Showing 72001 words to 75000 words out of 148964 words
Chapter 25 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt
rik'e da yaro d'aya, yayin da Hafcy take rik'e da d'ayan.
Aysha na janye da akwatin kayanta, Abida kuma na rik'e da jakar hannunta.
Har ranta ta ji sanyin tarbar da ta samu daga yaran.
A gidan suka tarar da Alti ta yi mata kunun tsamiya da awara mai dad'in gaske.
Ta sake jin dad'i sosai.
Da yamma da yara suka dawo sai ga Farha sun dawo tare. Ita da Noor suka kasa tsaye da zaune wajen ganin jariran. Aka bawa kowa d'aya ta rik'e.
Amal na tsaye tana fad'in "To ku bani nima. Duk suka hana ta, kowacce ta ce "Nata ne."
Bilki ta lallabata tare da fad'in ai su yara ne Adda Amal bar musu, ke za ki dinga goyasu idan ba school."
Ta yi tsalle tare da tafin jin dad'i.
Oga Asad na gefe yana kallonsu, yana jin dad'in yadda ya ga ta warware a cikin yaran.
Sai dai shi bata bude baki ta yi masa magana ba.
Da ya dawo daga masallacin sallar magariba ya tarar Abida ta tafi . Ya shiga dakinta ya zauna k'amshin turaren wuta da freshener din mkbees perfumery ya cika d'akin. Ta yi wanka ta shirya duk wani kumburi ya safe sai dan saura.
Ya tausasa harshe ya ce "Sannu Maigado! Kai ta daga tabbacin ta amsa. Ya had'iye ya ce "Zan je na karbo miki kayan Farha a wajen Momi. Ta dawo zata zauna da mu".
Ta yi shiru. Ya sake maimaitawa
A sanyaya ta ce "Da ka barta dama jira nake yi na samu lafiya sosai zan yi magana da Ansari ya zo ya dauke ta ya rik'e mini ita tunda shine yafi cancantar ya rik'e diyar Sulaiman tunda baba ya danne ni akan na yi hak'uri, na zuba maka ido, ka yi yadda kake so a gidanka".
Hankalinsa ya tashi ganin babu alamun wasa a yanayinta.
Ya matsa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "Haba Maigadona ba magana ta wuce ba, me ya kawo wannan batun da babu dad'in ji a cikinsa? Idan Baba ya ji kin ce haka zai shiga damuwa ne".
Ta yi yake ta ce "Ai kuwa zai ji don Wallahi Momi ba zata rik'e Farha a yanzu da girma ya hau kanta tana buk'atar hutu ba. Diyata ce halak malak, ka ce ba zaka zauna da ita ba, dole kuwa na mikawa dangin ubanta ita a maimakon na takura ta yi zaman sakabu a inda ba dolenta ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:51]
Takaici ya mak'ure shi ya rasa mai zai ce mata. Ya mike ya fice.
Kaitsaye gidansu ya nufa.
A masallacin unguwar ya yi sallar isha Shi da musulamn cikin Yan rakiyarsa.
Tare da Baba suka isa cikin gidan.
Sosai Baba ya yi masa nasiha akan ya rike gaskiya cikin aikinsa sannan ya yi iya kokarinsa wurin kaucewa cin haram. Daga haka ya zarce da nanata masa ya kula da kannensa gabad'aya, ya yi tsayuwar daka wajen gyaruwar zumuntarsu.
A tausashe ya ce "Na gode Baba a cigaba da yi mini addu'a in sha Allah komai zai daidaita. Sannan na zo karɓan kayan Farha ne.".
Baba ya murmusa ya ce "Ka gama gyare gyaren ne?"
Kansa na k'asa ya ce "Eh Baba ".
Ya numfasa ya ce "Zan yarda ta koma gidanka ne bisa sharadin wannan ne karon k'arshe idan ka samu matsala da Bilki ka ce zaka taɓa nata yarinyar nan. Zata jure komai amma ina rantse maka da Allah ba zata jure akan yarinyar nan ba.
