Showing 117001 words to 120000 words out of 148964 words

Chapter 40 - DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

da mu ya tayamu k'rbar gaisuwa ba. Sai ya sake bin y'ay'ansa suka bar mana gidan gabad'aya!
Haka shi da Yaya Asad da Yaya Faruk suka zubawa Abida ido ta tozarta aurenta saboda kaine mijin, da ace wanine daban da sun ce ta koma d'akinta tunda haka muka ga ana yiwa Yaya Hamida da Yaya Salaha.
Idanuwansa ya cika da k'walla.
Ya numfasa ya cigaba da fad'in still na danne komai da aurena ya zo takanas na niki gari na je har Abuja na gurfana a gabansa akan shi nake so ya karɓa mini auren.
Tabbas ya zo amma daga shi sai Yaya Usman a ranar kuma suka juya.
Ba kowa a bikina sai imu imu sai dangin MAMI.
Kenan laifin MAMI ya shafe nasabar baba K'arami, laifinta ya shafe hak'kin da muke da shi a kansa na shine d'anuwan mahaifinmu?"
Hawaye ya k'wace masa ya saka dukkan hannuwansa ya rufe fuskarsa.


*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da zasu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:15]
*Dinginshin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332

*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Ingattaun saiwowi daga daga Chad da Sudan da Nigeriarmu*.

Sai da ya shanye kukansa.
Sannan ya zarce da fad'in "Duk fa da haka a duk sadda ya faɗo mini ina masa waya na gaishe shi. Fisabidillahi idan mutum na gaishe aka d'auki lokaci bai jika ba adhe bai kamata ya lalubo ka ya ji lafiyarka ba? Ni ban masa komai ba. Ra'ayin uwata na girmama wnada ko uban da ya haife ni zan iya girmama ra'ayin uwata na bar shi. Da ta rasu na shiga taitayina na zubar da makaman yaƙina na gyara mu'amala ta da Ubangiji da kuma jama'a. Amman Baba da iyalinsa sun kulle zukantsu basa ganin rashin adalcin da suke yi mana. Na tabbatar idan y'ay'ansa na cikinsa da suka saba gaishe shi ya ji su shiru zai bibiya ya ji ba'asin shirunsu. Ni fa ba d'aya, da ace ko ya ya idan ya jini shiru tunda na zubar da makaman yaƙina zai lalubo ni ai zan ji dad'i. To amma sai na fahimci ma gaishe shi din nake yi bai d'auke shi abin arziki ba. Idan na kira shi zai amsa da murna, idan ban kira shi ba ya manta da ni, na cigaba da gaishe shine saboda alfarmar mahaifina. Wallahi duk sababin Baba k'arami ba zai share su Yaya Asad akan laifin Momi ba, zai bada hujjar ba ruwansa da ita, ba dan ita zai yi ba, dan ubansu zai yi."
Ya kammala da kuka na sosai tamkar ba namiji ba.
Wato Sulaiman kansa gabad'aya ya kunce ji ya yi gabad'aya tamkar an yi masa d'aurin huhun goro.
Ya yi ta maza ya aro jarumta ya ce "Ansari ka yi hak'uri. Ka sake hak'uri ka daure. Allah na son sulhu da kansa ya ce wa sulhu khair" .
Ansari ya ce "Na ji".
Dad'i ya kama Sulaiman ya ce "Yauwa Wazirin MAMI na gdoe maka".
Ansari ya ce "Daina gode mini don kuwa jinka ya zama dole yarda kuwa ban yarda ba".
Sulaiman ya ji tamkar an kwada masa guduma don yasan tantirancin Ansari.
Murya ba amo ya ce "Yanzu dai ya sake shiga rigar mahaifinmu, ka huce, mu je mu ba shi hak'urin ai ba gazawa ba ne. Idan ya dawo gida mu kanmu fi sai mun fi samun nutsuwar zuciya, kannenmu zasu daina gararanbar neman mafaka, za'a daina yi mana gorin gidanmu ya dare!
Sulaiman ya kammala jawabinsa cikin kwantar da harshe ainun.
Ansari ya numfasa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ka raka Yaya Hamida da Anisa sune basa nemansa ko kad'an amma Ni da Saddiqa muna gaishe shi. Ita kuwa anty Bilki ai tana hannunsa ko".
