Showing 132001 words to 135000 words out of 148964 words

Chapter 45 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

tana da ban mamaki".
Daga haka ta ce "Dady na gode Allah ya bar kauna, Allah ya saka maka da alheri. Baba na gode Allah ya k'addara saduwarmu gobe da asuba zan wuce ".
Faruku ya kalleta wato shi da Usman sun yi laifi kenan.
Ta mik'e ta ce Yaya Faruku na gode, Yaya Usman na gode Allah yasa zamu ganawa sai wataran".
Baba ya ce "Koma ki zauna".
Gargadin da jan kunne masu yawa Baba ya yi mata tare da babbar murya a k'arshe kuma ya ce ya soke batun bashi ko na diyyar da take nema a wajen Sulaiman. Ina kuɗaden da ta dinga karɓa a wajensa da wajen su Asad da yake bata na hidimar yaron?
Ina kudaden da Ansari yake turo miki from time time, ina hidimar da Bilki take yiwa yaron?"
Da kuka ta ce "Baba kenan dai saboda shi aka dinga ba ni kuɗaden ba dan ni da nake wahalar raino da tarbiya ba?"
Oga Asad ya ce "Ni dai ina bayarwa ne a madadin Sulaiman ba dan ke ba, ai kina aikinki kina samun kudade amma nake baki don ina matsayin uban yaron ba wai yayanki ba."
Takaici ya shak'eta ta ce "To shikenan na gode".
Yayin da d'adi ya mamaye Sulaiman an kubutar da shi jidalin Abida akan bashin da ta kago masa.
Ya kalleta ya tabbatar kawai ta amsa ne don tana son a kammala sulhu amma lallai sai ta karɓi wani abu a gunsa da hankalinta ya kwanta.
Aka rufe taro da addu'a.
Su oga kowa ya yi sallama da Baba da Momi suka tafi harkokinsu.
Yayin da Abida ta shige d'akinta ta hau had'a kayanta da na junior.
Ba dan azahar ta kawo kai ba duk runtsi yau zata tafi. Ta kuma ta gane Sulaiman ba zai yarda su tafi tare ba. Baba ma ba zai bari a raka ta ba tunda a gabansu ya fadi ba shi ya ce ta tafi ba, dan haka ta koma inda ta baro anan zata zauna.
Kafin magharib ta gama hade duk wani abu mai muhimmanci a gareta ta k'ira oga Asad ta roke shi akan gobe James zai kaita Funtua a motarta sai ya shigo motar haya ya dawo Abuja. Ya amince mata. A daren ta d'auki mota ta tafi asibiti tunda dama night zata yi. Kafin asuba ta kammala komai ya rubuta takardar ajiye aiki da asibitin gabad'aya.
Tana shigowa gidan ta shiga ta gaida Momi tare da yi mata sallama. Tausayinta ya kama Momi a dalilin ta ga tun jiya bata zauna ba.
Ta yi zuruzuru tabbacin bata cikin nutsuwa.
Momi ta ce "Allah ya kiyaye Abida. Lallai ki nutsu ki yiwa mijinki biyayya, ki girmama ra'ayinsa ki mutunta shi. Allah ya kiyaye gaba ".
Hawaye na zubar mata ta ce "Ameen momi na gode dan Allah ki yafe mini".
Momi ta ce"Ba komai Allah ya yafemu gabad'aya."
Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:30]
*Dingishin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332.

*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.

