Showing 42001 words to 45000 words out of 121560 words

Chapter 15 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3763

yayi kuskure ko laifi,
Babu me mulki ko muqamin wasu qasashen da baya shakka da tsananin tsoron Masarautar BOYEM da sultan dinta YASAR ALMAZ,
Babu matarsa ko imebētinsa da basa sunkuyar da kansu a qasa idan yana kusa
Amma duka wannan babu babban Buri me tsananin gaske ga sultan YASAR irin samun LEUL,

Ya batar da dukiyar da bata lissafuwa ko a gurin masu lissafi gurin sadaka da Malamai gurin adduar Neman haihuwan LEUL Wanda babu abinda bazai iyaba akan ya samu haihuwan Namijin.

jamaar qasar BOYEM da masoyanta a tsaye suke gurin addua da biyan malamai wasu harma da Neman manyan bokayen qasashe duk akan Allah ya bawa sultan YASAR magajinsa wato LEUL BOYEM,

Duk Wanda yasan BOYEM da Wanda yake cikinta koda bawa ne kuwa yasan da wannan tsantsan burin me girma da karfi na sultan YASAR ALMAZ BOYEM,

Wannan shine babban dalilin daya saka ake zabar masa imebēti daban daban yana kwanciya dasu babu kakkautawa sbd Neman haihuwan LEUL BOYEM wato magaji zakin BOYEM.
#MAMUH
#BOYEM
#BEST LOVE
#BEST ROYALTY

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

25
Ayanah tana cikin masu kulawa da yanayi na laulayin faree wato imebētin sultan wadda kwata kwata batai farin ciki da samun cikinba sbd yanda taso taci gaba da samun damar datafi mata komai duniya ta zuwa shimfidar namijin dayafi kowane namiji daraja a qasar BOYEM dama zagayenta,

A ranta tariga tasan kila itama macen zata Haifa tinda shine baya haihuwan namiji dan haka Sam bata wani doki da cikin gashi matiqar mace na laulayi baa kara kaita tirakarsa sbd baya iya mu’amalantar mace me laulayi sosai dan haka faree sai an yayeta sedai ta jira haihuwa idan tanada rabo zai sake buqatan kwanciya da ita,

Wannan quncin da baqin cikin ne a zuciyar faree wadda laulayi takeyi sosai ga qarin baqin cikinta shikenan ta zama macen da har abada bazata sake samun Wanda zai aureta ko kwanciya da ita har sai ranar da sultan YASAR baya duniya dan babu Wanda ya isa yana raye ya kusanci Matar da shi ya kausanta indai ta haifar masa ‘yaya kenan.

Baqin cikin dake cin zuciyarta da damuwan hakan ya saka laulayinta yake tsananta bata kaunar kowa ko komai Bayan hantara da kyara da rashin daraja ko kadan babu abinda take yiwa bayin dake mata hidima kaman zasu bata rayuwarsu.

Ayanah ma kusan so biyu tana qonewa a hannu da ruwan zafi sbd hidimarta da fadanta,

Duk wahalar da Ayanaah Tasha sosai ta rayuwar da suka fito ta qangin bautar kusrah ta wanke sosai lafiyar fatarta ta dawo haskenta ya dawo sosai amma ba duka ba sbd ba lallai ta koma asalin fararta qal ba har abada kila,

Tsayin gashinsu ya dawo sosai duk da akai akai ana yanke musu tsayinsa sbd tsafta baa wani son tsayin gasu sosai a gurin bayi dan haka duk Bayan watanni kadan ake yanke musu tsayinsa bawai aski ba kawai dai zaa yankesa baa son ya wuce iya wuyansu ya sauka kafada zuwa bayansu.

Gashinta ya dawo sosai da tsayinsa gashi lokacin yanke musu baiyiba dan haka take dunqulesa sosai a cikin hularta ta uniform,

Faree dukkanin bayin dake mata hidima kyawawa ne sosai bama kaman ita Ayanah din wadda sanyinta da nutsuwanta ke qara mata kyau da burgewa,

Faree jin tayi duk ta tsanesu bata ko kaunar ganinsu dan idan kaddararsu me kyau ce ko a cikinsu zaa iya zabar imebēti koma dukansu zaa iya zabarsu,

A duk lokacin data gansu tafasa da ciwon rai zuciyarta keyi dan haka ta dauki hanyar illatasu a cikin dabarar da bazaa taba zabarsu ba,

Hakanne ya saka so biyu tana kokarin koma Ayanaah da ruwan zafi sedai Allah bai saka ta taba samunta a Fuska ba sedai hannuwa kuma har so biyun babu inda fatar Ayanah tayi tabo sbd matiqar kanada tabon daya wuce numbernk ta Shedan bauta dake jikinka to Ka haramta ga zama imebēti.

