Showing 135001 words to 138000 words out of 148964 words

Chapter 46 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

Ta nade masa a poil pepper ta saka masa a leda tare da ruwa da lemo.
Duk da tasan dady ya bashi kud'i sai da ta bashi wasu.
Ya dinga godiya ya tafi . A Kaduna zai kwana da safe sai ya wuce Abuja.
*Katsina.*
Amrah da Faruk tare da Babansu da take dauke da Ifrah suna zaune a falo.
Amrah ta ce "Dady muna son mu je wajen Mahmah wannan hutun da za'a yi."
Ya nisa ya ce "To mamana idan na samu sukuni sai ku tafi".
Ta ce "mun gode".
Ya ce "Kwana nawa zaku yi to?"
Amrah ta ce "Gabad'aya zamu yi hutunmu a can tunda sau d'aya muka je sai kuma sunan twins da muka yi kwana biyu muka dawo saboda school."
Sai lokacin Faruku ya ce ",To zamu raba hanya kenan don kuwa ni kwanaki goma zan yi na dawo a gidan ubana".
Amrah ta kafe shi da ido. Yayin da Sahal yake nazarinsu gabad'aya.
Ya fahimci ita Amrah irin mutanen nan ne marasa damuwa tamkar dai Bilki. Komai nata bai tsole mata ido ba. Ko yadda bata bawa Hawwah matsala ya fahimci sak take bata ajiye damuwa a ranta ko kad'an.
Yayin da Faruku yake a murd'e. Baya shiga shirhin Hawwah har yau din nan. Amma yana kula Ifra tare da siya mata abubuwan yara na ci ko na wasa irin wadda zai iya siya.
Amma tsakaninsa da Hawwa gaisuwar safe sai kuma wata safiyar.
To yanzu kuma ya fahimci ba zai mayar da oga Asad ubansa ba duk da yana yayan mahmansu.
Dad'i ya ratsa shi a yadda ya ce zai dawo gidan ubansa. Daular da suke ganin uwarsu a ciki bata rude shi ba, don kuwa ba gidan ubansa ba ne.
Ya numfasa ya ce "Faruku kawai ka yi hak'uri ku dawo tare ban so ku raba hanya idan zaku dawo".
Kaitsaye ya ce "To zan duba na ga ni idan mun je. Kuma gaskiya Yaya ki rage yin kazallaha a gidan nan. "
Ta harare shi tare da fad'in "Ba ka ce ba ruwana da harkar ba, to nima ba ruwanka da harkata".
Ya yi dariya ya ce "Ni na huce fa Yaya. Kema ki huce da k'aninki. Amma gaskiya ba zamu yi 1 month ba. Na hak'ura mu yi 2 weeks sai mu zo Kano gidan Maman Kano mu kammala hutunmu. Idan kika yi candy sai ki je ki dade babu ni".
Ta yi masa shiru".
Ya ce "kin yi shiru yayar Faruk"..
A dan tunzure ta ce "Tunda kaine ubana ka tsara yadda za'a yi dole na amince ai".
Ya k'yalkyale da dariya ya ce "Nasan ma kin yarda yayata. Allah idan ba anan gidan ba, bana iya sakewa duk kayan alatun da suke can sai na dinga ji a raina ba dai gidanmu ba ne sai na ji duk na gundura na fi son gidan ubana fiye da ko ina ".
Wani irin matsanancin dad'i ya kama Sahal.
Tausayin kansa ya kama shi.
A zuciyarsa addu'a yake Allah ya buda masa. Ya jiyar da y'ay'ansa farinciki.
Daidai lokacin Hawwah ta dawo daga makaranta. Da ƙyar take tafiya ta gaji ga cikin da ya fara tsufa.
Ta kallesu ta watsar. Ba dan Faruku na wajen ba, da tsaki zata yi masa. Kullum ita da Sahal babu nutsuwa a dalilin babu walwalar aljihu. Babu kwalliyar da yake tsalawa a lokacin da yake neman aurenta. Save Restricted Content Bot, [Nov 14, 2025 at 16:21]
Ba komai a gidansa sai abinci irin na yaku bayi. Hatta kayan amfanin yau da gobe irinsu sabulu da Omo da ƙyar yake kaisu k'arshen wata.
Motarsa ta nan amma yafi hawa machine tunda rike Mota da hidimarta ma daban yake. Shiyasa ya kukuta ya karbi loan din machine.
Ita kuma bata hawa nisa hujjar karkon kifi ne an saba ganinta a mota sai ta koma hawa mashin. A halin da yake ciki kuma dole ya bata kudin napep. Don haka rayuwar dai sai hak'uri.
Babban farincikinsa yadda Amrah da Faruku suke samun tallafin uwarsu. Har yanzu suna girkinsu. Basa rasa snacks. Sannan a cikin walwala suke. Wani lokacin ma a gun Amrah yake samun kud'i idan Faruku baya nan. Don idan yana nan cewa yake yi basu da kud'i. Idan kuwa jar ya ga Amrah ta ba shi . Idan suka kebe ya dinga mata masifar ba fa zai yiwu uwarsu ta dinga basu kud'i don su yi abin da bai yi musu ba, ta dinga dauka tana ba shi yana yiwa wata matar hidima da kuɗinta ta bari baya so. Dole take lallaba shi tana ba shi hak'urin ba zata sake ba, don bata son ya yi abinda babansu zai muzanta a gabansu.
Faruku ya zama wani irin murdadden yaro na gaske. Amrah mamakin yadda baya tausayin Babansu ko kad'an take yi. Amma yau kuma ya shayar da ita mamaki da ya ce ba zai je ya d'ade a gidan da ba na ubansa ba ne. Kenan bai d'auki uncle police babansa ba?
Lallai halayyarsa sai shi.