Daga haka ta kinkimi junior da yake barci akan gadon momi tana fad'in "Bari a yi masa wanka."
Sai da aka yi masa wanka aka shirya shi sannan itama ta yi wanka.
Razina mai kula mata da Junior ma ta shirya don da ita zata tafi.
A tsastsaye ta kurbi ruwan tea. Sannan ta je Har dakin Baba bayan momi ta yi mata iso. Ta yi masa sallama tare da godiyar hidimar da aka yi da ita. Ta sake ba shi hak'uri."
Ya bat tabbacin ya huce. Amma ta ninka biyyayarta ga Sulaiman. Ta ajiye dukkan ra'ayinta ta bi nasa, sannan ta yi hak'uri da shi."
Da kuka ta baro d'akin, duk yadda ta matsu ta bar gidan sai da ta ji alhinin barin iyayenta.
Daidai lokacin James ya iso.
Yan aikin gidan suka dinga fita da kayayyakinta.
Ta fita zuwa d'akin Sulaiman.
Murya ba amo ta gaishe shi tare da fad'in "Zan tafi ba ni mukullin gidan".
Bai ce komai ba ya dauko ya bata har ta juya ta ce "Ba addu'a ba komai?"
A gajarce ya ce "Allah ya tsare sai na iso".
Ta ce "Allah ya kawoka lafiya".
Ta saka kai ta fice.
Sai da suka je wajen Bilki ta karɓi frozen snacks da sauran tarkace sannan ta tafi.
Bilki ta biyo ta tana fad'in Abida haka za'a yine ba wani dan gyara da zaki yiwa yayana irin wannan dogon lokaci ba'a hadu ba haba gaskiya tsaya Ki tafi da tsumin bojuwa herbs kin yi sa'a ma jiya kazar sababin da na yi order ta iso. Bari na yi miki warming dinta Ki ci hanya".
Abida bata k'i ba ya tsaya ta karɓa don tasan kazar da gaske ta sababi ce.
Ta ce "Ki yi mini order din Bridal package kawia Bilki sai a saka mini a motar Funtua. Ina son sanyi flusher irin sosia yake da kyau ".
Bilki ta ce to zan miki ai zan so Yaya Sule ya huta da kyau da kyau".
Abida ta tsume bata ce komai ba har aka yi warming kazar aka juye mata ta karɓa ta tafi.
Contact 08032773332 for your order.
Bilki tana mamakin yadda Abida ta yarda zata koma Funtua salin alin duk da yadda aikinta a Abuja yake. Dariya ta k'wace mata tana ayyana keburan Yaya Sule sun shige ta da kyau.
Suka gaisa da Yaya Hamida d ta kwana a gidan ta yi musu sallama ta tafi.
Hamida ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in Abidan Baba an yi tub'us. Sai ta bani tausayi Wallahi ".
Bilki ta numfasa ta ce "Yaya Sulaiman ya ce ba inda zai zauna sai a gida. Amma sannu a hankali zasu raya gidan Shi da ita . Na gane manufarsa akwia kuma hikima mai yawa a hangensa. Allah ya k'ara daidaita mu gabad'aya."
Hamida ta amsa da "Ameen ".
Cikin kasala.
K'arfe goma na Safiya oga Asad ya kammala shirinsa zai fice.
Ya leka d'akin Bilki suka gaisa da Hamida.
Ta ce masa yau zata je gidan Yaya Faruku ta yi masa nasa kwanan."
Ya ce ,"kin kyauta Allah ya bada ladan zumunci. Yanzu yaushe za ki dawo zuwan Bilki Kenan tunda kin ce yanzu wajena kika zo?"
"Zan dawo kafin na tafi ko yini na yi mata. Ko ban same ka ba dai zan dawo ".
Dariya ta subuce masa yasan so take yi ya sallame ta kawai.
Ya koma sama ya dawo ya mik'a mata rafar dubu dari ya ce "Ga shi ki sha ruwa a hanya na gode Allah ya sauke Ki lafiya."
Ta karɓa ta yi godiya. Har ya kai falo ta zabura ta bishi Bilki na rik'eta ta fizge, Bilkisu ta sake rik'eta ganin zai sauka ya sanya ta bude baki ta ce "Yaya Asad".
Ya juyo kan dole Bilki ta saketa. Ita kuma ta fita tana fad'in "Wallahi ba ki isa hanani na karɓa ba."
Ta fita zuwa bak'in kofar ta dan diririce ganin yana saurarenta. Ta kwafse ta ce "Yaya dama ina sonu tattauna ne".
Kaitsaye ya ce "To Bismillah ". Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:33]
Ya dawo ya zauna akan kujera.
Itama ta fito ta zauna a gefe. "Kanta na k'asa ta ce "Baba ya ce wanda ya yi imani da Allah da ma'aiki hadi da ranar lahira ya huce da d'anuwansa."
Kaitsaye ya ce "Hakane".
Ta nisa ta ce "To gaskiya na huce amma akwia abin ka yi mini wanda na kasa mance Shi, shine Zan fad'a maka don na daina ganinka da abin."
Ya gyara zama ya ce "Ina saurarenki Hamida ".
Bilki tana tsaye a bakin k'ofar d'akinta ta yi sororo tana mamakin k'arfin halin Yaya Hamida.
Ta waiwaiya ta ga Bilki ta ce "Kina nufin dan kin zama matarsa sai ba zan zo gabansa da damuwata ba sai kin mini tsaye a kai tamkar dogari? Ya ya hakane?"
Ya ce "Shiga ciki sarauniyar shaiba ".
Kan dole Bilki ta shige cikin d'akin cikin matsanancin mamaki.
