Showing 66001 words to 69000 words out of 148964 words

Chapter 23 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

a gidan da kake ƙirarin naka ne. Kuma Wallahi ba dan ina tsoron kada ka kawo wata bane zai hana na fice na bar maka gidan ba. Kunyar Baba ta sanya zan cigaba da zama a cikinsa har zuwa lokacin da zaka gama bayyana dukkan manufarka a kaina".
Ta yunk'ura ta mike. , kai tsaye bayi ta shiga don gabad'aya zufa ke yanko mata ta tashin hankali. So take ta ba shi hak'uri amma tunda ya kawo maganar Rukayya a muhallin da bai shafe ta ba to ba zata ba shi hak'urin ba. Zata yi hak'uri har zuwa ta haihu lafiya ya ga kalar tata tsiyar..
Shower ta sakarwa kanta. Mintina biyar sannan ta tsane jikinta ta fito. Yana zaune inda ta bar shi. Yayin da isa gaban wadirof ta bude ta jima tana nazarin kayan da zata sanya wanda bai da nauyi. Can ta hango riga da wando irin na Pakistan din nan masu taushi da tsada. Ta dauko ta saka bayan ta fesa spray din oriflame na lame skin care. For your order contact Aisha 07036662633.
Ta sake fesa turarenta na weekend.
Kaitsaye ta fice zuwa kicin dinta na da yake falon nata na samanta. Kulikulin Ummiel foods ta dauko ta juye shi a plate din ralzapalace08109544470.
Tana mamakin sabuwar ledar da aka canja masa ga kuma tambarin Nafdac a jiki. Yadda yake da d'adi ya kuma karbu a cikin kasar nan da wajenta dole Nafdac tasan da shi mussaman da ake samunsa a store daban daban a cikin Kano da Abuja.
Kulikulin Ummiel foods yafi kilishi dad'i ku siyawa kanku da iyayenku da aka hana su cin nama tabbas zai kashe musu kwadayi.
08036355535
For your order.
Ta bude firij ta dauko fresh milk ta zuba a glass cup sannan ta fito ta dawo falo ta zauna tana ci tana duba wayarta.
Amma gabad'aya bata gane komai. Duk d'adin kulikulin nan a yau taunawa take yi kawai. Haka fresh milk din ma bata jin dad'insa a baki.
Sakin da Sahal ya yi Mata ya yi mugun bugunta a dalilin ya zo Mata a bazata sannan yadd6ua ce don iyayenki masu son zuciya ya yi mata tsauri k'warai da gaske. Amma a yau hukuncin rabata da Farha ya buge ta fiye da sakin.
Hawaye ya dinga silalo mata. Ta kasa jurewa ta lalubo lambar Baba.

