Showing 102001 words to 105000 words out of 148964 words
Chapter 35 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt
ba kya zuwa samansa?"
Ta d'ago ta ce "Yaya Faruku kada ka shiga wannan batun don gaskiya ina jin nauyinka. Kuma Wallahi ina kan batuna matuƙar ba zai kwashe ba, ba zan je ba, kar ma ka ce zaka tursasa ni don kuwa wannan karon lallai ba zan yarda ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:51]
A rikice oga Asad ya ce "me zan kwashe?"
Ta kasa magana sai kawia kuka ya sake k'wace mata.
Tsawon lokaci tana kuka mai nauyi kafin ta sarara.
Faruku ya dinga rarrashinta har ya samu ta huce.
Oga Asad ya ce "Faruku ka tambaye ta me zan kwashe dan Allah?"
Cikin rarrashi Faruk ya ce "Menene zai kwashe? Faɗa mini n8a zan tilasata ki ba."
Da muryar kuka ta ce "Hotunanta ya girke ba d'aya ba, ba biyu ba. Kuma don son ya muzanta ni har akan side drower din gado.".
Jikin oga Asad ya mutu. Babu tantama tafi Rukayya zazzafan kishi.Ya kuma tabbatar sune suka fi nukurkusarta tunda tun farkon zuwanta ta daina zuwa saman. Shi zuciyarsa d'aya ya d'auka k'asaita ce kawai ta sanya ba zata bishi ba. Sai shi yake zuwa tare da yi mata uzzirin yarinya ce a kansa.
Ashe hotunansa da na Rukayya ne ba za'a ajiye ba. A ransa ya furta wanne irin k'arfin hali ne haka? Shekara d'aya tak suka yi tare. Amma take kishin matar da aka yi shekaru masu yawa da ita kuma ma bata duniyar.
A k'asan zuciyarsa kuma ya ji dad'i sonsa take, so kuwa ba dan kad'an ba.
Oga Asad ya yi maza ya ce "Zan cire su indai sune matsalar da ta saka kika bijire mini to zan cire su.
Na kuma yi miki alk'awarin ba zan sake kwatanta ki da Rukayya ba, bare na ce ta fiki ".
Faruku ya ce "Bilki idan aka kwashe hotunan shikenan ko akwia sauran damuwa?"
Kanta na k'asa ta ce "Shikenan."
Oga Asad ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwar ba zugata ake yi ba, ba kuma so take ta koma gidan tsohon mijinta ba.
Ya kalli Faruku ya ce "Kafin ka tafi ka roketa ta yi mini hakuri.
Yau din nan zan d'auke na kan side drower ba sai gobe ba.
Amma na falo ta yi mini hakuri sai nan da d'an lokaci k'alilan.
Ban so tashi guda na cire, yaran nan sun ankara tunda suna hawa saman. Ni dai ba yadda zasu yi da ni, amma ita zata yi bak'in jini ne a gunsu mussaman masu wayon tunda zasu zargi na cire ne saboda ita. Daga nan zasu sake jan baya da ita. Ni kuma na fi son su zauna lafiya su sota ta zame musu tamkar uwarsu.
Tausayinsa ya kama Faruku a dalilin ya fahimci ta kowanne bangare a cikin zullimin zarginsu yake.
Kai sabga da mata akwai rud'anin gaske. Ba ga yaransu ba, ba ga manyansu ba. Sun iya kacacccala al'amura da yawa, yana wahalar gaske su yaba k'ok'ari da adalcin namiji".
Faruku ya numfasa ya ce "Allah yasa yau ne zuwana na k'arshe gidan nan da nufin na yi muku sulhu".
Oga Asad ya ce "In sha Allah! Ai tunda na gane inda matsalar take to zan kiyaye".
Bilki bata ce komai ba.
Faruku ya ce "Sarauniyar shaiba ba ki ce komai ba".
Kaitsaye ta ce "Ai dama laifinsa ne, idan ya daina kunsa mini kuttu ta hanyar fad'in an fini a zuciyarsa, ya kuma cire mini hotunan maimurabus a wajensa ai shikenan. Yanzu ina ruwana da hotonsu na falon k'asa?
"To Allah ya yi miki albarka na gode sosia Allah ya shirya miki zuri'a."
