Showing 81001 words to 84000 words out of 148964 words
Chapter 28 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt
tamkar ba ranar aiki ba. Tun goma kuma twins suke wajensa.
Wayar Bilki ya dinga k'ira tunda ta ga shine take biris har sai da hankalin Alti ya kai kan kiran da yake shigowa. Ta ce "Mahmah duba ana ta miki waya ko Alhaji ne ga kukan Baba Babba Ina dan jiyowa." Bilki ta ce kunnenki ne Alti, ni ban ji ba".
"To amsa k'iran dai".
Dole ta amsa. Tana dauka cikin sigar umarni ya ce "Ki zo yanzun nan".
Takaici tamkar ta yi ta zunduma ihu.
Kan dole ta tashi ta nufi samansa tana jin idanuwan Alti na takura mata ba don kada ta dinga jin babu dad'i a ranta tare da jin bata isa da ita ba da ba zata je k'iran nasa ba.
Tana isa ta tarar kuwa baba Babba ke kuka sai dai kukan ya ragu ba kamar dazu ba.
Ya sassauta ya ce "Zo ki zauna. Bata musa ba ta zauna din. Ya dad'e yana kallonta. Ta gama sacewa duk wani kumburi ya sace ta yi kyau sosai hannuwanta d'auke da kalle mai ban sha'awa ga kuma zobunan gold suka sake kawata yatsun nata.
Ya nisa ya ce "Maigadona da alamu dai kin kwashe kayan rankatakaf a gaban ma'aikin Allah!.
Ta kawar da fuskarta gefe yaune zai ce Maigado. Kwanakin baya ai Bilki ya dinga cewa gatsal wanda Har zuciyarta ta ji wani iri tunda tun filazal baya ce mata Bilki. Amma saboda ya so k'ank'anci ya dinga fad'in gayan sunan nata".
Ya sassauta ya ce "Amsa mana sarauniyar shaiba ke dad'ina da ke rashin wayo".
Ta sake matsewa ta ce "Na'am ".
Ya nisa ya ce "D'akina ne ya yi kura sosai, da kanki nake son ki gyara mini mussaman shimfida gadon nan".
Nan da nan ta gane jirwayen nasa ya gaji da fishin don yana da bukatarta.
Ta jijjiga kai lallai kuwa zasu sake hawa sama don kuwa ba zata taba yarda ta kwanta akan gadon da aka girke hoton wata mace a gefensa ba ".
Ta mike ta ce "Bari na gyara maka ".
Ya yi maza ya ce "To zauna ki ba shi ya sha ban son idan kin fara gyara shimfidar ya katse ki da kuka".
Kaitsaye ta ce "Ai tuni bana Basu nono Sai Madara tunda ka ce baka san alherina ba, na daina basu Sai Idan Alti ta matsa, tunda shari'a ma ta ce idan ba zan iya ba, ka nemo wata ta shayar da su ka dinga biya ".
Ya yi sakare yana kallonta. Tabbas akwai matsala babu tantama Hamida and co sun yi tasiri a cikin gidansa.
Ya had'iye fishinsa ya ce "Na janye kalamaina. Dan Allah ki yi hak'uri, kada ki yi mini haka mana".
Ta yi shiru.
"Pls Maigado kin ga dai fiye da watanni biyu rabonmu da juna. Tsakanina da Allah na gaji hakanan, sannan bana son mu sake samun matsala da ke. Dan Allah kada ki gwada ni ta nan, akansu zan iya haduwa da hawan jini tsakanina da Allah. To ban da ma abinki, alherinki ai na daban ne, twins fa kika haifo mini sannan ke ce kika haifa mini boys din da ba ni da su, don kuma raina ya b'aci na yi subutul kalam sai ya zama kin manta komai".
Ta numfasa ta ce "To shikenan amma ka zaba ko dai na shayar maka da su ko na gyara maka shimfidar."
Ya yi shiru ya ce "Duka biyun nake so Maigado".
Ta kwakkwabe fuska har k'walla sun cika idon ta ce "Wallahi d'aya zaka zaba".
Ya yi kalar tausayi can ya nisa ya ce "Na hak'ura ki shayar da su sarauniyar shaiba".