Ayau ma umarnin su hada mata ruwan wanke kafa tayi su dukan haka suka hada ruwan mai dumi daidai yanda zai mata daidai a fata suka kawo suna ajiye a gurin hutawanta dake dan madaidaicin American garden dinta dake nan cikin bangarenta,

Tamkar wadda zatai wata gagarumar hidima haka aka tsara mata gurin suka shirya mata komai daidai yanda zata Ji dadin hutawan da wankin kafar da zaayi mata,

Ayanah da sakina ne biye da ita kansu a qasa a lokacinda take fitowa tana isowa gurin
Ayanah na dauke da wani lallausan showel din lullubawa mai tsananin taushi Wanda idan iskan gurin yayi mata yawa zaa rufa mata,

Sakinah kuwa wasu towels din da zaa goge kafafun ne idan an gama a hannunta suma masu Laushi suka qaraso,

Zaunawa tayi dukansu suka koma bayanta suka tsaya Sauran masu wankin kafar kuwa suna durqushe gabanta suna jiranta,

Farawa sukai ta jingina bayanta jikin lallausan kujeran tana Lumshe idanuwanta,

Tray din tea mai Zafin gaske aka kawo mata da snacks din da yanzu ne akai mata su da Zafin su aka kawo aka ajiye gabanta,

Zuba mata tea din akai yana wani irin siracin daya sakata zubawa hannun wadda ke zuba mata din idanuwa tana kallan yanda zara zara yatsun hannunta farare tas ke daukan ido take taji wani irin abu ya taso ya danne zuciyarta batasan lokacinda ta dauko ruwan tea din gabaki daya ta watsa musu su hudu dake gabanta ba duka a Fuska tareda wurgi da Kayan gaban nata tana jin Wani irin Zafin zuciya kaman zai kasheta.

Cikin tsananin azabar data ratsasu har cikin qwaqwalwa suka sauke kansu qasa batareda sun zabura ba ko magana bare nuna halinda suke ciki sedai idanuwansu sukai jajir suna sake sauke kansu qasa tareda bata hakuri akan abinda ya bata ranta.

Ayanah ma qasa suka sake yi da kansu cikeda wani irin sanyin jiki batareda sun motsa ba,

Cikin zafi da faree ta bude baki tace

‘Ina buqatar wani shayin ganye’

Miqewa sukai a natse suka bar gurin dan hado mata wani.

Suna barin gurin sakinah ce ta zagayo gabanta ta durqusa itada Ayanah suka fara wanke mata kafafun cikin nutsuwa da tattali kaman kafar zinari.

Suna cikin yi aka sake kawo mata sha yin ba Imani ta sake zubawa su Ayanah dake gabanta Wanda sakinah dake gefen Ayanah tafi samun ruwan sosai sbd dan karewa Ayanaah datai batareda lurar faree din ba dan haka suma take idanuwansu sukai jajir Wanda ya tabbatarwa da faree wannan Karan kam ta gama da bayin bangarenta babu wadda zaa iya zaba a cikinsu sbd duka konuwarsu a Fuska ne indai ta tashi to tabbas sun haramta har abada.

Hakan data ga ta samu ya sakata samun sassauci da sakewa hankalinta ya dan kwanta ta koma yar walwalarta.

Su kuwa gabaki dayansu su Ayanah kusan ruwan sun kona fatarsu sosai musamman sakinah wadda har wuyanta saida konuwar ta dan tashi dan haka kwana Ayanah tayi bawa sakinah kulawa sbd ita iya ruwan da suka sameta basu wani Konata ba ja kawai gurin yayi kuma koda gari ya waye jan ya rage kuma a kirjinta ne dan haka baa gani.

Haka suka shirya suka taho aikinsu kowa gefen Fuska da wuya a kone ga zazzabin azabar wutar ga radadi haka suke aikin.

