Showing 171001 words to 174000 words out of 197906 words
a damuwa daga fada Kuma ta koma rarrashi
Sai da ta sani a gaba naci abinci taga na dan saki Raina da duk nayi hakane dan na samu ta barni nayi tunani Mai kyau.
A ranar yadda naga Rana haka na ga dare.
Ina ga bana cikin wayanda zasu tab'a farin ciki a rayuwarsu
AT Garba kuwa sai gajiya yayi da kirana har mamaki nake yadda yake min waya yake da lokacina 24 6 kamar bashi da wata matar a fadarsa dai matarsa salaha ce bata da matsala ko Aure auren da ya nema a baya da Allah bai kaddara ba bata tab'a daga hankalinta ba.
Washegari na tafi gida dan Anne ta dage na koma gida zaa fara min gyaran jiki.
Wani irin rama nayi saboda tashin hankali
Maganar muhseena na raina kullum na kwanta sai na tashi da tunanin zata iya sakin videon.
A haka Anne ta tsaya a ka fara min gyaran jiki dan wata Yar uwar su ce tazo daga Maiduguri take min gyaran jikin.
Banda Abubuwan da take dirka min da nake shansu akan dole.
A yau na Kara tashi da text din muhseena akan nazo na sameta idan har bana so ta saki videon da nasan idan ta watsa videon dole a fasa Aurena
Inda a cikin text din ta turo da address din inda zan sameta.
Haka na wuni cikin tunanin ta inda zan bullowa muhseena dama At Garba yace zai zo indai zai zo Anne ke Dan hada masa Abubuwan ci.
Da yamma yake zuwa a palon muke hira.
Kamar kullum ban taba wani kwalliya Dan zai zo ba
Haka nake fita wajensa ni muni na ma nake so ya gani.
Idan har sai na je wajen musheena ne na amince da wanan rayuwar na gwammace ace fasa aurena akayi
AT Garba da ido ya ringa Bina kamar zai cinyeni Hira kawai yake min na yadda yake ji kamar ya jawo sauran kwanakin da suka rage ya hau min bayanin yadda yake fama da mafarkina.
Naga ya dan sako hirar yadda zamu soye
Har Yana wani lumshe ido.
Hade rai nayi nace masa bana San hirar nan dan har gobe Ina ganin yadda zan iya sakin jikina dashi.
Text din da ya shigo wayata na muhseena yasa idona ya kada yayi jajjur na zubawa wayar ido na gaji muhseena. So kawai take ta kasheni.
Wanan fargabar da tashin hankalin da take jefani na Neman sa zuciyata ta buga
Dagowa nayi na Kalli AT Garba inda na kira sunansa
Hakan da ya gani yasa ya gyara zamansa ya bani hankalinsa gabad'aya
Kau da kaina nayi Ina "Mai kake ganin zai sa ka iya fasa aurena"?
Na zuba masa ido Ina kallonsa
"Mutuwa Bby mutuwa ce kawai zata sa na fasa aurenki"
"Bayan mutuwa fa Mai kake ganin zai zama dalilin da zai sa ka fasa aurena"
"Wallahi Babu bby banga wani Abu da zai sa na fasa aurenki ba"?
"Koda na aikata mumunan abu zaka iya aurena"
Shiru yayi Yana Kallona
Hakan da na gani ne yasa na fara magana Ina " A shekarun baya lokacin da nake makaranta jss na yi abubuwan da basu dace ba"
Labarin muhseena na tsinci kaina da fada masa ba Abunda na rage har zuwa bibiyar da take min da videon da ta min zuwa barazanar da take min
Ina Kuka na bashi labarin komai labarin Aunty Hajiya ne kawai ban bashi ba inda na shiga inbox dina na Mika masa wayar ya karba nace ya duba irin messages din da Muhseena ke min dan kawai naki bari na cigaba da rayuwar da na tuba na daina
A karshe na Kara da "Kafin ranar auren mu nasan zata iya sakin videon kamar yadda tace shi yasa na ce kawai bari na fada ma idan zaka iya aurena a haka toh idan ba zaka iya ba ka samu mahaifina kawai kace masa ka janye wanan alfarmar kawai za ka min"
Na karashe Ina goge hawayen dake zubo min
Mun samu minti biyar a haka ba Wanda yayi magana wayar kawai yake juyawa a hannunsa
Sunana ya kira sabanin bbyn da ya Saba ce min
Inda na dago na kalle shi ya fara magana Yana "Kamar yadda na fada Miki wallahi mutuwa ce kawai zata d'aukeni kiga ban aureki ba,daga messages dinan da ta tura miki nasan da gaske kin tuba kin Daina wanan rayuwar.
