Showing 147001 words to 148964 words out of 148964 words

Chapter 50 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

a raina?"
Ya murmusa ya ce "Amma dai Bilkina ce uwarki, Abida ta haifa mata ke".
Ta ce "Har abada kuwa Dady".
Tunda ga lokacin bata sake tayar da maganar ba. Bata taɓa nunawa Bilki ta gane ba, tunda ta k'i yarda ta fad'a mata ba ita ta haife ta ba. Ba ma zata sake tambayar ba tunda ta ga bata so.
Shikenan ta sakawa zuciyarta Faruk ne mijinta tunda yana sonta ita ma tana sonsa.
Alti kuwa tunda Faruku ya fad'a mata ta dinga kula masa da Farha shikenan take taya shi yaki. Komai ta ga ni sai ta siya ta bawa Farha tana fadin toshi ne.
Har gobe bai son ya Dade a Abuja. Ko da Amrah yanzu bata nan ya daurewa zuciyarsa yana zaune a gidansu tare da Babansa.
A yanzu da ya fara hankali sosai yake tallafawa a cikin gidan tunda asusunsa baya rasa kud'i masu auki sosai. Oga ya tura masa. Mai sunansa ya tura masa. Hatta Ammar da yake kula da harkokin babansa a Abuja tura masa kudi yake yi. Yana sonsa don shine takwaran ABBAnsu na farko.
Haka nan Bilki.
Har gobe kuma suna tare da Alawiyya da take da yaranta.
Tana zuwa gidan wajensa lokaci zuwa lokaci tana yi masa gyara.
Sannan har Abuja tana lekawa wajen Bilki.

*Za'a buga hard copy mai bukata sai ta yi magana a buga da ita*

*Tare Littafin BAK'AR TA'ADA za'a buga hard copy Duk Mai so Sai Ta yi magana a yi da ita *.

Tana zaune a falon oga Asad tana jin littafin Malamin bogi da da ake k'arantawa a tashar limamin tsakar gida. Gaskiya Maman Afra ta sanya ta dariya sosai.
Daga nan ta tsallaka ainihin tashar tsakar gida tana jin Turken gida na marubuciya Janafty.
K'iran Abida ya fado wayar ta amsa.
Kaitsaye ta ce "Abida yau na yi dariya saii yau fa na kammala sauararon Malamin bogi na Maman Afra.
Yanzu TURKEN GIDA nake bi."
Abida ta ce "Hmm wani littafin nake ji yanzu yadda kika san almara kamar rayuwar gidanmu marubuciyar ta d'auko take rubutu komai tiryan tiryan tamkar a majigi. Zuciyata ta kasa nutsuwa na ce bari na kira ki ke ce mai gayyaar jama'a ko kinsan marubuciyar kin bata labarin mu ita kuma ta yi giggiwar rubutawa babu neman izinin kowa".

Bilki ta ce ya sunan littafin da kuma marubuciyar?"
"Dingishin KWAD'O
Ita kuma sunanta Surayya Dahiru Gwaram."
Abida ta amsa mata a takaice.
Bilki ta ce "Na dai saurari littafinta HALIN YAU, Sabo da Kaza a Tsakar gida. Amma Gwaram din ba na ce ga inda take ba fa".
Abida ta ce ni kam na karance su, kamar dai a Jigawa ne.
Amma kaina ya kulle zan yi magana da Yaya Munira idan kuwa labarinmu ta ji, ta yi kuskuren yayatamu a duniya sai mun gurfanar da ita a gaban kuliya".
Bilki ta kyakyace da dariya tare da fadin Abida kanwata. Amma bari nima zan bincika ya ma kika ce sunan labarin?"
"Dingishin kwado kuma Maigado har na shiga paid group dinta tunda ta kammala a can na ji k'arshen labarin, amma duk da haka kullun sai na sauarari na tashar maisanyi. Kuma duk na danna mata likes a episode 1 10 don labarin ya ja hankalina k'warai da gaske ".
Bilki ta ce "Nima zan koma na danna mata don ban yi ba, to ya batun gurfanar da ita kuma?"
Abida ta yi dariya ta ce "ke na hak'ura idan ma labarin namu ne Allah yasa ya zama aya da gargadi ga masu hankali."
Bilki ta ce "ameen."
Suka yi sallama.
Oga Asad ya kalli Bilki ya ce "Kuna nufin baku san Gwaram ba?"
Ta ce "Eh".
Ya jijjiga kai ya ce garinmu ne ni".
Ta kalle shi ta ce "Ta ina Baban Bilkisu?"
Ya ce tun shekarun baya mun je yiwa oganmu ta'aziyar rashin mahaifinsa a lokacin ina Calabar. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 16:00]
Garin manya ne fa.
Ai yanzu da zan ganta sai na yi saluting dinta don kuwa former I.G Sulaiman Abba Gwaram ba abinda da bai yi mini na alheri ba, ya taimakemu k'warai da gaske a lokacin da muke k'ananun y'ansanda.
Wataran zan d'auke ki mu je ki gaishe shi bamu da nisa da shi, daga nan na wuce Maitama na kai ki gidan NEPA kacokan dan ki gaida tsoho mai ran k'arfe Eng. Hamza Gwaram da iyalinsa gabad'aya, wataƙila ma ki yi katarin ganin marubuciyar a gidan. Daga nan sai ki gane Gwaram tana da manyan mutanen da suka kai k'ololuwar mukamin da ba zai yiwu ace an fade ta ace ba'a santa ba.
Idan mun je Kano kuma zan kai ki gidan sardauna marigayi Bello Maitama. Na wuce da ke gidan Justice Tijjani Abubakar Gwaram. Ke suna da yawa fa.
Ban da ma mutuwa da bata barinmu da na kira miki G.m. Dahiru Nepa yanzun nan a waya.
Ban da tsofaffin Y'an siyasar jiya Shugaban gwagwarmayar Nepu. Hon Sani Gwaram."
Bilkisu cikin alhini ta ce "Allah ya jiƙansu da Rahama".
Ya ce "Ameen Maigado.".
Lallai ya kamata marubuciyar ta yi rubutu a garinsu tunda ta yi a Funtua, Toro da Bulkachuwa.".
Koda yake ta ce saboda Justice Zainab Bulkachuwa ne ya sanya ta yi labari a Bulkachuwa."
"Sannu a hankali zata yi a garin nasu tunda ta yi a garin wasu ma".
Oga Asad ya fad'a a takaice.