Hamida ta muskuta ta ce "Ka saba yi mana alheri Kan alheri Yaya Asad Kuma muna jin dad'i tare da yi maka addu'ar cigaba da samun d'aukaka da gamawa lafiya.
Kana da kirki dukkan halayyar iyayenmu biyu ka kwashe Su tsaf. Shiyasa kullum nake mamakin da ka danne hak'kina da nake da shi a cikin dukiyarka. Annabi ya ce "Idan Allah ya yiwa mutum arziki a zuri'a to y'anuwansa suna da hak'kin a yi musu hidima da dukiyar. Alhamdulillahi kai kana kwatantawa. Mun gode. Amma dan Allah me yasa da aka shiga danbarwar nan ka daina ba Ni kason azumi da na sallah? Wannan abu Yana mini ciwo don mijina na sake girmama ni Idan ya ga makudan kudaden da yayana yake ba ni, motsi kad'an zai ce ai ni yar gata ce, ni d'iyar dattawa ce kanwar manyan Kass masu wadata. Amma Yaya Asad Sai da ka kunce mini zani a kasuwa".
Ta kece da kuka sosai.
Jikin oga Asad ya yi sanyi. Ya ji wani irin rauni da tausayinta ya kama shi. Zuciyarsa d'aya ya ce "Share hawayenki Hamida kuskure duka mun yi Shi tare da taimakon shaidan da sharrin zuciya. Amma daga Bana za ki ga sauyi kuma kari Zan yi muku ma d aya wuce yadda nake baku a baya".
Ta goge idonta da tissue din hannunta ta ce "Allah yasa, Allah ya k'ara Budi."
Ya ce "shikenan matsalar?"
Ta langwabe kai ta ce "Ai ni biyana zaka yi na bayan da baka bayar ba.
Azumi hud'u sallah hud'u kenan. Ga na ragon layya shima hud'u ne".
Ya yi sakare yana tuna danbarwar Abida da Sulaiman akan kuɗaden da ta ce zai biyata. Shine yau shi Kuma Hamida ta tisa a gaba da naata shakiyancin. Ko da yake da dukkan zuciyarta take magana ba tsokana ko ba'a take yi ba.
Ya kalleta sosai yadda ta langwabe kai ta yi kalar tausayi take kuma dakon amsarsa sai ta ba shi dariya ainun.
Ya dinga kyakyatawa. Ta jijjiga kai ta ce "Da kasan gorin da ake yi mini a dalilin rashin samun envelope Dinka ko alert dinka da ka tausaya mini k'warai da gaske. Har fa sai da aka kai jallin idan an biya Ni kudin hayar gidajena nake nunasu a matsayin kai ka ba ni".
Ya matse ya ce "Har haka kike rufa mana asiri ni da ke?"
Da azama ta ce "E to ya zan yi tunda mutanen yau sun siffantu da son yin gori don a saka mutum a bak'inciki mai tsananin gaske".
Ya ce "Ki yi hakuri da ikon Allah kin wuce kowanne irin gori Hamida daga yau din nan".
Ta dinga godiya cikin farinciki.
Ya mike yana fad'in sai mun sake had'uwa.
Ta yi maza ta ce "To lissafa ka ba ni na baya tunda na yi ta ranta maka ina nunawa mai shari'a kai ka bani."
Dariya ta sake k'wace masa ya ce "Wai dan Allah ke da Abida haka tsarinku yake ne? Haka siddan idan kun so nishadi sai ku ce kuna bin mutum bashi?"
Ta kwararrabe fuska ta ce "Yaya Asad Wallahi ina nuna kudi na ce kai ka bani, kuma dai tunda ka saba bayarwa ni ka daiana ba ni tunda an huce har na zo maka kwana gidanka ai sai ka yi mini adalci ka kirgo dukiyata ka ba ni cikin rarrashi da farincikin ka sauke nauyin zumunci".
Ya ce "Yanzu nawa kika lissafa kenan?".
Ka ga dai duk azumi kana bamu rabin milyan. Ka zo ka bamu barka da sallah sannan ka bamu kudin ragon layya. A kiyasina ba zasu gaza milyan biyar ba idan kuwa Keke da Keke za a yi sun saura sosai ". Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:36]
A fili ya ce "Tirk'ashi ".
Kan dole ya ce"Yanzu idan na je office na zauna zan turo miki abin da ya samu sai ki yi hak'uri ki yafe sauran".
Ta ce "To shikenan amma dan Allah Yaya a duba hak'urin da na yi kada a takure ni da yawa tuni na gama kasafin da zan yi da kuɗaden, hidindimu ne sun yi mini k'awanya Wallahi ".
A wannan karon ya kasa ce mata komai illah dariyar da yake ta sosai, a hakan ya fice ya bar gidan. Har ya isa office Yana dariyar Hamida. Tabbas ita da Abida danjuma ne da danjummai.
Bilki ta fito Hamida ta galla mata Harara ta ce"To na fad'a sai kisan yadda za ki yi da ni?"
Bilki ta murmusa tare da fad'in ya zan yi kuwa?"
Awa da d'aya da fita ta ji alert tana dubawa ta ga milyan guda.
Ta yi murna sosai. Amma ta kalli Bilki ta ce "Kawai na hak'ura ne amma ba haka nake binsa ba".
Bilki ta yi tamkar ta ce "Kada Ki hak'ura mana".
Amma tasan idan ta fadi hakan ta tsokano tsuliyar dodo ne.
Dan haka ta murmusa tare da fad'in "Yaya Hamida kina sharafinki".