*Abuja*.
Juyin duniya Sulaiman ya yi akan ya wuce da Hamida da Anisa Amma Hamida ta ce "Sai ta yi sati ba zata tafi ba mijinta ya ce gidansa ne yafi yi Mata dad'i. Tunda ya ce ya bata sati to sai ta yi kwanaki takwas ma har da ƙari "
Dariya mai tsananin gaske ta bwa Sulaiman.
Ya ce "Ni wacece ta zo da ƙyar ne?"
Ta ce "Hamida ce yanzu kuma ba zata fi ba sai ta huta".
Dad'i ya kama Baba ya ce "Ki yi zamanki sai ku tafi rana daya da Salaha. Ku shiga jirgin Kano ita kuma ta shiga na Lagos. Tunda sun koma Lagos da zama."
"Hakan za'a yi baba ".
Sulaiman ya kalli Anisa ya ce "Ke ma ba za ki bini ba?"
Ta ce "Eh sai Yaya zata koma zamu wuce tare."
Ya ce "Ai shikenan kun hutar da ni zuwa Kano da Katsina kaitsaye sai na wuce gida Funtua."
A daren suka yi sallama da shi. Faruku ya zo ya d'auke su ya tafi da su gidansa har da Salaha.
Yana tashi gidan Bilki ya nufa don ya yi mata sallama.
Farha na ganinsa ta ruga ya rungume ta. Haka take yi masa Shi da Ansari.
Ya d'ora ta kan cinyarsa don ta ji dad'i.
Noor ma ta zo kusa da shi. Itama ya d'ora ta kan d'aya cinyar yana tambayarsu karatunsu."
Rairai suke masa state and capitals kuskure suka zarce da sabon national anthem da sabon shugaba ya dawo da shi.
Ya ce "Ah lallai dole junior ya ce a makarantarku Zan saka shi. Ina Amal?"
Suka ce ta yi barci.
"Ya kalli agogo tara saura. Ya ce "To ku sai yaushe zaku kwanta?"
Suka ce "9".
Ya ce "Kuma lokacin ya kusa cika."
Bilki ta ce "To ku k'yale shi ya ci abinci".
Suka sauka daga jikinsa suka yi d'akinsu. Aysha Hafcy da Bilkisu suka zo suka gaishe shi. Ya dinga jansu da hira kafin suka tashi.
A marairaice ta ce "Yaya Sulaiman sai kuma ka bar Abida ta tafi ita kad'ai?"
Kaitsaye ya ce "Tunda fitowa ta yi babu iznina ba yadda za'a yi na tafi da ita."
Ta numfasa ta ce "Dan Allah yaya Sulena yafe mata komai ya wuce ban son Abida ta janye nadamar da ta yi ".
Ya murmusa ya ce "To dazu ma Baba Babba ya gama nema mata afuwa. Ai na huce tunda ta tafi Funtua babu dogon turanci ta yarda da hukuncina babu inkari".
Dad'i ya kama Bilki ta ce "Allah yasa k'arshen alamarin kenan".
Ya ce "Ameen Bilkina".
Yaya Sulaiman amma zaku bar Funtua nan gaba?"
Ya ce "A a matuƙar ina Nigeria to kuwa ina Funtua. Duk inda zan je zan dawo gida ne, iyalina zasu zauna a Funtua ".