*
Oga Asad ya shirya musu tafiya Shi da Bilki zuwa k'asr itali dan su dubo Bilkisu da ya haihu daga can su zarce Canada.
A birinin rome take zaune dan haka a can suka yada zango. Kwanansu biyar a garin. Ta kaisu gidan Anty zaliha Maman safiyya. Don sosai ta zame mata uwa take kulawa da ita.
Bilki ta dinga Godiya da fatan alheri ga anti zaliha.
Daga Rome suka wuce birin suak shiga jirgin kasa zuwa birinin Caserta don kaiwa abokiyar karatunta a B.U.K. Aunty Fauziya Fiji ziyara.
Sun samu kyakkwar tarba ta mussaman. Sun jima kafin su tafi bayan oga Asad ya yiwa yaranta alheri.
Fatan alheri ga yayata Anty Fauziya Fiji da anty zaliha usman da iyalinsu gabad'aya da suke zaune a kasar Italy.
Daga nan suka wuce k'asar Canada takanas don Bilkisu ta gaida takwararta Barr Bilkisu Garba Ibrahim.
Duk yadda Maigado tasan barista mai karamci ce sai da ta gane ashe bata ga komai ba cikin karamcinta sai da ta je muhallinta.
Saukar girma ta samu. Bilki ta dinga nazarin barista tana daukar kwas din sirrin gayu da kwalliya da kuma alheri da iya mu'amala.
Fatan alheri gareki da iyalinki Barista.
Allah ya shirya miki zuria ya kara arziki.
Littafin nan na kud'i ne.
1k.
Ga mai buk'atar sauke hakki.
2384876855
Surayya Ibrahim
Zenith.

Sun dawo gida Nigeria lafiya.
Rayuwa ya cigaba da gungurawa kowa na hakuri da yadda k'addara zaba masa.
Haihuwa dai ta tsayawa Bilki.
Ta ce tunda da bakinsa ya ce tana yin 43 ta gama, yanzu da take 42 ma ai duk d'aya ne. Dole ya hak'ura ya k'yale ta.
Sai baje kolin soyayya da tattala juna tamkar ba Hausawa ba.
Tafiya ya same Shi da tawagar Shugaban kasa zuwa k'asar burtaniya.
Kan dole ya tafi Babu ita.
Bilki tsabar sangarta har da kuka wiwi.
Yayin da ya dinga lallabata tare da bata hak'uri akan ba dadewa zai yi ba.
Kwanansu daya ya k'irata.
"I miss you Gwarzona."
Balki ta faɗa cikin taɓara jikinsa ya mutu.
"Na yi kewarki Balkina. tamkar na tsero na dawo.
Shirya bari mu yi vedio call ko na rage Jim kewar nan ta ki."
Ya katse wayar.
Ta tashi ya shirya irin shirin da yake so.
Ya k'irata kuwa suka gama sheke ayarsu tamkar ba oga ne yake zaro manyan kalamai masu nauyi ba.
Cikin son ta sake narkar da zuciyarsa ta ce "Baban Bilkisu ina sonka, ina son na rayu da kai ina jin dadinka sosai".

"Allah Maigadona? Ki ce zan samu tarba ta mussaman."
Ta ce "irin wacce ba'a taba yi maka ba."
Ya murmusa ya ce "Na gode Allah ya yi miki albarka."

