Showing 135001 words to 138000 words out of 197906 words

Chapter 46 - GABA KURA BOOK COMPLETE BY SADNAF.txt

Sadnaf   

02 Nov 2025

4551

kudin kayan naga itama muhseena ta karaso da kwandon kayan da ta siya.

D'auke kaina nayi kamar banganta ba


Dan idan har tamin ma magana a gaban Ishama nunawa zanyi bansanta ba


Sai naci Sa'a bata cemin komai ba mun Kuma riga ta biyan kudin kayanmu.

Ledar kawai na karba daga hannun Ishama nayi waje dan so kawai nake mu bar super market din.

Muryar ishama naji daga bayana tana "wai saurin me kike haka ne ba zaki jirani ba"?

Abin hawa kawai na tare mana dan bana so muhseena ta fito ma ta ganmu


Sai da na ga mun bar super market kafin na samu nutsuwa

Koda muka isa gida a ranar wuni nayi da tunanin abinda ya kawo muhseena Nigeria, Nijeriyar ma garin da nake.

Ganin Muhseena na nufin na Kara komawa ruwa tsundum idan har na biyewa zuciyata da Muhseena ba zan tab'a daina wanan abin da ya har kasan zuciyata nake san na daina gabad'aya ba.

Addu'a kawai nake akan Allah ya sa kar na Kara ganinta ko ta San inda nake dan musheena Sam bata san abinda ake cewa Abun kunya ba.

A ranar muka danyi soye soyen tarb'ar Abba dan sai kiransa muke a waya.

Washegari kasancewar akwai makaranta

Da sassafe na tashi na dan taya Ishama aiki kafin na shirya na tafi makaranta.

Nayi mamaki da Muhseena bata wani matsa min akan baya ba.

Na kusa isa titi naga wani mota na ta min horn ta bayana

Ban waiga ba dan idan da sabo na Saba da bina da samari ke yi a kafa ko a mota.

Ban ko juya ba har sai da na fara k'ok'arin tsallaka titi ban da karatun mu ya dau zafi banso ma zuwa makaranta ba tsabar matsuwar da nayi naga Abba.


A gabana motar ta tsaya Kara matsawa nayi dan koma waye ba kula shi zanyi ba.

Banda Saleem ma ni ban taba ganin wani naji Ina sha'awar kulawa ba dan gani nake ma idan na tsaya kula wani Saleem zai iya sani dan daga yadda yake yawan min magana akan kula samari nasan zaiyi kishi sosai.


Gashi samarin balain nacin tsiya garesu har gidan Ishama suke biyoni.

"Sai kizo ki hau mu sauke ki a makarantar"

Dagowa nayi na Kalli ta inda naji muryar muhseena

Tana kame a baya sanye da wani bakar doguwar riga

Murmushi ta sakar min ta Bude motar tafito tana "Ai nasan dole zaki je makaranta shi yasa nace bari na tareki ta nan ai yanzu ba zan bari ki Kara Raina min hankali ba"


Muhseena dan Allah dan Annabi ki rabu dani na daina wanan rayuwar da kike so mu ringa yi ki kyalleni dan girman Allah

Nace tare da tsallaka titi da saurina na hau tafiya Ina Jin tana Kiran sunana ban ko kulata ba har sai da na yanki lungun da zai sadani da makarantar mu.

A takaice gabad'aya haduwata da musheena ya jagula min lissafi.

Idan har na biyewa musheena kila kunyar da ta sa muka ji a Cameroon kadan ne akan Wanda zanji a yanzu.

A ranar ban wani gane Mai aka koya mana ba har aka tashi.

Sai dai me Koda na fito muhseenar na Kara cin karo da ita a gate

Haka ta tare min hanya ta hana ni wucewa ta hau cemin itama ai ba wani abu tace zamu yi ba shikenan ba zamu yi kawance da ita ba kenan

Duk ta inda na bullo mata haka ta kafe ta nace a karshe sai cewa tayi idan ban bata lambata ba ita gidanmu zata bini idan kuma bana so tazo nazo naga gidansu"

Haka na bawa muhseena lambar wayata ba dan raina naso ba inda tace Koda wrong number na bata zan ganta a gidanmu.

Nasan kadan da aikinta shiyasa na bata lambar nawa.

