Showing 12001 words to 15000 words out of 197906 words
a Palo ta dora kafa daya akan daya.
Tana balain tsoron Balaraba da ko muryarta taji sai taji gabanta ya fadi
Bata manta irin mugun dukan rashin tausayin da ta mata ba
Ji take kamar ta koma ciki da ta ga ta zuba mata ido tana Kallonta
A cikin hausar da ta fara koya kadan kadan ta gaida Balaraba tana sunkuyar da Kai.
Ga mamakinta balaraba cikin sakin fuska ta amsa mata gaisuwar har da dan murmurshinta ta Kara da "Unguwa Zaki je"?
Duk da bata gane mai balaraban ta fada ba Kai kawai ta gyada mata tana k'ok'arin maida mata murmushin yake duk sai take ganin kamar wayo balaraban ke San yi mata sai ta saki jiki ta taso ta rufeta da duka tunda yanzu ma cikinta ya fito abinka da ba tsayi gareta sosai ba.
Shiyasa cikin nata ya turo kamar wacce ta kusa haihuwa dan har Jafar ce mata yake Allah yasa ta haifo masa Yan biyu duk Maza.
"Sai kin dawo toh"
Balaraba ta daga mata hannu tana Jin wani farin ciki na ratsa ta dan zaman nan da tayi tunanin kawai take na yadda zata samu shiga dakin kudirat din dan tasan shi kadai ne ya rage a cikin binne binnen da Mallam yasa ta tayi.
Kudirat waje tayi da saurinta da ta ga balaraba ta daga mata hannu alamar bye bye.
Tsorata ma tayi da taga yadda balaraban ta sakar mata fuska a yau.
Balaraba tana ganin kudirat ta fita ta mik'e da saurinta ta rufe k'ofar palon ta d'auko layyar dake d'auke da sunan Jafar da kudirat da aka caccaka wa allura ta nufi dakin kudirat da bata Sha wahalar Bude shi ba dan duk spare keys din gidan na dakinta.
Wani bakin ciki ne ya rufeta da ta ga yadda dakin kudirat din ke cike da kayan Ishama har dasu gadon bby.
Kusan duka ma kayan Jafar yanzu Yana dakin kudirat.
Ji take ma kamar ta samu fetir ta Kona dakin dan tsananin bakin ciki.
Amma da ta tuna aikin da mallam Yayi akansa da bata da haufi tasan sai aikinsa yayi tasiri akan Jafar da kudirat sai ta dan ji sanyi a zuciyarta.
Jefa layyan tayi a masan ta fito tana Jin zuciyarta fes dan kila kafin Jafar ya komawa kudirat tunda itace da girki.
Aikin ya kama shi har hararo duka da Korar Karen da zai yiwa kudirat take.
Rabon da tayi wani kwalliya tayi girki Mai dadi dan tarb'ar Jafar har ta manta amma dayake ta san muguntar da ta hada har da Jan kunshinta tayi kwalliyar tarbar Jafar har da girkinta Mai dadi.
Koda kudirat ta dawo daga asibitin cikin sakin fuska ta mata sannu da zuwa dan tasan kila daga yau watan tashin hankalinta ya kama.
Koda Jafar ya dawo yayi matukar mamakin canjin da ya gani a wajen Balaraba.
Dan har kasa boye mamakinsa yayi sai da Balaraba ta saki dariya tana ya bar mamaki ita kawai tayi wa kanta fada Allah ya basu zaman lafiya yaransa ma nata ne ai rabo yasa ya auri kudirat din.
Jafar kuwa sai ya tsinci Kansa cikin farin ciki ya hau mata alkawarika ciki kuwa har da bata bbyn da kudirat zata haifa.
Balaraba kuwa da ta san tsiyar da ta shuka Godiya ta hau masa tana Allah ya basu zaman lafiya.
A ranar Jafar cikin farin ciki ya kwana Yana Jin wani nutsuwa dan har ga Allah zai ji dadin hadin kan balaraba da kudirat.
A ranar bai leka kudirat kamar yadda ya Saba ba.
Kudirat kuwa a ranar sai ta ringa Jin fargaba da faduwar gaba sai ta rasa me yake damunta.
Ko bacci bata iya yi ba haka kawai taji tana tausayin kanta.
