Showing 1 words to 3000 words out of 213309 words

Chapter 1 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5866

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Bismillahir rahmanir rahim. In the name of Allah,the most gracious and the most merciful.

*PROLOGUE*..Khilishi



*APRIL,2018*...

Dakine madaidaici dake daukeda katuwar katifa shimfide kasa se wardrobe irin na katakonnan dake manne jikin gini ta gefe daya. daga daya bangaren kuma akwatuna ne guda uku inda aka jerasu daya kan daya,daga gefen akwatunan kuwa handouts da notebooks ne jere neatly gwanin ban sha'awa sekuma yar madaidaiciyar madubi da'aka manna da gum jikin bango. tsananin ringing din da wayarta keyi ne yasata tashi daga nannauyar baccin datakeyi hakanan cikin magagin bacci tadaga wayar tana kokarin wartsake idanunta don ganin wanene wannan me shegen kiran kamar wani kayan jaraba,ganin sunan *Habiba* datayi jikin screen din wayarne yasata tashi zaune kafin ta daga call din cikin sauri ganin kiran yakusa tsinkewa,tunkanma tayi magana taji Habiba daga daya bangaren tana fadin "wai lafiyar ki kuwa Rukayya? Inata kiranki bakya dauka. ina kika jefarda wayartaki ne wai?" hamma budurwar da aka kira Rukayya tasaki tana lumlumshe idanu alamun baccin begama isantaba kafin akasalance tace "Habiba am bacci nikeyi sanda kikayita kira,banmasan kinyita kira ba sabida seyanzu naji ringing din wayar.

Daga daya bangaren cikeda mamaki Habiba tace "bacci fa kikace?" Rukayya tace "Eh bacci nikeyi,akwai laifine aciki? naga yau ba makaranta public holiday ne".

Habiba da haryanzu take cikeda mamaki tace "wai bakiga text dina bane jiya da daddare?" cikeda rashin damuwa Rukayya tace "bangani ba Habiba,nayi bacci dawuri ai" Habiba tace "lallai kam toh wallahi kitashi kishirya kishigo school yanzu yanzunnan muyi submitting assignment din Dr. Isma'il dan yace 10:00am dot yakeson kowa yakawo,dukwanda baizoba kuma bazai karba ba sannan zero zaisaka mai batareda yadamu ba".

Aitunda Habiba ta ambaci Dr. Isma'il Rukayya taji dukwani guntun baccin da yake idanunta sun wartsake,ta dafe kirji tace "nashiga uku, Habiba wallahi banga text dinki ba anma ganinan zuwa kuma dan Allah kujirani muje in group" Habiba tace "kidai yi sauri kizo. Inbakizoba yariga ki zuwa submitting zamuje muyi gamunan zaune duk jiransa mukeyi yazo,kindai san halinshi" daganan Habiba ta kashe wayar dif. Rukayya daketa faman yimata magiyar tadai jirata suje taren taji takatse call din,duban wayar tayi kafin tayi wurgi da'ita kan gado sannan tadubi wall clock din dake manne jikin bangon dakin 9:48am,wani irin dukan uku uku zuciyarta yashigayi,yanzu tayaya zata isa BUK kafin goma?kafin tafita daga layinsu tasamu titin samun abun hawama aikine barekuma inta isa school dinma dole tayi traking zuwa department din wanda shima wani nisanne.

Ganin tsayuwar da takeyidin wani bata lokacin ne yasata karasawa jikin wardrobe dinta tabude tadauko wata doguwar riga ta atamfa tasaka cikin sauri batareda tacire riga da gajeren wandon baccin dake jikinta ba. bandaki tashige cikin sauri ta kuskure bakinta tareda dan watsa ruwa afuskarta sannan tafito tadauko hijabinta tasaka,ta rataya jakarta na makaranta datake da tabbacin assignment din naciki sannan tadauki niqabinta dake kan akwatunan dake jere gurin tatsaya gaban yar karamar mirrorn dake manne jikin bangon dakin tana daurawa.