Ta mik'a masa hannu akan ya bata yaron. Bai ce komai ba ya mik'a mata. Ta gyara ta fara shayar da shi, yayin da ya tsura mata ido yana ganin yadda ta zarta yaron hasken fata. Sosia suka yi masa kyau. Ya shiga tashin Baba K'arami don shima ya sha.
Har zata yi magana sai kuma ta k'yale shi. Sai da yaron ya k'oshi dan kansa. Sannan ta saka shi a kafaɗa ya yi gyatsa. Ta kwantar da shi a gefenta. Shi kuma ya yi maza ya mik'a mata Baba k'arami ta karɓa babu musu ta shiga shayar da shi. Shima sai da ta saka ya yi gyatsa sannan ta kwantar da shi kusa da d'anuwansa ta mike ta ce "Sai anjima".
Ya kasa cewa uffan, illa ido da ya bita da shi har ta bacewa ganinsa. A zuciyarta kuma ta kud'ire Wallahi indai a d'akinsa zata kwanta to kuwa sai idan babu hotunan maimurabus duk sababinsa kuwa.
Ya numfasa a fili ya ce "Yadda na shaida musulunci gaskiya ne, haka na shaida mata ja'iran halittu ne masu tsiyatakun da suke gigita mazaje. Mata da manta alheri suke. Ka ciyar da su safe, rana, dare cimuka kuma gwargwadon k'arfin arzikinka, haka suturar ma, mazaje su sha wahalar gina gida su saka mataye a ciki har a koma fad'in gidansu, su kula da lafiyarsu amma idan ka kuskure musu sai su manta komai na alherin namiji har su iya bude baki su ce me ake yi musu? Ai ciyarwa da tufatarwa ba alfarma ba ne wajibine hak'kinsu da ya rataya aka sauke.
Mata da butulci suke shiyasa Annabi ya ce butulcin mace ne ya sanya suka fi yawa a wuta.
Ya nisa ya ce "Allah ka shirya mana wadannan karkattatun halittum tunda ka jarrabe mu da sonsu. Duk wahalarmu akansu ce amma gabad'aya sun rantse idanuwansu sun mayar da maza abokan hamayyarsu".🤣
Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:52]
*Surayya Gwaram*
*Wannan littafin na kudine*
*Pay 1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.
08032773332.
*Don samun damar karantawa cikin aminci a telegram*.
*Teemah data service mtn monthly*
*1gb @550*
*2gb @950*
*3gb @1450*
*5gb @1700*
*Dm 08112392177*
*Call 8037026306 Fatima Musa Ibrahim opay*
*For your beautiful kids wears:tees,shorts,trousers,dresses,kids towels, perfumes,body mist contact 08067239846*
*Saudiyya.*
Tunda Abida ta ga Sule ya yi d'iban karan mahaukaciya da ita sai ta yi maza ta kame kanta. Tsakaninta da shi ina kwana, ko ina yini idan ya zo duba Baba.
Gabad'aya sai ta canja salon addu'ar ta. Tunda ta yi imani addu'ar kiranyen da ta dinga buga masa ne ta karbu sai ta koma buga masa ta a jarrabe shi a kanta fiye da yadda aka jarrabe ta a bayan ya bace mata. Ta yi dawafi akan kada ta wulakanta a hannunsa ba adadi. Tana kammala dawafin kuwa zata yi ta buga nafila tana kama sunansa a sujjuda akan a cika zuciyarsa da tausayinta da zai hana shi matsa mata. A kuma cika k'irjinsa soyayyarta da zata hana shi jarumtar damfara ta da k'asa.
Sai ta yi addu'a ta jero sunansa har kan ubansa na biyar.
Duk sadda ta gan shi ta ga ya dauke kai itama sai ta kwafse a ranta kuwa tana fad'in "Da ni kake zancen Malam Sule dan Uzairu. Babzai yiwu ka tafi ka bar ni shekaru uku da watanni sannan yanzu na yarda da wani nau'in wulakanci ba. Duk sababinka da zarar na koma d'akina Sai mu fafata don kuwa ba yarda zan yi na bayyana maka soyayyarka da take k'irjina ba bare ka samu Dama a kaina ".
Sulaiman.
Yana kwance shi kad'ai a d'akinsa ya yi shiru yana tunanin yadda zai bi su Baba Nigeria a jibi.