Sai ta hau tuna iyayenta da kanenta sai taji tana san yin nadamar bijire musu da tayi ta zabi Jafar a kansu.
Duk da Jafar bai tab'a Mata wani Abu da zai Sosa mata zuciya ba Yana iya k'ok'arinsa wajen ganin ya faranta mata.
Haka ta tashi sukuku jiki a sanyaye Ishama nada dan kuka ga cikin da take dashi na dan sata bacci Mai nauyi.
Ko Yaya Jafar yaji kukanta haka zai fito ya ma fita iya rarrashin ta take zata koma bacci Koda kuwa a wajen Balaraba yake indai yaji kukanta sai ya fito ya rarrasheta.
A ranar sai ta danyi mamaki da taga Ishama nata tsalla kuka amma Jafar bai fito kamar yadda ta Saba ba.
Ga Kuma bacci da ya fara fusgarta sama sama ga kukan Ishama.
Haka ta mik'e ta fara rarrashin Ishama dak'yar ta samu Ishama ta koma bacci.
Inda sai a lokacin itama ta kwanta baccin dan tasan kila idan Jafar zai tafi massallaci zai leko ya tasheta tayi sallah kamar yadda ya Saba idan baya dakinta.
Ga mamakinta a ranar bai leko ba dan budar ido kawai tayi taga gari ya waye har takwas na Safiya ya kusa haka ta mik'e ta daura alwala tana tunanin akwai dalilin Mai k'arfi daya Hana Jafar leko su a haka ta yanke idan ta iddar da sallah zata leka Palo taga ko lafiya.
Jafar kuwa Koda ya tashi sai ya tsinci Kansa da Jin haushin kudirat na ba gaira ba dalili har Yana Jin baya San ganinta.
A haka yaci abincin da Balaraba ta masa ya fice daga gidan batare da ya Kalli ma dakin kudirat ba.
A takaice daga wanan ranar kudirat ta fara ganin canji a wajen Jafar Dan Koda ta fita bata iya tambayar balaraba inda Jafar yake ba haka ta koma daki tana Dan tunane tunane.
Da yamma tana jin muryarsa ya dawo sai ta hau zuba ido taga ko zai shigo sai dai shiru bai shigo ba har karfe takwas.
Kamar zata fita sai ta fasa dan tasan gobe itace da girki kasan zuciyarta Kuma tana ta mamakin mai ya hana Jafar zuwa dakinta kamar ma Ishama ta San babanta bai shigo dakin ba sai kananan koke koke take.
Balaraba da ta fara ganin canji daga wajen Jafar din wani irin farin ciki ta tsinci kanta a ciki kamar ta taka rawa sai take Jin mai ya Hana ta yin wanan Aikin tun lokacin ma da aka auro kudirat din da kila a lokacin tayi wanan aikin da bata isa ma haifar Ishama ba.
A washegari da kudirat ta karbi girki Balaraba da ta san tsiyar da ta shuka kwalliya taci tazo ta kame a Palo.
Kudirat kuwa kamar yadda ta Saba haka ta danyi aikace aikacen ta na tarb'ar Jafar Ishama a goye a baya zuciyarta duk ba dadi dan tunda ya auri Jafar bai tab'a Mata haka ba.
Jafar kuwa har ya fita aiki bai ji Yana San ganin kudirat ba dan idan ta fado masa sai yaji ransa na b'aci
Koda ya dawo a Palo yayi zamansa ya hau cewa Balaraba ta bashi abinci zai ci.
Balaraba kuwa cikin kirsa tace masa ya manta ba itace da girki ba kudirat ke da girki.
Sunan kudirat data kira yasa ransa b'aci na ba gaira ba dalili cikin hade rai yace ta tashi ta kawo masa abunci shi dai yaci.
Balaraba kuwa ta girgiza masa kai tana ita dai ba itace da girki ba bari ta kira kudirat ta kawo masa abunci ta mik'e ta nufi dakin kudirat tana Jin kamar ta fasa ihuun murna.
A gefen gado ta tarar da kudirat ta buga uban tagumi Ishama na cinyarta da alama bacci take.
Ga kuloli nan da ta jera a tsakiyar dakin.
Shigowar Balaraba cikin fara'a ya katse mata tunanin da ta tafi na mamakin canjin da ta fara gani a wajen Jafar Dan a iya saninta lafiya lau suka rabu bata masa wani laifi ba.