A parlour tasamu *Sajeed* yaron dabazai wuce shekaru takwas zuwa taraba yana kwance gaban TV yana kallon cartoon tace "Sajeed my boy?" cikin sauri yadago yana kallonta sannan yace "Aunty Ina zakije? bayau ba makaranta ba?" Kaman me shirin sakin kuka tace "Sajeed assignment zanje submitting,be a good boy,banda barna and kazo karufe kofa inna fita sannan dukwanda ya kwankwasa kofar karka bude seka tambaya wayene kaji?" Yace "Toh Aunty" kafin yatashi yabi bayanta don rufe kofar wanda alokacin ita harta fice daga gidan.

Sanda ta'isa bakin titi tasamu abun hawa 9:54am,tabbas duk saurinta tasan bazata isa kafin 10:00am ba,ga nisa,ga hold-ups din garin kano gakuma traking din dazatayi inta isa makarantar ma wani abune. Fatan ta daya Allah yasa shi malamin karya isa makarantar dawuri.

Sa hannunta tayi cikin jaka don laluma wayarta takira Habiba tasake rokonta kanta jirata anma wayam babu wayan,seyanzuma tatuna ashe akan gado tabarta garin sauri. Wani irin takaicine yaziyarceta hakanan takejin kamar takarbi tukin napep din tayi ganin baya sauri, cikeda kosawa tace "Mallam don Allah ka kara gudu,ina sauri ne" Mai napep dinma dake dan iya bakar magana ne yace "haba Hajiya duk wannan saurin danakeyi? Inbadai sokike inatashi sama bane kuma toh?" Itadai batakulashi ba ahaka harsuka Isa makarantar tasallameshi inda tawuce department dinsu. harabar makaranta shiru kaman ba Monday ba inbanda tsirarrun dalibai dake wulgawa dai dai bakaganin komai,abakin kofar department dinsu taga wani security dake zaune yana sanye da uniform tagaida shi tareda tambayar shi lokaci inda yacemata "10:21am" zare idanu tayi kafin tayi gaba tanayi mishi godiya.

Tunda tadoso office dinnasa bataga alamar colleagues dinta ko dayaba da alamar sunyi submitting sunwuce gida kenan,dukan uku uku zuciyarta yashigayi yayinda takarasa jikin kofar office din tasa kunnenta don jin ko akwai wani aciki anma shiru dukda tanada tabbacin shidin yanaciki tunda ga karan Ac tanaji akunne.

Gefe daya tasamu najikin office din tajingina da jikin gini tareda lumshe idanunta tanajin yanda zuciyar ta ke racing haryanzu. jitayi anja kujera daga cikin office din alamun yatashi kenan yayinda taji kakkausar muryarsa nayima wani magana daga ciki yace "Mallam Hamisu kagama hada dukka assignments din guri daya?" jitayi wanda aka kira da Mallam Hamisun yace "Eh Yallabai nahada" tanaji yayima Mallam Hamisun godiya kafin yace ya ajiye masa cikin drawer inda shikuma yanufo kofa yana jadaddama Mallam Hamisun da ya rufe masa office kafin yafito.

Cikin sauri tashige wani lungu dake gefen office din ta rakube guri daya ayayinda yabude kofar office din yafito inda Mallam Hamisuu ke biyedashi yanacewa "Yallabai nima bazama zanyiba. gida zanwuce yanzu".

Haka suka fito Mallam Hamisu yarufe kofar duktana boye cikin lungu tanaji suna hirarsu sama sama,ga kamshin turarensa daya zame mai natural kamshin shi haryanzu tanaji yana ziyartar hancinta. Idanunta suna lumshe haryazo yawuce wanda ba foot steps dinshi bane yasa tagane a'a kamshin turarenshi daya kara kusantan tane and that genuine feeling datakeji aduk sanda yazo guri. bata ankara ba taji Mallam Hamisu na tambayarshi koyana bukatan wani abune ganin ya tsaya cak daga tafiyar dayakeyi din.

