Showing 3001 words to 6000 words out of 121560 words

Chapter 2 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3752

tafiya duk da baa taba kamasu ba amma bibiyan da ake musu idan ya kaiwa gari hari ya kwashe mutane yana basa Tangardar mutuwa bayinsa sosai sbd basa tsaya wa duk tsananin rashin Kyan ruwa haka suke tafiya a cikinsu batareda sun tsaya kowace qasa ba dan hakanne bayin da sukayo safara suke mutuwa sosai sbd rashin sabo amma a yanzu idan baa saniba tafiyar kwanciyan hankali zasu yi ba jigata bayi har zuwa BOYEM Wanda tsafa da Kyan bayinsa zaisa wannan Karan su samu shiga BOYEM din.

Tutar bada izinin farauta ya miqa hannu ya fizgo ya daga sama cewa

‘Cikar burin kusra’

Cikin tsananin Murna da sauti me karfi na mutane masu yawan gaske ya ringa tashi suna amsa wa da

‘Cikar burin kusra’

Dajin gabaki dayansa da ruwan haka maganar ta ringa amsa wa dan haka take aka juya kan Jirgi zuwa baya inda suka baro zaa tsaya.

Da Asuba suka isa inda Jirgin ke tsayawa kuma a cikin asubar suka hawo qananun Jirguna suka koma kusan su sama da dari biyu suka yada zango a cikin dajin inda zasu zauna kafin fadawa garin.
#MAMUH
#ROYALTY
#WEALTH
#LOVE
#BEST MALE CHARACTER
#NUAB ALMAZ BOYEM
#GHAZ
#KUSRAH
#BEST LOVE/ROMANCE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

3
Daga wannan ranar burin kusra gabaki dayanta ya koma Akan ANJOM,

Sun yada zango a duhun dajin kauyen ba shakka ba tsoro ba fargaba sbd babu abinda yake basu tsoro kuma daman su daji da cikin ruwa ne gurin rayuwansu,

Idan suka saka Buri Akan gari to tabbas sai sun cika wannan burin ta hakanne sukai suna sukai karfi suka zama abin tsoro da shakka ga garuruwan daba manya ba,

Abu na farko da suka fara fuskanta shine dajin na dauke da tarin macizai da babu Wanda zai iya tsallakewa ya wuce dajin gaba ya isa cikin hanyar garin dan sun fara rasa mutanensu sosai da dafi dan haka suka sauya mataki ta hanyar fara farautarsu amma kaman dai dajin babu abinda yake cikinsa sai tarinsu dan haka suka fara Neman hanyar shiga.

Khams shugaba kuma me sarautar kusra shi kadai ne yake iya keta dajin ya shiga harya fita babu abinda ya samesa sbd tsananin abubuwan dake jikinsa na tsari da kariya daga kakanninsa,

Dan haka shi kadai da Kansa ya shiga yayi tafiya me Nisan data daukesa kusan wani daya sai gashi a farkon garin ANJOM Wanda ya sakasa tsayawa cikin tsananin farin ciki yana Jin wani irin Mazarin ganin hasken samun cikar burinsa Wanda samun wannan garin zai cika masa,

Jajayen idanuwansa ya rintse da karfi ya bude su ahankali yana shakar iskar garin me tsananin dadi da nutsuwa tareda kwanciyan hankalin da zai juya musu zuwa tabbataccen baqin cikin da baza su taba mantawa ba a tsawon tarihi,

Juya wa yayi ya fara kallan koina dake nuna arziki a garin,
Mutane daddaiku dake hidimar gabansu a farkon garin ya ringa bi da kallo wainda kowannensu yake harkar gabansa cikin farin ciki da annashuwa batareda sun Lura dashi ba sbd sanin baqon da baida shedan shigowa baqunta daga GHAZ baya taba shigowa garin.

Wani iskan farin ciki da tsananin Jin dadi khams ya sake yana daga kafafunsa yaci gaba da takowa zuwa cikin garin yana Jin kaman ya kamasu a lokacin ya bude ido yagansa a bakin ruwan shiga qasar BOYEM.

Tafiya yake yi yana sake Jin zalamarsa da tsananin rashin imaninsa yana fadada sbd yana qara shiga yana ganin tsananin mutanen da garin zai yi Wanda zasu cike dukkanin abinda yake nema.

Ahankali daidaikun mutane suka fara kallansa suna shiga tsananin mama ki da fargaba sbd yanayin baqinsa da yayi yawa da muninsa tareda kalar kayan jikinsa da komai yake baqi babu abu ko daya dayake jikinsa dayake da wata kalar Bayan baqi.

