Showing 138001 words to 141000 words out of 148964 words
Chapter 47 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt
ta fice zuwa d'akinta itama ta shiga wanka.
Da ta fito ta tsinci kanta da wani irin zumudi da bata tsintar kanta a ciki ba. Cikin gaggawa ta bude coconut oil na oriflame da Bilki ta koya Mata shafawa don ita tafi son verseline. Amma yadda man ya karɓi bak'ar fatarta ta yi taushi yake fitar da Mata ainihin kalarta mai duhu ya sanya take son shi. Bilki dai na da jama'a iri iri. Don duk abin da zata siya zata ce tana da wadanda suke da shi mai kyau Wanda babu tsada ko algush.
Dan haka daga Kano suke siyan dukkan oriflame products wajen Aisha lame dama dukkanin da ya shafi costumes.
........
Hatta man gashi da turarenta zababbu lamen take basu. Don haka Abida cikin gigiggiwa take bin dukkan nau'in jikinta tana goga mai da turaruka daban daban.
Ta shirya cikin irin rigar da yake son ya dinga ganinta a ciki mussaman ta yi order ta a wajen Maman biyu mazauniyar Egypt......
Ta zunduma hijab din gunis da ya sha kambasa.
Ta zunduma hijab din gunis ta fita.
Sai da ta shiga kicin ta d'aukar masa ruwan da ya zame masa k'aidar shi idan ya kammala jijjigata.
Tana shiga ya mike a bakin gadon ya ce "Har na kosa fa, da bin ki zan yi ai".
Ya karɓi ruwan ahannunta ya ajiye akan side drower.
Ya juyo ya ga ta cire hijab din.
Zuciyarsa ta harba da ya ganta a zahirinta.
Ya bude mata dukkan hannuwansa.
Bata tsaya yauki ba ta yi gaggawar isa ta fad'a mishi. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:58]
Ya rungumeta sosai har suna jin yadda zukantsu suke dokawa.
Zuciyarta ta karye a dalilin rabon da ya yi mata irin tun safiyar da zasu yi hatsarin da ya yi ajalin Baba K'arami.
Hawayenta har kan k'irjinsa.
Murya ba amo ya ce "Kada ki yi mini haka, kinsan bana son kuka ko?"
Cikin kukan ta ce "Dan Allah yaya Sule ka yafe mini, ka manta komai, Allah ya baka hak'uri ".
Ya sake rik'e ta sosai yana fad'in"Is ok na huce na manta, amma kada ki sake, kada ki sake Abida!
Murya na rawa take fad'in "Na gode sosai dadyn junior, ba sai ka ce komai ba, ba zan sake ba koda wasa kuwa".
Ya d'ago fuskarta da ta yi jagejage da hawaye ya tsura mata idanuwansa. Itama ta zuba masa nasa da suke cike da k'walla.
Gabad'ayansu shauk'i ya yi musu dabaibayi, soyayyar juna ta dinga taso musu. Ya saka harshensa yana lashe hawayen da bai daina silalowa ba.
Daga ya hade bakinsu ya shiga laluben harshenta. Tsayuwar ta nemi gagararsu da ƙyar suka dangana da Gado suka cilla sama jannati. Abubuwan da suka biyo baya kuwa nauyinsu ya kai k'urewa wajen bayyanawa. Amma dai anci uwar sabada an yi tumbidin ruwa irin sosai din nan don dukkansu sun yi kewar juna a kuma matse suke.
Barin Abida da ta sha gyara da kayan bojuwa herbs.
Tsananin farinciki ya sanya dukkansu hawaye ba tare da Dr Sule ya fahimci hawayen.ke zubar masa ba. Don gabad'aya sun karaya da tunanin zasu sake samun kansu a cikin irin wannan yanayin.
Kirikiri ya kasa zuwa sallar la'asar. Lokaci ya k'wace masa.
Sai da suka samu nutsuwar da ta dace da su sannan suka yi wanka, suka yi sallar wanda biyar ta wuce.
Suna kan sallayar tana nade a jikinsa.
Ya ce "How far ya ya marar?"
Ta rufe ido tana dariya ta ce "Da sauran nauyi nauyi kad'an.
Ya kece da dariya ya ce "Kina sharafinki Abidan Baba ".
