Showing 33001 words to 36000 words out of 121560 words
da basu azaba dan haka daular bayin take da bangarora manya manya daban daban.
Isowan Sarkin bayi tareda sabbin bayin daya siyo din ya saka aka bude babbar kofar da bangaren bayin Ana jiran saukowansu daga mota daya bayan daya bayan anyi parking motocin kenan.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
20
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
********
Ayanah na saukowa kanta a qasa yake sai data sauke ajiyan zuciya kafin ta dago ahankali tana bude idanuwanta da sukai Zurfi sosai ta kalli fadin harabar inda tarin motocin masu girma suke babu adadi masu yawan gaske,
Akan wadda suka fito ta dawo da idanuwanta ta tsayar tana kalla jikinta na Wani irin sanyin da babu tinanin komai a cikin kwakwalwanta lokacin dan haka ta tsayar da idanuwanta Akan Zuhrah dake saukowa a sanyaye itama babu Sauran tinanin kanta ko ‘daya daya rage musu.
Hannu Ayanah din ta daga zata miqawa Zuhrah sakina dake kusa da ita tayi saurin riqeta ahankali tareda dan girgiza mata kai batareda ta juyo ta kalleta ba sbd a dokar bauta baa yan uwantaka a nata sanin duk da kusan kowace nahiya da yanda suke nasu dokar.
Gefen Ayanah din Zuhrah ta tsaya Sauran suka qarasa fitowa kafin aka Dora su a hanya Ana wucewa dasu kansu duk kaf a qasa sbd duniyar da suka samu kansu wata abace da Allah bai taba nuna musu ko a mafarki ba,
Kaf dinsu kusan qalilan ne suka fito na gidajen alfarma ba da rufin asiri me girma,
Sunga daula iri iri me daukan hankali da iyalinsa duniya me rikitarwa amma kuma a nan inda suke gani yanxu ya wanke tinani da kwakwalwansu tas babu Sauran abinda ya rage sbd sun gama tabbatarda sunzo inda babu kamarsa a duniyarsu da idanuwansu suka gani hakama babu ranar komawansu ga iyalai ko qasa ko kuma taba ganin Wanda ma idanuwanka suka taba gani har abada dan hakanne kowane bawa a cikinsu jikinsa yake a sake sun gama saddaqarwa su yanzu basu din bane tace bayin BOYEM kuma da wannan sunan zasu mutu subar duniya.
Wata doguwar hanya aka wuce dasu me tsayin gaske wadda ta rabasu kwata kwata da harabar gurin inda bazasu sake ganinta ba zuwa babbar doguwar kofar shiga bangarensu me girman gaske.
Daya bayan daya aka fara shiga dasu dakin da ake fara shiga kafin wucewa ciki,
Daki ne babba Wanda yake tamkar office da cameras a ciki da tarin computers da wasu abubuwan da duka dai basu taba gani ba a rayuwarsu,
Daya bayan daya ake shiga dasu Ana yiwa kowa hoto tareda Id card dayake dauke da sunan kowa da hotonsa tareda uniforms da Sauran abubuwan amfaninsa.
Wuni akai Ana wannan aikin nasu har aka kwana anayi
saida aka kwana biyu Ana wannan aikin nasu kafin aka gama yiwa kowa,
Duk Wanda akaiwa shine kadai yake wucewa ciki Wanda baayiwa yana waje saida suka kwana a waje kuma kusan a tsaye,
Su Ayanah ne kusan na karshe sunji jiki sun galabaita sosai har basa iya tsayuwa daidai a rankwafe suke tafiya,
Suna shiga suma a kwai jakadiyar Sarkin bayi ta mata dake ciki itace kai tsaye ta basu nasu dakin,
Cikin saar da basu zata ba aka basu daki daya su uku tareda wasu Mutum uku din sbd duk daki Mutum shida ne.
Koda suka isa dakin akwai Mutum uku dake dakin daman wainda daman sun jima sosai a BOYEM din.
Basa nan suna gurin aikinsu da aka raba musu dan haka kai tsaye umarnin da jakadiyar bayin ta basu kowa ke kokarin cika wa Banda Ayanah data jingina jikin bangon dakin nasu Bayan ta shigo ta silale qasa tana rufe idanuwanta dake tsananin radadi quncin dake soya jini da gangar jikinta tana jin zuciyarta na Wani irin zafi da ciwon baqin cikin rayuwa me girman gaske dan batasan tayaya zata fara sabuwan rayuwar data samesu ba ta har abada babu Iyayenta da Nurat da Abaas ba a cikinta,
Batasan tayaya zata rayun bama sbd zuciyarta ta mutu gangar jikinta ne kawai ranta rage,
Zuhrah ma dawowa tayi gefen Ayanah din ta zauna ahankali tana kwantar da kanta a gefen kafadar Ayanah din tareda saka hannunta cikin nata suka sarkafe ahankali bata ce komaiba ta rufe ido hawaye masu dumi suka gangaro mata suna sauka a kan hannuwansu dake sarqe.