Dan haka ki kwantar da hankalinki zan d'auki Mataki dan da kin fadamin da wuri ma da ta dade da rabuwa dake cikin sauki San da nake miki ba kadan bane Siyama ba Abunda ba zan iya yi akanki ba"
Bance masa komai ba dan har ga Allah mamaki naji ya rufeni dan na d'auka ko yayane zan ga canji a wajensa.
Cemin yayi na ara masa wayar zai tafi dashi inda nace masa toh da haka Muka yi sallama ya tafi akan washegari zai dawo.
A ranar nasan nayi bacci Mai cike da nutsuwa dan ji nayi kamar an zare min wani kaya daga kirjina da na fadawa AT Garba Halin da nake ciki da musheena.
Har makara nayi a ranar.
Wajen Sha biyu sai ga Anne ta shigo dakin tana na tashi At Garba yazo"
Mamaki ne ya dan rufeni dan nasan baya zuwa da wuri.
Hijabi kawai na sa na fita waje.
Yana cikin Mota bai sauko ba
Glass din kawai ya sauke inda yace na shigo mota wani waje zamu je
Yanzu zamu dawo
Koda na tambaye shi Ina zamuje cewa yayi kar na damu idan muka je zan gani.
Ciki na koma na cewa Anne zamu fita da At Garba inda ta mana adawo lafiya
Na fito na hau motar.
Yaja muka tafi
Ganin bai cemin komai ba yasa nima ban masa magana ba sai tunani nake Inda zai kaini.
A takaice Ashe iyayen muhseena da Muhseena ya Kai wajen Yan sanda.
Musheena taci kuka ta gode Allah dan kamar ma At Garba yafi babanta kudi dan hakuri kawai suka ringa bamu sai da Muhseena da iyayenta suka sa hannu akan bani ba ita kuma ta goge duk videos din.
Bansan irin godiyar da zanyi wa AT Garba ba dan ya gama min komai.
Da haka na samu nutsuwa da kwanciyar hankali sai a lokacin na bawa Ishama hadin kai aka cigaba da shirye shirye.
Ban wani yi komai ba a gidan Ishama kawai aka yi kamu
Ba Wanda na sani ita ta gayyaci mutane gidanmu a cike fal da dangi da bama mu san dasu ba wai duk dan Wanda zan aura Mai kudi ne.
Na Sha gyara ciki da waje
Anne da wasu daga cikin dangin Abba ne suka gano gidan da zan zauna dan At Garba yak'i bari ko cokali Abba ya siya.
Koda suka dawo labarin haduwar gidan kawai suke suna nayi goshi
Ishama ma tafini murna dan cewa take ai ta fadamin idan Allah ya tashi ikonsa Wanda yafi Saleem zan aura.
Nidai duk wanan daular basa gabana ba abinda naji ya wani burgeni
Saleem kawai nake tunani Ina Jin dama dashi zaa daura auren
Gefe guda Kuma AT Garba karara yake nuna yadda yake maitar San ya kasance Dani dan ana gobe daurin aure da ya zo.
Dak'yar na kwaci kaina ina mamakin yadda ya kasa hakuri a daura auren
A haka na kwana da fargaba ban ko runtsa ba dan ana daura Aure zaa Tafi Dani.
Tun jiya Abba ke zabga min nasiha da Yan uwa.
Kayana kuwa duk an tafi dashi.
Kuka kawai nake ishama ma ta ci kuka ta gode Allah dan kukan rabuwar da zamu yi da juna kawai muke tunda baa gari daya zamu zauna ba
Nayi Nisa naso At Garba ya barni anan amma fir yak'i.
Kamar wasa sai gashi naji ana sanarwar Aurena a babban massallacin dake kasan layin mu
Na dai zama matar AT Garba
Karo na biyu kenan da ake daura min aure Ina fatan mutuwa ta raba mu duk da bana kaunarsa zan koyi San shi.
Ina Jin mama na rantsuwar da ita zaa kaini Anne na ba inda zaaje da ita.
Mama dai yanzu a zauce take dan bata fiye hankali ba.
Haka kawai zata samu gefe ta zauna tayi ta surutu ita kadai.