Kuma saboda na baka damarkw ta maigida ka yi hukuncin da ya gamsar da kai a gidanka shiyasa na danne maka ita, amma da tuni ta sake fitowa ta bar maka gidan. Komai zaku yi kada ka sake ce wa Farha ta dawo, ka sakata cikin y'ay'anka babu banbanci. Kuma ko yanzu ai ka b'ata al'amarin don kuwa zata sake gasgata baka son Sulaiman, tunda a gabana ta taba fad'in Sulaiman ba Shi da alfarma a wajena da wajenka. Kuma abin da ka mance ba Sulaiman ya bata yarinyar nan ba, Abida ta bata ita. Bilki kuma bata dauki alamrin da ya Shafi Abida da sauki ba, sai kuma aka yi sa'a Sulaiman nata ne uban d'iyar. Ina tabbatar maka idan ka matsa zata iya zubar maka wadannan tagwayen da ka mak'ala su a ranka don ta rayu da Farha kad'ai ".
Murya ba amo ya ce "Baba to ai da tun lokacin ka ankarar da ni hakan ".
Baba ya yi tari ya ce"Da ka zo fad'a mini ai ba shawarata ka nema ba. Hukuncin da ka yanke ka fad'a mini. Ni kuma na ce maka to ne, saboda ni uban Bilkine ba naka ba, kada ka zarge ni da bin bayanta tamkar yadda Sulaiman ya yi mini akan Abida ".
Jikin Asad ya yi sanyi a ransa kuwa kuzawa Sulaiman ashariya yake yi kala kala. A duniya a yanzu ba abin da ya damu ubansu irin rashin ji daga Sulaiman. Babu yadda za'a yi su zauna a gabansa bai yi musu maganar Sulaiman ko ta kannensa ba. A tsukun nan ma abin yafi ta'azzara ainun. Shiyasa jiya Farouku ya ce masa jinin Baba ya hau sosai da suka je asibiti ganin likita.
A ransa ya yi alk'awarin idonsa idon Sulaiman sai ya gaggaura masa maruka Allah bar shi ya cakume shi da fad'a. Amma tabbas sai ya wulakanta shi kamar yadda ya wulakanta Baba don yana ganin babu Baba K'arami tunda da ya san yana raye bai isa ya yi masa hakan ba ko da giyar wake yake sha kuwa."
"*Oh oh ni Surayya da kaina na matsu na ga wannan danbarwar ta Sulaiman da y'anuwansa, matarsa da ma Babansu gabad'aya.😀 Ko yana raye ko ya mace sai Allah sai alkalamina.*"
Oga Asad ya numfasa ya ce "Ka kara hak'uri Baba. Ina ganin ya kamata ka je ka yi umrah ka dan samu nutsuwar zuciya daga nan Sai Ga likita a can. Faruku ya ce 'Idonka ya matsa maka a kwanakin nan, duk Sai ka Ga likita a can".
"Kayya Asad bar batun asibitin nan zan dai je na yi ibada amma kasan da Faruku zan tafi ko?"
Wani irin kishin Faruku ya kama Asad wanda ba shi da alak'a da hassada ko k'yashi. Kawai dai ji yake yi inama dai shine Faruku?
A raunane ya ce "Na sa ni baba da shi za ku tafi har da Abida itama ta je ta tayaka addu'ar Allah ya bayyana wannan yaron da kuka makala shi a ranku alhalin shi ya manta da ku".
Babu kuzari Baba ya ce "Abin da yaoe had'a ni da kai, baka gane girman da ya hau Kanka Yana buk'atar hak'uri da juriya Hadi da kawaici. Abida na son mijinta. Ni muma ina son d'ana to ya za'a yi mu ga farinka idan kana kushe mana shi? Ya ya zaka samu kan Bilki idan ta gane baka damu da dan'uwanta ba? Ka dai dinga lissafi daidai oga Asad".
Dariya ta subuce masa yadda Babana ya ce masa oga. Ya ce "Baba Allah yaran basu da mutunci gabad'ayansu Wallahi! Raininsu ya kai k'urewa haba, haba dan Allah! Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:53]
Baba ya ce "Ina dai yi maka nasiha ka gama girmanka ka ƙara hak'uri ka koyi yafiya da sadaukarwa.".
Daga haka momi ta shigo d'auke da tray din kayan shayi.
Da sauri Asad ya tashi ya karbe ta yana jin dad'in yadda har yau momi take hidimar Babansu da kanta babu gajiya, ba yadda za'a yi ta saka yan aiki su yi mata hidimar Baba.