Bugu d'aya ya dauka bai yi mamaki ba don kuwa yasan za'a sha artabu da ita.
"Ya ya ne Bilkisu?"
Ya tambaye ta cikin kulawa.
"Baba ka fad'a masa sakon da na faɗa maka na cewa da Farha da Alti zan je gidansa?"
Ta fad'a cikin shesshekar kuka.
A sanyaye ya ce "Na fad'a masa, ya ce kuma ya amince. Amma ranar da na yi masa ba dadi akan lamarinki da yadda ya zuba ido tarbiyar y'ay'ansa ta lalace ya bani hakuri tare da alk'awarin zai gyara, zai kuma yi garanbawul a gidan. Ya roke ni arzikin na rik'e miki Farha har zuwa lokacin da zai kammala gyare gyaren da zai yi a gidan ".
Ta yi shiru.
Ta nisa ta ce "Ka amsa masa ka amince da wannan batun nasa Baba? D'iyar da aka bani ita tun bata zo duniya da shekeru sama da goma ne zai yanke ta a jikina? Sahal da ba ni da alakar jini da shi ya zauna da ita cikin adalci sai shine zai ce ba zai rik'e ni da ita ba, alhalin sai da na ce a faɗa masa da ita zan zo masa, ya amince da hakan. Baba ni kam gaskiya wannan hukuncin ya yi mini tsananin gaske tsakanina da Allah ba dan kai ba, da na yi rikicin da kowa zai san an taɓa ni.".
Baba ya nisa ya ce "Na gode da kika hango ni, yanzu ki saurare ni da kyau. Ai ya ce mini ya baki Bilkisu, Amal da Noor to yanzu ki jasu a jikinki irin yadda kike yi da Farha suma y'ay'an ki ne kin ji Maigado.".
Ta kasa cewa komai don kuwa bata taba ganin mutum irin Asad mai son kansa ba. Shi dai a yi masa yadda yake so ba ruwansa da damuwar wani, tun tana k'arama ya dasa mata k'insa saboda azabarsa shine har yanzu ba zai shafa mata lafiya da takurarsa ba?
Cikin kuka ta ce "Baba yanzu shikenan an raba ni da ita? Ni kad'ai nasan yadda nake ji a zuciyata da tunanin y'anuwanta na Katsina. Ban gama warkewa da rashinsu ba sai a sake raba ni da ita kuma duk a zuba ido ana kallo?" Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:25]
Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali.
A sukwane ya ce "Zata dawo fa, ya ce yana gyare gyare ne. Ki yi hak'uri mu ba shi nan da ki haihu, idan bai yi magana ba, zan shiga maganar a lokacin. Kin ga mu maza bama son a zo a yi mana hukunci a gidanmu. Ki yi hak'uri, ki zuba ido ki ga iyakacin gudun ruwansa. Tunda ya ce ba dama ya baki umarni ki ce to kaitsaye sai ya yi fama da ke".
Ta kasa cewa komai wato dai Asad mugune lamba d'aya. Sai da ya gama fadan laifukanta sannan ya yaudareta ta bishi a gabansu. K'arshen tozarci da muzanci ya yi mata. Ba kuma komai bane ya sanya ya yi Hakan ba saboda Yana ganin ita nympho ce. To kuwa zata ba shi mamaki.
Matuk'ar ita mace ce yadda ya gurfana gurfana gaban Baba ya ce a bawa Momi rik'on Farha, da kansa zai sake gurfana akan ya je d'auko ta. Shine da kansa zai dauko ta ya kawo mata ita ba waninsa ba.
Ta had'iye kukan ta ce "To Baba."
Ya dinga sanya mata albarka da fatan Allah ya sauke ta lafiya.
Ta ajiye wayar tana mai tsurawa cikinta da ya yi tsiri ido. Lah shakka wannan ciki ya yi mata shigar sauri, k'addararsa ne ya sanya ta auren Asad.
Gabad'aya ta ji duniyar ta yi mata zafi tunaninta ya kulle. Ba wacce take so ta faɗawa wannan matsalar Sai Abida. Amma kuma Duk yadda Abida bata jingina Farha gare ta hakan ba zai kore itace ta haife ta ba. Bayan haka ta sani bayan baba da Momi Abida bata so wani kamar Asad a gidansu ba. Ta tuna a ranar da suka kammala Fgc Bakori. A ranar da ta yi alkawarin bata abin da zata fara haifa ta ce ina sonki Bilki fiye da Yaya Faruku da yaya Munnira. Ita kuma ta ce so nake ki soni fiye da Yaya Asad. Amsar da ta bata shine ba zan miki karya ba Maigado don kuwa ban so wani a cikinmu kamar Yaya Asad ba.
Ta zukar da fuskar b'acin rai tana hakaito yadda shima baya iya karar daidaita su a lokacin da suke yara, sai da suka zama y'anmata ne da ya fara sonta shine yake nuna equal suke har ma ya fara dank'a mata abu idan zai basu tare a maimakon ya bawa Abida yadda ya saba.
Yaya Faruku ne da Munira basu taba nuna mata Abida ta fisu asalima Munira bata shiri da Abida ne a dalilin yadda take takura mata. Haka ma Yaya Faruku.
Amma Asad kam dama tun can mai son kai ne na gaske yanzune take sake fahimtar haka tunda da ya daina banbantasu ma ai jarrabarsa aka yi da sonta ba dan haka ba, ba zai daina ba.