Zuciyarsa sai harbawa take yi a dalilin yadda al'amura masu nauyi suka dabaibaye shi.
Ya rasa me yasa yake yawan jin fad'uwar gaba matuƙar ya d'ora idanuwansa akan Abida.
Bai zaci sonta na da k'arfi a zuciyarsa ba har yanzu. Ba sonta ya daina ba dama, amma dai ya yi raunin da yake jin zai rabu da ita, rabuwa ta har abada kuwa. Don bai yi lalacewar da zata zagi uwarsa ya kuma tsaya rarrashinta ba. Bayan haka ta cire ciki nisa hujjar ba zata sake had'a jini da shi ba. Duk kuma aka zuba mata ido saboda sahaffafiya ce y'ar Madara.
Ya juya yana tuno siradin da ya tsallake wanda bai samu kansa ba sai shekara d'aya da ta shud'e.
Tunda ya bar Nigeria ya isa Germany kwanansa biyu kacal gwamnatin k'asar ta kama shi tare da wasu bakaken fata su uku bisa zargin suna kai yara mata k'ananu karuwanci k'asar ba bisa k'aida ba.
Birinin Barlin ya sauka. Ya yi niyyar ya dan yi kwanaki biyu kafin ya wuce birin Hermburg.
Da aka tsananta bincike sai aka sake jingina masa laifin ya shiga k'asar ne ta haramtacciyar hanya. Ya yi kokarin nuna shaidarsa amma ya nemi passport d'insa sama ko k'asa ya rasa.
Wanda ba shi da laifi ko kad'an illa mugayen mutanen da suke aikata laifin sun had'a wurin zama a jirgi da shi. Da aka kamasu ne don tsananin k'eta da mugunta suka ce tafiyarsu d'aya da shi.
Haka aka tattrata aka kai su prison. Ba'a waiwaiye su ba sai da suka shafe watanni goma sha uku. Bisa hujjar da embassy ta gabatar basu shiga k'asar legally ba don haka ba zasu bibiye su ba. Sa'a daya ma kurkukun ba irin namu ba ne. Amma dai kam nadama da kaicon barin gida Sulaiman ya yi shi yafi cikin kwando.
Kan dole ya hak'ura ya koma ga Allah ya dinga Ibada tukuru. Amma gabad'aya ya gigice da tunanin makomarsa. Idan ya mutu a wajen nan shikenan ba wanda zai san ya mutu. Idan ya tuna Bilki, Baba da Farha sai ya sake rikicewa k'warai da gaske su kad'ai ne idan ya tuna su ya kan ji rauni na kama shi.
Yana cikin haka kwatsam tawagar likitoci da hadakar kungiyoyin jin k'ai daban daban suka kai ziyara gidan yari. Nan ya ci karo da babban malaminsa kuma ogan asibitin da ya yi aiki da su shekarun baya.
Da madaukakin mamaki yake tambayar Sulaiman ba'asin zamansa.
Tiryan tiryan Sulaiman ya yi masa bayanin azal din da ya fad'a ya nuna wanda yake sanye da irin kayansa ya ce "Ga masu laifin nan daga k'asar Alge suke. Sune da alhakin komai." Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:59]
Gabad'aya aka kamu da tausayinsa don kuwa hatta b'acewar passport d'insa sune suka cire masa a ƙaramar jakarsa bayan sun isa masaukinsu a ranar da suka sauka a birinin Berlin.
Sai da suka ga sun dade a gidan suke neman afuwarsa tare da ba shi hak'uri wanda ya zama na banza.
Gabad'aya wajen duk jikinsu ya yi sanyi tare da tausayin Sulaiman k'warai da gaske.
Haka wannan Malamin da sauran kungiyoyin suka shiga al'amarin Sulaiman bayan an kai komo mai yawa sannan ya shaki iskar y'anci bayan watanni biyu. Idan an fahimta Sulaiman ya shafe watanni sha biyar a gidan yari a babban birinin k'asar Jamus.