Bude idanuwa Ayanah tayi ahankali ta kalli hawayen yanda suke gangara a fatar Bayan hannunta ta Lumshe ido ta bude tareda Dora hannunta daya Akan fuskan zuhrah ta Shafa ahankali tareda juyowa kadan tayi sumbaci tsakiyar kanta da babu dankwali sun zama tamkar mahaukata ta sauke ajiyan zuciya tareda bude baki ahankali tace
‘Zuhrah hįyįwetēni bemulu,ye’īne aleem zuhrah(Zuhrah my whole life, zuhrah my world)
Allah ya hanani dandana rabuwa dake,
Ina rokon Allah ya dauki rayuwata kafin kaddarar da zata rabani dake tazo..’
Tsananta gudu hawayen Zuhrah sukai ta sake shigewa jikin Ayanah din tana fidda kuka Mara sauti tareda girgiza kai tana cewa
‘Ayanah idan babu ke wlh zan kashe kaina na biku duka bazan iya rayuwa a duniya ni kadai babu ku dukanku ba,
Na Roki Allah kaman yanda yabarmu muka rayu a tare zuwa yanzu ya raya mu a tare mu mutu tare mubar duniyar tare.’
Girgiza Kai Ayanah tayi idanuwanta na qara yin jajir tace
‘Abaas…’ sai ta kasa cigaba da magana ta rufe idanuwanta tareda sauke Numfashi me zafi.
Sun jima a hakan tsawon lokaci kafin sakinah da itama tana rabe a gefe ta taimaka musu suka miqe kafin suyi wani motsi aka fara buga wata qararrawa me karfi ta kiran kowa da anfada musu maanarta tin kafin a basu daki dan haka a sanyaye babu me iya miqewa tsaye daidai suka fito.
Kusan su Dari harda qari ne bayi mata sababbi da aka kawo yau din dan haka iya su dinne a bangaren yanzu sbd tsofin bayin basa nan duka suna gurin aiki dan haka suna fitowa a wani babban guri me fadin gaske dayake shafe da tiles fari qal da hanyar wucewan ruwa da famfuna babu adadi da hanyar wucewan ruwa Wanda yake nuna alama da gurin wanki ne,
A ciki gabaki daya aka turasu daya bayan daya aka saka kowace su ta tube Kayan jikinta aka sakar musu ruwa daga samansu batareda sunsan ta inda ruwan ke fitowa ba,
Ruwa sosai ne yake sauka akansu inda wata irin dauda take jiqa a jikinsu me yawan gaske tana gangara qasa take tiles din gurin ya sauya Kala haka ganin farinsa ko kadan ruwan daudar jikinsu ne kawai ke kwarara a qasa,
Wani irin qarni da tsami tareda wari ne sosai ya gauraye gurin take Wanda ya saka maaikatan mata sake ja baya suna nesa dasu dan duk bawan da aka kawo BOYEM sai an tsaftace sa sosai tin asali dan haka kowane bawa dake BOYEM ya samu Kansa a irin yanayin,
Umarni daga cikin lasifikar dake hannun jakadiyar ne ya shiga kunnuwansu cewan kowa ya Shafa abinda aka basa su wanke jikinsu sosai sosai.
Maaikatan da zasu tsaftace su ne suka fara shigowa daya bayan daya dauke da trays masu girma suna Jeruwa har suka gama shigowa kusan su goma sha biyar kafin jakadiyar ta shigo daga karshe.
Layi aka fara jansu daya bayan daya,
Ta farkon da aka fara da ita shaving cream aka shafe musu jikinsu dasu inda yake da gashi kafin aka dauki lafiyayyan almakashi aka Kama gashinta kai tsaye aka yankesa sosai aka bar Wanda tsayinsa bai wuce tsayin rabin biro ba.
Haka aka fara yi musu daya bayan daya Ana fesa Musu wani abu a cikin gashin Wanda take yake kashe dukkanin qwari ko qwarqwata idan akwai a ciki.
Haka aka ringa musu daya bayan har aka zo kansu Ayanah wainda idanuwansu suke a rufe zuciyar kowannensu na qarasa macewa tana barin gangar jikinsu.
Kama gashin Ayanah akai me tsananin tsayi take aka yankesa duk da akwai wainda suka fita tsayin gashin da yawa tinda su kusan a qasashensu babu mara gashin daman suna rage tsayin gashi yayan sarautarsu ne kadai basa rage gashi sosai sbd cikon al’ada ne ga dukkanin jinin sarauta,
Na Zuhrah ma dayake da tsayin dayafi na Ayanah haka aka yankesa Wanda ya sakata sauke ajiyan zuciya sbd shi Kansa gashin a yanzu tamkar azaba ce a garesu.