Shiru yayi nawasu dakiku kafin yasake dawowa baya yanadan dube dube kaman meneman wani abu,cankuma yadubi Mallam Hamisu yace "nikam akwai yarinyar datazo ne bayan daliban nan suntafi?" girgiza masakai Mallam Hamisu yayi alamun a'a kafin yayi gaba.
Jin footsteps din Mallam Hamisu ne yasa tagane suncigaba da tafiya,lekowa tayi ahankali tana binsu da idanu hartadaina ganinsu ayayinda idanunta ke zubda ruwan hawaye masu dumi. ta gwammace tayi loosing marks dinnan than taje submitting assignment din itakadai. haka tabar department din weakly takoma gida.

Koda tadau wayarta missed calls din Habiba ne ba'adadi batadamu dabin kiran nataba don kota kira dinma batada abun cemata, it'll only make matters worst because the more she think of submitting this assignment the more complecated it'll be for her life shiyasa ma tayi deciding ta hakura.

Washegari Tuesday schools sukayi resuming don daman hutun good Friday da Easter Monday aka basu and hutun yakare tunda yau Tuesday. seda tayi dropping Sajeed a school sannan tawuce BUK,koda tashiga makarantar ko'ina very busy, student nata kai kawo cikin harabar makarantar alamun kowa yadawo normal daily activities dinshi nada. Straight museum din department dinsu tawuce kasancewar batada lecture se 12:00pm. katon room ne dake daukeda bencina da kujeru farare gwanin ban sha'awa sekuma side daya da akayi gini da katako inda akasaka glass amatsayin kofar daza'abude gurin in anyi sliding dinta.

Different kinds of specimen ne na fossils acikin daya gefen glass din yayinda dayan sashin kedauke da samples na different types of rocks da akadauko daga field. babu kowa cikin museum din kasancewar lokacine da yawancin dalibai kedaukan lecture and moreover inba specific reason ba daman daliban basucika zuwa museum din department dinba.

Samun daya daga cikin kujerun tayi taja tazauna sannan ta ajiye jakarta kan desk din tana kokarin fiddo da drawing materials dinta da wayarta don fara assignment din Professional Ahmad daya basu sanda yazo, aranta tana fadin "gwanda inyi yanzu inhuta tunda inada time dan inna tsaya wasa sede inji mutumin nan yasake dawowa" dayake visiting lecturer ne dayake zuwa daga ABU Zaria.

PDF dake dauke da questions din yaturama class rep dinsu inda shikuma yatura musu a WhatsApp group. tunda tayi downloading batabi takan questions dinbama seyanzu datake budewa,maps ne yabasu sunfi kala ashirin yayinda yace sufidda *Geologic Cross section* din kowanne,wani irin ajiyar zuciya tasaki tana ayyana wahalar course din " *Structural geology* ko wahala? ".

Wuraren goma da rabi sega call din Habiba nan yashigo wayarta,dagawa tayi suka gaisa kafin Habiban tatambayeta inda take fada mata tayi kafin sukayi sallama,ba ajimaba kuwa sega wata madaidaiciyar budurwa dabazata wuce shekaru ashirin da dan dori ba tashigo,karasawa tayi kusa da Rukayya fuska daukeda fara'a tana fadin "kekam kinmin wayau kinata assignment dinki inacan inata shashanci agida" murmushi Rukayya tasaki wanda dukda niqabin dake fuskarta hakan baihana bayyana fara'ar fuskarta ba tace "naga banida abunyi ne yanzu shiyasa nayi deciding nazo narage ko kadan ne" Habiba tace "Aiko kinkyauta ma kanki nima ba infara nawa kafin time din *Geophysics yayi* ".