Oga Asad ya yi maza ya ce "Idan shima zai zama issue duk zan cire su a hankali. Fatana ki daina damuwa, ki kuma daina tayar mini da hankali."
Yaya Faruku ya ce
"To kin ji ko Sarauniyar shaibà. Dan Allah ki kwantar da hankalinki".
Daga haka Faruku ya mike ya yi musu sallama. Ya ce "Zan dawo mu zauna Maigado."
gidan suka tsaya.
Murya kasa k'asa oga Asad ya ce "D'an koma Faruku ka sake yi mata nasiha akan yau din nan ta huce, ta bar komai ya wuce, mai tsiya ce fa! Kuma batun hotuna ka sake jaddada mata zan ciresu ba da jimawa ba, ta yi minihak'uri. Don idan ka tafi tana iya ce wa sai lokacin da na cire din zata saurare ni".
Bai ce masa komai ba ya juya din tare da amannar Asad bai so wani abu irin Bilki ba.
Oga Asad zuciyarsa a tsaye take, ba shi da tsoro ko kad'an, shiyasa aikin d'amara ya dace da shi. Amma a yau ya tabbatar yana tsoron fishin Bilki. Yana tsoron ta bijire masa.
A zuciyarsa murna yake yiwa Bilki don kuwa ta auri wanda yake sonta da dukkan zuciyarsa. Duk da itama a yanzu yasan oaga Asad take so. Ta kuma gane shi son zumunta take yi masa ba na sha'awa da birgewa ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:54]
Yana shiga falon ya ganta a tsaye da wayarsa a hannunta.
A sanyaye ta ce "Yauwa ga shi da kai maka zan yi, ka tashi ka barta."
Ya karɓa ya ce "To zauna dama so nake ya bamu guri, mu yi sirri".
Ta sake zama a k'asa.
Ya sassauta murya ya ce "Yanzu ke Bilki ba ki iya y'ar kissar nan ta mata ba ko kad'an? Sai idan miji ya b'ata miki ko ya yi miki ba daidai ba. Ki ta kunci kina ta dogon fishi har ki lalace irin haka? To ba dabara kika yiwa kanki ba. Ai idan kika yi kuskuren da ya fara jurewa fishinki to zaku kai gwadaben da shi zai musguna miki kuma ke ce za ki ba shi hak'uri don kuwa shima fishin zai dauka. Matsalar hoto ce za ki bari ta dama miki lissafi tsawon lokaci irin haka? Yo ko tana raye ina ruwanki da ita, indai mijinki na sonki bare baiwar Allahn nan mutumiyarki ce".
Ta kawar da fuskarta gefe ta ce "Kafin yanzu ba".
Ya yi dariya kad'an a ransa ya ce 'ban da yanzu kenan?'
Ya zarce da fad'in da kin iya ma, ai juyar da hotunan kawai za ki yi idan ba ya nan. Idan ya dawo ya ga ni zai gane yaren da kyau da kyau. Amma ki bar k'aramin abu a ranki har ya yi yunkurin haifar da matsalolin da ba zasu gyaru ba. Ki daina dogon fishi kin ji sarauniyar shaiba, kuma ki dinga bude baki kuna tattauna damuwarki.
"Kwanaki da na ce ki koyi kissar da kika ce ba ki iya ba ashe kuwa zama kika yi ba ki saka d'ambar koya ba ko?"
Ta yi shiru kanta na k'asa.
Ya sake maimatawa.
Murya ba amo ta ce "To ni ai tunda ya ce mini ba ni da alheri na kasa jure komai."
Ya nisa ya ce "Bilkisuu gaskiya ki canja taku. Ta ya ya daga zuwanki za ki bari ya fahimci kishi kike yi da matar da ya shafe shekaru sama da ashirin da biyar da ita?
Kuma abin kaicon ba cikin dabara da iya taku ba?
Nasan kina da kishi amma ban yi zaton a yanzu da kika mallaki hankalinki za ki bari kishi ya rude ki da yawa irin haka ba.
Tsananin kishin mace alamun tana cikin garari ne duniya da lahira kuwa.
Wai kina lissafin idan har za ki dade a duniya ma kin cinye rabin rayuwarki kuwa?
Menene ya yi miki dad'i da za ki bari matar da ba ki zauna da ita ba, ta dama miki lissafi, tunaninta ya hana ki nutsuwa balle ki samarwa da mijinki nutsuwar da ta dace da shi.