Sannan har yanzu Baba baya tafiyar kwana ba da ita ba. Ko asibitine matuk'ar zasu bar k'asar nan. Ita da Faruku kam tamkar rigar sawarsa.
Fuska ba walwala ta amsa gaisuwarsa. Baba ya ce "Kayan d'iyar Bilki ya zo karɓa".
Ta d'auke kai ta ce "Ai ni ba dan kai ba Alhaji da tuni na aikawa Ansari ko Saddiqa ita, tunda su dolenta ne ai".
Baba ya yi maza ya ce "Kash amma ban rufe kofar fadar wannan maganar ba ne?"
A tausashe ta ce "Ka yi hak'uri Allah ya bata mini rai dattijo da shi amma idan ya tafka wani abin ko Aysha d'iyarsa ce ta yi a yi mamaki, gabad'aya Faruku ya fishi dad'in kasafi".
Oga Asad ya yi k'asa da kai yana tu'ajjibin yadda fahimtar Bilki da ta momi ta zama iri daya wanda shi a ransa babu wannan tunanin ko kad'an. Gaskiyar magana mata sun iya damalmala magana ba ga yaransu ba, kazalika ba ga manyansu ba, duk haka suke da sakawa maza tension.
Kafin ya ce komai baba ya ce "Kin ji wai umrah zamu tafi daga nan na ga likita".
Tana bude baki ta ce "Allah ya bada lada amma da Faruku zamu tafi"
Oga Asad ya tsinci kansa da fad'in "Ni da Usman aikin damara ya nisanta mu a zuciyarku."
Nan da nan suka ji wani iri soyayyar d'a da mahaifa ya taso musu.
A tausashe Baba ya ce "Asad babu wani d'a da arzikinsa ya yi mana rana ya hana mu kuka irinka. Daga nan har karshen rayuwarmu muna roka maka Ubangiji ya tsare ka ya yiwa dukiya da zuri'arka albarka! Faruku kuwa ya shiga ranmu saboda shine duk cikinku gabad'aya bai taba nisa da mu ba. Haka nan shi wani irin mutum ne da mu kanmu da muka haife shi kunyar mu bata masa muke ki don tsananin biyayya da sadaukarwa. Duk abin da ya gane muna so ya dinga son abin nan kan jiki kan k'arfi, haka nan idan ya gane bama son abu zai taya mu kinsa da dukkan iyawarsa. Ubangiji ya azurta shi da wata irin kyakkwar zuciya da ba kowa yake rabauta da irinta ba. Allah ya yi muku albarka gabad'ayanku".
Murya ba amo Asad ya amsa da fad'in "Ameen Baba Allah ya k'ara muku lafiya da nisan kwana mai albarka."
Daga haka momi ta tashi ta fito masa da akwatin kayan Farha. Ya karba ya yi musu sallama ya dauka da kansa ya fice.
...
Sai bayan goma ya isa gidansa. Ya shiga dakin Bilki ya tarar da Amal Noor tare da Farha sun yi barci akan gadonta. Alti kuma ta shimfida ƙaton bargo a kan kafet tun tana zaune amma jariran kowanne nad'e cikin lallausan bargo suna kwance a gabanta.
Yayin da Bilki ke kan kujera daga gefe tana shan shayi.
A ladabce Alti ta ce "Sannu Alhaji, sannu da dawowa".
Ya amsa a nutse.
Idon Alti ya sanya Bilki yi masa barka da dawowa.
Da kanzagi ya amsa da fad'in "Sannu Maigado ya jikin dai?"
A hankali ta ce "Alhamdulillah".
Ya mayar da hankalinsa kan Alti ya ce "Jarirai a k'asa Alti? Ba zasu takura ba kuwa?"
A ladabce ta ce "Babu komai kafet din ai mai nauyi ne, ga bargo sannan ga nasu bargunan."
" A a Alti wadancan da suka haye gado suka bar nasu a d'akinsu a sauko da su inda kuke. A mayar da jariran kan gado kada su kwashi sanyi".
Da girmamawa Alti ta ce "To Alhaji! Ta mike ta kinkimo Amal, sannan ta ɗauko Farha, Noor da take k'arshen gadon ita ta dauko a k'arshe. Sannan ta mayar da twins kan gado.