Tana Jin lokacin daya dawo Amma bai shigo ba
Kila ta masa ba daidai ba shiyasa yake fushi da ita bata sani ba a yanzu zaman da take so take idan ya shigo sai ta bashi hakuri.
Balaraba kuwa sai da taje tsakiyar dakin tana sakin murmurshin mugunta bayan ta gama karewa dakin Kallo ta dora idonta akan kudirat dake kallonta.
"Toh tsinaniya zamanki a gidanan ya kare haka kawai Ina zaune da mijina kinzo daga sama Zaki kwace min shi ta hanyar cika masa gida da Yaya bayan ke baki san wahalar da na sha dashi ba shegiya kedara kije ki Kai masa abinci Allah ya sa ya lafta miki duka a yau ya hada miki da saki uku"
Kudirat Sam bata gane mai Balaraban ke fadi ba amma daga ta gane kalmar shegiya.
Bata cewa Balaraba komai ba inda balaraba ta saki murmurshi ta nuna mata kular da k'ofa tana ta Kai wa Jafar zai ci abinci"
Daga haka ta fice daga dakin.
Kudirat kuwa sai ta kasa motsawa dan bama zata iya fadar halin da take ciki ba daga karshe ta gane Mai balaraban ke nufi kawai abinda ya daga mata hankali Jafar bai tab'a Mata haka ba.
Haka ta mik'e jiki a sanyaye tayi waje da farantin abincin
Gabanta na faduwa ta nufi wajen Jafar da bai dago ya kalleta ba.
Balaraba kuwa na kame a gefe tana kallonsu.
Kudirat kuwa da ta tsinci gabanta da balain faduwa haka ta isa gaban Jafar ta ajiye farantin ta hau gaishe shi kamar yadda ta Saba.
Jafar kamar Wanda yaga Kashi haka ya kyabe fuska Ya matsa da sauri har da toshe hancinsa Dan wari yaji Yana busowa daga jikin kudirat din.
Ya mik'e da sauri Yana ta d'auke abincinta ba zai ci ba.
Yayi dakin Balaraba da saurinsa dan har ji ya ringayi kamar zai yi amai
Yana shigewa dakin Balaraba ta kwashe da dariya ta mik'e tabi bayan shi.
Kudirat da kafafunta ke rawa tabi su da Kallo dan Sam bata gane mai ya faru ba a yanzu
Idan har ba tabin hankali ta samu ba kamar toshe hanci Jafar yayi akan tana wari.
Tafi awa daya a zaune ta kasa hade tunanin abinda ta masa da ta cancanci haka daga wajensa.
Kukan Ishama ya sa ta tashi dakyar ta shiga daki.
Daga lokacin ta Jafar ya juya mata baya sai tafi sati biyu bata Saka shi a idonta ba dan ko dakinta baya zuwa.
Idan kuwa ta fito haka zai ta toshe hancinsa akan wari take tun tana kuka har sai da ta koma yin na zuci dan Sam bata kawo wai Jafar baa cikin hayyacinsa yake mata wulakanci ba.
Ko dakinta baya shiga balle ya dauki Ishama.
Haka ta ringa rainon Ishama da cikin jikinta tabi ta zabge saboda tunani Sam bata kawo Jafar zai iya mata haka ba.
Daga lokacin ta fara nadamar zabar Jafar akan iyayenta dan koma mene iyayenta ba zasu tab'a guje mata ba amma sai gashi Jafar yasa kafa ya Shure duk alkawarikan da ya mata ya bude babi Babi na wulakanta ta.
A haka ta shiga watan haihuwarta duk batare da Jafar ya Kara bi ta kanta ba ta fara addu'ar Allah ya sauketa lafiya dan tana haihuwa zata kwashi yaranta ta tafi garinsu.
Balaraba kuwa Sam ba haka taso ba dan taso ace ba iya tsanar kudirat yayi ba taso ace ya saki kudirat din sai dai ga mamakinta ya kasa sakin kudirat din bayan Mallamin nata yace sakin kudirat zai yi.
Haka ta ringa zuba ido taga ko zai saki kudirat din.
Wata ranar laraba kudirat ta tashi da nakuda.
Kuka kawai take dan ta rasa mai taimaka mata ga Ishama itama da ta tashi take ta kuka har sai da ta fado daga kan gado.
