insa. Abin da take son ya ci, Shi zata yi masa kuma dole su ci tare if not ya yi laifi. Ya numfasa yana tunanin lokacin Rukayya dai ya dawo yake bada order din abin da zai ci charity ta girko ta kawo masa. Tunda ta gane haka yake so bata sake tayar da hankalinta ba. Amma y'ar yarinyar nan ta ce ba haka za'a yi ba, kuma dolensa ya hak'ura yadda take so din yake yi. A fili ya ce "ikon Allah oga Asad a hannun Maigado".
D'akin da ta cire rigarta nan ta sake shiga. Ta cire na jikinta ta mayar da na farkon.
Sannan ta fito ta shiga dakinta.
Ta tarar Alti na fama dasu. Ta goya baba K'arami tana rike da Baba Babba a hannunta.
Da sauri Bilki ta karbi na hannunta tana fad'in "Sannu Alti. "
Sai da ta gama basu.
Ta kalli Alti ta ce "Bari na kaisu wajensa. Ki yi sallah sai na zo mu d'ora abinci".
Alti ta ce "To".
Ta fita zuwa d'akinta da kuzari don tunda ta ga Bilki na b'are b'are tasan an shirya sannan walwalarta ta dawo babu k'unci da share k'walla akai akai.
Ja'ira itama ta ji jiki".
Alti ta fad'a a ranta.
Ta hadesu a babban shawul ta ciccibesu ta yi samansa.
Yana ganinta ya zabura ya mike daga kwanciyar da ya yi. Ya tare ta jikinsa har rawa take yi.
Ya ce "A a wannan ganganci ne Maigado. One by one za'a dinga kawo su, ko ki dinga cewa na zo na d'auke su da kaina. Yayarsu bata nan ne da ba ki ce ta ɗauko daya ba?'
Baban Bilki tunda ta fara service fa sai yamma take gida ai".
Kuma su Hafcy kowa na makaranta."
Ya kwantar da su yana duba jikinsu ko an matse su.
Har ta juya ya ce "Wai me zan ci ne Maigado?"
Ta dawo ta bude k'aramin firij din da yake cikin dakin.
Ta d'auko fresh milk ta bude ta dauko tumbler ta cika masa ya karɓa ya kwankwade.
Ta rufe ta mayar.
Ta d'auko inibi ta fita zuwa k'aramin kicin d'insa ta wanke ta zubo a bowl ta kawo masa gabansa.
"Na gode sarauniyar shaiba".
Ya fad'a yana kallonta.
Ta ce "Zan je na yi girki".
"To a yi lafiya a gama lafiya".
Ta duka ya sumbace shi kad'an.
Ta juya ta tafi ba tare da kalle shi ba.
Ya sake binta da ido. Shi kam ana masa k'arfin hali. Angela ba zata yi girki ba indai zai dawo gida ya yi lunch. Breakfast din yara da wanda suke tafiya da shi school kawai ne aikin angela na dole. Idan ba haka ba, sai ta ga dama take yarda ta yi girki a gidan. Sai idan za'a yi bak'i da yawa ko idan za'a kai masa office da yawa. Shine zata yarda ta yi wasu daga cikin abincin da za'a kai tunda kala kaala ake yi musu.
A fili ya ce "Ban da dai na yi laushi ya za'a dinga mulkata irin haka? Kuma an hutar da ke amma don fitina ba zaki huta ba? Allah sarki Rukayya, Allah ya yi miki rahama ".
Ya fad'a a sanyaye don ita a haka ta rayu. Komai yake so bata da y'ancin yi masa musu matuƙar abin kaitsaye shi ya shafa. Ya sa ni a bayan idonsa tana yin abubuwan da ta ga dama.
Amma ko kad'an bata samu damar da Bilki ta samu a wajensa ba. Faricincikinsa d'aya ma yadda bai yi mata iyaka da kuɗinsa ba. Ta yi facaka da kud'i son ranta.