Haka Habiba tashiga kokarin ciro nata drawing materials din daga jaka tana fadin "nayita kiranki jiya bakya dauka" Rukayya tace "kibari kawai nabar wayan agidane fah tsabar rudani" Yar dariya Habiba tayi sannan tadubi Rukayyan dakyau tace "Anma dai kinsamu kinyi submitting koh?" Jiki sanyaye Rukayya ta jijjiga mata kai alamar a'a cikeda mamaki Habiba tace "how comes? bakizo bane?" Rukayya tace "nazo mana Habiba" Habiba tace "bakisameshi ba kenan?" Rukayya ta gyada matakai alamar eh don tafara gajiya da questions din Habiban and it'll be worst inta nuna mata bata yi submitting dinba Habiba tace "sede inhakan dan yatambayeni ke,yacemin Ina wannan kawartawa mesa niqab?meya hanaki zuwa? nace masa bakisani baneba amma nakira nafada miki you'll be on your way" Habiba takarada "Ke wallahi yabani mamaki. ashe duk tsare fuskarsa da jan ajinsa yana noticing dinmu inbahaka ba ya akayi harya sanki yake tambayarki Rukayya?" Rukayya datakejin kamar zuciyarta tayi exploding tayi karfin halin cewa "Waya fadamiki noticing dinmu yakeyi? yadai gane nine sabida issues din dayita hadamu a field dakuma farkon zuwanshi" Habiba tayi murmushi sannan tace "kumafa kinada gaskiya dan wannan mutumin yanda fuskarsa ba annuri hakanan yana shasshan kamshi bana tunanin zai rike fuskar kowa,kedinma dan kinasa niqab ne shiyasa yake ganeki may be" itadai Rukayya bata kuma cewa komai ba hakanan tanata kokarin yaki da zuciyarta da tadaina raya mata abubuwan da basu baneba.

Muryar Yunusa colleague dinsune yafiddo da'ita daga duniyar tunanin datashiga yace "tundazu niketa nemanki Rukayya" da mamaki tadubeshi dankuwa basabawa sukayi ba bare ace wani abun zai hadasu dahar zainemeta hakanan duk yan ajin nasu ma babu wanda take interaction da inba Habiba ba sannan dukansu sunsaka mata idanu kancewa itan tanada girman kai da kyale mutune bayan itakuma bawannan ne dalilinta naqin sabawa dasuba,she has a good reason,reason dinda itakadai tasan abunta dakuma mahimmancin yin hakan.

Haryanzu mamaki baibar fuskarta ba tace "bangane kana nemana ba,meya faru?" fuska ba yabo ba fallasa yace "Dr. Isma'il ke kiranki yace kisameshi a office dinshi yanzu yanzunnan" daganan Yunusa yajuya yayi tafiyarsa batareda yajirajin amsar Rukayya dinba. wani irin jirine taji yazo mata lokaci guda hakanan take jin zuciyar ta na race.

Habiba dake gefenta secemata takeyi tatashi tajeta anma ina hankalinta baya jikinta, she's in the outta world for a moment. jijjiga ta Habiba tayi ganin yanda ta sandare guri daya tanafadin "bakiji me Yunusa yace banewai?".

Jiki sanyaye tace "naji" Habiba tace "Toh kitashi kije mana,am sure dan assignment din yake kiranki tunda nafada masa uzurinki jiya" gyada ma Habiba kaitayi kamar wata wawiya kafin tashiga tattara takardunta tasaka ajaka tayi gaba,tasan ko giyan wake tasha Habiba bazata rakataba sabida tsananin tsoronsa dasukeyi.

Harta isa bakin kofar office din batadaina zullumi ba. tunda yazo makarantan bata taba yarda tahadu dashi itakadai ba sede tareda Habiba ko da other colleagues dinsu inwani abu yakaisu office dinsa shiyasa yaudin takejin wani irin nervousness,she's afraid her heart will explode infront of him, she's afraid actions dinta na'iya sawa yagane ta yau din bayan duk kokarin datayi wurin boyemasa kanta for more than two months now.