Allah Allah nake na isa gida dan nasan kila Abba ya karaso.

Murnar haduwa da Abba yasa na manta da wata muhseena

Ina zuwa gida na tarar da Ishama a cikin shiri da duk abincin da tayi na tarar Abba ni kadai take Jira dan tace ta kira Abba ya iso gidan ne dai ba karasa ba


Uniform kawai na cire na Saka doguwar riga nida Ishama muka nufi gidanmu da niki nikin Abubuwan da muka ajiyewa Abba.


A tsakar gida muka tarar da mama tana tsintar shinkafa

Ishama ce kawai tayi sallama ni ko kallonta banyi ba na doshi dakin Abba na Bude.

Gyaran da muka danyi wa gidan yasa ko'ina yayi fes fes.

Ciki muka shiga muka ajiye kulolinmu.

Ishama kuwa ta Ciro sabon zanin gadon da ta zo dashi muka Kara shimfidawa akan katifar muka zauna zaman jiran dawowar Abba.

Mama kuwa sai Kai da kawowa take tana kallon dakin da muke zaune.

Dirin motar da najiyo yasa na mik'e nayi waje da guduna dan har ga Allah na matsu naga Abba


Koda na fita Abba ne a tsaye wajen boot ana sauke kayansa gefensa Kuma wata mata ce fara ta Sha lullubi da bakin mayafi.


Ban tsaya wani kare mata Kallo ba na Kankame Abba tare da rushewa da kuka

Dan na gama cire rai da Kara haduwa da wani nawa yau bayan Ishama ga Abba da naga tsufa kawai ya dan karayi da rama amma Yana nan a yadda na San shi.

Dak'yar ya janyeni daga jikinsa Yana bubbuga bayana da "Kukan Kuma na menene ba gashi nan na dawo ba"

Muryar mama naji akaina cikin ihuun murna tana "Jafar Kai nake gani ko mafarki dai nake Kai Alhamdulillah Allah na gode ma da ka dawo min da mijina lafiya"

Abba hade rai naga yayi ya juya ya Kalli matar dake tsaye a gefensa har lokacin fuskarta d'auke da murmurshin Yana "Anna kizo mu shiga ciki Siyama ku d'auki kayan nan mu shiga da shi ciki"


Daga haka ya d'auki wani akwati matar da ya kira da Anna ta hau bi shi abaya

Ishama da itama tun fitowa ta ta biyoni waje rungume Abban ne dai kawai ba tayi ba amma itama ta karasa wajen da muke tsaye


Ciki muka shige gabad'aya da kayan da suka zo dashi.

Kai tsaye Abba ya shige dakinsa matar dai na biye dashi

Mama kuwa sai cewa take ikon Allah wanan Kuma fa?

Ba Wanda ya bi ta kanta har muka shiga dakin Abba gabad'aya muka ajiye kayayyakin hannunmu


Inda Abba ya zauna a gefen katifa matar Kuma ta zauna a kasa tare da tankwashe kafarta


Hada baki muka yi wajen gaishe ta inda ta amsa cikin fara'a.

Mama kuwa da naga gabad'aya hankalinta a tashe yake ta fado cikin dakin tana "Jafar wanan Kuma waccece"?

Abba ko kallon maman baiyi ba inda ya kalli matar da muka Ji ya kira da Anna Yana "Anna ga yaranki nan da nake baki labari


Ishama,Siyama ga mamanku nan itace matar da na aura sati biyu kenan da daurin aurenmu"


Wani mugun Ashar mama ta narko tare da ja da baya kamar an watsa mata ruwan zafi


Inda ni Kuma naji wani balain sanyi a zuciyata kamar yadda naga Ishama itama fuskarta ta washe cikin farin ciki.

Dan har ga Allah Idan muka ce bamu ji dadin auren da Abba yayi ba nayi karya

Mama masifa ta hau cikin ihuu tana ita Abba zai yiwa haka duk wahalar da ta sha dashi sakayyar da zai mata kenan

Ai ko kallonta Abba baiyi ba ya ruko hannuna Yana nazo na bashi labarin Cameron.

Kuka wiwi mama ta ringa yi dan duk ba Wanda ya kalleta tana Kallo muka zuzuba abincin da muka yiwa Abba da Aunty Anna da muka lura tana da fara'a.