Bilki ta numfasa ta ce "Allah ya taimakemu gabad'aya ".
Ya ce "Ameen Bilkina. Gobe da asuba zan kama hanya dazu na je wajen Saddiqa na yi mata sallama. Hamida da d'iyarta Anisa kuma sun ce suna nan Babansu kuma ya goyi bayansu". Save Restricted Content Bot, [Nov 14, 2025 at 16:22]
Ta yi dariya ta ce "Ai kuwa d'iyarta don Anisa bata bin ra'ayin kowa sai na Yaya Hamida".
Ya ce "Allah ya cigaba da ganar da ita."
Bilki ta ce "ameen".
Ya zarce da ba shi labarin yadda ta wakana tsakaninta da oga Asad.
Dariyar da Sulaiman ya yi ba yar kad'an ba ce. Ya ce "Anya kuwa muna da cikkaken lafiyar kai, tsiyatakun alhalin gidanmu masu yawa ne tamkar muna da jinnu da gaske fa ".
Bilki ma ta dinga dariya sosai.
Ya ce "Allah ban da shakiyanci ya ya zata ce tana bin oga bashi, bata bar shi na kuma shaida ya bata. Kinsan adadin kudin da wacccar yar darun ta yanke mini na diyyoyi da bashin da ta yi ta ranta mini kuwa?"
Ya faɗawa Bilki adadin kudin.
Dariya ta k'wace mata. Ta ce yanzu ya aka karke Kuma?"
Ya ce "Bori na dauka mana akan to ta cigaba da zama idan na samu na kawo mata. Ta ce ita na bata abin da yake hannuna zata bini ba shi.
Na bijire akan babu bashi a tsakaninmu kuma yanzu ba Zan Fara ba. Milyan d'aya kacal na ce Zan bata. Idan kika ga yadda take kuka tana fad'in na dai sake dubawa sai abin ya daure miki kai wato y'an gidanmu y'an sababi ne na gaske kowa ba shi da sauk'i idan aka taba shi, barin ma su Abida da Hamida".
Gaskiya Yaya Sule milyan d'aya ta yi kad'an gaskiyar magana kenan".
Ya ce "Hmm ai tana can tana jirana duk yadda Baba ya ce ya soke maganar bashi nasan sai na bata wani abin da na samu nutsuwa. Abida Abida iron lady ".
Bilki ta kwashe da dariya ta ce "Ta hadu da iron vendor".
Ya murmusa bai ce komai ba.
Daga haka ya fad'a mata next month zai zo ya dauki baba sun gama magana ya amince zai koma gida babu gardama ko neman shawara da kowa, wanda hakan ba k'aramin dad'i y yiwa Sulaiman ba".
Jikin Bilki ya yi sanyi ta ce "Shikenan sai ku barmu mu kad'ai?"
Ya ce "Eh dama a sama kuka same shi anan. Ke da Oga ku yi hak'uri. Mun fiku buk'atarsa. Sannan komawarsa can shine rufin asirin kowa da kowa shine darajarmu gabad'aya."
Ya mike ya ce "yau oga ya yi nisan kiwo."
Ta ce "Meeting suke yi."
Ya ce "To ki gaishe shi ki fad'a masa na zo yi masa sallama baya nan Zan wuce da asuba amma zan masa waya in sha Allah".
Daga suka yi sallama ya wuce.

*
Bilki na kwance kan kujera ƙafafuwanta na kan cinyar oga Asad yana jan yatsunta tamkar ba shine ya dawo a gajiye ba.
Murya ba amo ya ce "Ta shi mu shiga ciki ki taimaka mini na watsa ruwa. So nake na sauke miki gajiyar da nake fama da ita".
Bata ce komai illah mikewa da ta yi ta mik'a masa hannunta ya kama ya mik'e.
Hakan kuwa aka yi,.tare suka yi wankan a daddafe ta shafa mai tare da shafe jikinta da turarukan *mkbees oil perfumery* masu sanyayyen kamshin dad'i da tsayawa a zuciyar masoya 07032456061.
Yayin da shi ko mai bai shafa ba body spray kawai ya fesa daga nan ya shiga sauke mata gajiyar da ya yi niyyar yi. Ita kuma tana karɓan dukkan sakonsa cikin jin dad'i da walwala don haka ta sakar masa jiki tare da mayar amsa da martani irin yadda yake so".