Ta ce "Hmm Abidar Yaya Sule dai tuni ka k'wace masa ai. Da ƙafafuwana fa na taho Funtua na baro baba da Momi babu zullimin komai".
Ya sake yin dariya ya ce "To ba kewata kike yi mai tsananin gaske ba?"
Ta jijjiga kai tare da fad'in "Da kewa ce kawai da na cigaba da shan kanwa da lemon tsami, na dinga gasa wajen da ruwan dumi da gishiri. So ne mai tsananin gaske dadyn junior ".
Karon farko da ta furta masa Kalmar soyayya babu kunbiya kunbiya.
Ya ce "Amma fa Abidata bata yin soyayya bata ma yarda da ita ba".
Ta boye idanuwanta a k'irjinsa ta ce 'A a Yaya Sule Abida dai bata son soyayyar nan ta masifa. Amma a yanzu ai ta gane wata soyayyar jarabawa ce. Don haka ta daina ganin beken masu yinta babu sassauci zata dinga yi musu addu'a kawai don ita kad'ai tasan tsananin da ta shiga a lokacin da ka yi mata nisa."
Ta fashe da kuka sosai tana fad'in na ga rayuwa Yaya Sulaiman.!
Tausayinta ya kama shi don duk abin da ya saka Abida yin laushi irin haka da kuka na gaske to tsananinsa ya kai k'urewa.
Ya dinga shafa bayanta yana fad'in "Very sorry".
Da kuka ta ce "Ka yi mini alk'awarin ba zaka sake guduwa mini ba Baban junior".
Ya ce "Ba zan sake ba mana, ki daina kukan nan bana so".
Sai daf da magharib ya shiga bayi don ya doro alwallah.
Tare da ita suka fita a d'akin.
Ya zauna a falo ita kuma ta shiga dakin junior.
Daidai lokacin ya fito daga bayin fuskarsa da ruwa tabbacin Fitsari ya yi da kuma alwallah Razina ta yi masa.
Don tana cikin bayin bata fito ba.
Ta ce "Ka tashi, alwallah ka yi?"
Ya daga mata kai don haka yake zama miskili idan ya tashi a barci.
Ta ce to mu je ku tafi masallacin don ya riga ya saba zuwa masallaci tare da Baba. Duk lokacin sallah shine dan rakiya haka zai tisa shi a gaba su tafi".
Suka isa falon Sulaiman ya mike ya daga shi sama. Ya ga bai yi masa walwala ba.
Ya ce "Kana jin yunwa ne?"
Kai ya daga masa tabbacin eh".
Ya kalli Abida ya ce "A ba shi abinci ya ci, sai ya yi sallar a gida".
Ta ce "To".
Yayin da junior ya kwararrabe fuska zai yi kuka".
Abida ta ce "Sai kun dawo zaka ci abincin?"
Ya ce "Eh" cikin kuka. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 16:01]
Sulaiman ya jijjiga shi ya ce "Kada ka yi kuka mu tafi ".
Bai dire shii ba sai da suka je koridon da zai fitar da su waje. Ya ajiye ya saka takalmansa da suke gefe.
Da daddaren ma nasu sararawa juna ba. Ana ta biyan gangar jiki kewar da ta sha na tsawon lokaci mai yawa.
Kwanakin biyun da suka biyo amarci ake sha gangariya wanda babu k'wange a gidan Dr Sulaiman na Dr Abida ".
To be continued.
08032773332.
*Dingishin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332.
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
🖤 BA NI DA IKO...
*Littafin Farida Abdallah*
*Ku zo mu yi tafiyar da babu nadama a cikinta*.
*1k ne a manhajar telegram*
*7039080978, Opay, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 07039080978*.
*Abuja*
Farinciki da walwala tare da fahimtar juna sun samu muhalli a gidan oga Asad. Don tunda ya gano abubuwan da yake yi suke tunzura masa sarauniyar sheba shikenan ya kiyaye yinsu a gabanta mussaman yin kwatance da maimurabus ta bakinta da fada.
Ya barta a zuciyarsa yana bin ta da adduar rahama don kuwa ba zai yiwu ace ya manta da ita ba.
Yayin da Bilki take kaffa kaffa tare da kiyaye yin abin da zai saka ya murd'e mata tunda ta fahimci so baya hana shi ya nukurkusa mace da bak'in ciki mai saka kuka da rama a tsaye, idan ta nemi raina shi ko bijire masa.