*
Da yamma Sulaiman a gaban Baba yana masa sallama zai tafi Katsina gobe da sassafe tare da Anisa.
Ya sake ba shi hak'uri akan dukkan abubuwan da Sia wakana. Baba ya bashi tabbacin a yanzu Babu bacin ran kowa a zuciyarsa. Ya yi kowa afuwa ya yafe komai.
Jin haka da Sulaiman ya yi sai y samu k'warin guiwar tuntubarsw da batun da shine ya yi musu saura.
Kansa a k'asa cikin nutsuwa ya ce "Baba zan roke ka arziki da alfarma dan Allah".
"Ina jinka Sule".
Baba ya fad'a a takaice.
"Baba so nake yi ka bani Dama na mayar da kai gida Funtua".
Wata irin nutsuwa ta dirarwa Baba.
Ya ce "Yaushe kake so na koma?"
Kan Sulaiman na kasa ya ce "Ni dai ko yanzu na shirya Baba don tuni na gama gyara gidan gabad'aya cike da yaƙinin ba zaka juyawa buk'atata baya ba. Don idan momi ta kammala shirya muku kayayyakinku kawai waya zaka yi mini na zo na tafi da ku".
"Allah ya yi maka albarka Sulaiman, Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka. Yau muna 10 ga wata idan Allah ya kaimu 10 ga watan da zai kama sai ka zo mu tafi. Kafin lokacin duk mun kamallah da komai ".
Sulaiman ya dinga godiya da fatan alheri ga Baba.
Ya sake cewa Baba na sake rokonka?"
Baba ya ce "Roke ni Sulaiman".
Baba ka dawo tare da Yaya Faruku tunda shima a can ya rayu kuma duk mun sani yafi son zamansa a Funtua. Ya dawo na taya shi cigaba da kula da ladi farm ".
Baba ya ce "Hakan za'a yi Sulaiman in sha Allah. Ai kasan ma ba zai yiwu muna Funtua Faruku na wata duniyar ba. K'afata kafarsa. Allah ya k'ara had'a kawunanku ya sanya muku tausayi da soyayyar junanku."
Sulaiman ya dinga amsawa da ameen.
Baba ya numfasa ya ce "Na roke ka Sulaiman?"
Kan Sulaiman a k'asa ya ce "Umarni zaka ba ni Baba".
Baba ya ce "Batun ba a gwadaben da zan baka umarni ba ne. Dan haka dole rokonka zan yi."
Jikin Sulaiman ya yi sanyi mussaman da ya ga yanayin Baba ya sauya zuwa alhini.
Murya ba amo ya ce ina jinka Baba".
Ya ce "Ka yiwa Allah ka yi hak'uri akan Abida ka yafe mata, ka yi mata adalci. Mace ce ita mata kuwa suna da rauni akan komai. Ban tab'a ganin abin da ya raunana Abida ba sai kai, ta yi laifi tabbas, amma tunda ta yi nadama ta yi kuka, ta bada hak'uri dan Allah ka yi dukkan iyawarka ka manta da wanccan laifin ka rik'e ta da amana, ka ji tausayinta kada don tana sonka ka yi amfani da hakan ka kulle zuciyarka akanta dan Allah Sulaiman".
Tausayinsa ya ratsa Sulaiman don kuwa a bayyane yake Baba na son Abida kowa yasan da hakan har ana rasa wa yafi so tsakaninta da Faruku.
Murya ba amo Sulaiman ya ce "In sha Allah komai ya wuce Baba. Na yafe mata, har zuciyata na huce da ita".
Dad'i ya kama Baba ya dinga fad'in "Allah ya saukar da albarka a tsakaninku, Allah ya shirya shirya muku zuri'a ya muku arziki marar yankewa.".
Daga haka suka shiga hirar duniya iri iri.