Ranar da ya dawo cikin dare ya sauka.
A bakin k'ofar falo ya tarar da ita
"Welcome back Gwarzona."
Ta faɗa cikin wata irin murya.
Ga mamakinta sai ji ta yi ya sunkuce ta zuwa cikin falon sannan ya dire ta. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 16:03]
Ita kuma ta yi masa wani irin juyo don ya ga mutanen nasa da kyau. Don wata irin lalatacciyar riga ta sanya da ya fito da figure 8 ɗinta.
Ya kidime ya jata jikinsa yana fadin "I really missed you Maigadona".
A daddafe suka hau sama. Ya yi wanka ya ci abinci marar nauyi sannan aka shiga cin uwar sabada.
Hankalin Bilki ya kwnata. Don oga Asad ya mayar da ita queen ta sosai a cikin gidansa. Dukkan niimar rayuwa Ubangiji ya yi mata. Hak'uri da juriya da ta yi ta ga sakamakonsa.
Ubangiji ya yi sakayya a tsakaninta da Sahal don ko da basa tare tana sane da har gobe yana cin arzikinta.
Ta tuna tsananin da ta shiga a farkon aurenta da oga Asad.
Baba Babba ya yi ta jadadda mata kalmar ta yu6 hakuri, da ba ta yi hakuri ba da yau ba ta san inda wata kaddaran za ta sake jefata ba. Don ta riga ta gane duk inda ka je a duniya sai ka fuskanci k'alubale ka kuma yi hak'uri. Yin gaggawa yana nufin yin da nasani mai tsananin gaske.
Shiyasa yadda a kullum take yiwa iyayenta addu'ar samun rahama haka take yiwa Baba Babba addu'ar ya gama da duniya lafiya don ya yi dukkan k'ok'arinsa akan aurenta da dukkan al'amarinsu gabad'aya.
Sannan Yaya Faruku tana roka masa bene hawa na kololuwar masu daraja a cikin aljanna. Don ya yi mata zumunci iyaka, ya yi sadaukarwa mai yawa. Don haka tana masa kallon uba ne ba Yaya ba. Yana cikin kariman mutanen da ta ga ni a dukkan tsayin rayuwarta. Duk kuma nasarar da ta samu a duniya tana da tabbacin da tallafinsa a ciki, don ko auren nan na oga da take jin dad'insa a yanzu shine dai sila.

Cikin dare tana kwance jikin oga. Ta yi ligi ligi ya k'ure mata jarumtarta.
A tausashe ya ce
"Na gode Maigado, kkin sabumta tsufana, kina bani shwarwari kina kula da y'ay'ana da gidana.
Ke alheri ce."
A kasalance ta ce "Ni ma na gode da kokarinka a kaina gwarzona"
Yana Jin dadin gwarzon da take fad'a masa.
"In sha Allhu, ba zan taɓa gazawa ba, ina roƙon Allah ya cigaba da bani karfin da ko da yaushe za ki ji kin gamsu da ni, Alllah ya yi miki albarka Allah ya kara ma Baba Babba Lafiya Allah ya ba ma Faruku aljannah, Allah ya jikan Baba karami da mami Allah ya haɗa mu da su a darusslam."

"Amin Amin Gwarzon Bilki uban Bilki kuma I.G din gobe da yardar Allah."
Balki ta faɗa kwalla na ziraro mata, ta dago tana kallonsa cikin wani irin shauki.
Shi din gwarzone , namijin duniya ne na gaske. Mai adalci ne. Baya yiwa duk wanda ya dangance shi kwangen dukiyarsa bare kuma su iyalinsa.
Ta ba shi lambar yabo a zuciyarta da idanuwanta.
Ya rumgumo ta yana faɗin" Amin Amin my BABYY."
Bilki ta kyayace da dariya, tana maimaita sunan, shima dariya yake yi, kafin su kama bakin juna suna sumbata cikin shauki da soyayya mai tsayawa a zuciya.



*Tsokaci*.
*Assalamu alaikum, barkanmu da yini ya iyalin?*
*Allah ya taimakemu gabad'aya*.
*Ina ta samun k'iran waya daban daban akan ingancin kiranyen da Abida ta yiwa Dr Sule*.
*A gaskiyar magana na saka me don hi Shirin labarin*.
*Don haka a daina tambayar fatawar ingancin, kawai duk addu'ar da za'a yi akan tsarin shari'a tare da cikkaken yaƙinin in sha Allah Ubangiji zai karɓa*
*Bayan haka ina son na sanar da ku cewar gabad'aya labarin nan kirkirarren labarine(fiction) bai faru a gaske ba, bai shafe ni ba, bai kuma shafi wani nawa ba*.
*Haka sunaye da garuruwan da na ambata duk kirkirarrune bana kowa ba ne".*


*ALHAMDULILLAHI*
*ALHAMDULILLAH*


*Godiya ga dukkan waɗanda suka siyi labarin nan.*
*Na gode, Na gode da hak'urinku Allah ya ya bar zumunci. Allah ya yiwa dukiyarkubda zuri'arku albarka*.

*Yan comment section*
*Ina matuƙar godiya a gareku gabad'aya*.
*Mussaman*
*Anty Maryam Saminu Sulaiman*
*Sarauniyar sharhi*.
*Da*
*Anty Nana Bauchi*
*Da dukkanku da ba zai yiwu na iya kama sunanku gabad'aya ba*.
*Na gode Allah ya saka muku da alheri ya bar zumunci*.

*Godiya ta mussaman ga*
*Haj Rabi Sani madakin Gini*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login