Da ya fito yana k'arkashin kulawar hukumar jami'iar da ya yi karatu da taimakon kungiyoyin sa kai. A haka dai har kes d'insa ya kai gaban mahukuntar k'asar da taimakon ofishin jakadancin Nigeria a k'asar. Watanni biyu da fitowarsa ya samu aka yi masa passport din da zai iya barin k'asar sannan gwamnatin k'asar ta ba shi makudan mahaukanta kudade don ya rage radadin bata masa lokaci da aka yi ba bisa hakkinsa ba. A lokacin ya so barin k'asar amma malaminsa ya hana shi, ya saka ya koma makaranta don ya sake kwarewa a b'angaren ido wanda zai yi kwas na watanni goma sha biyar. Gabad'aya nadama da danasani sun masa k'awanya. Ya tabbatar hakkkin barin Baba Babba a halin jinya ba tare da ya yi masa sallama ba, bare ya saka masa albarka ne ya sanya ya hadu da taskun duniya. A dole ya zauna yake karatun nan.
Ya kammala karatun cikin nasara, da ya ce zai tafi gida shine aka tura shi aiki asibitin k'asar Jamus da ke Birnin Riyadh, da nufin Idan ya fara aikin a hankali Sai ya je ya Ga iyalinsa. Watansa shida aka dawo da asibitin da yake birinin Makka. A yanzu watansa biyu a birinin Makka.
Zuwa lokacin hankalinsa ya karkata matuk'a da son komawa gida don ya murmure ba wanda zai gan shi a tagayyare, kud'i kuwa ya yi shi ba na wasa ba. Yana yawan tuna Baba dasu Hamida.
Bilki kuwa yana da labarinta Hatta ajiye aikin da ta yi ya ji, da barinta Katsina ta bakin abokinsa Salim Buba wanda sanadinsa ya samar mata aiki a UmYU. Wanda ya samu lambarsa a Facebook ne bayan ya fito da gidan yari.
Sai dai bai ji labarin auren da ta yi ba.
K'arshen wata dama ya yi booking din tafiya Nigeria sai kuma suka yi kicibis da shi a tsakiyar wata.
Ya juya ya numfasa wato ba k'aramin nauyi da kunyar Baba ne suke yi masa rubdugu ba. Zai bi shi Nigeria zai kuma karbi dukkan sharuddan da zai gindaya masa, amma kam bai huce da Asad da Abida ba.
Yana kwance yana hakaito ta, tabbas har yanzu bai ji ya tsane ta ba, amma kuma a shirye yake da ya rabu da ita don kuwa uwarsa tafi komai a wajensa. Matar da yake aure kuwa ta yi kad'an ta rainata ko ta fadi maganganun banza akanta ta kuma kwashe k'alau. Har a bayan ranta tana da alfarma matuƙar yana shakar numfashi.
A yadda kuma yake ganin take takenta tanan nan da sauran zafin kanta, bai gama goge mata hadda ba. Ya nisa a fili ya ce "Da sauran ki kuwa, da sannu za ki gane na kerewa duk wasu tsiyatakunki."
*Abuja*
Bilki na zaune a d'akinta k'arfe shabiyun dare tana bawa Baba K'arami nono. Alti na zaune tana jiran ta gama ba shi ta mik'a mata Shi tunda ita take barci da su.
Kira Sai shigowa wayarta yake yi ba kakkautawa. Ta Kuma san oga ne.
Kan dole ta amsa k'iran.urya ba amo ya ce "Ki kawo mini shayi yanzu."
Daga haka ya katse wayar.
Har d'aya saura kwata bata tashi ba, ita kuma Alti bata san komai ba. Amma ita da kanta tana ganin tunda Bilki ta fara sallah tuntuni ya kamata ta koma turaka mussaman da ta ga sati biyu da suka suka wuce an kawo mata kayan mata na mussaman daga Kano na Bojuwa herbals 08032773332.
Ita ce ma ta dumama mata kazar da ta iso da sanyinta tunda idan wani garin za'a tura sai an yi freezing dinta ta zama kankara sosai gudun kada ta lalace ko ta yi tsami. Haka na matsi duk ta kammala amfani da su da taimakon Alti da take tafasa mata., Sanyi flusher kuwa tun dadewa aka kawo ta sh na sati biyu. Amma duk wannan gyaran da take yi bata ga tana zuwa wajen miji ba. Shiyasa yake yini da kwana yana zarya tsakanin samansa da na Bilki wanda Alti take jin kunyar hakan k'warai da gaske. Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:00]
Cikin rarrashi da girmamawa ta yiwa Bilki magana da ta ga wayar da ta amsa don tasan ba mai k'iranta a daren sai shi.