K'arfe uku daidai suka isa k'ofar gidan. Zuciyarta ta harba rabonta da garin gabad'aya tum rasuwar MAMI. Mamakin yadda aka to renovating gidan take to, don kowa ya kalla Sai ya sake kallon gidan an yi masa fenti mai kyau mai karshen tsada. Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:39]
Ba kuzari ta bawa James mukullin don ba tantama gidan ne ba batan kai suka yi ba.
Ya karɓa ya fita ya bude katafaren gate din zubin mahadi ka ture.
Ya dawo ya shiga motar suka isa cikin farfajiyar gidansu.
Abida ta dinga juya idanuwa tana tu'ajibin yadda gidansu ya Koma. Yaya Sule kud'i ya yi ne haka bata sani ba?"
Ya yi kokarin gaske ta tabbatar milyoyin da gidan ya kashe ba kad'an ba ne.
Ta nunawa James part din da zai kai kayanta. Razina ta dinga daukar wanda zata iya.
Ta bude k'ofar shiga part ɗinta.
Ta sandare a tsaye ganin yadda aka shirya mata falon tamkar a turai.
Ta leka kicin ta ga nan ma komai sabo ne cooker kuwa har an had'a da alamun ya kunna ya yi amfani da ita.

*Gobe ba zaku jini ba sai Friday in sha Allah*.
*A mini uzziri*.

*Na gode*

*Surayya Dee*
08032773332.
Save Restricted Content Bot, [Nov 14, 2025 at 16:19]
*Dingishin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332.

*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.

Ta leka store ta ga ya ajiye komai na abinci.
Ta fito ta shige d'akinta mamaki ya sake kasheta don kuwa kayan gadon masu k'ololuwar daraja ne.
Ta shiga bayi ta doro alwallah.
Ta shiga daya d'akinta ta tarar da k'aramin gadonta an yi k'aramar wadrof da ta dace da gadon. Dad'i ya kamata duk yadda aka gyara gadon sai da ta gane abinta.
Yanzu ya zama na junior don d'akin yafi dacewa da shi.
Sai da ta idar da sallolin azahar ta shiga kicin ta Fara soyawa James samosa da spring rolls dui da sun tsaya sun ci abinci a restaurant.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login