Yana kallo har ta kammala shimfida su. Ya ce "sannu Alti. Ko da rana ban son a kwantar da su a k'asa gadajensu na hanya in sha Allah".
"Za'a kiyaye, Allah ya raya su kan sunnah".
Ya ce Ameen na gode".
Ya mike yana fad'in "Bilki zo ki karbo muku maganin da ba'a samu a asibitin ba, an siyo a pharmacy."
Ya fice zuwa falonta ya zauna bayan ya rufo musu k'ofar. Ya ji dad'in ganin yaran a d'akinta suna barci duk da ya fi so su kwanta a d'akinsu amma yasan dokin y'anbiyu ya sanya su kwana a d'akinta. Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:57]
Tsawon lokaci Alti na dakon ta ga Bilki ta tashi amma ko motsi bata yi ba.
A kufule Alti ta ce "Ki ci gaba dai da zubar mini da mutunci a idonsa yana ganin bana fad'a miki gaskiya. A gabana ya kira ki amma ko gezau ba ki yi ba, wai ya ya haka ne gabad'aya kina ta watsi da kyawawan dabiunki ne Haj Bilki?"
Bilki bata ce komai ba ta mik'e ta nufi hanyar fita don amsa k'iransa.
Yana ganin ta fito ya mike ya yi saluting dinta.
Ta wuce shi ta zauna akan kujera.
Ya biyo ta ya zauna a hannun kujerar da take zaune. Hucin tsadadden tureen Boss da nata na weekend suka cakude suka bada k'amshi na ban mamaki.
A tausashe ya ce "Sannu Maigado. Kin shayar da ni mamaki fa. Amma menene hujjarki ta boye mini twins za ki haifa mini?"
Ta yi masa wani irin kallo ta ce "Wai dan na takaita maka zumudi da zak'uwar isowarsu".
Ya ruko hannunta da azama ya ce "A a da kin fad'a mini ai da na yi musu shirin tarba ta mussaman".
Bata ce komai ba haka nan fuskarta ba walwala. Yanzu me kika tsara za ki yi?"
Bata kalle shi ba ta ce kamar me kenan?"
Batun suna nake nufi".
Ta girgiza kai ta ce "Bana taron suna ni".
"Wannan kuwa za'a yi Maigado. Mu samu tagwaye mu kasa yin walimar da za'a ci a sha! A godewa Allah?"
A takaice ta ce "Kullum cikin godiyar Ubangiji muke ai."
Ya yi shiru yana kallonta yayin da ita kuma ta kurawa allon talabijin ido duk da ba a kunne take ba.
Ya nisa yana jin wani iri, a takure yake jinsa a dalilin shariyar da take yi masa.
*Ina iyayen Yara da suke son d'inkunan Yaya mata masu kyau masu zam a jikinsu cif da cif?*
*Tabbas nake da shi akan k'warewarta don haka ku tattara d'inkunan ya'yanku Mata ku bata daga nan ba Zaku sake ko.ka matsalar dinkin yara ba*
*A Kano take amma ana turo Mata daga ko ina*.
08080266674
Ya nisa ya ce ",Ina deciding a bar taron sunan sai upper week sai a yi ranar zagayowar haihuwata wataƙila ma ya yi daidai da ranar da za'a yi mana bikin karin girma"
"To"
Ta fad'a a takaice.
Ya yi shiru don ya tsani wannan shirun da ta gindaya a tsakaninsu.
Duk yadda ya so ta ware su yi hira, bata yi hakan ba. Kan dole suka yi sallama ta tafi d'akinta yayin da ya haye samansa.
Komai na tafiya daidai gidan oga Asad don hatta Hafcy idan ta dawo school tana zuwa ta ga twins Aysha kuwa kullum safiya tana zuwa ta gaida Bilki sannan ta ga tagwaye sai ta koma wajensu.
Kakarsu, uwar Rukayya da k'anwarta Surayya tamkar su hadiye zuciya tsabar bak'in cikin haihuwar maza da Bilki ta yi. Fadi suke yi rabon haihuwarsu ne ya yi sanadin rayuwar Rukayya babu tantama. Tsabagen hada'ma ma sai ta fara da biyu wataƙila ma ibilishiyar Abida ce ta dinga bata magani da allurar da zata haifi y'an biyu tunda ita tana sonta.'