A takaice sai da muka Kai dare a gidan

Mama kuwa ta rufo kanta a daki.

Kafin mu koma gidan Ishama Abba ke fada mana yadda ya Auri Aunty Annan da Allah ne ya hadasu


Tana da Yara biyu mata suna gidajen mazajen su mijinta mutuwa yayi.

Nidai naso tunda Abba ya Kara auren na ace sakin mama yayi amma Banga alamar zai saketa bansan Kuma Mai yasa ba.

Abba a yanzu nasan Shima zai dan samu nutsuwa da Auren da ya Kara muma kanmu hankalin mu yanzu ya kwanta munsan akwai Mai kula da Abba.


Washegari ma Ina dawowa daga makaranta muka Kara komawa gidanmu


Da abincin da Ishama tayi.

Dan munsan ko Wanda muka Kai na jiya ba lailai su iya cinyewa ba.

Aunty Anna na da balain kirki dan janmu kawai ta ringayi a jikinta tana mana Hira.

Mama Kuma k'ofar dakinta a kulle bata nan ji nayi dama kar ta dawo ma ace ta tafi gabad'aya kenan


Satin Abba daya da dawowa Saleem yazo ya gaishe dan a ta waya na fada masa akan Abba ya dawo kullum muna makale a waya


Muhseena kuwa kira da message da take min kuwa baa magana

Reply kawai nake iya mata akan tayi hakuri ni ba zan iya cigaba da wanan rayuwar ba dan yadda ma Ishama ke samin ido duk abinda nake idonta na Kai,musamman take karbar wayata ta duba duk da karamar waya ce a hannuna


Kira ko message din muhseena duk gogewa nake dan ban ma yi savin lambarta ba.

A haka Saleem yazo ya gaida Abba a lokacin Munyi hutun zangon karshe inda da mun koma ss3 shikenan mun gama makaranta.

Fadar San da nake wa saleem da shakuwar dake tsakanin mu bata bakine


San Saleem ya danne komai a zuciyata Wanda a yanzu bani da buri ko mafarkin da ya wuce naga ya zama miji a gareni


Zuwan da yayi na karshe yake cemin Abba yace ya turo manyansa a tsayar da magana.

Koda fadamin haka ban mamaki ba dan naga Abba kamar ya matsu yaga nayi Aure

Dan idan ta shine ma bana Jin zai barni na gama secondary din


Ishama kanta kullum bata da maganar da ya wuce na aurena da saleem

A washegarin da Saleem zai koma yazo gidan Ishama da yamma dan dama a gidanta nake har lokacin ba yadda Abba baiyi ba akan na dawo gida dan ya dan gyara daya dakin amma firr Ishama ta dage akan a gidanta zan zauna.

A inda muka Saba zama dashi muyi hira muka zauna inda gabansa Kuma cake ne da dan lemon da na kawo masa dan ya tab'a dan indai zai zo sai Ishama ta sa min masa girki ganin ba wani ci yake ba yasa muka koma yi masa snacks.

Magana yake min akan zuwa Cameron wajen Ammu inda yace kafin yaje wajen Ammu akwai wani Abu da yake so yayi kafin ya tafi yana tafiya idan ya dawo in sha Allah zai turo manyansa.


Murmushi kawai nayi dan har ga Allah Ina balain Jin kunyar Saleem

Sunana da ya kira yasa na dago inda ya fara magana Yana "Kina ganin yanzu idan ummi ta ganki zata gane ki"?

Indai zai min maganar Aunty Hajiya sai naji gabana ya fadi

Ji nake dama ba itace Mahaifiyar sa ba

Murmushin yake nayi Ina dan Jin tashin hankali na rufeni da tambayar da yamin

"Mai zai hana zata iya ganeni mana ai ba wani canjawa nayi ba Mai yasa kamin wanan tambayar"


Shafa Kansa ya hau yi har da cire hulan da ya sa ya ajiye sai da ya dan murmurza yatsar sa cikin dan murmushin da idan yamin sai naji kamar na narke saboda Sansa da nake ji Yana Kara fusgata

"Wallahi ummi ta matsa min akan zata zo ta ga wacce zan aura ni Kuma so nake sai na aureki kafin ta ganki dan gani nake idan har ta gane ke zan aura zata yi fushi sosai dani Dan baki ga Neman da ta Miki da na d'auke ki ba,kinsan baa Dade da ta fara daina min maganarki ba nasan zata ji ciwo idan ta gane duk Neman nan da nake miki nasan inda kike toh wanan abin kawai ke balain samin fargaba wallahi


Yadda ta rantse akan sai ta ganki dinan da kyar ta bari manya su zo batare da ta zo ta ganki ba tukunna"

Danne tashin hankalin da nake ciki nayi inda na jefa masa tambayar "Toh yanzu ya zaka yi kenan kasan koman Daren dadewa dole dai ta gani?