Lura da hakan ya zame ya dawo wajen gari ya fara dakun damar shiga garin har dare yayi sosai tukuna ya sulalo cikin garin yana zagaye wa ya gama Karance yanda rayuwan darensu take sedai abinda ya fahimta babu yanda zaa yi ya isa ko kusa da hanyar gidan shugaban garin Wanda a cikin Daren ya sake tabbatarda kafi ne a garin ta yanda yana buqatan karyasa kafin su samu daman shigowa su samu abinda suke so dan haka ya dawo farkon gari.

Bakin wani qaramin gidan dake farkon garin ya tsaya yana zubawa gidan idanuwansa da babu komai a cikinsu sai rufe wan ido na rashin tausayi ko kadan.

Kallan gidan yayi sosai kafin ya saka hannunsa jikinsa ya zaro wata wuqa baqa qirin me tsananin kaifi da dafi ya tinkari kofar shiga gidan yana isa kofar shiga wadda take ta itace kafarsa ya saka ya turata da karfin gaske Wanda take ta fadi sedai batai wani qara ba sbd kasancewanta ice ba karfe ko katako ba.

Shigowa yayi Kai tsaye ya nufi dakin farko dayake gidan yana shiga dakin ya fizge labulen dake dake take hasken farin wata ya ratso cikin dakin,

Yara ne su hudu a kwance jere suna bacci cikin nutsuwa

Wuqar hannunsa ya daga bai tsaya komaiba ya qaddamar musu ya fito dakin hannuwansa da fuskansa duka jini ya fada Dayan dakin acan iyayen suke take ya take kan Baban da kafarsa ya soka masa wuqar hannunsa da karfi a gefen hannunsa yana fizgo maman itama ya doke wuyanta da karfi take ta yanke jiki ta some a gurin.

Fizgo Baban yayi cikin tsananin karfi ya sake soka masa wuqa a gurin daya soka masa farko ya miqar dashi cikin rashin tausayi ko kadan ya dauresa ya durkusa ya dauki Matar yajasa da igaya ya fice dasu.

A cikin duhun Daren ya biyo daji dasu ya Baro garin
Tafiya me tsanani sukai har gari yayi haske tukuna suka samu tsallake rabin dajin zuwa me hadarin ga mamakinsa suma babu abinda ya samesu harya tsallake dasu suka sake nusawa

Matar na farfadowa ya sauke ya daureta tareda mijin yaci gaba da jansu cikin Axaba da rashin tausayi ko kadan.

Sai dare ya sosai ya iso wajen dajin dasu inda mutanensa suka taso suka tarbesa tareda karban masa.

Azaba suke tsananin cikin musamman Baban da jininsa ke fita a hankali daga yankar da yayi masa,

Maman kuma bakinta da dukkanin yawun jikinta sun gama bushewa daqyar dukkaninsu suke numfashin azaba da kafafunsu da duka sun fashe daga tafiyan.

Kusrawa basu tsaya komaiba suka hau gana musu sabuwan azabar data saka kowannensu some wa amma a hakan suka cigaba da basu azabar data saka mijin mutuwa sbd jininsa daya qare qaf daga jikinsa.

Duk wani sirrin ANJOM sun samesa a bakin Matar wadda azaba take daf da dauke ranta,

Sun samu sanin komai da sanin asalin mene ze karya musu garin su samu shiga a bakinta batareda tasan mijinta ya mutu ba sbd ta tsiratar dasu ta fada musu abinda suke son ji.

Azabarta bata qare ba sun saida suka tirsasata ta samo musu jinin GHAZ,

Sbd Neman kubutar dasu mijinta ta dawo ANJOM inda ta fadi duk abinda ya faru Banda cewa mijinta na raye zata samo musu jinin GHAZ dan tseratar dashi,

Da farko jinyarta akai a cikin iyalinsa sbd yanayinta da tausayin mummunan halin data shiga na rashin ‘yayanta duka da mijinta datace ya rasu batareda tasan da hasken ya rasu ba,

Adalci da tsananin tausayin GHAZ Ali ya saka ya dawo da ita cikin iyalansa da qarin shakkar zasu iya dawowa su dauketa ko kasheta tinda taga inda suke.

Raunika na fili da boye ne a jikinta da suke kokarin zama baraza ga rayuwarta duk da hakan tayi alkawarin tseratar da mijinta dan haka zamanta a cikin asalin GHAZ shine isharar datake ganin kaman Allah yayi mata Akan ta kubutar da mijinta sbd a farko tasan bazata taba iyawaba dan babu ta inda zata samu kusanci da ahalin GHAZ bare samun jininsu koda diqo daya ne sai gashi batareda tsammani ba Allah Kai tsaye ya shigar ita cikinsu.