Dan haka suke zaune K'alau cikin mutunci da girmama juna.
Amrah da Faruk junior sun isa gidan sun samu karɓa daga dukkan ahalin gidan.
Don Amrah ma a d'akin Bilkisu take, tare suke kwana akan gadonta. Haka Su Hafcy da Aysha basu bada matsalar koami ba.
Ga khadija ta zo hutu wanda watanni kad'ai suka yi saura akan ta kammala gabad'aya.
Don haka gidan a cikin hada hada yake mai dad'in gaske.
Baba ya faɗawa ya'yansa Sulaiman zai mayar da shi Funtua.
Gabad'ayansu babu wanda ya yi raddi. Oga Asad ne ya ce "To Baba ai sai an shirya don gyaran da za'a yiwa gidan nan ai ba kad'an ba ne".
Baba ya ce "A a tuni Sulaiman ya kammala. Kai naka ido ne an hutar da kai an gode maka oga Asad".
Yau ma dariya ya yi don kuwa idan baba ya ce masa oga tunda ga zuciyarsa dariyar take fitowa.
Ammar din Faruku da yake shiga shekarar k'arshe a jami'a.
Tunda ya k'yalla ido ya ga Amra ya ji a ransa ya yi mata. Rashin hayaniyarta da nutsuwarta sun yi matuƙar burge shi. Mutumin Bilki ne na sosai.
Sannan yadda Faruk yake da haba haba da fatan faran haka shima yake.
Da yammaci ya isa gidan.
Kaitsaye ya haye saman Bilki yana fad'in "Mahmah Mahmah".
Bilki na zaune akan kujera ita kad'ai. Alti ta bi yaran sun fita.
Ta kalle shi ta ce "Ammar ka yi ta faman doka mini k'ira tamkar makaho".
Ya yi dariya ya zube a gabanta akan kafet.
Ta girgiza kai ta ce "Fadi yau kuma da me ka zo?"
Ya ce "Mahmah kin ce ke ce mai saka mini lallen aure ko?"
Bilki cikin alfahari ta ce "K'warai da gaske don kuwa Yaya Salaha da Yaya Hamida dolensu su hak'ura don sun san ni ce mafi kusa da Abbanka".
Ya ce "To Alhamdulillahi Mahma. Yanzu kuma idan Amrah ce amaryar fa?"
Zuciyarta ta harba da saurin gaske. Dole dai soyayyar nan ita da Yaya Faruku sai Allah ya kullata akan yaransu.
Idanuwanta suka ciko da k'walla. Ta shanye kukan ta ce "Ko ita ce don kuwa kaine d'ana ba ita ba, ita ma k'anwar uba ko yayar ubanta ce mai saka mata lallen. Amma fa Ammar bata kammala sakandire ba yanzu ne take ajin k'arshe ".
Ya jijjiga kai ya ce "Na sa ni Mahmah. Nima ai sai bana zan kammala digirin farko, kawai ina son ta san da zamanka Manya ma Su sani don ABBA ya ce mini nauyin baki na sakawa a rasa abin da ake so mai k'ololuwar daraja."
Ta yi shiru amma so take ta rushe da kuka. Ta tabbatar Yaya Faruku ne ya ce ya faɗawa Amrah idan har yana sonta da gaske.
Kafin ta yi magana ya ce "Ki faɗawa Dady don Allah. ABBA ya ce "Shine babana shii zan faɗawa, ni kuma ba zan iya faɗa masa ba".
Cikin jarumta ta ce "Zan fad'a masa kuwa don tasan ba zai iya din ba da gaske saboda idan Baban Bilkisu na guri nutsuwar da yake yi ta daban ce.
Ya nisa ya ce "Zan fad'a mata don nima a tsorace nake kada wani ya yi mini shigar sauri".
Bilki bata ce komai ba don kuwa yana da gaskiya itama k'addara da rabon haihuwarta da Faruku ne ya sanya Sahal yiwa zuciyarta da take son fari mai kyau kutse alhalin bai fi ya zo a dan aikent ba. Sai dai dama ta kud'ire a ranta ba zata bari Amrah ta yi irin kasassbar da ta yi yayin zancen mijin aure ba. Shiya6duo sadda suka zauna take yi mata bitar kyaun namijine abu na k'arshe da zata duba. Addininsa da halayyarsa tare da nasabarsa sune a farko.