Ya dawo sallar la'asar sannan ta gabatar masa da abinci.
Ya sauko tare da ita suke ci.
Yana ci yana yaba dad'in abincin. Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:39]
Tabbas ya gamsu ta iya sarrafa girki daga ita har altin tata.
Ranar haka bai fita ba. A gida Aysha ta dawo ta same shi.
Haka ma sauran yaran. Ya zauna cikinsu suka dinga hira kowacce na fad'a masa abin da take so ya siya mata. Shi kuma ya amince zai siyawa kowa abin take so.
Gida ya kacame da murna tunda cewa ya yi ma su shirya after Isha za'a fita shopping da kansa kuma zai tukasu.
Idan ya fita da su da kansa suna jin dad'i don komai suka dauka baya iya hanasu sabanin idan su kad'ai ne account mai takaitaccen kudi yake basu damar tabawa.
Ya kalli Bilki da ta bishi sama ya ce "Da ke zamu je ne ko sai daga baya zan kai ki?"
Dan ya ji dad'i sai ta ce "A a zan biku na tayasu zabe kada yaran su debo abubuwan da ba wani amfanarsu zasu yi ba".
Dad'i ya kama shi ya ce "yauwa Sarauniyar sheba dama nafi son na tafi da iyalina gabad'aya".
Aysha da Hafcy suka hawo saman Bilki suka d'auki jariran suka fara ficewa.
Farha ta kalli Alti ta ce "To me kike so na siyo miki?"
Dad'i ya kama Alti don Farha na nunawa irin ita ce tata tunda tare suka zo gidan.
Ta ce "Ki siyo mini Rufaida da kulikulin Ummiel ".
Farha ta ce"To nasan Dady ma zai siyowa su Momi da Baba".
Bilki na d'akin oga tana tsaye ya gama shiryawa.
Tuni ta shirya cikin tsadaddiyar Yasmin abaya.
Ya kalle ta ya ce "Dr Sulaiman fa ya ce ya kamata ki ga likita".
Ta ce "Baban Bilkisu k'alauna fa Wallahi. Tsabagen kuttun da kake nausa mini ne ya nemi zautar da ni. Yau kad'ai duk wanda ya ganni ya ga real Bilki ba wacce aka share ake kuma nuna mata wata mace ta fita ba!
Mamaki ya kama shi.
Ya yi maza ya isa kusa da ita ya ce "Ba a fiki ba, ba kuma za'a fiki ba sarauniyar sheba. "
Surayya Dee
08032773332.
Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 10:59]
*Surayya Dee*
*08032773332*
A yammacin wannan ranar
Abida a falon baba na ciki. Kusa da Baban tske zaune tana nuna masa videon yadda ya wakana tsakanin.oga Asad da Dr Sulaiman.
Dad'i ya kama shi k'warai da gaske.
Da kuzari ya ce "Amma shine ba ki nuna mini wannan abin farincikin ba sai yanzu?"
"Baba da muka dawo ka shiga ciki.
Yau kuma sassafe na fita zuwa asibiti.
D'azun nan na shigo ".
Murna kan murna yake yi tamkar an zauna an yi sulhu komai ya wuce a tsakaninsu.
Addu'ar fatan alheri ga oga Asad da Dr Sulaiman ya yi musu ba adadi.
Motsi kad'an zai ce "Sake kunna mini na ga gaisuwar mai d'amara da civilian ".
Abida aka dinga kunna amsa ba gajiya.
Suna cikin haka ta ce "Baba dai har yanzu baka huce da ni ba. Kana ta yiwa Dady da Yaya Sule addu'ar tsari daga abin k'i da kuma albarkar rayuwa amma ni da na yi maka wannan vedion da ya sanyaka farincikin da kake ciki baka yi mini addu'ar ba."
Ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki albarka Abidan Baba, Allah ya shirya miki zuri'a."