Mintina qalilan aka sake sakar musu ruwa masu yawa sosai aka sake wankesu sosai a karo na biyu kafin aka sako musu ruwan sabulu me kumfa sosai shima anan wankan sosai aka sakasu sukai tareda wanke kansu Wanda wasu hadda jini yake fitarwa tsabar qwarin dake cikin gashin suna Shan jininsu a maqale,
Sosai aka sake wankesu da ruwa me kyau kafin aka sake zuba musu kumfa sai da sukai wanka kusan so goma kafin aka sallamesu ana basu saqi na zanin Daurawa me kauri daya bayan daya suna wucewa.
Koda suka koma daki kusan da yawansu zazzabi ya gama rufe su na wankan duk sun shaqa ruwa wasu kuma sanyin ya shigesu sosai dan haka magani aka sake rabawa kowa koda haka zazzabin ance kowa ya sha.
Uniforms suka saka wainda bazasu iyaba kuwa zazzabi me karfi ya kwantar dasu Wanda ya saka da yawansu basu iya fitowa karban abinci ba harda su Ayanah wainda suke kwance sosai har jijjiga sukeyi.
Sakinah ce ta iya fita tabi Layi ta karbo musu abinci ta dawo dakin ta taimakawa Ayanah taci kafin ta taimakawa Zuhrah itama taci kafin ita taci daga baya.
Basu iya Shan maganin da aka basu ba sbd basusan tayaya zasu iya shansa ba,
Shiru sukai a daki babu Wanda yake iya ko tashi zaune a cikinsu sbd itama sakinar daga baya zazzabin bugar da ita yayi.
Sai dare kusan karfe daya tukuna suka Ji shigowan Sauran Mutum uku din dake dakin.
Babu wadda ta iya tashi a cikinsu suna dunqule guri daya sunyi Laushi sosai,
Dayar cikin wainda suka shigo dakin ce ta iya isowa inda suke taga yanda suke jijjiga sbd zazzabin dan haka tayi saurin daukan maganin da aka basu ta jiqasa da ruwa ta fara kamo kan Zuhrah ta bata a baki Tasha sosai sbd kishirwa take ji.
Sakinta tayi ta Kama Ayanah itama ta bata tareda ruwa sosai kafin sakin daga qarshe.
Amai sosai zuhrah tayi sosai Wanda ya saka Ayanah tattara karfin Hali ta miqe sbd kulawa da ita cikin wahalar nata ciwon.
Sakina ma karfin halin miqewa daga ciwon tayi itama suka taru dan kulawa da Zuhrah wadda take jin jiki sosai harma hankalin Ayanah yayi mugun tashi tsoro me karfin gaske ya kamata.
Daqyar suka samu gari ya waye jikin Zuhrah din ya dan samu sauki sosai tayi bacci wadda bata taba samuba a watannin.
Itama Ayanah baccin ne ya dauketa na wahala har tsawon lokaci Wanda shine ya taimaka musu suka samu Wani irin sassauci me girma da qwari sosai.
Guraren 10 na safe aka buga kararrawar kira wadda ta fiddo kowa suka bi Layi aka raba musu abinci suka dawo daki suka zauna suka Turawa cikinsu sbd basajin dadin rayuwar bare abinci
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#BEST ROYALTY STORY
#BOYEMS
#GHAZ
#NUAB BOYEM
#LOVE
#ROMANCE
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
21
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
************
Wuni sukai a daki ba komai ba wani hayaniya ko doguwar motsi koina tsit sbd kowa ya fice sai su sabbin zuwa,
Sai yamma aka sake kiransu wanka haka aka kuma wankesu tas suka dawo daki yau kusan kowa da Kansa yasha maganinsa sbd abinda ya hanasu Shan na farko rashin sanin yanda zasu sha amma ganin ya taimaka musu jiyan sai kowa yasha.
Da dare ma haka aka kuma kiransu aka raba abinci sukaci suka kwanta Wanda take baccin wuya ya dauke dukansu kamar bugaggu Wanda basu saniba harda maganin bacci ake basu sbd anason su samu ishashen baccin da zai warware qwaqwalwarsu ta sake sbd gudanar da rayuwarsu a natse dan komai a BOYEM nutsuwa ce tsagwaranta yake buqata.
Washe gari ma haka aka kuma basu ci da wanka tareda magani suka wuni suna bacci da hutawa,
Duk yanda zuciya da kwakwalwan su Ayanah yake cikin wani irin qunci da damuwa me nauyi maganin da aka Dora su akai fin karfinsu yayi bacci suke yi sosai batareda sunsan ma tayaya kansu ya fara sakewa ba yana dan dawowa da tinaninsu Akan hanya daga fatan mutuwar da sukewa kansu kullum.