Shirin da baa gama yi ba na tafiya Dani yasa aka bari sai washegari wajen Sha biyu At Garba ya Aiko da motocin daukar amarya
Naci kuka na gode Allah dak'yar aka banbareni daga jikin Abba Da Anne
Hannuna na cikin na Ishama muka hau bayan motar
Dan da cewa tayi ba zata iya zuwa kaini ba sai da Abba ya Mata da gaske
Rarrashina kawai Ishama ya ringayi da matar baffa dake gaban Mota suna kar na damu zasu na zuwa ganina ai ba na tafi ba kenan.
A takaice wajen biyar muka karaso
Ina iya ganin hadadeen layin da muka shigo ta lafayyar dake rufe a fuskata
Gidajene iri daya suna Kallon juna painty ne kawai ya bambanta.
Matar baffa naji tana gidan kishiyata zamu fara shiga kafin a kaini gidana
Inda wasu suka shige gidana
Matar Baffa ta rike hannuna ta Kara rufe min fuskata muka shiga gidan Ishama na biye dani a baya nidai kirjina dukan uku uku yake dan bansan tarb'ar da matarsa zata min ba banma San ya take ba
Anne da kanwarta ma suna cikin wayanda suka biyo mu.
Ishama Kara Jan lullubina tayi ta rufe Kaina.
Da Bismillah na shiga palon dan su suke min jagora.
Bansan ma inda nake cila kafata ba
Kamshi da sanyin Ac ne suka bugi hancina.
Ina iya Jin muryoyi a palon ana lalle marhaban sannu da zuwa kawai ake mana
Jikina rawa kawai yake.
Inda naji ana ga waje mu zauna.
Kafet din da na taka yasa nasan na zo tsakiyar palon
Hannun ishama na rike gam a cikin nawa
Har lokacin jikina rawa yake.
Gaishe gaishe aka Kara kaurewa dashi muryar wata na ta mana ya gajiya da hanya ai da mun huta kafin muzo.
Inda matar baffa ta karbe akan ba komai ai tunda ni kanwa ce dole nazo na gaida Yayata a damka mata Amana ta.
Matar da muke Jin muryarta ce ta karbe da ai an zama daya an karbi Amana kar su ji komai.
Inda naji muryar wata na "Ba komai Allah ya bamu zaman lafiya"
Godiya su Anne suka yi inda naji matar dake magana a farko na bari a biyo mu da ruwa da lemo
Mikewar da naga su Anne sunyi da Ishama yasa na mik'e Nima
Sai dai Ishama fusge hannunta tayi daga cikin nawa ta kwalla ihuuun "Hishammm"
Maimaita sunan nayi a akaina tuna waye Mai sunan yasa na yaye lafayar kayana da sauri.
Inda naga Ishama taje ta rungume Hisham dai kaninmu dan tsayi da girma kawai ya kara kamaninsa na nan"
Jikina rawa kawai yake na nufi wajen su
Inda har lokacin Ishama ke Kankame da Hisham da Shima ke ihuun "Aunty Ishama Aunty Ishama innalillahi wa inna ilaihi rajiun Aunty Siyama yace cikin ihuuuu.
Inda na fada kansu na rushe da ihunn Kuka.
"Hishamaaaa Siyamaaaa"
Muka ji an kira sunanmu
Juyawa muka yi inda naji kaina ya mugun Sara min dan duk da kankantar shekaruna ba zan iya manta momi ba
Ishama naji ta saki ihuuun "momy"""
Inda momy ta daga hannunta dake karkarwa ta nuna ni tana "Kece co wife Dita"?......
Wai Allah sai jibi wayata hauka take min
[7/17, 22:31] SADNAF: MATAN GIRMA MATA MASU AJI
MACEN DA TA SAN KANTA ITACE TAKE GYARA
A&Z COLLECTION TA KARA DAWO MUKU DA ZAFINTA MASOYA KAYANMU.
A&Z COLLECTION TA ZO MUKU DA ZAFAFFAN KAYAN GYARAN FATA,GYARAN JIKI CIKI DA WAJE MAI DA TSOHUWA YARINYA WANAN KARON A&Z TA SHIRYA TSAF DAN TA GYARA AURE GYARA BUDURWA,GYARA MATAR AURE,HAR DA BAZAWARA.
Wa.me/2349037870422
A&Z COLLECTION TA ZO MUKU DA ZAFAFFAN SUPPLEMENT KALA KALA
HAJIYATA IDAN KINA DA KYAU KI KARA DA WANKA GYARA DUNIYA NE A YANZU AN BARMU A BAYA KARKI SAKE DA KURUCIYARKI KI JERA DA SAARKI A RINGA MIKI KALLON TSOHUWA SABODA RASHIN GYARA.