Yanzu kuma lah shakka ta sani laifin Sulaiman ya jingine Abida har tana kukan nemansa ne ya sanya shi hucewa akan y'ar da bata san shi ba.
Ya manta ba Sulaiman ne ya bata Farha ba Abida ce.
Kuma ko da ba Sulaiman ne ubanta ba, zata so ta, zata yi mata riko na amana sannan a bakinta dai wani ba zai ji ta furta ba ita ta haife ta ba. Sai kuma aka yi sa'a irin na gam da katar Sulaiman ne ubanta. Yadda yake jin yana son Abida haka take sonsa, haka nan yadda yake jin yana son ya'yansa fiye da haka take sonta don idan ta ce tafi jin yarinya a ranta fiye da su Amra ba k'arya ta fad'a ba. Duk tijararsa matuƙar zata amsa sunan matarsa to sai ya zauna da Farha, ko baya so kuwa.
Ta janye tunanin faɗawa Abida wannan badakalar don kuwa tasan ko ya ya sai ta ji babu dad'i. A dalilinta kuwa ba zata so su sami sabani ba.
Kaitsaye ta kira Faruku. Ta daure ta had'iye kukanta.
Ta yi masa bayanin halin da ake ciki.
Yana bude baki ya ce "Ki yi hakuri Momi zata rik'e miki ita, kuma ma ba kwaanan za ki haifi wata ko wani ba?"
Ta ce "A a Yaya Faruku kafin na haifi wannan din da kake maganar zan haifa, ai ina da wasu. Amma kuma dukkansu ba zasu maye mini gurbin Farha ba".
"Bilkisu ki yi hakuri mu zuba masa ido kin ji".
Ta kasa cewa komai.
Ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta, tare da bata labarin yadda yau Aysha ta dinga kukan a ba shi hak'uri. Ki bi shi a hankali ya gamsu ya isa da ke, da kaina zan kawo miki ita. Don hankalinki ya kwanta ya sanya na d'aukar miki Alti. Idan komai ya daidaita zasu dawo kin ji Maigado ". Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:27]
A sanyaye ta ce "To Yaya Faruku na gode. Amma fa gaskiyar magana raina ya b'aci da wannan abin da ya yi mini, kuma Wallahi darajar baba da k'imar ka ya sanya zan yi shiru na zuba idon na ga ni din. Amma ba dan haka ba da mun yi tawarwatse a yau din nan".
Ya ce "Na gode miki Maigado ai tunda kika yi sa'a kina jin maganar manyanki ko bata yi miki dad'i ba komai zai daidaita miki sannu a hankali."
Daga haka suka yi sallama.
Daidai lokacin ya fito daga dakin nata.
Ya kalle ta ya ce "Kin gama buge bugen waya kina kai k'arar a tursasani na zauna da waɗanda bana son zama da su ne?"
Uffan bata ce masa ba. Ya gama tsayuwar jiran ta tanka. Amma tsawon lokaci bai ji ta ce uffan
ba.