Folding hannayenta tayi a kirji in order to get hold of herself,bata ankara ba taji Mallam Hamisu tsaye kanta yana fadin "Rukayyatu lafiya kike tsaye nan?" cikin sauri tadago tadubeshi yana tsaye da alama yazo zaishiga office dinne yaganta tsaye murya narawa tace "lafiya Mallam. Ina kwana?" Mallam Hamisu yace "lafiya Lau. bakisami H.O.D dinnaku bane?" yayi maganar yana pointing windown office din Dr. Isma'il din cikin sauri tagyada masakai tareda juyawa dan tafiya inda Mallam Hamisu yabude kofar yashiga ciki, ganin office din Ogannasa bude kuma yana hangoshi daga inda yake yasa yakoma waje yana kiran Rukayyan yace "kidawo yananan,ashe bakima duba ba"

Dole tadawo badan tasoba gashi bugun zuciyarta se karuwa yakeyi. abakin kofa suka kusa yin karo da Mallam Hamisu zaifita inda hannunshi kedaukeda wasu files da alama abunda yadawodashi office dinnashi kenan.

Seda yawuce kafin tashige,daman Mallam Hamisu shine secretary din Dr. Isma'il wanda seka bi tagurinshi kafin kasamu office din Dr. Isma'il din dake can ciki. daga inda take tana iya hangoshi zaune dayake kofar office dinnashi bude take.

Karasawa tayi tayi sallama inda ya amsa batareda yadago yadubeta ba.

Shiga tayi tarufe kofar daga ciki sannan tashiga gaishe shi cikin muryarta dake karkarwa,amsawa yayi ayayinda yadago yasaka idanunshi cikin nata saurin sauke nata idanun kasa tayi. Matashin saurayi ne dabazai wuce shekaru talatin da dan doriba,shiba fariba shiba baki ba. zadai mu'iya kiran kyakyawan fatarshi dayake smooth da chocolate colour dinnan,kala mai tsada.

Kallo daya zakayi mishi kagane bafulatani ne usul gaba da baya sabida yanayin fuskarshi,karamin bakinshi dayake shiba pink bakuma bakiba,hancinshi dayake very pointed kamar karas yayinda idanunshi kenan medim dashi gwanin ban sha'awa,sajenshi kadai Inka gani zai tabbatar maka da kyawun gashin kanshi. yana sanye da coffee brown gezna datasha dinkin zamani yayinda kanshi kedauke da hula shima me touch off din coffee brown din. Idanunshi nasanye da medicated glasses daya karama fuskarshi haiba da kwarjini.
Murmushi yasaki ganin tasauke idanunta kasa yana mamakin yaushe tafara jin kunyar ganin cikin idanunsa,dan gyaran murya yayi yakoma bossy type dinshi lokaci guda kafin yace "Your friend told me that you were not aware za'ayi submitting assignment jiya. Why?"

Batareda tadago tadubeshi ba tace "I was not informed" yace "But your class rep posted on your WhatsApp group,don't you have an Android phone?" yanzunma kanta na kasa tace "Yes Sir" kallon dayan hannunta dake rikeda Android phone yayi wanda tanajin intense gaze dinsa kan wayar,cikin sauri ta boyeta abayanta nervously.
Murmushi yasaki sannan yace "where's the assignment?" jiki narawa taciro jakarta daga kafadunta tajefa wayar ciki dasauri kafin tashiga neman papers din datayi assignment din".

Mika mishi tayi yakarba ya ajiye tana fadin "Thank you sir" ayayinda muryarta na karkarwa gyada matakai yayi yayinda tajuya don fita,harta isa bakin kofa zata bude taji yace "Nanaah"
tsayayawa tayi cak kaman statue tana kokwanton abunda taji din,jin baisake cewa komai ba yasa tayi tunanin ko imaginations dinda takeyi kullum ne yaudinma......