Dad'i ya kamata don rabon da ya ce Abidansa ta mance.
A sanyaye ta ce "Ameen Baba.
Ya nisa ya ce "Dazu Sulaiman ya ce mini jibi ko gata zai tafi Kano. Zai yi aikin ido a asibitin Makka na cikin Kano . Wanda wata gidauniyar tallafawa k'asashe masu tasowa ta Saudiiya take d'aukar nauyi.
Ya ce sati biyu zai yi ya dawo."
Jikin Abida ya yi sanyi.
Ta fara kukan da ya tayar da hankalin tsohonta.
A sanyaye ya ce " menene na kukan kuma?"
Tsawon lokaci ta kasa magana.
Sai kuka take yi k'asa k'asa amma mai nauyi ainun.
Jikin Baba ya yi sanyi. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri Abida. Ki yi addu'a komai zai wuce tamkar ba'a yi ba".
Da kuka sosai ta ce "Baba na yi hak'uri, na yi addu'a. Da kanka ka fad'a mini Yaya Sule yafi k'arfina. Yanzu da ya dawo ai sai ka taya ni. Nauyinka zai saka ya hak'ura. Kuma Wallahi Baba da ace Bilki ce a gida, Dady ya ce zai yi tafiya cewa zaka yi ya tafi da matarsa, ni nasan hakan zaka yi masa ko ba ya so, sai ya tafi da ita duk laifinta zai zama ka roka mata afuwa.
Amma ni dukkanku ana kallo zai tafi ya bar ni, ana kallon bai yi wani motsin sama mini inda zan zauna ba. Duk tsawon lokacin da ya rataye ni amma ya dawo da niyyar cigaba da rataye ni. Kuma ba wanda ya yi ko da tari ne a cikinku"
Ta rushe da kuka wiwi har Momi da take kicin ta fito a sukwane.
Cikin kuka sosai Abida take fad'in "Baba ka shiga tsakanina da shi. Ka ba shi umarnin ya dauki iyalinsa ka gaji da rik'e masa. Ka yiwa Allah ka tursasa shi yadda ka ke tirsasa Dady da Yaya Usman.
Wallahi na gaji. Ba wani aikin ido da zai je yi. Gidan iyayen yarinyar da yake nema zai je. Daliba ce a Saudiyya suka hadu. Yanzu da na dawo, wajensa na fara shiga, na tarar yana band'aki. Na ga wayarsa na dauka akan na k'ira lambata don na samu layinsa sai kawai na ga hirarsu. Wallahi Baba ce wa ta yi ya je ya gaida iyayenta daga nan sai ya tura manyansa".
Murya a dakushe Baba ya ce "Nutsu ki saurare ni."
Tsawon mintina biyu yana kallonta tana kuka mai dauke da nauyayyen gunji.
Tausayinta ya daskarar da su hatta Momi idanuwanta sun cika da k'walla.
Yadda ba ya nan nan da junior kad'ai ya sanya sun gane Sulaiman ya yi nisa bai zo da niyyar sulhu tsakaninsa da ita ba.
Yaron kansa jikinsa ya yi sanyi baya wani d'okin ya je wajensa.
Baba ya numfasa ya ce "Ki kwantar da hankalinki Abida. Kada ki mayar da duba wayar namiji dabi'arki. Yanzu ga shi kin ganowa kanki abin da zai hanaki sukuni. Abu d'aya ne ya sanya na Zan iya tursasa Sulaiman akan Ki ba saboda Ni na haife ki. Anan falon a inda kike Bilki ta fad'a mini na zuba miki ido ban mayar da ke d'akinki ba saboda Sulaiman ba Shi da wata alfarma. Kuma Wallahi a bakinsa ta ji wannan kalaman.
Yanzu ta ina zan fara cewa ya d'auke Ki, alhalin a lokacin da ya kamata na ce ki kma din ban yi iko da ke kin yarda ba.