GHAZ Ali ya shigo da itane cikinsu shi kuma sbd ya sakata tsaro sosai ta yanda ko akwai wani abin bazata samu damar yi ba ko fita gari.

********Da wannan dalilin Asamah ta zama cikin iyalin GHAZ tareda jinya me kyau ta warke sosai ta zama tamkar amintacciyar ahalin sbd lokaci daya ja sosai hakama kusrawa suna bangaren sun kafa garin kansu sbd burinsu Wanda suke jiran ranar cikarsa.

Lokaci ya tafi sosai kauna da shaquwa me tsafta ce a tsakanin dukkanin GHAZ da Asamah wadda kulawa da gabaki daya yaran gidan ta dawo hannunta duk da sun zama yan mata amma itace ke kulawa da komai nasu musamman Abaas Wanda yayi wata irin shaquwa da ita,

Duk tsawon shekarun datai a cikinsu burinta Akan kubuto da mijinta bai taba fita a ranta ba duk da lokuta da dama tana Jin kaman ta hakura da hakan sbd tsoron illar da kusra zasu iya shigowa gari suyi Wanda a yanzu cikin garin ANJOM iyalan GHAZ ne kadai take dasu sbd tausayinta daya zamo kauna me karfi a gareta.

A yanzu da shekaru suka ja kusra hakurinsu ya fara qare wa dan haka ahankali suka fara farautar duk Wanda zai fito daga garin dama hanyar makusanta hanyar dajin garin ta yanda gabaki daya nahiyar ta zama ta gagari kowane dan Adam bi a tahiri sbd duk Wanda ko hanya ta biyo dashi ta nahiyar ko gawarsa baa samu dan haka duniya da dukkanin nahiyar tarihi bin nahiyar ya zama tamkar tarihi sbd gabaki daya zagaye suke da dajin ANJOM Wanda ya koma babu shiga dajin babu fita dan haka rayuwar ANJOM ta fara shiga wani irin halin tsanani da rashin kwanciyan hankali da fargaban ko Yaushe komai ze iya faruwa garesu.

Tin masifar na waje dajin nasu harta fara shigowa sbd kisan yayi yawan da a bakin gari suke samun gawarwakin mutanensu.

Wannan tashin hankalin ne ya saka GHAZ fara tinanin iyalinsa da bazai iya barin wannan masifar dake kokarin afkowa ANJOM ta shafesu dan haka yasa aka fara Ramin fita garin ANJOM ta baya ta inda yake saka ran babu kusrawan zuwa ruwan dazai iya kaika nahiyoyi da dama dan tsira.


************
Zaune suke a wata irin lafiyayyan rumfar hutawarsu kowannensu na Zaune gurin cike da yayan marmari masu kyau sai qatuwar kwaryar dabino da shima yake da daukan ido.

Ayanah ce kadai bata gurin sbd shirinta dayake daukan lokaci dan haka tana fito wa tareda baiwarta daya Sakeena dake biye da ita.

Rumfar ta tinkaro a natse cikin takun dayake bayyanarda tsananin nutsuwarta da mulki yake ciki,

Qarar sarkar hannunta data kafarta me fidda dan sautin daukan hankali ce ta saka Asamah dake sake jere Kayan marmari fara dagowa ahankali ta sauke idanwanta Akan hanyar tana zubawa halittar Ayanah dake daukan idanuwa duk Wanda zai kalleta ido Tana ambatar Masha Allah Masha Allah cikin zuciyar.

Abaas ne ya juya ahankali shima yana kallan Ayanah din yana zubawa kyakkyawan fuskanta ido yana Godiyan Allah ako Yaushe da Ayanah ta kasance jininsa wadda yakejin kaman jinin da suka hada bai ishesa ba yana tsananin son ace ya sake hada wani abu da ita Wanda zaisa ace yafi duka Sauran yan uwansu kusanci da hada jini ita.

Ganin idanuwansa akanta kaman koyaushe yana kallanta cike da kauna me tsanani ta jini bude bakinta tayi wani kyakkawan murmushi ya mamaye fuskanta har saida hakoranta suka dan bayyana ta qaraso gurin tana miqa masa hannunta dayake sanye da fararen azurfa masu kyau da rashin sirki.