*****kaman yanda doka da kaidar Masarautar BOYEM take sai anyi sati biyu cif Ana basu abinci fa Hutu sosai kafin Ayi wata daya Ana horar dasu komai na masarautar Bayan an gama tababbatarda sun yadda ce tarihinta da sanin kowane irin bayani Akan bautar da zasuyi dakyau Wanda idan Baka da qwaqwalwar haddace komai da riqe komai kan hidimar dake gabanka shine ake Tura Mutum bangaren wahala da azaba inda zaka gwammace rayuwa a wata qaramar masarautar daji da babu gabas bare yamma.
Haka su Ayanah suka share sati biyu Ana basu Hutu duk da babu Wanda yake cikin dadin zuciya ko kadan a cikinsu amma jikinsu da fatar su ya samu lafiya sosai dan kuwa ko gurin Kwanciyansu a tsare yake da tsafta da dokoki,
Sun sauya sosai gangar jikinsu ta samu nutsuwa dan haka aka fara koyar dasu mataki ma biyu Wanda kullum ne ake koyar dasu yanda ake aiki da komai a masarautar irin su wanke toilet da gyara tareda iya aikin koina da yanda zasu iya fuskantar rayuwarsu idan sun tsayu a gaban duk Wanda yake jinin BOYEM.
Rayuwar bayin BOYEM hatta inda zasu iya dagowa su kalla a qayyade yake hakama yanda zaka iya bude baki ko fidda Numfashi me sauti a gaban jinin BOYEM Akan kaida da doka yake hatta dukkanin gangar jikin bawa da abinda yake gangar jikinsa Akan kaida da tsari tareda amarni yake.
Wasu irin kaidoji da dokoki tareda tsari masu tsauri da karfi aka fara dorasu dan kuwa ko tafiyarka a tsari take aka dorasu,
Lokutansu na bacci da fitowa fara aiki tareda wata irin tsaftar gaske duka Akan tsari suke da yanda ma zaka dago kai Ka iya kallan inda kake sbd kaida ne koyaushe Kanka ya zama a qasa,
Duk jin dadi da nutsuwar da suka samu a BOYEM din tsari da dokokin tini suka daga hankalinsu tareda shiga tsoro me tsanani sbd laifuka da kurakuran da zasu iya rabaka da ranka a masarautar yawa ne dasu sbd mafi yawan hukuncin kasar cire kai ne kawai kokuma ciyar da dabbobi namanka dan haka babu Wanda yake yadda komai tsananin tsautsayi yayi laifi dan tsira da rayuwa,
Mataki mataki ne na bayin masarautar sai Wanda yakeda matakin saar karshe ta rayuwa yake samun damar yin aiki a inda asalin jinin BOYEMs din suke.
***Ayanah da Zuhrah harma da sakina basuda Sauran kowane zabi Bayan mayarda hankali suna daukan karatun da ake musu tareda samun qarin nutsuwa sbd a yanzu damuwa da kuncinsu a natse ma yake cinsu,
Sun sauya sosai kawai dai quncin dake kwance a zuciyarsu ne yake hanasu yin jiki ko mulmulewa suna nan basu wani qara kiban komai ba kawai dai yunwa tabar jikinsu.
Kullum da safe a kaida da doka zasuyi wanka su shirya a cikin uniform dinsu tsaf tsaf su isa gurin karban abinci abi Layi su karba abinci su ci kafin masu wucewa aiki su wuce su kuma su isa inda ake karantar dasu acan suke wuni sai yamma suke dawowa.
Sakinah data Saba da bauta zuwa yanzu ta sake ta karbi sabuwar rayuwarta da babu matsi hannu bibbiyu tareda samun nutsuwa da gode wa Allah daya rayar da ita ta fito daga hannun kusra batareda rasa komai nata ba dan haka a yanzu batada doguwar damuwa saita Ayanah wadda koda minti daya quncin dayake zuciyarta bai taba fita ba zuciyarta a qulle take tamau da wani irin qunci da damuwan da har abada kila bazasu fita ba dan rayuwarta ta Riga tayi rushewan da bazata taba gyaruwa ba,
Tana komai Akan lokaci tareda komai da ake Dorasu akai a natse babu hayaniya babu rawan jiki komai nata yayi sanyi ya koma zallan nutsuwa bata sake bude baki ta Ambaci Abaas ko Nurat ba komai ta tattara ta ajiye sa a cikin zuciyarta yana cin lafiyanta da kwakwalwanta a hankali ahankali batareda sanin kowannensu ba,
Sakinah datafi su wayo da shekaru sosai