Da dan kuzari Sulaiman ya ce "To ko auren oga da Bilki da Baba ya k'ulla ai ya isa ka gane baya kinmu. Haka oga Asad din baya kin MAMI. Kuma ko dan Yaya Faruku ma wani abin Duk a barshi ya wuce.".
A zafafe Ansari ya ce "Oga Asad kawai ina kallonsa ne.
Wallahi ba dan mutuwar MAMI ta sauya mini rayuwata gabadaya ba da na marawa Yaya Hamida baya mun maka Asad a kotu bisa aurewa MAMI d'iya da ya yi. Zamansa Babba Bai amfane mu da komai ba. Ni fa da ya dauke Baba Babba a farko ban ga laifinsa ba. Yana da damar da zai yi hakan. Aman da MAMI ta rasu Bai yi tsayuwar daka ya dawo da gidanmu da ya wargaje ba tun lokacin nake kallonsa kawai gaba ne ba Zan yi ba.
Amma ba ruwana da shi. Kai ko fa Yaya Farukun da kowa yake fad'in karamine Ni ban ga karamcinsa ba don kuwa ban ga gudunmawar da ya bayar wajen gyaran zumunci ba. Ni fa yini na gano Baba k'arami ba Shi da wata alfarma tunda MAMI ta yi laifi to shima ya yi.
Ka ga ba dan ka tafi ka bar Anty Abida na tsawon shekarun nan ba da Slsai ka sahale mata idan ya so ta samu wanda za'a nuna masa daddatako. Amma tunda ka yi shekaru hud'u ka barta da aurenta ba kuma ta gajiya ba to nasan ta jiki. Kai kuma ka wuce iyaka wajen hukuncin shiyasa na hak'ura. Ba dan haka ba Wallahi matuƙar ka ce zaka zauna da ita to sai na gurfanar da kai gaban shari'a ina nemawa mami hak'kin an wulakanta ka saboda ita amma ka kafe kana zaune da ita". Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:17]
Zuciyar Sulaiman ta harba wai waddane irin yan bala'ine su haka?
Tabdi jam. Lah shakka idan suka ji kalaman Abida akan Mami sai yak'i ya sake ballewa kuma matuƙar bai sahale mata ba, sai sun maka shi a kotu ba wai daina mu'amala zasu yi da shi kawai ba. A a sai sun nemawa mami hak'kinta akansa. Lallai Abida kanta na ja da ta roki arzikin ya boye musu.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Sulaiman yake fad'a a fili don ya rasa kalmar da zai furta ko guda.

*Abuja*

Hafcy da murana ta dawo daga makaranta a dalilin an akfe musu result dinsu na second semester.
Sosai sakamako ya yi kyau don kuwa tana matakin ajin farko(first class).
Da kuzari ta nunawa Aysha. Ta ce Yaya aysha duba Ki ga ni".
Ta karba ta gani ta murmusa ta ce "Hafcyn Dady lallai yau kina da kyauta. Saura ki tafi gunsa ban sa ni ba ".
Hafcy ta murmusa ta ce "Idan zan hau saman ba zan manta ba Zan leko na fad'a miki.
Daga haka ta wuce zuwa d'akinta.
Da daddare sai da ya dawo daga sallar isha sannan Hafcy ta. Hau sama da yan rakiyarta Aysha da Bilkisu.
Yana zaune yana rik'e da Baba K'arami yayin da Bilki ke gefensa tana shayar da Baba Babba.
Suak shiga a nutse bayan an basu damar Su shiga.
Kusa da shi suka tsugunna suna sake gaishe shi.
Da murna sosia Hafcy ta ce "Dady albishir".
Da walwala ya ce "Goro fari kal Hafcyna".
Ta mik'a masa takardar hannunta.
Ya gyara kwanciyar Baba Babba a jikinsa ya bude.
Ya duba ya d'ago da garin ciki ya ce "Gaskiya kin cancanji albishir da abu mai daraja.
Dad'i ya kashe ta don idan suka yi kokari kyautar bajinta yake yi musu tun suna yara.
Ya ce ",Ki nutsu ki rubuta mini dukkan abubuwan da kike bukata, da ikon Allah zan yi miki.
Kafin nan ma yanzu zan Baki kyautar abu mai k'ololuwar daraja a zuciyata. Ki taya ni adanawa, ki tafi da shi har gidanki, ki ta kallo kina jin dad'in na miki kyautar a in da nake matuƙar so.