Ita kinsan irin sadaukarwa da hak'urin da ta yi tsawon shekarun da suka shafe tare?
Maimakon ki mayar da hankalinki wajen gina kanki ta yadda ko bai mance da ita ba, to kuma za ki hana shi tunaninta akai akai. Amma sai ki ta yi masa k'unci da tashin hankalin da zai saka ya yi ta tunaninta tare da ganin ba zai samu mai irin alherinta da hak'urinta ba!
Ya nisa ya yi shiru yana nazarin yadda jikinta ya yi lakwas. Ya cigaba da fad'in "ki duba y'ay'an da ta haifa masa mana. Kada ki yaudari kanki dole tana da alfarmomi. Amma idan kin iya ina tabbatar miki zai ta jin kunyarki akan sha'aninta. Zan kuma fad'a miki wata magana da hakikanin gaskiya ce. Oga bai so wata mace a duniya irinki ba Hakan da na gasgata ya sanya na bar masa ke. Amma fa idan ba ki iya ba, sannu a hankali za ki ta wanke soyayyar nan da kanki, don kuwa mu maza dukkanmu mun fi buk'atar kwanciyar hankali da sadaukarwa a gun wacce muke so. Idan muka rasa samun nutsuwa to fa mace fita take yi a ranmu fit. Ki nutsu ki yiwa kanki gini mai k'arko a zuciyarsa ta yadda ba za'a tsere miki ba. Ki kula da y'ay'ansa iyakacin iyawarki. Ki yi masa biyyaya kan jiki kan k'arfi. Ki kuma amsa kiransa a kowanne lokaci matuƙar kina lafiya kina cikin tsarki".
Kanta na k'asa ta ce "To "
Ya zuba mata ido yana nazarin yanzu ne ya gasgata ta ajiye makaman yaƙin d ta shirya yi da oga Asad. D'azu dungu ta yi masa kawai.
Surayya Dee.
08032773332
Alalh ya kaimu Monday.
Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:33]
*Surayya Dee*
*08032773332*.
*Wannan littafin na kudine*
*Ga mai son biyan hak'kin wahalata 1k ne*
*2384876855*
*Zenith Bank*
*Surayya Ibrahim*
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*
*DINGISHIN KWAD'O*
Ya numfasa ya ce "Sarauniyar sheba ya ya dambarwa ta kare ko kuwa da saura?
Yanzu kin amince da rok'on da ya yi miki na batun cire hotunan. Za ki yi masa hak'uri kamar yadda ya roke ki ko kuwa?"
Ba ja in ja ta ce "Na amince tunda ya saka ka a al'amarin sannan ya ce zai cire na cikin d'aki a yau."
"Yauwa Bilkisu yayar Abida Allah ya saka miki da alheri, na gode. Lallai, lallai ya ga sauyi, ya gane yayanki ya zo gidansa ya yi masa gyara ".
"To"
Ta amsa kanta na k'asa.
Ya mike ya ce "Da yake ba a nutse nake ba ban tambayi twins ba. Nasan manyan na school."
"Wanka ake yi musu zuwanka".
"To a shafa mini kansu".
Ya fita ya iske oga Asad jingine a jikin motarsa.
Dariya sosia ya yi ya ce "Oga ka kamu fa y'ar yarinya ta susuta ka irin haka?"
"To ya zan yi Faruku? Al'amarin mata akwai tayar da hankali duk jarumtar mutum kuwa."
"To sai ka shiga ka sake rarrashi har ka samu kanta na gama gyara maka komai. Kuma Wallahi ka kiyaye misali da mai murabus a gabanta."
Faruku ya faɗa cikin matsananciyar dariya. Don shi sunan gabad'aya dariya yake ba shi. Ya kuma gasgata basu gama gane tsiyar Bilki ba.
Cikin dariya oga Asad ya ce "Wane ni na sake!
Faruku ya gintse dariyarsa ya ce "Oga ka kiyaye motsawa sarauniyar shaiba kishinta. Na rantse maka har yau ban ga mace mai kishinta ba a duniyata. Ka ga irin kishin Jamila, ka ga kishin Rukayya to Wallahi ba kishi suke yi ba.