"Kinsan me nake tunanin zanyi"?

Girgiza masa kai nayi

Inda ya hau magana Yana "zan San yadda zan tsara ta manyan su fara zuwa,idan har suka zo din to da sadaki zasu zo a daura auren kawai idan har na tabbata da an riga da an daura Aure nasan Koda ga baya ta zo ta ganki fada kawai za tayi min ta hakura tunda an riga da an daura auren kinga hankalina ma a kwance zan karasa Shirina nasan kindai riga da kin zama matata ko ya kika ce"?

Kai na gyada masa dan har ga Allah hankalina a tashe yake idan na tuna abinda ya shiga tsakanina da Aunty Hajiya sai naga ko an duara auren zata iya sawa ya sakeni duk da nakan yi tunanin kila Kuma ba zata yi haka ba dan dole idan ta dage ya sakeni sai yaji dalili,dalilin kuwa da nasan itama ba zata so danta ya tab'a sani ba har ta mutu.

A haka muka dan tab'a hira ya mik'e akan zai tafi.

Dama a motarsa yazo har waje na raka shi inda yace na daure na yi charging wayar da ya kawo min mu ringa Dan charrtin ko ba yawa

Karya dama na masa akan babbar wayar d'auke min hankali take daga karatu shiyasa bana son amfani dashi.

Nan kuwa Yana kawo wayar ishama ta Kara kwace wa ta boye.

Ina tsaye Ina daga masa hannu har sai da ya bacewa ganina

Ina k'ok'arin juyawa na koma ciki na hango muhseena ta nufo wajen da nake tsaye

Fitowa nayi daga cikin gidan gabad'aya hankalina a tashe da ganin musheena da na rasa yadda zanyi da ita ta kyalleni

"Ko ki barni na shiga gidanku na zauna muyi hira ko kizo muje kiga gidanmu Siyama dan wallahi ba zan daina zuwa wajenki ba kinji na rantse Miki nace miki Nima na daina ko ba wani Abu zamuyi ba"

Yadda muhseena ta dage nasan idan har na barta ta shiga ciki Ishama sai ta mata kaca kaca dan daga yanayin dressing din da take ba Mai ganinta ya Mata kallon matuniyar kirki.

Na ji Dadi da Saleem bai ganta ba da bansan kallon da zai min ba

Duk yadda naso na koreta akan taje zan zo ki tayi.

Akan dole naje na hau motar da driver ne ya kawota muka nufi gidansu.

Gidansu a GRA yake katoton gaske Hira kawai take Jana dashi ni kuwa Allah Allah kawai nake naga gidan nace Mata zan dawo Dan gabad'aya hankalina na gida bana so Ishama ta gane bana nan.

Duk yadda na so tsayawa a waje musheena sai da ta dage min na shiga cikin gidansu.

Muhseena so take ta maidani ruwa ni kuwa ba zan tab'a biye mata ba dan ni kadai nasan dauriya da danniyar da nake da zuciyata dan na yakice wanan mumunan abun daga Raina.

Na riga da nasan halin musheena da duk wani wayonta gidansu Babu kowa kuwa

Hade rai nayi da naga tana wani nanarkewa inda nace Mata nidai tafiya zanyi tunda naga gidan ni zan ringa zuwa kar ta sake ta Kara tunanin zuwa gidan yayata nan na Kara rantse mata akan nidai ba zan sake wanan abin ba ni Aure ma zanyi ya kamata ace itama tayi auren mu ajiye Wanan abin da ba abinda yake haifar wa mutum sai tashin hankali da Jin kunya

Murmushi kawai tayi tace min taji itama ai bata ce wani Abu zamuyi ba kawai ita dai na ringa kulata muna kawancen


Toh kawai na ce mata na ce mata zan tafi


Haka ta fito na Kara hawa motar suka maidani gida inda ta dage min da itama fa ta Daina na saki jikina da ita.