*Contact*
*Deenah cakes and more -Kano*
*09038055790*
*IG @Deenah cakes and more *
*For all your*
Snacks such as :
*Birthday cakes*
*Cupcakes*
*Samosa*
*Springrolls*
*Meatpie*
*Frozen snacks*
*Event snacks*
*Pls Patronize my daughter*.
Ya ce "Ai tunda rashin kunya ne makamanki sannu sannu zan bi na karairayesu."
Still bata ce komai ba illah ido da ta zuba masa babu kiftawa.
Ya tsargu da kallon da take binsa da shi. Don ya ga ta zama wata iri. Don haka ya had'iye maganarsa ya hau samansa.
Ba jimawa ya fito sanye da kakinsa hakan ya tabbatar mata office zai wuce.
Kwanaki suna ta shud'ewa Bilkisu ta dank'ware ranta. Tsawon sati kenan da ta shata layi da mijinta. Tsakaninta da shi gaisuwar safe bayan haka bata sake bude baki ta yi masa magana. Ta koma yanayin shirun da tun filazal yake fad'in ya yi masa yawa. Ta k'i bari ya kebe da ita, Idan ya matsa sai ta fara kukan ciwon ciki, kuka kuwa mai tsananin gaske. Haka ya hak'ura ya zuba mata ido. Bilkisu Amal da Noor suna tare da ita ko da yaushe, sai dai ita din bata da walwala. Haka Aysha da Hafcy sun ajiye shakiyancinsu da kaso tamanin cikin dari. Kawai hawa samanta su zauna ne basa yi. Amma suna gaishe ta cikin mutunci..
Yanayin da ta koma ya damu oga Asad k'warai da gaske.
Haka suke tafiya har aka shafe kwanakin wata.
Ranar da ta cika kwanaki talatim da dawowarta gidan tura ta kai bango ya kusance ta a dole wanda babu armashi a had'uwar ko kad'an k'arshe sai da kuka aka kammala.
Daga bisani kuma ciwon cikin da take karya da shi kullu yaumin ya taso mata haikan.
A gigice ya shirya ta sannan Shima ya kinsta ya sunkuceta zuwa mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja motar da kansa ya fice. Y'ansanda da suke tsaronsa suka bisi a mota d'aya. Kaitsaye asibiti kai zaman kansa() da take awo ya nufa da ita.
Nan da nan kwararrun likitoci suka rufa a kanta.
Shud'ewar awa guda, sannan likitar da ta jagoranci dub Baki ta fito zuwa ofishinta. Asad ya bita.
Da girmamawa take yi masa bayanin halin da Bilki ke ciki. "Oga jininta ya hau fiye da kima sannan yaran a zaune suke Wanda ba'a son Hakan".
Da yake a rude yake sai bai fahimci kalmar jimillar yaran da aka yi ba.
Murya ba amo ya ce "Yanzu ya za'a yi ne, bana son ta samu matsala Dr. Last year na rasa first wife d'ina bana son na sake rasa wannan!
Dr ta numfasa ta ce "Dole zamu rik'e ta on bed rest don gaskiya tana buk'atar hutu da nutsuwar zuciya. Bayan haka kuma zamu dinga duba yanayin zaman cikinta har zuwa komai ya daidaita don idan ba a bata kulawa ta mussaman zata iya haihuwa a yanzu wanda da sauran lokaci a k'aida. Ka yi hak'uri zamu rik'e ta har zuwa ta fita daga had'arin da suke ciki ita da abin da yake cikinta.
Hankalinsa ya dungunzuma ya tashi tare da k'alubalantar kansa me yasa ya yi mata batun da shine sanadin da janye dukkan walwalarta? Me yasa yau ya matsa mata alhalin da gaske bata son ya kusance ta? Gabad'aya ya ji so yake ya fita da ita zuwa UK don lafiyarta da ta babynsu ta tsira.
Haka ya kwana da ita tana kwance ana kara mata ruwa bata san inda kanta yake ba.
Sai washegari sassafe ya buga ya faɗawa Momi sannan ya k'ira Faruku ya sanar masa a asibiti suka kwana.
Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:05]
*Surayya Dee*
08032773332