Sa hannu tayi kan handle din kofar zata bude takuma ji yace "Nanaah" shiru yayi nadan wasu dakiku kafin yayi magana yace "Atunaniki bazan ganekiba?" wannan karan araunane yayi maganar,muryarshi na nuna how much he missed her and how much he yearns to call that special name.

Yatashi daga zaunen dayake yadawo yatsaya tsakiyar office din yayi folding hannayenshi a kirji tareda zubama bayanta idanu yanajin yanda kukanta ke ratsa duk wani sassa na illahirin jikinshi,cikin wata iriyar murya mecikeda kewa,tausayi,pain dakuma kauna yace "indai kinyi tunanin banganekiba tunsanda nafara daura idanuna cikin naki bakiyima soyayyar danakeyi miki adalciba,bakiyima connection din dake tsakanin mu adalciba,bakiyiwa bond din dake tsakanin mu adalciba sannan bakiyiwa alkawarin damuka daukar ma juna adalci"....

Baima kai ga karasa zancenba tasa hannunta jikin handdle din kofar tabude tafice aguje tana kuka maitsuma zuciya. Zuciyar ta nada rauni akan wannan bawan Allah,indai tacigaba da sauraronsa toh tabbas zata iya manta duk wasu abubuwa dasuka faru abaya takarbe shi hannu bibbiyu bayan kuma things are not like before.
He deserve someone more better.

Adaddafe ta'isa gida,straight dakinta tawuce tarufo kofar daga ciki sannan tazube jikin kofan tana rusan kuka haryanzu.
Miyasa zaidawo cikin rayuwarta alokacin da ta ajiye past dinta agefe tafara sabon rayuwa? tariga tadaukar ma kanta alkawarin nisantar dukwani dayake da alaka da past dinta dayake cike da kunci,nadama,bakin ciki dadai sauransu. miyasa zai tuno mata da pains dinda haryau inta tuna suna hunting dinta?

She thought she started afresh,a new life where babu wata gwagarmaya na rayuwa datasha abaya sede kash! yau gashi mutumin da taji anakira da Dr. Isma'il yadawo cikin rayuwarta,ya tuno mata daduk wasu pains dinda tayi going through a rayuwarta,a pain that's she's been carrying in her heart for more than 8years now,pain dinda itakadai take gwagwarmayar dashi acikin ranta batareda tayi sharring dakowaba even though it hurts,even though she needs a shoulder to cry on wanda tanada tabbacin inta fadama wani it'll be like a relief, it'll ease her pain. Toh anma wazata fadamawa? waye takedashi dazai iya tausayi mata yace "Rukayya kiyi hakuri everything will be alright"....

Ayanzu batada kowa dazata iya sharring wannan tarihin dan dukwanda take tareda su din tayi musu karya for years dabazata iya gogeshi ba yau kadai. idanunta sunyi cazir sun canza launi hakanan tanaji yana knocking kofar yana kiran sunanta anma ko gezau batayiba harya gaji dan kanshi yatafi.

Idanunta ne suka sauka kan litattafanta dake jere gefen akwatunanta and then an idea came right away. tashi tayi jiki ba kwari takarasa gaban litattafan nata sannan tadauki katuwar long note dinda tasaya tun last week don practicing drivations na *Geophysics* tadauki pen cikin jakanta sannan takarasa kan study table dinta dake can wani gefe a dakin...

Zama tayi ta ajiye littafin kan study table din tareda bude first page tana tunanin "may be inta rubuta tarihin rayuwarta taji sauki aranta,may burden dinda take carrying for more than 8years yaragu,may be her heart will somehow be at ease for a moment da inma takamane she'll published the book and distribute it to the world,taba ma mutane su karanta suji tarihin rayuwarta,su tausaya mata suce Rukayya ke jaruma, Rukayya kinyi kokari Allah ubangiji yasaka miki, Rukayya you'll have a better future ahead" and may be intaji wadannan motivational words din zataji sauki aranta,zata samu courage din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login