Farinciki ya lullube zuciyarta.
Yayin da Aysha ta tafi tunanin wanne abune haka za'a baw Hafcy?
Tana kallon yadda shimfide yaron da ya yi barci.
Ya mike.
Ya mik'a hannunsa ya d'auko tafkeken hotonsa da mominsu da aka zanasu tamkar a kirasu su amsa.
Ya mik'a mata ba tare da ya ce "Uffan ba".
Wani irin farinciki ya kamata. Aysha kuwa murnar ya ce hoton uwarsu na da k'ololuwar daraja ya sanya ta tashi ta rungume shi cikin shagwaba take fad'in "Amma ni fa Dady? Na kawo maka sakamakona.masi irin wannan darajar amma baka taɓa mini irin wannan kyautar ba."
Bai ce komai ba ya sake ta ya dauko d'ayan da suke sanye da k'ananun kaya cikin snow a k'asar Canada ya mik'a mata ya ce "Ga shi ke ma shikenan?"
Tana dariya ta ce "shikenan".
Yana juyawa ya ga Bilkisu na kuka.
Ya isa da ita ya ce "Zo nan y'aruwata menene".
Cikin kuka ta ce "Ni ban samu ba daddy."
Ya ce "Zan lalubo miki wani a d'aki ki saka a gefen gadonki. Idan kima na falon k'asa ma kina so na bar miki shikenan?"
Ta daga kai tana goge hawaye.
Bilki tana kallon Aysha da take ta fallin ya basu kyautar abin da yake tsananin so. Ta girgiza kai bata ce komai ba. Amma cikin ranta fad'i take yi da kinsan dalilin baku hotunan da kin sake takure zuciyarki da bak'in ciki.
Suka tafi cikin murna da godiya mai yawa.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shikenan na kwashe hotuna, ba sauran damuwa ko sarauniyar sheba?"
Ta yi gajeran murmushi ba ta ce uffan ba.
Ya ce "To ki bugawa Faruku waya ki ce masa na cire hotunan maimurabus don akai akai yake tambayar na cire kuwa?"
Dariya ta k'wace mata ta sosia. Ba dan komai ba, sai yadda ya ce maimurabus.da bakinsa.
A d'akin Aysha suka dire.
Ta kalli Hafcy ta ce "Oh Astagafirullah muna ta zargin Dady ya mance da momi yana cin duniyarsa da tsinke ashe ba haka bane. Ashe dai ta nan mak'ale a zuciyarsa.
Hafcy ta ce "Yau na tabbatar Dady namijin duniya ne. A gaban anti Maigado ya ce hotonsa da momi shine k'ololuwar abu mai daraja a gunsa wow".
Ta yi juyin nishadi. Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:19]
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya jiƙan ki momi, yau kam munsan kina da alfarma."
Bilkisu da bata fiye magana ba
Ameen kawai ta ce.
.......
*Kano*
Sulaiman Hamida, Ansari da Anisa.
Suna zaune a falon Hamida.
Dukkansu kowa ya tunzura Idan aka cire Anisa da bata um bata um um a cikinsu.
Amma dai tafi karkata ga ra'ayin Yaya Hamida.
Yayin da Hamida kuma ta canja shawara tunda Ansari ya ce ba zai je Abuja ba itama ta matse akan bata da lafiya ba zata iya doguwar tafiya ba. Sulaiman ya ce su tafi a jirgi ita da Anisa shi kuma ya d'auki Ansari su tafi a motarsa.
Yana kallonta tana kallon Ansari suna magana da ido.
Sulaiman ya yi shiru yana kallonsu cikin tsananin mamakinsu. Da ido suke magana kuma su fahimci junansu.
Suan cikin haka mijinta ya dawo.
Ya zauna yana marabtarsu tare da tsokanar Anisa ina nassa Yajin?
Ta sinne kanta a k'asa don bata iya sakewa da shi.
Ya ce "Sulaiman yaushe ne tafiyar taku?"
Sulaiman ya kass boye mass ya ce "Ni da a son Raina mu tafi gobe zuwa jibiu zauna don Ansari ya Koma saboda aikinsa.
Amma ka gansu nan sun canja shawara wai kuma ba zasu ba".