"Mahmah gaskiya fishin ya isa indai ba so kike na bar miki gidan ba. Yini yake yi yana son ya faranta miki, magana d'aya tak idan kika yi masa kamar an masa bushara da gidan aljanna don zumudi amma sai tumbatsa kike sake yi kullum. Idan fa kika koya masa jurewa fishinki ke ce a ciki. Haka nan irinsu Alhaji fa da kud'i da ilimi ya zauna musu har ofis dinsu ake kai musu mata da suka kai mata. So kike sai ya fad'a tarkon shaidan ne. Haba abin ya yi yawa fa gaskiyar magana. Ki tashi ki sake wanka ki tafi dakin mijinki."
Da rawar murya ta ce "Allah Alti nima ina son na huce amma gaskiya ba zan je d'akinsa irin zuwan da kike nufi ba, kowacce kusurwa fa hotonsa da na matarsa ce. Ya je na barwa hoton shi. Kuma fa abu kad'an sau ya ce ita ba haka take yi masa ba, ita mai biyyaya ce" .
Ta fara kuka sosai.
Alti ta yi sakare tana mamakin Kishin da take ganinsa har a idanuwanta. Wanda ita kam bata ga ta yi kishin Hawwah irin haka ba.
A fili ta ce "Tirk'ashi. To ban da abinki Mahma ba sai ki fad'a masa a hankali cewar ba kya so ya daina ba, sannan da kin iya AI da tuni an cire hotunan daga dakin ya dawo da su dakin y'ay'anta".
Ta girgiza kai ta ce "Da Dai yana sona ne zai yi hakan, nima ai mun yi hotunan da suka fi nata kyau ma amma bai girke su ba , saboda baya sona".
Hawaye ya sake k'wace mata.
Alti ta numfasa tare da fad'in "ko makaho ya zauna da ku yasan yana sonki mana, ki yi hak'uri, ki kwantar da hankalinki da sannu za ki mayar da shi irin yadda kike son ya zama. Amma wannan fishin da kauracewar da kike yi masa nisanta kanki kike yi a zuciyarsa fa".
Daidai lokacin k'iran ya sake shigowa bata amsa ba suka ji an yi knocking k'ofar sau d'aya.
Kan dole ta bawa Alti yaron ta d'auki hijab ta saka sannan ta fita.
A bakin k'ofar ta gan shi. Ya saka hannu ya ruko nata hannun. Bai ce komai ba, itama bata ce komai ba, tiryan tiryan har samansa.
A falo ta turje ta ce "Bari na hado maka shayin".
Ya girgiza kai tare da fad'in "Ke nake bukata ba shayi ba, tunda ke ba kya gane al'amura sai an bayyana miki".
Ta bata fuska ta ce " To zo mu je wajena".
Da hanzari ya ce "Alti ta nan ga yara nan kin dawo da su kwana wajen ki, shine nima zan je cikinsu na kwanta?"
"D'akina guda nawa ne?"
Ta tambaye shi idonta a cikin nasa.
Ya juyar da kai ya ce "Ina ce d'aya d'akin su Amal ke kwana a ciki?"
Ta ce "To d'ayan fa na kusa da shi?"
Kaitsaye ya ce "Amma dai kinsan zasu iya jina tunda bana iya kama bakina idan ina tare da ke ko?"
Ta ce "Sai ka fara rikewa ko na samo salatif na manne maka shi".
Ya zuba mata ido baya son ya tunzura tunda a matse yake. Kan dole ya kwantar da kansa cikin rarrashi ya ce "Tunda fa kika zo gidan nan sau uku tak kika kwana mini kullum ni nake bin ki. Tunda yanzu gun na ki da mutane ya kamata ki mutunta ni ki dinga zuwa mini, ta ya ya zan yi ta jele a gaban yara da masu aiki fisabidillahi fa Maigado?"
Ta cuna baki tare da juyar da fuska gefe. Ta kasa bude baki ta ce masa hotunan matarsa ne ba zasu bari ta iya kwna ba.
Ganin tana tsaye ba alamun zata yi masa yadda yake so ya sanyaa shi fad'in"Shikenan