Kama hannunta Abaas din yayi cikin kulawa yana sake nasa murmushin me kyau daya qawata tasa fuskar dasuke tsananin Kama dan shi Kansa kyakkyawa ne da ake fadarsa a garin ANJOM Wanda lokuta da dama iyayensa ke tinanin bakin mutane ne ya saka ya kasance me rauni.
#MAMUH
#ANJOM GHAZ
#AYANAH GHAZ
#ABAAS GHAZ
#BOYEM
#BEST ROYALTY/BEST LOVE/BEST ROMANCE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

4
Zaunawa Ayanah tayi gefen dan uwanta tana kallansa Fuska cike da murmushi da sakewa tace

‘Godia nake GHAZ Abaas’

Dariya yayi yana sake hannunta yana cewa

‘Ayanaah….

Katsesa Zuhrah tayi batareda ta Bari ya fara fadar maganarsa da ako Yaushe take ta yanda yake Jin bazai iya rayuwa ba Ayanah bane wadda koyaushe damuwansa wani lokacin ta yanda zatai sure wata ran ta tafi tabarsu.

Dariya dukkaninsu sukai ganin yanda ya juya ya harari zuhrah cikeda kauna itama sbd yanda ta katsesa da cewan sun gaji da maganarsa daya kullum.

Fararen idanuwan Ayanah ta juyo ta sauke Akan fuskan mahaifiyarsu dake Zaune Nurat na kwance jikinta ta bude baki tace

‘Amma Barka da hutawa,kin tashi Lfy?’

Hannu Amman ta miqa ta Shafa fuskan Ayanah din tana Jin tsananin son yarta tace

‘Barka Ayanah ghaz,kin tashi Lfy kema’

Murmushi tayi tana dan Dora tafin hannunta Akan hannun Amman dake kan Fuskanta tana Jin kaman ta hadiye tace

‘Lafiya kalau Amma’

Juya wa tayi tana kallan zuhrah tace

‘Ki Dena damar mun da GHAZ Abaas sbd baya buqatan gorinki tareda dashi zan tafi duk inda zani kokuma na zabi zama a cikin ahalina har karshen rayuwata’

Nurat Baro jikin Amma tayi ta dawo gefen Ayanah ta lafe jikinta tana Jin kaman ma hakan ya kasance a rayuwar su kada suyi aure su rabu su tabbata a tare har abada
Bude baki tayi tana kallan Ayanah data kalleta cikin sanyi tace

‘Ayanah inason na tabbata tareda ku duka mu tsufa mu mutu tare banason ko aure ya rabamu,
Zan cewa Abaa(mahaifinsu) koda zamuyi aure abarmu da mazajenmu muyi rayuwa a cikin GHAZ batareda munje kowane gida aure ba’

Wani iri Ayanah taji a zuciyarta na Ina ma hakan zata kasance datafi kowa farin ciki sbd yan uwanta sune rayuwarta amma kuma kaman hakan bazai yiyu ba,

Numfashi ta sauke tareda Kai bakinta cikin kauna ta sumbaci tsakiyar kan Nurat din tana Shafa gefen fuskanta tace

‘Nurat babu abinda zai raba mu a duniyar nan Bayan mutuwa sbd kune rayuwata’

Amma datake Jin kaman kada ta taba aurar ‘yayan nata sbd ganin baza su iya kowace rayuwa batareda junansu ba wani irin sanyi jikinta yayi ta Kama hannun Ayanah takai bakinta ta sumbata tana kallanta tace

‘Kece rayuwansu suma musamman a lokacinda zaku samu Kanku ba iyaye idan tsufa ko mutuwa tazo dan haka Ayanah kici gaba da zama uwa kaman yanda kike kaman mahaifiyarsu a yanzu’

Qurawa Amman idanuwa Ayanah tai tana Jin zuciyarta na sake cika da tsananin kaunar mahaifiyata,

Gyada Kai tayi tana kwantawa jikin Amman batareda ta iya cewa komaiba.

Abaas ne dayake Jin a jikinsa shikam da Ayanah baza su taba rabewa ba koda basa a raye sai yana Jin kaman baza su rabu ba dan kuwa tsananin so da kaunar dayake wa Ayanah da aure ya Halasta a tsakanin yan uwa to da bazai taba barin kowa ya dauke masa Yar uwa ba zata zauna a karkashinsa koda ba aure zai killaceta ya Hana kowa koda ganinta sbd kada kowane ido yayi mata illa,

Duk da ba aure tsakaninsu yanada Alkawari da fatar duka yayan dazai haifa a rayuwarsa su hada jini Ayanarsa,
idan kuma mace Allah zai basa to adduarsa koyaushe a cikin ibadarsa shine ta kasance tamkar Ayanarsa koda hakan shine burinsa na karshe yana fatar Allah ya cika masa shi koda a ranar mutuwarsa ce.