Mai shari'a ya ce "Amma Hamida ai mun gama magana gobe zasu tafi. Har na ce Baffah ya siyo mata ticket ta ce wai zaka siya musu. Na d'auki kudin na bata na ce ta rik'e sai ta yiwa Baba tsaraba tunda na yi niyya. Amma me ya saka ki canja shawara haka Hamida?"
Ya tambaye ta cikin sassauci.
Kanta na k'asa ta ce "Saboda an nuna mana bamu da kowa, to mun tsyaa a hakan Allah ya isar mana, gorin da ya janyo mana kuma a gidajen aurenmu nan ma da sanin Allah."
Ta kece da kuka na tashin hankali.
Anisa ma ta shiga yi. Ansari ma ya fara.
Yayin da Sulaiman ma ya amsa jarumta shima ya kifa kansa a hannun kujerar hawayensa na diga.
Jikin mai shari'a ya yi sanyi ainun.
Ya sassauta murya ya ce "Ita rayuwar nan ai gabad'ayanta k'alubale ce. Hak'uri ne kan gaba. Idan har zan fad'a muku gaskiya ku yarda dole ku bi Baba Babba. Ko kuna so ko ba kwa so wan mahaifinku ne.
Bari yau na fad'a miki abu d'aya ba dan na yi muku sulhu ko dan ki ji dad'i ba ne, a a iyakacin gaskiyata kenan. Ke ce kike gaba da shi amma shi ba ya yi da ke. Ko kinsan akai akai yake k'irana?
Na saba gaishe shi, to idan ya jini shiru zai kira ya tambayi lafiyarki da ta y'ay'anki tare da sake jaddada mini na yi hak'uri da ke saboda ke mace ce mai rauni. Tabbas ina sake yin hak'uri da ke ne saboda shi. Ba irin rigar mutuncin da bai sanya miki ba a idona. Duk da kin shata layi da shi bai fasa siya miki mutunci a matsayinsa na uba kuma walliyinki."
Da kuka ta ce "To yana yi maka hakan amma ka goranta mini ka tozarta ni har kana fad'in zaka kore ni a gidanka?"
Ya sake sassautawa ya ce "Ba fa Har cikin zuciyata na fad'a ba, na fad'a ne dan kiji irin ciwon da nake ji idan rashin k'irkinki ya motsa. Na fad'a ne dan ki ji ciwo Ki gyara kuskuren da kike tafiya a kansa.
Amma yanzu ki yi hakuri Hamida. Ki warware zuciyarki ki karbi gaskiya. Idan kika ji Maganata ni kad'ai nasan ke zan yi miki. Na farko da azumi da ke Zan tafi umrah kinsan bara ban tafi da ke ba, to bana Zan tafi da ke sannan ni da kaina zan raka ki Abuja. Yanzu gobe kai Sulaiman ka tafi da Ansari da Anisa. Ni Kuma zamu taho da hajiyata da yamma Sai Ku tare mu a airport ku kaimu hotel din. Da safe sai ka zo ak d'auke ta zuwa gidan Baba."
Sulaiman ya yi maza ya dinga godiya da fatan alheri, yana jin nutsuwar ya samu mai taya shi saita su.
Mai shari'a ya ce "Hakan ya yi ko Hamida?"
Ta kalli Ansari da ido. Ya Mata alamar ya amince.
Murya ba amo ta ce "Ya yi ".
Da walwala ya ce "Allah ya yi mini albarka yanzu tashi ki kawo musu abunci. Kina Babba kin tasa su a gaba da kuka. Dan Allah ki zama jaruma ko Sulaiman din da yake babba Idan kin nutsu ai uwace ke. Maza maza je ki saka a shiryo musu abinci. Idan kin so ma ku dan fita wani wajen da zai saka ku nishadi da walwala sai ku ci abincin a can.".
Ya tashi ya shige ciki.
Ansari ya hak'ura ya yarda zai je don kuwa mijin Yaya Hamida da Yaya Sulaiman sun kashe shi da kabaki da ba'adi. Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:21]
Sulaiman ya kalli Anisa ya ce "Yaushe kuka Koma Katsina ne?"
Ta ce "Bamu wani jima ba. Yanzu ma kuma tashi zamu yi".
An masa transfer zuwa Yola."
"To Allah yasa albarka yanzu ina yaran?"
Ta ce suna wajen Hajiyarsa tunda aka yi hutun makaranta"..
Ya ce "Hakan ya yi".