Daidai lokacin Jamilan
Faruku ta iso tare da Alti d'auke kwandon da abinci.
Sai kusan azahar Abida ta mayar da Baba da Momi gida.
Yayin da aka yanke shawarar Abida da Alti su kwana da ita.
Da yammaci direba ya kawo su Aysha dukkansu suka dubata.
Daidai lokacin Abida ta dawo tare da Farha da junior akan Yaya Faruku zai juya da su tare da matarsa.
Farha ta kalli Bilki da take kwance tana barci .
A fili ta ce "Allah na gode maka da Mahmah ba guduwa mini ta yi ba kamar yadda muka guduwo su Yaya ba."
Asad da yake gefe ya ji wani irin abu ya soke shi. Gabad'aya k'alubalantar kansa yake yi. Akan me zai mata wannan batun a halin da take ciki?
Me yasa bai bari ta haihu lafiya ba? Ga shi yanzu ya janyo ta shiga tashin hankalin da bai san yadda zai dire ba. Ba abin da yake tayar masa da hankali irin yadda aka tabbatar ita d abin da ke cikinta suna cikin garari.
So yake ya ganta cikin nutsuwarta ya bata tabbacin zai dawo mata da d'iyarta har ma da Alti. Sai dai da alamun komai ya k'wace masa don tun jiya take kwance tana barci bata san wanda yake kanta ba.
Gabad'aya hankalinsa ya yi mugun tashi. Daga Faruku har Baba ba wanda ya tuhume shi.
An zuba masa ido.
Komai ya tsaya masa cak. Idan ya koma gida ya ga yara ne su kad'ai suke rayuwa sai ya ji damuwarsa ta sake rub'anya ga su Noor da suke tambayarsa yause Mahmah da Farha zasu dawo ne a kullum?
Sa'a daya ma bai sallami y'ansanda mata da ya dauko lokacin da zai tafi Calabar ba.
Wasa wasa sai da Maigado ta shafe sati biyu a asibiti. Zuwa lokacin ma an hana yin zarya da sunan dubata. Alti da Abida ne a wajenta sai shi da kullum sai ya je sau uku.
Ta shiga watan haihuwarta ta kuma dawo cikin hayyacinta. Sai dai kuma ta koma yanayi na shiru sosia. Yana wahalar gaske ta yi magana mussaman ace da Asad ne. Gara gara tana yiwa Abida da Alti suma ba haka siddan ba.
Amma ko Farha da Alti take cewa a kawo mata ita idan ta zo hannu kawia take mik'a mata.
Hankalin Amrah da Faruk ya tashi da basa jin muryarta, kullum Alti da Abida cikin kwantar musu da hankali suke yi tare da basu tabbacin jikinta da sauki.
Ranar juma'a Abida ta zauna kusa da ita ta ce ",Yanzu Bilki ba za ki dinga yiwa yaran nan magana ko hankalinsu ya kwanta ba?
Ba hutun school ake yi ba bare su taho su gan ki. Idan ba za ki yiwa kowa magana ba, ki taimakemu su da basa kusa ki yi musu mana. Haba da tausayi fa! Ta dinga yi mata nasiha da rarrashi har ta samu ta bude baki ta ce "Ni maganar ce bana son yi Wallahi!
Da kulawa Abida ta ce "Kada ki yiwa kowa amma su ki daure ki dinga amsa wayarsu. Yanzu tunda suna gida bari na kirasu ku gaisa dan hankalinsu ya Kwanta".
Bugu d'aya Amrah ta d'auki wayar tare da fad'in "Ammi ya jikin Mahmah dai?"
Da walwala ta ce "jiki da sauk'i gata ma".
Ta mik'a mata wayar. Ta masa suka gaisa. A sanyaye ta ce "Amrah na ji sauki sosai idan na yi magana da yawa gajiya nake yi ne, ba wai ciwon ne ya tsananta ba. Ai kinsan ko da ina nan wani lokacin maganata na daukewa ko?"
"Eh Mahmah "..
Amrah ta masa babu kuzari.
To idan baku jini ba ku daina damuwa, da sauki sosai jikina. Ina Yaya Faruk?"
Ya karbi wayar ya ce "Mahmah idan bamu jiki ba, gaskiya munsan ba ki da lafiya, maganar kada mu damu kuwa babu ita".
Ta murmusa kad'an ta ce "To yanzu da kuka jini hankali ya kwanta?".
"Eh amma ba sosai ba, sai mun zo mun ganki da idonmu. Ina Farha?"

*Wannan littafin kudine*
*Duk wacce ta karanta bata biya hakkkn wahalar rubutu ba, ina bin ta bashi*.

Ta ce "Yau bata zo ba."
Daidai lokacin oga Asad ya turo kofar d'akin ya shigo. Alti ta gaishe shi ta fice, don shi kam bata saba da shi ba, babu sakin jiki a tsakaninsu.
Ya tsaya a kusa da Abida yana sauraren Bilki na magana cike da mamaki.

Daidai lokacin ya jiyo Faruku na fad'in "Dady ma ya ce "Idan mun yi waya na fad'a miki yana yi miki sannu".
Ya kurawa Bilki ido mussaman da ya ji ta ce "Na amsa ka ce masa "Na gode, ina k'anwarku?"
"Lubaba tana nan an yayeta jiya."
Faruku ya fadi hakan. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:08]
"To ka siya mata biskit da sweet idan Daddy ya baka kudin break ranar Monday ".
"To Mahmah guda nawa zan siya mata?".
"Guda shida shida".
"To zan siya mata , dazu ma Yaya Amrah ta soya mata samosa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login