Duk yadda zan mayar da Sulaiman ya zama dana ai Dai ke ce na haifa. Da ace ba ni na haife ki ba to da na gwada masa kwamjina amma a yanzu da ya tafi a fahimtar mun zuba miki ido kin bijirewa zama da shi alhalin bai yi miki komai ba, bai kuma sake ki ba , kin ga ai ni ba ni da bakin magana. Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:02]
Kuma ma menene abin damuwa dan zai k'ara aure? Ina ce ko zaune kuke k'alau zai iya k'ara aure tunda an halasta masa.
Kanta na kasa hawaye na tsere bi da bi.
Wani irin cunkushewa mak'oshinta ya yi. Ga k'irjinta ya yi nauyi tamkar an d'ora gingimemen dutse.
Wato dai da gaske Sulaiman sai ya nukurkusa da bak'in cikinsa.
Ta dinga jin ya kamata ta tsayawa kanta. Ta yi laifi, ta karbi laifin, ta bada hak'uri, ta janye amma duk bai kalli nadamarta da bibikonsa da take yi ba.
Tunda aure yake nema zata hak'ura don kuwa ko shine dagi wajen fad'a ba zai yi aure ita tana zaune a gidan ubanta bata san matsayinta ba.
Tunda bai ga nadamarta ba bari Kawai ta ɗauko rigarta ta mayar. Zata koma Abidan Baba ta da, ba Abidan yanzu da ruwa ya daki babban zakara ba.
Daidai lokacin suka jiyo shi a falon farko yana kwada sallama a sukwane.
Momi ta mike tana fad'in "Sulaiman ga mu a nan".
Da hanzari ya shigo yana fad'in "Ina Baba?"
Ganin Baba ga Abida durk'ushe kanta na k'asa ya sanya tsugunnawa.
A diririce ya ce "Baba ka ce mata ta bani kayayyakina da ta kwashe mini. Tun ranar muka dawo ban ga passport dina ba.
Dazu da safe ta shiga ina barci ta kwashe mini duka ATM dina.
Yanzu kuma ta dauke mini wayata guda daya da ledar takalmana."
Baba ya yi shiru k'walla na cika masa ido don kuwa Baba k'arami ne yake masa yawo a zuciyarsa. Shine yake yi musu Sharia tun suna yara. Sai idan Sulaiman bai gamsu da hukuncin Baba k'arami ba sai ya zarto ya kawo masa kara tare da gabatar da hujjar Abida na kwashe masa kayayyakinsa tana boyewa saboda Baba k'arami yana bata kariyar tunda bai ga lokacin da ta dauka ba to kuwa ba ita ba ce, alhalin ita ce ba kowa ba.
Shi kuma Baba Babba idan ya lallabata tare da yi mata kyautar talotalo ko dawisu ko tattabara sai ta je ta fito masa da abin da ta boye. Mussaman takalmi haka siddan idan ta ga takalminsa a bakin k'ofa sai ta kwashe ko ta d'auke kafa daya ta bar masa d'aya. Bisa hujjar yana ce mata bak'a mummuna, ko Abida kwaila mai gwalli.
Baba ya numfasa tsawon lokaci ya kass magana.
A dabarance ya goge k'wallar idonsa wanda Sulaiman ya ga ni.
Jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa ta karye da tausayin Baban nasu.
Ya kalli Abida ya tabbatar kuka take yi. A ransa tamkar ya rufe ta da dukan da zata yi kukan gaskiya. Har yanzu ba zata bar Baba ya huta ba. Ta zo ta tisa shi a gaba tana kukan munafurci ga shi shima har ya fara.
Ya kuma san bincike ta yi masa a wayarsa shine ta ga abin da ya dameta. A ransa ya ce "Ki adana kukanki zuwa gaba yarinya.
Baba ya yi k'arfin halin cewa "Je