SUMA WAYANDA KUKE GANI SUKE BAKU SHA'AWA SUMA FA BA ZAMA SUKA YI BA DAGEWA SU KAYI DA GYARA.
KUMA A YANZU AN YI ITIKAFIN BA ABINDA ZAI GYARAKI YA DAWO MIKI DA KURUCIYARKI KIYI CAS CAS GWANIN SHA'AWA SAMA DA SUPPLEMENT ????
TO KE KUWA ME KIKE JIRA?KO KIN FI SON MAI GIDA KO SAURAYINKI YA SHAGALA DA KALLON MATAN TIK TOK DA BASU FIKI DA KOMAI BA SAI GYARA??
WAI SHIN MENENE MA SUPPLEMENT? SUPPLEMENT WANI NAU'IN MAGUNGUNA NE DA AKE HADAWA DA GANYAYAKI WASU ITATTUWA WASU KUMA SPICES A MAIDA SU CAPSULES WASU PILLS WASU SOFT GEL DAN SU MANA SAUKIN AMFANI.
MISALI ROYAL JELLY DA FARIN ZUMA MAI SAKA AKE YINTA.
UlTIMATE MACA SHI KUMA DA MACCA ROOT ITACE NE AMIRNA AKE YINTA
WASU KUMA DA ITACEN KANINFARI,WASU DA KIMBA DUK AKE YINSA.
INA WANDA BATA SO TAYI FARI TAS?
INA WACCE KUMA FARIN TAKE SO AMMA BA IRIN NA BLEACHING BA FARI TAKE SO TAYI IRIN NA YAN GAYU WAYANDA HUTU YA RATSA SU?
INA MACEN DA TAKE SO TA YAKI SANYIN DAYA HANA TA SAKAT?
INA MACEN DA TAKE SO TA GIGITA OGA?
MASU FAMA DA MATSALAR RAMA KINYI KINYI KIN GAJI?
TOH MUN TANADARMUKU DA INGANTACIYAR ZUMAR KIBA SADIDAN ??KIBA ME KYAU ZATASAKI TA YANDA BAWANDA YA ISA YA GANE ME KIKESHA SAI DAI AGA TSATSAN KALAR HUTU KAWATA??
MUNA DA NA???
NA BREAST
NA HIPS
HADIN AMARYA
HADIN MAI JEGO
NA RAGE KIB'A
NASA KIB'A
NA GASHI
NA NANKARWA
NA KARIN NI'IMA
DAMA SAURANSU??
HAJIYA DUK NA ABINDA KIKE SO KAWAI KI MANA MAGANA TA NAN???
KIRA KO WATSAPP
09037870422
KUMA KAYAN MU A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA
ALHAMDULILLAH DUK WANDA YAJI PRICE DIN KAYAN MU ZAIYI FARIN CIKI MUSAMMAN WANDA SUKA SAN KUDINSU DA YADDA AKE SAI DAWA
MUNA NAN A GARIN KANO RIJIYAR ZAKI MUNA TURA KAYAN MU KO'INA CIKIN AMINCI??
MASU FAMA DA MATSALAR RAMA KINYI KINYI KIN GAJI?
TOH MUN TANADARMUKU DA INGANTACIYAR ZUMAR KIBA SADIDAN ??KIBA ME KYAU TA YANDA BAWANDA ZAI GANE ME KIKESHA SAI DAI AGA TSATSAN KALAR HUTU KAWATA??
IN DEDICATION TO BBG
*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE KIJI TSORON ALLAH KARKI MIN SHARING KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN BANA KALLONKI ALLAH NA KALLONKI DASHI ZAN BARKI HAKKI DAI BA WASA BANE BA IDAN KINA SO KI BIYA 500 INSTEAD OF 700 ZUWA GA WANAN ACCT DIN 0078986629 STERLING BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN A WANAN LAYIN 08033719070 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA LAYIN NAN 08033719070 KO TA WANAN LAYIN 08068484400 KU SHA KARATU CIKIN AMINCI AMMA HAR GA ALLAH DUK WACCE INA POSTING TA FITAR MIN NA BARTA DA RABBI YA MIN SAKAYYA YAN NIGER KUMA KIYIWA LAYIN NAN MAGANA +227 96 82 89 84*
*GB KR*
*Page 53*
Kudirat
Waiwaye
Da wuka mahaifin ta ya biyota a lokacin da ta koma garinsu bayan wahalar da ta Sha na Neman inda suka koma.