Na gode da hak'urinku.
Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:50]
*Dinginshin kwado*
08032773332.
Suna dawowa masallaci da Baba ya shiga ya gaida Momi tare da yi mata sallama. Ta amsa da walwala tare da sake ba shi hak'urin akan sha'anin Abida.
Ya amsa mata da fad'in "komai ya wuce ai momi a dai cigaba da yi mana addu'a."
Ta shiga kicin ta juyo amsa pepper chicken din da aka yi masa tun dare.
Tare da ruwa da lemo a leda.
Ya karɓa da godiya ya fice waje tunda Baba na tsaye yasan sai ya ga tashinsa da ya shigo.
Har mota Baba ya raka shi yana masa addu'ar ya sauka lafiya da kuma jan kunnen ya yi tuki a hankali cikin nutsuwa".
Ya dinga amsawa cikin girmamawa. Baban kuwa bai shiga ciki ba sai da motar Sulaiman ta bar farfajiyar gidan.
Ya sauke ajiyar zuciya a fili ya ce "Alhamdulillahi. Allah kasa k'arshen rikici da hatsaniya da zamu fuskanta kenan a cikin zuri'armu. Allah yasa duk fitinar da zata taso a cikinmu kada ta zama mai tsananin gaske. Allah ka sanya soyayya da tausayin juna a tsakanin dukkan yaran nan. Wanda aure ya shiga tsakaninsu Allah ka zauanr da su lafiya ka kade dukkan fitina da sharrin shaiɗan da na zuciya".

*Duk wacce ta siya littafin nan tana da discount idan zata siya kayan gyaran mata gangariya, don haka ina saving cont6din Duk wacce ta siya*.
*Ragi na gaskiya Zan yi muk ba na wayo ba*
*Na gode muku*
*Ku tuntube ni kaitsaye a WhatsApp don ganin kayyaki masu kyau daga Chad da Sudan*
08032773332.
*Bojuwa herbs*.