Ya sake cewa y'ay'an Bilki na zuwa gidanki kuwa?".
"Suna zuwa sosai. Nima in zuwa na gansu ko na yi musu aika.
Amrah ta shiga
S. S 3 next year zata kammala sakandire ".
"Ma sha Allah! Ni ban je ba, al'amura sun sha kaina sosai amma idan na dawo zan je na gansu"
*Abuja*
Da yamma Sulaiman suka isa Abuja. Anisa ya ta ce a kaita wajen Saddiqa ta kwana gobe Sai Su zo tare.
Sulaiman ya Kira Saddiqa ta bada tabbacin akwia Dakin da zata sauketa. Don ya imyi zaton irin d'aki d'aya ne tunda a Kaduna suke zaune zuwa Abuja take yi kawai lokacin Hutu.
Suka kaita sannan suka gaisa da ita cikin farinciki tunda ita ta bata ganshi ba sai lokacin.
Suka rabu akan sai gobe mijinta zai kawo su tunda tasan gidan.
A hanya sai da Sulaiman ya yiwa Ansari wuta wuta kafin ya yarda ya bishi ya sauka gidan Baba. Da ya ce zai je ya samu masauki ya zo gobe kawai.
Tare suka shiga falon. Baba na zaune yana dakon a k'ira sallar magariba ya wuce masallaci.
Ya dinga marabtarsu cikin walwala.
Suna durk'ushe a gabansa kan kafet.
Cikin girmamawa suka gaishe shi.
Ya amsa cikin bayanannen farinciki.
Tare da tambayar Ansari iyalinsa.
Ya sanya su a gaba suka tafi masallaci tare.
Sai da suka dawo Momi tasan sun zo, suka gaisheta ta amsa da tambayar maijego tunda matar Ansari ta haihu wata daya da ya shud'e an samu MAMI.
Aka basu abinci. Suna ciki ci junior ya fito.
Yana ganinsu ya tafi da sauri kusa da su. Ya tsaya yana kallonsu.
Yayin da Baba Babba ya tsaya yana kallon yaron.
Can ya matsa kusa da Sulaiman ya ce "Dady yaushe ka zo?"
Sulaiman ya ce "Dazu na zo".
Ya kalli Ansari ya ce "Uncle ina yini ?"
Baba ya ce "A ina kasan uncle din?"
Ya ce "Na gane shi fa. Ammi tana nuna mini hotonsa tana ce mini idan Dadyna bai dawo ba shine Dadyna kuma ta ce mini shine ya siya rago biyu na sunana".
Jikin Ansari ya yi sanyi Ashe Abida tana nunawa yaron shine makaddashin ubansa ba su oga Asad ba.
Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi.
Ya mik'a masa hannu ya ce "Lafiya lau junior ya kake?"
Ya ce "Ina lafiya, ammina ma tana lafiya ta je hospital ta kusa dawowa".
Ansari ya kafe shi da ido yana kallon carbon copy na Dr Sulaiman.
Junior ya kalli Sulaiman ya ce "Dady yaushe zamu tafi gidanmu ne? Ina son ka saka ni a school ".
Murya ba amo ya ce "Zamu tafi junior."
Baba ya ce "Zo ka zauna kusa da ni ka barsu su ci abinci kai tambayoyinka bass k'arewa.
Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce "Baba dukkanmu zamu hadu da safe anan gobe matan zasu iso da wuri in sha Allah."
Baba ya amsa da fad'in "Alhamdulillahi Allah ya yi muku albarka gabad'ayanku".
Suka amsa da Ameen Baba.
A daren Baba ya k'ira dukkan y'ay'ansa ya fad'a musu gobe su zo da safe.
Cikin ikon Allah Salaha tana gari, tana gidan Bilki sai Abida ta tashi a asibiti zata biya ta d'auko ta.
Sai da suka dawo daga sallar Isha sannan suka rabu da Baba.
Suka yi d'akin da zasu kwana shi kuma ya yi cikin gida.
A wannan daren Baba bai runtsa ba . Kwana ya yi yana sallah da adduar samun nasara da alheri cikin zaman da za'a yi. Idan ya yi addu'a, ya yi kuka a sujjuda, ya yi wuridi har asuba bai runtsa ba.
Ya tashi da yaƙinin Ubangiji ya ji shi.
Oga Asad ya murd'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login