Kwana biyu konuwar tayi ta dan caccabe haka dan haka faree ta sake samun nutsuwa suka ci gaba da hidimarsu,

Sakinah da Ayanah take kulawa da ita sosai idan sun koma daki sai tata wutar ta Riga ta Sauran warke wa amma ba kwata kwata ba gashi kusan sati biyu kenan suma Sauran tasu ta warke sama sama,
Tsoro biyu ne damuwa biyu take cinsu akan konuwar sbd idan ranar zabar imebēti tayi aka sameka da tabon dayake sabo ba tsoho ba to tabbas kanada hukunci me tsauri dan hakan yana nuni da sakacinka dan kuwa ko yancin raunana Kanka baka dashi sam tinda jikinka ma ba ikonka bane dan haka suke cikin tsananin tsoron hukuncin hakan.

********A daren ranar da zaa tara bayi mata kaf kwana Ayanah tayi Zaune itada sakina cikin wata irin damuwa da sanyin jikin hukuncin da sakinah zata iya karba na qaton tabon konuwarta,

Dukansu damuwansu daya ne kada a sauyawa sakinah guri a cikin hukuncinta a rabasu,

Ta Dayan bangaren kuma acan qasan zuciyar Ayanah dake sosuwa sosai da qunci shine inama itace ta kone din,

Basu wani rintsa ba da damuwa me nauyi da sanyin jiki suka gama komai suka fito zuwa aikinsu.

A kaidar zabar imebēti daki daki ake bi dan haka Layi bai iso bangaren imebēti faree ba Sai dare Wanda tenya ce da kanta tareda bayinta kusan su goma biye da ita cikin nutsuwa da taqama da wani irin kwarjininta ta iso take dukansu suka zube qasa hadda faree wadda itama kanta yake qasa sbd ten’ya kwarjininta nada nasaba da matsayin datake riqe dashi na ita kadai ce takeda power ta zabawa sultan macen dazai kwanta da ita,ita kadai ce takeda power ta zabar wadda zata iya daukan cikin sultan ta haifar masa ‘yaya kuma itama tanaji a jikinta insha Allah a cikin zabinta ne zaa samu macen da zata kafa tarihin haifar LEUL na wannan zamanin dan hakanne ma wannan Karan mata shida zata zabar masa lokaci daya yana dawowa saiyayi sati kullum yana Bare sabuwar mace.

Kai tsaye idanuwanta ta sauke akan fuskokinsu zuwa daya bayan daya tana binsu da kallan nutsuwan da kyau ne zalla take gani a tattare dasu sedai kowacensu babban tabo ne a Fuska,wuya da hannuwansu,

Batace komaiba ta zubawa faree ido tana karantar yanayinta kafin ta maida idanuwanta akan tabonsu dayake nuna wuta ce a jikin kowannensu,

Kyansu ta sake kalla da kyau take ta fahimci komai ta tabbatarda meya faru dan haka kai tsaye akan Ayanah ta tsayar da idanuwanta wadda kanta ke qasa.

Cikin bayinta ta kalli daya kai tsaye wadda ta fahimci me take nufi take ta matso gurin Ayanah ta saka hannu ta zare Hular kanta gashinta dayake dunqule take ya zubo ahankali yana sauka a bayanta.

Faree da kanta ke qasa har lokacin wani mummunan yawu ta Hadiye zuciyarta na harbawa da karfe sedai kafin su dake jan Numfashi su fitar take ten’ya ta kalli Ayanah ta bude baki tace

‘Tashi ki bisu’

Ayanaah da bata gane me hakan ke nufi ba miqewa tayi ahankali tareda bin Bayan bayi biyu da akace ta bi tana adduar kada hukuncin da zaa yiwa su sakina daya saka akace ta tafi yayi tsauri.

Tafi me dan tsayi kadan sukai suka isa wani babban guri nai shegen kyau da tsari Wanda a cikinsa zaa yiwa duk macen da aka zaba gyaran fitar hankali na ciki da waje na wata daya.

Tana saka kafarta cikin gurin taga mata a jere tsaye gabanta yayi mummunan faduwa ta tsaya cak tana kallan gurin da idanuwanta Wanda ke fahimtar da ita menene yake shirin faruwa a gurin.