Azabar da take Sha yasa ta kasa ma daga Ishaman haka ta rike bayanta ta ringa sallati tana Kiran sunan Jafar.
Tura k'ofar da akayi yasa ta kallon k'ofar inda ta ga balaraba ce ta shigo ta Maida k'ofar ta rufe tana Kallonta.
Tsintar kanta tayi da faduwar gaba ga Ishama da kukanta ya karade dakin har lokacin tana kwance a kasa.
Hannun balaraba na goye a bayanta.
Kudirat kuwa ta fara girgiza Kai dan tasan duk yadda akayi balaraba shigowa tayi ta kasheta.
Balaraba kuwa da idonta ya rufe tayi kan kudirat da ta Bude kafarta da alama so take ta haihu dan har faya ta fashe ta fara nishi......
6/25/24, 10:41 - SADNAF: *THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA*
*GABA KURAA*
*NA SADNAF*
*Page 6*
Balaraba jikinta har rawa yake wajen sunkuyawa dan ba wani bacci take ba saboda masifar da ta dora wa ranta na san ganin bayan kudirat.
Kamar a mafarki taji kukan Ishama da sallatin kudirat.
Inda ta juya ta Kalli Jafar dake ta sharar bacci duk da tasan ta shiga tsakanin su gani take kamar har yanzu Yana Santa tunda har ya kasa sakinta.
Baya ga haka ma tunda ya juyawa kudirat baya ya Wani susuce Sam Babu wani walwala a tare dashi.
Wani zubin haka zai ta kallon dakin kudirat.
Da dukan alamu aikin bai kama shi yadda take so ba dan ita burinta ya saki kudirat ta tafi da yaran ta zauna daga ita sai shi.
Tunanin ko dai nakuda kudirat din keyi yasa ta tashi da sauri ta nufi dakin kudirat din dan zata je ne kamar taimaka mata take so tayi amma ba taimakon za tayi ba tunda ba Wanda zai ganta sai ta shake kudirat da bbyn sun koma.
Dan gani take idan har ta bari kudirat din ta sake haifar bbyn rabuwarta da Jafar zai Kara mata wahala.
"Ki bari na taimaka miki ga kan bbyn ki nan"
Balaraba tace cikin san hana bbyn fitowa matse ma bbyn take so tayi.
Kudirat da ke nishi da k'arfi da hawaye dake zubo mata na ganin malaikar mutuwarta.
Ta kama hannun balaraba biyun da k'arfi ta saki nishi da k'arfi sai ga jaririya ta fado.
Balaraba kuwa sai k'ok'arin kwace hannunta take amma kudirat ta tattara duk wani karfinta ta riketa gam.
Kudirat cikin harshen turanci tace " I will not allow you hurt my bby"
Balaraba kuwa da ta fara tsorata da irin rukon da kudirat ta mata idonta a warwaje ta fara k'ok'arin fusge hannunta tana "taimaka miki zanyi ki cikani kinga jaririyarki a cikin jini"?
Kudirat kuwa kamar Kara mata k'arfi ake dan gani take tana cika balaraba zata shake jaririyar.
Ga Ishama dake ta tsalla ihu ga kukan jaririya
Jafar a hankali ya bud'e idonsa kamar Wanda aka tashe shi daga bacci.
Ba abinda ya sauka a kunnensa sai kukan Ishama da jaririya.
Kudirat ce ta fado masa a rai dan yasan itace Mai ciki.
Bai tsaya dogon tunanin ba ya mik'e da gudunsa yayi waje.
(Haihuwar da kudirat tayi da jinin da ta zubar ya karya asirin da Balaraba ta masa hakan na nufin ya dawo hayyacinsa")
Bankada k'ofar yayi dan rufewa balaraba tayi.
Inda yayi tozali da Balaraba dake ta kokawa da kudirat nasan kwace hannunta.
Ga Mahaifiya bata fado ba ga jaririya a cikin jini.
Wani irin sallati ya saki yayi wajen su da gudu dan take ya gane mai ke Shirin faruwa dan da dukan alamu Balaraba zuwa tayi dan ta cutar da kudirat.
Kudirat kuwa shigowar Jafar ya sa ta saki hannun balaraba ta zube a kasa dan bata da kwari ko kadan jiri ma ke dibarta.