Aysha dai da a yanzu an karya lagonta bata ce uffan ba, haka nan bata jin son yaran kazalika babu kiyayyar yaran a ranta. Amma ta ga Hafcy sosai take son yaran dan har ta fara sauko da su wajensu.
Gagarumin biki aka yi a ranar goma ga watan goma. Ranar da gwamnatin tarayya ta shirya tabbatar da su oga Asad a hukumunce. Sannan a ranar aka yi taron sunan twins hadi da birthday celebration din mai girma oga Asad.
Tsayawa fayyace irin kudin da aka narkar da hidimar bikin zai zama kauyanci amma dai tabbas an yi harkar girma.
Abida da Bilki sun yi gayu mai sunan gayu. Tun safiya har yammaci kaya na garari iri d'aya suke sawa. Aysha ta bisu da ido tana jin Anty Abida yanzu ta samu yadda take so babu Momin da bata so. K'walla fal a idanuwanta a dalilin kallon banza ma bata ta yiwa Anty Abida ba.
Yayin da Surayya da Laura suke d'auke hawaye akai akai na bak'in ciki da alhinin rashin tasu y'aruwar. Ba abin da yake d'agawa Surayya hankali irin yadda Rukayya ta yiwa kanta sanadin rayuwarta, a dalilin ta burge oga Asad ta je ta yi surgery din da ya yi sanadin kaita kushewa. Shekara d'aya tak da mutuwarta ya samo irin macen da yake so, yarinya akanta, sannan mai cikakkiyar halittar da yake so. Yana ta bare bare akanta, tamkar budurwa ya dauka. Ga shi y'ay'a mazan da bai samu ba, tana zuwa ta haifar masa. Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 11:01]
Ita gani take yi sune kad'ai ma suke tuna Rukayya tare da kukan rashinta shi kam shan sharafinsa yake yi da wacce ta fi matarsa k'uruciya. Ta kuma yi amannar duk tsananin son ya'yansa da yake yi yanzu sai yafi son wadannan akan nasu yaran.
Bilki ba juyin da bata yi da Yaya Hamida akan ta zo ta ce taa yi hak'uri ba zata samu zuwa ba, amma tabbas zata zo ta ga tagwaye nan ba da jimawa ba. A zuciyar Hamida kuwa ta kud'iri aniyar zata je, amma sai oga Asad da Baba sun yi tafiya zuwa wata k'asar. Don ba zata iya shiga Abuja bata je ta gaida Baba ba, ita kuma zuwan ne bata son yi, idan kuwa baya nan ai shikenan. Oga Asad kuwa ganinsa ma bata buk'atar yi, mugunta ne da zalunci ya sanya shi makalewa Bilkisu. Ba don Bilki ba, ko hanyar da ya bi ba zata bi ba matuƙar ta sa ni, bare ta je gidansa da ƙafafuwanta mugu mai azabar son kansa. To da ya d'auke ubansa daga cikin gidansu bai ji labarin suna yawo a titi suna neman wanda zai zame musu uba ba. Haka nan da ya yi sanadin b'acewar yayansu bai gansu durk'ushe a gabansa suna neman alfarmar ya zame musu bangon jingina ba. Ko auren Bilki dan dai Baba ne ya d'aura auren sannan Bilkin bata yi turjiya mai yawa ba, ba dan haka ba da ya ga masifar duniya don kuwa sai ta yi masa tijarar da idan ance ma ya kalli y'ay'an Mamin da bai zo ta'aziyarta ba, saboda yana jin haushinta da sunan so ba zai fara ba, ba dan Baba ba na da rai ba, sai ta maka shi a kotu don a nemawa Maminsu hak'kinta, akan me ya washeta! Amma zai aurar mata d'iya yana amfanar kuruciyarta? Alhalin ko ita ba sa'an aurenta ba ne bare Bilki. Ya ga halitta iya halitta shine ya shiga ya fita tare da taimakon ubansa da y'anuwansa masu son zuciya ya aure ta.
Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:37]
*Surayya Gwaram*
*Wannan littafin na kudine*
*Pay 1k via