Asamah da dukkanin jikinta yayi tsananin sanyi da kaunar ahalin GHAZ din da baka gane wane yafi wani kaunar dan uwansa Jin takeyi Inama nata ahalin sunanan da yayanta zasu yi girman su zuhrah da Abaas sbd itama ‘yaya mata biyu ne da ita sai namiji daya kaman Abaas,

Hawayene masu tsananin zafi da radadi suka ciko idanuwanta ‘dacin rashinsu na taso mata Wanda daman a tsawon shekarun nan bata taba manta radadin ba koda na qanqanin lokaci ba,

Hadiye hawayenta tayi sbd kada su bayyana a gabansu.

Juya wa tayi Bayan ta gama jere komai ta kalli kakkaifar qaramar wuqar dake kan Kayan da zata bar gurin dasu ta yanka Kayan marmarin taga yanda take daukan ido,

Zuciyarta ce tahau Kai kawo cikin tsananin qunci da baqin cikin daya taso mata na rashin yayanta da tsananin buqatar son dawowan mijinta gareta Wanda zuwa yanzu tasan azaba ta dade da sauyasa zuwa wata mummunan halittar amma tanason abinda a hakan.

Shedan da zuciyarta dake rufewa idan abin ya taso mata Wanda yake tamkar tabin kwakwalwa batareda sanin kowaba suka saka zuciyarta rufewa tafara taku daya na biyun ta saki gabaki daya Kayan hannunta a jikin Abaas Wanda wuqar ta yanki gefen qafarsa take jini ya fara fito wa Wanda ya saka dukkaninsu miqewa cikin tsananin tashin hankali da damuwa

Asamah ma cikin tashin hankalin da tsoro me tsanani ta zube gabansa tareda rigan kowa saka hannunta a kafarsa tana wani irin rawar jiki da kukan dayake fito wa daga qasan ranta tana basa hakuri cikin kulawa sbd a qasan ranta tasan kofar wata rayuwar ce zata bude wa duk Wanda yake garin ANJOM wadda bata San wace iri bace dan kuwa a gefen rigar jikinta ta goga jinin me yawa daga qafar Abaas batareda lurar kowa ba.

Cikin sauri sakon fitar jini a jikin GHAZ Abaas ya isarwa Abaa dinsu wanda ba bata lokaci ya iso gurin Wanda ya saka duk Sauran bayin dake zagaye da gurin na kowannensu dake rumfar ja baya sosai cikin girmamawa.

Wuqar da jininsa ya taba ya fara bada umarnin a karba hakama take aka kawo ruwa masu yawa a babbar tasa me kyau aka saka Asamah wanke duka hannuwanta da jinin Abaas ya taba kafin take GHAZ Ali din da Kansa yasa aka kawo magani ya karba yana kallan Abaas din Wanda hankalinsa yake son tashi sbd fitar jininsu tamkar hadari ne ga dukkanin ANJOM gabaki daya sbd da jininsu ne kadai ake iya karya komai dake ANJOM dan haka Sam baa taba yadda da kowa ba game da duk wani digon jinin GHAZ.
Amma ganin Asamah ce ta raunanasa bada ganganba kuma tamkar ahali take sai hakan na hana zuciyarsa shiga tashin hankali da tsoro sosai.

Kukan da Asamah ke yi ya saka Ayanah rarrashinta tareda Zuhrah

Nurat da Amma kuwa suna jikin Abaas din cikeda damuwa suna kallan yanda GHAZ ya saka masa garin maganin da take jininsa ya tsaya ya Dena zuba.

Ajiyan zuciya GHAZ ya sauke yana dagowa ya kalli Abaas din cikeda kulawa da qara tabbatar masa da tsananin mahimmancin jinin dayake yawo a jikinsu.

Cikin nutsuwar mulkin dayake yawo jikinsa da kulawa tareda tabbatarda kiyayewa GHAZ ya bude baki yace

‘GHAZ Abaas ya koma dakinsa a tabbatarda an kiyaye danyen yankan kafarsa ta warke da kyau batareda ya sake fitowa ba’

Gyada Kai kowa yayi suna amsa wa da cewa

‘Angama’

Juya wa yayi ya bar gurin kowa yayi tsit cikeda damuwa da alhini har saida ya fice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login