Yadda Taga Jafar ya shigo tasan zuwa yayi ya taimaka mata.
Balaraba kuwa da hankalinta ya tashi da taji sallatin Jafar a bayanta ta wayance da "Zuwa nayi na taimaka mata ka ka Nemo Reza a yanke cibiyar dan Kudirat ta zaro Mahaifiyar da kanta.
Jafar da jikinsa ke balain rawa ya nufi wajen drawer kudirat ya dauko sabon Reza Yana "Balaraba Mai na miki kike san ganin bayana"
Balaraba da ta fara tunanin Jafar ya dawo hayyacinsa ta d'auko Ishama da har lokacin take kuka dan bata so Jafar ya zargi cutar da kudirat din tazo yi.
Yadda taga Jafar yayi kan kudirat din bata Isa matsawa kusa da ita ba.
Zuciyarta kuwa cike da Fargaba da tsoron dawowar da Jafar yayi hayyacinsa aikin da ko wata biyar baiyi ba har ya karye.
Jafar shi ya yankewa Jaririyar cibiya ya d'auketa ya rungumeta Yana Jin hawaye na sauko masa.
Dan sai yake ganin kamar duk a mafarki ya share kudirat ya tsaneta na ba gaira ba dalili.
Yadda ya shigo yaga Balaraba na kokawa da kudirat kawai ya tsaya masa a rai.
Ga kudirat idonta na rufe sai numfarfashi take.
Tsananin tausayin kudirat haka ya rufe shi.
A yanzu ba zai tsaya bi ta kan balaraba ba,sai ya tabbatar da Lafiyar kudirat da Jaririyar.
Balaraba kuwa sai zare ido take tana ita wallahi zuwa tayi ta taimaka wa Kudirat ya yadda da ita.
A cikin zani ya nannade Jaririyar bayan ya goge mata jikinta tas dan ya dan iya komai tun akan Ishama dan har sa napkin da komai ya iya.
Karbe Ishama yayi daga hannun Balaraba Yana Jin kamar yayi shekara rabonsa da ita Sam bai san mai ya hau Kansa ya juyawa kudirat baya ba.
Da taimakon matar makocinsa da shi Kansa makocin nasa suka Kai kudirat asibiti aka duba Lafiyar ta da ta jaririya aka tabbatar da Babu wata matsala sai maganguna da ya siya da kayan shayi da ya siya
Da yawa.
Kudirat kuwa bata ce masa komai ba duk da binta da yake da ido Yana zuba mata sannu
Fadar bakin cikin dake dankare a zuciyarta bata bakine.
Sai da aka zo sallamar su ta Kalli Jafar dake rike da Ishama Jaririyar Kuma na rungume a kirjinta.
Ta kira sunan Jafar tana ita ba zata koma gidansa ba,ya bata Ishama zata Tafi garinsu ba zata iya cigaba da zama dashi ba ta hada da masa godiyar wulakancin da ya mata.
Fadar tashin hankalin da Jafar ya shiga bata bakine dan da gaske kudirat take akan ba zata koma gidansa ba dan a fadarta ganganci ne ma ta koma gidansa bayan balaraba bata da burin da ya wuce taga ta cutar da ita.
Ita Koda iyayenta ba zasu karbeta ba zata shiga duniya.
Jafar kuwa duk ban baki da magiya da rantsuwar da ya mata haka kudirat ta kafe akan ba zata koma gidansa ba.
A takaice a yadda Jafar ya Kara sakin Balaraba kenan inda yaci alwashin ya gama zama da ita.
Ya tattara duk kayanta ya bita dashi.
Dan har ga Allah ya tsaneta saboda mugayen abubuwan da take aikatawa da duk a yanzu ya fara tunanin tana da hannu a juyawa kudirat baya da yayi.
Ya so ya mata adalci saboda haihuwar da bata yi Amma tunda mugunta ta sa a gaba gwara su rabu ya zauna da iya kudirat uwar yayansa.
Sai a wanan lokacin kudirat ta dan san dadin Aure ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali.
Dan sosai Jafar ke kula da ita da yaranta dake ta girma kamar Yan biyu.
A yanzu shirye shiryen zuwa garinsu kawai suke dan gabaki daya hankalinta ya koma wajen iyayenta so kawai take ta gansu