Na ringa zuwa gidan su ita bata da kawaye ne a kasar tunda suka dawo

Ita kadai ce da mamanta da Yan aiki.

A haka dai suka saukeni bayan na mata alkawarin kulata.

Na shige gida da saurina

A lokacin ana kiraye kirayen sallah Magriba

Koda na shiga dakina na shige dan nasan idan har ba shagari ne ya dawo ya cewa Ishama bai gani a waje ba Ishama za tayi tunanin yanzu Saleem din ya tafi.


Saleem

Kunnensa ya baza Yana kallon Hajiyar Shagalin da ta runtse idonta hawaye nata zubo mata


Tunda suka dawo Nigeria ya Sako ta a gaba akan ta Kai shi wajen dangin mahaifinsa ko ta bashi labarin abinda ya rabasu har take yiwa mahaifinsa wanan kiyayar

Sai dai duk lokacin da ya mata magana sai tace masa ba yanzu ba ya bari ta nutsu tukunna ita dai ya kaita wajen matar da zai aura ya ganta.

Idan har ba bori yayi mata ba bai ga alamar ta shirya nuna masa dangin mahaifinsa ba

Wanda a awanan gabar Yana bukatar saninsu ko dan su shige masa gaba wajen Neman auren da yake so yayi.

A haka ya Sako Hajiyar Shagalin da yaga tana ta kauce masa har sai da ya samu yau ta yadda zata bashi labari.

Sai da ta kwashi mintuna wajen ashirin tana sharar hawaye Kafin ta fara bashi labarin

Auwal mahaifinsa......


AUNTY ZEE MOM MUJAHID KAYAN MATA 08162859027

ASSALAMU ALAIKUM AYAUMA DAI GASHI NAZO MAKU DA NAU IKAN KAYAN GYARA SANYI SAIDA GYARAN HQ INA WADDA NI IMA TA DAUKEMAWA DAFATAN KINSAN MUHIMMANCIN NI IMA DAFATAN KINA BANBANCE NI IMA DA RUWAN INFECTION DAN WATA INFECTION YAYI MATA KATUTU A MATANTAKARTA AMMA TANA RAWAR KAN NI IMA TAYI MATA YAWA

KINTABA SHAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCIN DA A LOKACIN DA DUK KIKA SAYA SAIKIN QARA KO KUWA DAI TARKACE AKE BAKI

INA WADDA TA BUDE DUK SANDA ZA AYI HARKA SAI AN HADE CINYOYI SHINKINSAN AMFANIN MATSI KO KUWA ZAUNE KIKE HAKANAN TO BARI NAGAYAMAKI INDAI HARKINSAN KIN BUDE KI SHA MAGANIN DA ZAI MATSE KI CIKI DA WAJE DA MIJINKI ZAI SAN MACE YAKE AURE KEMA KANKI IDAN KIKAJI KIN MATSE KINFI GANE ABIN YANDA YAKAMATA

SHIN RASHIN GAMSUWA NE KIKA TABBATAR MIJINKI BAYAYI DAKE SHIYASA WULAQANCI KALA KALA KIKE FUSKANTA A WURINSHI KIZO ABAKI KAYAN DA ZAKI SAN FARINCIKIN AURE A KALLEKI DA DARAJA FA ARZIKI NE


AKWAI BANGAREN MAZA MARASA SHA AWA WANDA DA ANYI SO DAYA ANGAMA SAIKUMA WANI SATIN KO WANI WATAN SO DAYAN MA KE BAKI SAMUN GAMSUWA AKWAI MAGANIN DA ZAKI BASHI ZUBA MASHI KO A LEMU NE KIBA DAN ALBARKAN? GYARAN AURE NE KIKAYI DUK A CIKIN TAIMAKO NE INDAN KINSAN MASU HAWAN JINI BASU SHANSA

MAGANIN SANYI MAI KANKAT MAI AIKI MAI SUNAN SHA KI WARKE KO WACE IRIN MATSALAR SANYI NE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE KODA YA KAI YA TOSHE MAKI HANYAR CIKI ZAI WANKE HARKI DAUKI CIKI IDAN ALLAH YASO

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login