Ta riga da tasan iyayenta ba zasu tab'a saurarta ba dan tafi kowa Sanin yadda suke da kafiya
Har tsine Mata mahaifin ta yayi a lokacin da makauniyar so ya rufe mata ido.
Bata manta bakin cikin da suka shiga ba a lokacin tasan da wuya dama su suarareta
Rantsuwar da mahaifin ta yayi akan idan ta Kara taka kafarta ta shigo masa gida sai ya kasheta yasa ta hakura tayi kukan har ta gaji
Dan har wajen pastor dinsu taje taga ko zai iya shige mata gaba wajen bawa mahaifin ta hakuri
Bata ga Mahaifiyar ta ba tana so ta ganta kila ita zata iya saukowa.
Sai dai ta rasa wa zata tambaya dan ko Yan uwanta ba Wanda ta gani.
Dak'yar pastor ya saurareta dan korarta shi ma ya so yayi dan kowa yaji haushin zabar Jafar da tayi akan iyayenta har Kuma ta bar Addinin su ta musulunta.
A wajen pastor take Jin labarin Mahaifiyar ta rasu shekara uku da suka wuce haka ta ringa fama da hawan jini bama ta yadda za'ayi wani ya tab'a saurararta dan sunce sun yafeta a cikin yayansu
Kuka taci sosai ta gode Allah fadar nadamar da tayi na bin Jafar bata bakine.
Abinda kawai ba tayi nadamarsa ba shine musuluntar da tayi dan tun tana ma yarinya
Take kaunar musulunci takan zauna tayi wa kanta tambayoyi yadda suke gududanar da rayuwar su.
Daga abinda suke fada ma kafin addu'a tasan ba yadda za'ayi ace Jesus shine Allah Kuma ace dan Allah ne shi
Shi yasa tana haduwa da Jafar bayan San da take mi shi Yana mata tayin musulunci ta musulunta.
Pastor ma dagewa Yayi akan idan tana so Mahaifinta ya saurareta dole sai ta Kara barin musulunci yayi mata wanka ta dawo Christian kila mahaifin ta ya saurareta
A takaice haka ta baro garin dan daidai da Yan uwan Mahaifin ta da na Mahaifiyar ta korar kare suka mata.
Tasan da kila Mahaifiyar ta na rayye da zata iya yafe mata tunda ita uwa ce.
Koda ta tashi sai ta rasa inda zata je.
A karshe dai sai motar Abuja ta hau
Fadar tashin hankali da damuwar da take ciki bata bakine
Yaranta da ta baro a hannun Balaraba da take Jin har ta mutu ba zata iya yafe mata ba kawai take tunani
Tsanar Jafar kuwa da take ji a ranta na cutar da ya mata karuwa kawai yake a ranta.
Jafar bai rike alkawari ba akansa ta guji kowa nata Amma sai gashi sakayyar da zai mata shine ya juya mata baya
Tasan yaranta zasu Sha wahala a hannun Balaraba sai dai tayi ta musu Addu'a.
Inda take dan Jin sauki a zuciyarta idan ta tuna Jafar na kaunar su dan sai taga kamar Ita kadai Jafar ya tsana amma Yana san Yara.
Koda ta iso tashar Abuja sai ta rasa Ina zata je dan ba wanda ta sani.
Tafi sati daya tana walagigi dak'yar take samun abinda take sawa bakinta.
Idan dare yayi sai ta shige kasan wani lallatacen mota dake fake a tashar tayi kwanciyar ta
Ido daya Bude daya rufe take bacci.
Sai da ta samu sati daya a haka Kafin Allah ya hadata da wata Mai kosai
Da ta roketa akan zata ringa mata aiki ta ringa bata abinci da wajen kwana
A cikin Tashar matar da ake cewa Furera Mai kosai take sanaar siyar da kosan.
Ji tayi kamar an Mata bushara da gidan Aljanna da ta amince akan zata na bata abinci sau uku za Kuma su ringa tafiya gidanta tare.
A haka ta samu ta ringa aiki kamar jaka dan ba iya tayin sanaar kosan take taya furerar ba,aikin gidanta gabad'aya ita take jibgawa har da wankin yayanta Maza dan bata da ya mace
Tun karfe uku da rabi take tashi ta hau surfa waken da za'ayi kosai
Kusan kwanu hudu wani zubin biyar
Bayan ta wanke sai ta Kai markade ita zata riga ta zuwa tashar ta hura Mata wuta kafin ta karaso.
Tun tana