Tana fa yarinya bata fi 13 zuwa 14 na yi aure ba. Amma shekaru biyu ta yi bata yi mini magana. Hanyar da tasan ina bi ma, bata bi don kada ta ganni. Ba k'aramin jan ido baba K'arami da Baba Babba suka hadu, suka yi mata ba kafin ta yarda muke gaisawa. Hakan ma sai da ta ce zata gaishe ni amma a tabbatar mini ita ba budurwata ba ce. Kai duk baka san wannan ba tunda ka yi nisa ".
Oga Asad ya ce"Zan kiyaye in sha Allah ai na ga jalala".
Ya shiga motarsa ya tafi, yana cigaba da dariyar maimurabus. Oga Asad kuma ya nufi cikin gidan cikin d'oki mai yawa.
Kaitsaye ɗakinta ya nufa ya tarar da ita zaune tana shayar da Baba Babba. Alti na rik'e da Baba Babba da shima yake ta kusur kusur din neman nono.
Alti ta gaishe shi cikin girmamawa.
Ya karbi yaron hannunta. Ita kuma ta d'auki hijab dinta ta fice zuwa d'akinta da yake k'asa don ta yi wanka.
Ya zauna kusa da ita, kafaɗarsu na gogayya da juna.
Ya ce "Sarauniyar sheiba my luv".
Kawai sai ta ji dariya ta k'wace mata.
Ta dinga dariya fararen hakoranta suka bayyana.
Ya kalle ta yana sake samun nutsuwar lallai ta huce don zai iya cewa rabon da ta yi masa murmushi na sosai tun zuwansu Calabar .
Da murmushi ya ce "menene ya saki dariya irin haka? Don na ce miki my love ko kuwa dan kin ga tasirinki mai k'arfi ne a zuciyata?"
"Allah Baban Bilkisu dariya kake ba ni idan kana wani luv love din nan".
Wannan karon shi ma dariyar ce ta subuce masa. Ya gyra zama ya ce "Fad'a mini menene abin dariya dan na ce miki my love. Wato tsufa na yi ne ko kuwa me?"
Ta sake kyalkyalewa da dariya ta ce "Ni ai nasan baka tsufa ba. Tunda dai gamgam nake jin ka, kawai kunya ce take kama ni idan na tuna wai Yaya Asad din nan ne ke mini yar murya da ambaton kalmomin soyayya ".
Ya murmusa ya ce "A gabanki idan ina son nutsuwa ai dole na warware fuska na kuma datse shekaruna su zama irin naki."
Ta yi gajeriyar dariya bata ce uffan ba.
Ya nisa ya ce ". Ya yi barci ne?"
"Eh ya yi".
To cire shi d'anuwansa ya sha".
Ba musu ta daga shi. Ya yi gyatsa sannan ta kwantar da shi. Ta karbi d'ayan.
Shima a hakan ya yi barci. Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:35]
Ya mike ya ce "K'ira Alti ta zauna da su sai ki zo".
Ta numfasa ta ce "Ai sun yi wayo ba sai ta zo ba".
"A a k'irata dai nafi son ana kula da su ko suna barci".
Bata sake musu ba ta ce "To".
Ta k'ira alti ta dauka.
"Alti zan kaiwa Baban Bilkisu shayi ki zo wajen yaran".
Alti da murna aka ce "To ga ni nan , mai nake shafawa na fito daga wanka."
Daga haka ya fice yana fad'in"ina fa jiranki ".
"Ta ce" to".
A sanyaye.
Ta sake gogo oils masu dad'in k'amshi a duka gabobinta. Ta shafawa kanta man gashi masu dad'in k'amshi.
Ta d'auko wata farar lingerie mai matukar kyau.
Ta rik'e a hannunta bata snaya ba.
Daidai lokacin Alti ta shigo.
Da walwala ta ce "Je ki kai masa daga nan ma ki gyara masa d'akin".
Bilki bata ce komai ba, amma dai ta gane hausar.
Yana shiga ya cire ƙaton hotonsa da na Rukayya da yake kallon k'ofar shigowa yana maka barka da zuwa, ya mayar da shi bangon' da k'ofar take ma'ana ba zaka ganshi kamar da ba, dole sai ka shiga cikin falon ka nutsu.
Sannan ya zarce bedroom ya d'auke na kan side drower ya saka a cikin drawer. A fili ya ce "Allah ya jiƙanki Rukky. Masalaha na bi. Allah ya yi miki Rahma ".