A yanzu da Bilki take cikin shekarun hankali ta gane abin da take ji akan oga Asad shine so wanda bata ji ko da kwatar hakan a zuciyarta akan sahal ba. Haka nan yadda take girmama tare da mutuntunta duk abin da ya shafi Yaya Faruku ta gane kauna ce wanda babu abin da zai shafe ta a zuciya.
A fili ta furta "Allah ya tabbatar da wannan batun, na yi murna. Allah ya saka albarka ".
Ammar ya mike ya ce "Ameen Mahmah na samu k'warin guiwa dan haka na samu nutsuwa".
Bata ce komai ba .
Ya ce "Ina yanmatan na ki, yau gidan babu dad'i shirunsa ya yi yawa".
Ta ce "Aysha te debe su sun fice".
"Har da twins?"
Ya tambaya a takaice.
"Hmm har da su kasan Alti da son ta yi yawo ta ga Abuja. Har yanzu bata gaji da ganin titunan Abuja ba".
Ya yi dariya tare da fad'in "Da fa zuwa na yi na d'auki takwaran abba mu yawata gari, shi kad'ai a cikin mata".
Ta ce "Ai kuwa shiyasa ma baya wani d'okin zuwa sai dai ka dawo gobe idan Allah ya kaimu".
Ya ce "Zan dawo".
Ya tafi Bilki ta bishi da kallo tare da sake girmama ikon Ubangiji.
Ta fad'awa oga Asad sakonsa shima ya yi murna ba kad'an ba.
Amma ya ce "Karatu zata yi tunda tana da k'ok'ari dan haka ba yanzu za'a yi magana ba. Kawai dai ya dinga nuna mata cikin hikima yana sharewa kansa hanya.
Can ya kalli Bilki ya ce Amma kuma idan itama ba mai fahimtar share hanya da raragefe ba ce ba fa?"
Ta yi dariya ta ce "Baban Bilkisu ba fa zan gaji da baka amsa da fad'in cutata ka yi da ka k'i bayyana da k'arfinka ba. Wacce mace ce zata tankwabar da tsadadden namiji irinka a cikin hankalinta?"
Dad'i ya kama shi amma cikin alhini ya ce "Amma Maigado a karo na biyu ma da na bayyana da karfin nawa ai kin tankwabar da ni. Sai da na shiga rigar Faruku fa sannan kika amince da ni".
Ta dan murmusa tare da cewa"Yanzu fa? Baka gama mamaye zuciyata da kalolin soyayyarka da yakanarka ba?"
Ya murmusa ba tare da ya gamsu ba.
Ta sake shige jikinsa ta ce "Ban fa so wani a duniya irin ka ba Baban Bilki, don ban tab'a jin ina kishin wani namiji a duniya irin ka ba."
Wani irin dad'i ya kama shi amma sai Ya ce "Maigadona ki fad'i gaskiya. Anya kuwa, kin fa so yaron nan, sannan Faruku fa?"
Ta ce "Na fi sonka fa akan komai da kowa. Shi Yaya Farouku ina rasa wa na fi so tsakaninsa da Yaya Sulaiman. Amma babu tantama nafi jinsa fiye da Ansari ".
Oga Asad ya saki ajiyar zuciya tabbas yanzu ya gamsu tana sonsa ba shine kawai yake dakon soyayyarta ba.
Ya jata jikinsa ya kankame yana sake jin tana mamaye kowanne loko da sako na zuciyarsa.
A wannan ranar suburbubudar da ta sha a hannunsa mai matuƙar tsayawa a rai ne, haka nan mai sakawa ta yi ta sonsa ne. Tana samun nutsuwa da gamsuwa a duk sadda ta shiga hannun oga Asad. Basa yiwa juna k'wange a wannan fagen.
***""
Sulaiman na zuwa Kano ya kwana biyu ya dawo Funtua. Yana ganin masu lalurar ido a matsayin babban likita a asibiti Makka eye Hospital.
Abida Na zaune tana cin hadasden Ciccibin bojuwa herbs Kano da ta yi order dinsa jiya. Da yake da kankararsa ya iso Mata Sai ta jefa Shi a freezer shine Sai yau ta yi warming take ci.