Kasa daga kafarta tayi sbd toshewan da kanta ke Neman yi ta juyo ahankali ta kalli wainda suka kawota zatai magana numfashinta ya dauke cak bakinta ma kafewa yayi komai nata ya Dena aiki ya tsaya cak sbd idanuwanta da suka sauka akan Zuhrah da aka shigo da ita itama……
#MAMUH
#BEST ROYALTY STORY
#BEST LOVE
#LOVE/ROMANCE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

26

*_UMMU ASLAM COLLECTION_*
08035014107
-Ina mata yan kwalisa masu son burgewa?
-Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so?
-shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema?
-kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali?
-kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so?
-ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso?
To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki.

***********
Dauke wuta kafafunta suma sukai maqoshinta na wata irin bushewa qayau yawun bakinta suma suka dauke,

Wani yaji yaji taji yana cike idanuwanta sbd tashin hankalin da baida ‘dan uwa a gareta,

Zuciyarta kuwa harbawa take a kirjinta da mugun karfi da wani irin rauni dayake gauraye gangar jikinta na ganin Zuhrah Ayau cikin idanuwanta a Karan farko Bayan rabuwarsu kusan shekara guda,

Ayau idanuwanta sun samu haske da rahamar da suka rasa,
Ayau zuciyarta ta samu abinda ta rasa na haske da bugawa daidai Bayan shekara guda,
Ayau dukkanin duhu da yanar dake zuciyarta sun haskaka da ganin gudan jininta ruhinta Zuhrah wadda itama Zuhrah dake cikin tsananin qunci da baqin ciki komai nata sakewa yayi da ganin Ayanaah dinta rayuwarta,kuzarinta,gangar jikinta,bugun zuciyarta harma ganinta sbd a tsawon wannan lokacin ita ko na minti daya bata taba walwala ko farin ciki ko misqala zarratan sbd da gaske Ayanah ce rayuwarta hakama bata tareda kowa da zai kaunace ta ko kulawa da ita ko Wanda zatai wa magana ko kalla taji sassaucin komai ita kadai take rayuwarta babu kowa a cikinta Wanda hakan ya taba rayuwarta da zuciyarta sosai harma da kanta sbd babu abinda take ako Yaushe koda da dare ne Bayan zubawa guri daya idanuwa tana ganin duka ahalinta a idanuwanta ba kamar Ayanaah ba datake tareda Sakinah,

Ganin Ayanah a gabanta yau cikin idanuwanta ya gama cike dukkanin gurbin matacciyar zuciyarta da bugawa kadai takeyi babu abinda ya rage a cikinta,

Ganin Ayanah Ayau ya farfado da rayuwarta dake gap da barin duniya sbd tana cikin tsananin qunci da azaba sbd a inda take babu sauki ko kadan ta rame sosai tayi Wani irin fayau alaman kowane lokaci ciwon dake zuciyarta zai buga zuciyarta ta tafiyarta itama,

Kokarin gazawa kafafunta sukeyi dan mutuwan da duka jikinta keyi yana sanyi amma a hakan take daga kafafunta ahankali tana tako wa ahankali sbd wainda suke tareda ita,

Qasa tayi ahankali da idanuwanta a daidai lokacinda suka iso gurin da su Ayanaah din suke tanajin zuciyarta na Wani irin yanka da radadin dayafi na kullum babu abinda ruhinta da gangar jikinta da zuciya ke tsananin so a lokacin Bayan jin jikinta dana Ayanaah ya hadu sun rungume juna sunji dumin juna sun Ambaci sunan juna sun Shafa fuskan juna sunji muryoyin juna,

Da zata samu hakan tabbas da ciwon dayake cin zuciyarta zai warke koda kuwa warkewan tafiya ce to tabbas zata so hakan,

Ayanaah ma da zuciyarta ke wata irin bugawa kaman zata faso kirjinta ta fado sbd tsananin so da kaunar yar uwarta daya taso mata ahankali ta sauke kanta tana Jin kowane sautin takun Zuhrah na sauka kunnuwanta yana dukan kirjinta a lokacinda suke kokarin wucewa ta gefensu sunaji suna gani kowannensu ya sauke kansa daga kallan junansu,

Rintse idanuwa Ayanah tayi ahankali wani radadi na sake cikesu suna yin jajir
duk abinda ta juyo tayi magana akansa bace wa yayi daga kanta da tinaninta sbd ganin Zuhrah Ayau ya tsima duka abinda take danne wa da jurewa,

Kamannin Zuhrah dinta sun sauya sosai ta koma tamkar ba ita ba duk da tayi haske sosai amma babu abinda kai tsaye yake bayyane a jiki da fuskanta sai damuwa da qunci me tarin yawan gaske da tabbas zata iya rasa ranta da bugawan zuciya,

Bude idanuwanta tayi ahankali radadin cikinsu na qaruwa tanajin takunsu har lokacin a bayanta suna tafiya suna nisantar ta.