Na ce ba.
Rayuwa fa continuation ce. Idan kika mutu tabbas mijinki zai yi aure ya cigaba da rayuwa wataƙila ma ya so ta fiye da ke.
Ki fa yi ibada Hajiya. Ki nemi kud'in halali.
Ki yi alheri. Ki yi sadaka.
Ki yawaita addu'ar a tsare miki imaninki, a tsare ki daga zazzafan kishi da zai saka ki shirkar da za ki kafirta don kuwa kwanciyar kabari kad'ai da take gabanmu abin mu ji tsoron Allah ne mu nemi lahira tamkar gobe zamu tafi.
Tana fitowa ta shige d'aya d'akin ta cire rigar jikinta ta snaya wannan lingerie din da ta tsaya iya guiwarta. Gabad'aya rigar ya ji jikinta ya kwanta. Ta juya yana kallon yadda shape don mazaunanta suka fito sosai a cikin rigar.
Ta isa gaban madubi ta warware gashinta da yake makale cikin ribon ta taje shi tare da sake shafe shi da mai ta kuma fesa masa turaren gashi.
Duk wani lokon jikinta ta shafe shi da oils masu dad'in gaske don kuwa tasan yau ba dama lasar da za'a yi mata ba mai sauk'i ba ce. Ita da kanta zumudi take yi mai yawa don da kanta kewarsa take yi ainun.
Open abaya ta dora akan lingerie din.
Cikin sanda ta bude k'ofar d'akin ta fito a hankali ta janyo ta rufe d'akin ba dan komai ba sai don haka kawai bata son Alti ta leko ta ga irin kwalliyar da ta yi.
Kaitsaye falonsa ta shiga. Ta yi turus ganin babu hoton da yake saka ta faduwar gaba. Ta juya Sai ta gan shi a d'ayan bango. Ta tsura musu ido komin hassadar mai hassada hoton ya zanu. Duk wanda ya zanasu lallai yana da fikira.
Ta juya ta nufi dakin ta hangi side drower ta ga babu hoton.
Ta yi sallama. Da hanzari ya kariso bak'in kofar ya rik'e hannunta yana fad'in "welcome welcome Maigado.
Ya saka hannu ya cire abayar.
Ya kalli yadda rigar ta bi jikinta. Ya riketa ya juyata ya kalli bayanta.
Ya kasa hak'uri ya rik'ota tare kai dukkan hannuwansa bayan da suke daukar hankalinsa.
Murya ba amo ya ce "Anya Maigado ba sai na saka an yi mana crossing of the sword ba kuwa?"
Ta yi murmushi tare da fad'in."ka ga kuwa ina so yana matuƙar birgeni".
"Za'a yi miki kuwa sarauniyar sheba. Ya sake juya ta, ta fuskance shi. Da wata irin murya ya ce "Wannan wanka da me zan siye shi ne. Iye cancadi, kin yi kyau Maigado irin totaly din nan".
Kanta ya yi gingiringim.
Ta ji dad'i. Abin da ya tokareta a k'ahon zuciyarta ya fad'a mata.
Ya rik'eta zuwa kan kujerar da take cikin d'akin.
Shi ya zauna sannan ya zaunar da ita akan cinyoyinsa.
Ya ce "Na gode Maigado. Amma ina son mu yi wata magana guda d'aya don mu rufe duk k'ofar da zata iya kawo mana dogon rikici ".
Cikin nutsuwa ta ce "To".
Ya nisa ya ce "Ina son na fad'a miki ni ba'a mini tsarin iyali a gidana".
Ta kalle shi ta ce "Yi mini bayani yadda zan fahimce ka."
Ya ce "Ban son a tare mini haihuwa. Idan kika duba yaran nan za ki ga ba wani tsira a tsakaninsu idan kika cire Amal da ta bawa Noor shekaru masu dan dama." Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:36]
Ta yi shiru.
A tausashe ya ce "Pls mana Maigado Ki yi magana."
A nutse ta ce "Amma Baban Bilki da Sai ka fad'a mini tun kafin mu yi aure ".
A sanyaye ya ce "A lokacin fa ba Sona kike ba yaushe ma zan tunkare ki da wannan maganar. Yanzu kuma sai nake ganin ko ba komai ba