Sulaiman yana kallonta ta ce Na iya mata ne.
Ya jijjiga kai ya ce "Ke da Bilki munubarku da yawa Wallahi. Ku dinga yi mana a hankali. Ku ta kid'ima mu haba dan Allah. Oga da kansa da na gansn a gaban Bilki Sai da na rike baki".
Ta k'yalkyale da dariyar nishadi tare da fadin Baban junior ina ce dai kana jin Zamzam?"
Ya Sosa kansa ya ce "Idan gaskiya zan fad'a cicif nake jin ki Abidan Baba ".
Dad'i ya kamata ta kuma tabbatar kayan Bojuwa babu algush kodayake duk kayan da Bilki take tallata mata babu na banza.
Bojuwa herbs
08032773332
For your order.
Ta ce "To kwalliya ya biya kudin sabulu tunda ka yaba".
Kamar yadda aka yi alk'awari jiya tara ga wata Sulaiman ya dira a Abuja tare da junior. Ba yadda bai yi da Abida ba akan su tafi tare ba ta k'i. Ta kafe akan zata zauna ta yi musu girkin tarabarsu. Don tun jiya laraba aka bude wajen ta kamawa Razina suka gyara gidan ya yi fes. Ita dai Abida mamakin yadda Yaya Sulaiman ya kashe makudan kudade take yi wajen gyan gidan. Bangarensu baba ma komai sabo ya zuba musu.
Ta tsinci kanta da addu'ar Allah yasa kada Dady ya ce Baba ba zai dawo ba. Ta tabbatar Dr Sule ba zai yarda ya dawo shi kad'ai cikin kwanciyar hankali bw mussaman yadda ya tafi da k'arfi da guiwa da farinciki.
Haka gyara b'angaren Baba da ya yi ta tabbatar bai d'auki al'amarin dawowarsa da sauk'i ba.
Ranar goma ga watan goma jirgin da ya dauko su daga Abuja ya sauke su a Kano.
Suka shiga motar Sulaiman da ya barta a airport suka d'auki hanyar Funtu.
Daga baba sai momi sai junior. Yaya Faruku zai dawo amma sai ya kammala da komai sai ya dawo tare da iyalinsa. Ammar dai zai zauna a gidan oga Asad ne ya cigaba da karatunsa da kuka da harkokin Babansa.
Yan aikin Momi tare da mai gadin gidan wanda shima asalima dan Funtua ne James zai tuko su a motar Baba.
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
Cikin nutsuwa Sulaiman yake tuki don baba baya son gudu.
Lafiya lau suka isa Funtua.
Baba ya dinga mamakin yadda gidan ya zama sabo. Ya tsaya a farfajiyar gidan yana kallon tafkeken gidan nasu. Wanda tazarar da ta tsakanin shashi zuwa wani shashin ba kad'an bane. Amma gabad'aya Sulaiman ya gyare gidan ko ina sai d'aukar ido yake na ban mamaki.
Wani irin abu ya mamayi zuciyarsa shikenan zai yi rayuwa a gidan babu Baba k'arami. Hawaye ya k'wace masa da ya hango jikin bishiyar da yafi Zama a k'arkashinta matuƙar bai tafi Ladi farm ba.
A fili ya ce "Allah ka jiƙan Isah ka gafartawa mahaifanmu".
Sulaiman ya yi maza ya ce "Ameen Baba. Allah ya kara maka lafiya da hak'uri tare da nisan kwana mai albarka."
Momi ta ce "Ameen Ameen".
Daidai lokacin Abida ta fito tana yi musu barka da zuwa.
Suka dunguma suka shiga b'angaren Baba. Mamakinsa ya fad'ada ya ce "Sulaiman irin wannan hidima bata yi yawa ba kuwa? Ka yi ta'adin kudade masu nauyi fa".
Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce "Da ina da ikon yi muku fiye da hakan da na yi Baba ".
Dad'i ya kama Baba ya ce "Kai madallah da Dr Sule angon Abida k'anwar Bilkisu ".
Dad'i ya ratsa Abida ta ce "Ameen Baba ".
Yayin da Sulaiman ya yi maza ya ce "A a malama daina yin murmushi don an ce angonki, ke uwargida ce."
Ta yi dariya