Rufewa idanuwanta da zuciyarta sukai babu abinda take so Bayan sake saka Zuhrah a cikin idanuwanta dan haka ahankali ta juya batareda karfin jiki ba ta nufi cikin itama tana mantawa duka kwata kwata da abinda yasa aka kawo su gurin,

Taku sukeyi suna qarasa shiga ahankali a bayansu Zuhrah din Wanda Zuhrah na jin sautin saukar kowane takun Ayanaah din dake bayanta yana karya zuciyarta tana jin a daidai wannan lokacin ma Allah ya cika mata burinta tana taka guri daya tareda Ayanah tana shakar numfashin guri daya da Ayanah,jajir idanuwanta sukai itama tana ci gaba da taku mai sanyi batareda alaman ko juyowa ba kaman yanda itama Ayanah bata dago kai ba kanta a qasa yake tana bin sawun da Zuhrah ke wucewa da idanuwanta kaman ta durqusa ta sumbaci gurin,

Ciki gabaki daya inda wani fadeden gurin gyaran jiki da wankan asalin lalle da qamshi dayake cike da pool din ruwan dumi da har wani hayaqi me qamshi yake tashi a cikinsa,

Su tara ne cif aka zaba dan haka duk wadda aka shigo da ita ahankali ake tayata zare Kayan jikinta ta shiga ruwan Lallen da qamshi masu dumi Wanda zaa jiqa su a cikinsa tsawon wuni guda kullum haka zaa musu tsawon kwana uku sbd lalle yana tsotsewa da kashe kowace irin cuta dake jikin dan Adam dan haka sai an riqa jiqa su tsawon kwana uku sun rabu da kowace irin cutar wahala dake jikinsu tsaf kafin a fara jiqasu cikin ruwan madarar nonon raqumi shima.

Zuhrah dake gaba bayin dake tareda ita ne ahankali suka zare mata Kayan jikinta daga ita sai kamfai irin na jikin kowa Wanda ake raba musu tareda uniform sai qarama rigar halfvest datake kame nonuwansu qarama ce sosai,

Kama hannunta sukai suka isa bakin pool din da ita suna riqe da hannuwanta duka biyu ta zura kafafunta ahankali ta shige ruwan idanuwanta da zuciyarta babu inda suke Sai a tinanin Ayanaah dake bayanta wadda itama ahankali aka zare mata nata Kayan take gashinta ya sauka bayanta aka sakota cikin ruwan ahankali ta tako ta iso gefen Zuhrah wadda itace karshen shiga ruwan a tare suka zauna cikin ruwan ahankali gabaki daya jikinsu na shigewa har zuwa sama kirjinsu iya inda ruwan ya tsaya kenan.

Wata Mutum daya ce aka sake shigowa da ita ta karshe kafin aka taho da wani sabon lallen mai dan yawa aka zuba a cikin ruwan tareda ruwan zafi dazai qarawa ruwan nasu dumi sosai ta yanda lallen zai ratsa koina a jikinsu sosai.

Ana gama zuba musu komai Juyawa maaikatan sukai gabaki dayansu suka fice daga gurin tareda rufe kofar suka tsare bakin kofar sbd bazaa taba budewa ba sai lokacin fitowansu ruwan yayi.

Daga Ayanah har Zuhrah babu tinanin dayake ransu Bayan son kasancewa a tare daidai wannan lokacin tareda son jin junansu dan haka gabaki daya sun manta da mummunan qazamin lamarin daya sakosu gurin fatansu daya kawai su kasance tare.

Shiru gurin yayi kowacensu su taran da abinda yake ranta na wannan nannauyan kaddarar data hau kansu,

Ratsasu ruwan dumin lallen keyi tako Ina suna jin dumin me zafi har cikin zuciyarsu sbd tsoron d suke ciki yafi komai yawa a cikin zama imebēti sbd kowane lokaci zasu iya rasa rayuwarsu dan haka kowa shiru yayi jiki a sanyaye ba kowane irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login