Hawaye ya silalo masa wanda na farinciki ne, ko yanzu ya mutu ya tabbatar bai bar su a wargaje ba, bai barsu da gillin juna a zukatansu ba.
A hankali ya ja kafarsa zuwa ciki.
Gaf da azhar ya isa Funtua.
Tun a farfajiyar gidan yake jiyo k'amshin turaren wuta da k'amshin girki mai tada yunwa. Ya rasa k'amshi irin haka. A gidan Bilki yake jin k'amshin spice's din nan har ma da k'amshin gidan da yake ji a yanzu irinsa yake ji a gidan Bilki.
"Wato wadannan yara sun iya munuba."
Ya fad'a a fili.
Ya gama rufe gate din kenan ya taho wajen motarsa, ya ga an bude k'ofar wajensu. Ya tsyaa sai ya ga junior ya fito a guje ya nufo shi.
Dad'i ya kama shi. Ya budewa yaron dukkan hannuwansa tare da durkusawa kadan.
Ya iso ya fad'a masa ya ce "Dady kai ma ka zo?"
Ya ce "Na zo junior ya ka ga gidanmu ne?"
Ya ce "Very big and beautiful amma babu upstairs irin na gidansu Farha".
Ya yi dariya ya ce "junior ka dinga addu'ar Allah ya bani kudi sai na yi mana irin nasu".
Ya ce "To Dady. Jiya mun yi barci Ammi bata yi kuka ba, komai na gidanmu sabo ne".
Sulaiman ya dire shi ya ce "Komai sabo da gaske?"
"Junior ya ce "Da gaske fa, thank you Dady ".
Ya ce "saura a saka ka a school ko?".
Ya ce "eh Dady ".
Ya ce "Zan saka ka a makarantar da tafi kowacce inganci a Funtua ".
Dad'i ya kama shi ya dinga tafi yana fad'in thank you.
Yayin da haka kawai k'walla ta cika idanuwan Sulaiman. Tausayin yaron ya kama shi from no where. Sannan yadda yake tsaye a harabar gidan nasu zuciyarsa ta karye ainun Yana fatan nan ba da jimawa ba gidan ya dawo da kwarjinin da yake da Shi a da.
Haka nan yana son gidan ya dawo matattarar farinciki ga kowa da kowa a cikinsu.
Ya ajiye yaron. Ya bude bayan motar ya ba shi ledar takalmansa shi kuma ya d'auki jakar kayansa da ta laptop d'insa.
Ya rufe motar ya rik'e hannunsa suka nufi cikin gidan.
A tsakiyar falon ya tarar da Abida ta ci kwalliya cikin dankareren leshin da ya lashe makudan dubba darirruka. Kalar ta haskata.
Da yake bata kwalliya mai nauyi daga powder sai lipstick. Sai ya ga yau ta canja gabad'aya. Ya yi nutsu yana son ganin me ya sauya ta ne?
Take ya gano janbakin da ta sanya ne sannan ta canja d'aurin dankwalinta da a kullum take yi na ture ka ga tsiya, yau sai ta yi irin Zahra Buhari.
Ya saki hannun junior ya isa kusa da ita k'amshin turarenta design6 na cool water ya buge shi.
Jikinsa na bari ya jata zuwa jikinsa ya rungume. Ba zato ya ji tafin junior a kunnensa. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:55]
Ya yi maza ya sake ta.
Ya zauna ya jata zuwa kusa da shi ya zaunar da ita.
Murya ba amo ya ce "Ba wannan Abidar nake so ba. Me yasa kike son canjawa?"
Idanuwanta ya cika da k'walla ta kasa magana.
Ya zaro tissue ya shiga goge mata janbakin da ta saka. Ya saka hannu ya cire mata dankwalinta.
Ya ce "Ina abin da kike sakawa cikin dankwalin?"
Ta ce yana kan madubi.
Ya dauko ya saita shi ya nade sannan ya dauara mata irin daurinta.
Ya ce this is my real Abida".
Ta murmusa guntun hawaye ya ziraro mata.
Murya ba amo ta ce "Sannu da dawowa ya hanya?"
"Alhamdulillah".
Ta ce "Haka ka gyara gidan?"
Ya ce "Ya yi miki?"
Ta ce "irin sosai fa".
Ya ji dad'in yabawarta. Ta ce Amma na ga duka gidane ya canja".
Ya ce "So nake Ubangiji ya taimake ni na dawo da shi yadda yake a da, dan haka na gyra Shi gabad'aya.
Ta ce "To Allah ya taimaka, ya cika maka buri".
Ya mike zuwa d'akinsa ta bishi da jakar hannunsa.
Ya saka mukulli ya bude. Suka shiga ta ga d'akinsa ma komai sabo ne amma gadonta yafi nasa kyau da tsada nesa ma ba kusa ba duk da shi din ma mai kyau ne ba wai mai araha ba ne.
Ta ce "Baban junior gaskiya ka kashe kud'i sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara budi na halal. Allah kums ya bada ikon biyan bashi".
A ransa ya ce "Nasan za'a yi haka".
A fili ya ce"Ameen na gode ".
Ya shiga wanka ita kuma ta fita zuwa kicin.
Spice's din Amreesh duniya ne don daga jiya zuwa yau har k'amshinsu ya fara kama gidanta. Idan ta fara girki kuwa kamshi har waje.
Tunda ta ji a gidan Bilki shine ta sa ta yi mata order din Bridal package din.
For your order 09093510131.
Yana fitowa ana k'iran sallar azahar.
Dama ya d'oora alwallah dan haka ya shirya ya k'ira junior ya yi masa alwallah ya rike hannunsa suka tafi masallacin kusa da gidan wanda iyayensune suka gina shi.

Ya dawo suka ci abinci tare sannan ya hau keken atisaye da yake d'akinsa don ya motsa jikinsa a dalilin gajiyar da yake ji a tare da shi.
Abida ta shiga ta tarar da shi ya had'a zufa akan keken ta ce "Sannu."
Ya ce "Yauwa. Wai so nake na warware dan kada na kasa iyawa da ke tunda kin ce kina cikin kewa sosai".
Ta murmusa bata ce komai ba.
Ya sauko ya shiga bayi don ya watsa ruwa tunda ya jike sharkaf da zufa.
Ita kuma ta fita zuwa d'akinta.
A falo ta tarar da junior yana barci a zaune.
Ta saka hannu ta d'auke shi zuwa d'akin da yake da k'aramin gadonta. Ta kwantar da shi.
Ta kalli Razina da take zaune a gefe daya.
Ta ce "Ki je ki zubo abinci ki ci, idan kin gama ki yi wankewanke".
Ta ce "To".
Daga haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login