Showing 96001 words to 99000 words out of 121560 words
ya fara,
Juya fuskarsa yayi a slow yana maida kallansa inda NUAB yake ya Dora idanunwansa da suke cikin rudani akansa ya kafesu akan bayansa dayake daukan ido sbd haske da lafiyar fatarsa idanuwansa suka sauka Akan tsakiyar bayansa da sunan ‘GHAZ’ yake rubuce cikin wani irin rubutu daya sakasa saurin dauke idanuwansa Akan rubutun yana miqewa kafafunsa na wata irin rawa ya Riga NUAB saurin isa tsakiyar fadar ya zube gaban sultan a hankali yana sunkuyar da Kai ya bude Baki zaiyi magana daidai nan NUAB ya iso gurin ya tsaya cak tareda dagowa ya zare shades din fuskarsa ya saukar da idanuwansa da suke zak na ubansa da suka sauya babu abinda yake bayyana a cikinsu Bayan zallar wutar bacin rai na shakaru ya sauke su Akan sultan Wanda idanuwansa suke kafe Akan NUAB din tin daga lokacinda ya sako kafarsa a fadar yana takowa a cikin takun dayake tabbatarda shi din jininsa ne tsatsonsa ne da a kowane hali bazai taba dana sanin haihuwansa ba da rayuwar da suke akai yanzu,
Cikin tsakiyar idanunwan NUAB din yake kalla cikeda Wani irin yanayin dayake tabbatarda alfaharinsa da samun cikar burinsa da NUAB ya rayu a duniyar datake cike da maqiyansa,
Ya rayu ya zama tsayayyen da zai iya tsayawa Ayanah ya bata kariya da rayuwarsa batareda shakkar kowa a duniya ba,
Babban burinsa ‘dansa jininsa ya tashi ya rayu a duniya batareda shakkar komaiba bare kowa ba Bayan Allah daya haliccesa,
A yanda ya tashi ba shakka ba tsoro ba fargaba ba kunya ba wasa babu abinda yake girgiza dan kuwa ko mutuwa baya tsoro koyaushe tazo zai amsa kiranta haka yake burin jininsa ya kasance gashi burinsa ya cika harya zarta sbd Zafin wutar dayake gani a idanuwan NUAB bayajin akwai abinda zai kashesu,
Ba qiyayyarsa yake gani a idanuwansa ba zafinsa da fushi me tsananin gaske yake hangowa Wanda yasan da hakan yana ganin hakan tin yana yaro dan haka bai damu ba tinda ya zama Zakin dayake fatar ya zama ko da wannan qiyayyar ta idanuwan NUAB din zai rayu tinda a cikin idanuwansa take baa zuciyarsa ba,hakama indai wannan fushin nasa da nisan dake tsakaninsu zaisa ya tsayu a cikin zarrarsa sa fushi ne yake da qarin karfin riqeta ya shirya rayuwa da hakan har sai ya tabbatarda yahau mulkin da shine zai gama bawa Ayanah cikakkiyar kariyar dayake mata yaqi hakama dashi kansa da ake fatan fizgewa daga tarihin BOYEM dan haka saiya tabbatarda wannan burin nasa Akan NUAB din ya cika kafin ya nemi kusanci da ‘dan nasa dayafi masa duniyarsa gabaki daya.
Cikin sautin daya saka fadar sake daukan tsit NUAB ya bude Baki muryansa ta shiga kunnuwan duk Wanda yake gurin kaman saukar Aradu yana juyowa yace
‘Waye yaga ya kamata a aika bayin Amminah kirana???
Rufe idanuwa sultan yayi a hankali Wani radadi na ratsa zuciyarsa na yanda ‘dansa ya zabi kasa masa magana a bainar mutanen fada da suma duk sukai tsit sbd kafe fadar da Yaransa sukai da ido ba ko kyaftawa kamar robot suna jiran Wanda zai motsa bada amsar shine su fasa kansa da bindigar dake hannuwansu ko Jeho masa wuqar da zata tsaga kansa biyu dan haka ganin sultan baice komai ba har lokacin kallan NUAB yake son dayake masa yaci karfin mulkinsa da matsayinsa dan haka sukai shiru babu Wanda ya dago tukuna dan kuwa duk karfin mulkin BOYEM aka fasa kan mutum da bindiga kafin masautar ta dauki mataki ko nuna ikonta da zafinta Akan hakan andai Riga Kai an kasheka a banza da wofi ihu ne kawai ze biyo Bayan hari gashi da alama kafiran samudawan thugs din dake tsaye basu San dokokin masarautarba tukuna dan haka ba wata bata lokaci zasu aikaka ba shiri.
ASIM ne ya motsa cikin tsananin mamaki da baqin ciki me girman gaske ya miqe shima ganin NUAB bai durqusaba ya kalli NUAB din ransa na tsananta tafasa da quna mai tsanani ya bude Baki zaiyi magana NUAB din ya sake bude Baki da mahaukaciyar muryan data saka ASIM din ja da baya cikin sauri
‘Waye ya nuna wannan rashin daar ga mahaifiyata????
Aleeyyy……….
Cikin karfin murya datake tattare da umarni da iko mai karfi Sultan ya Katsesa sbd hanasa abinda yake niyar yi koma menene yace
‘LEUL NUAB ALMAZZ ka nutsu kasan inda kake,
A gaban me BOYEM kake,
Nine me mulki a nan ba kaiba,
Nine me fada aji anan ba Kai ba
Nine Wanda ya isa ya kira kuma dole a amsa,
Sake kallan jikinsa sultan yayi cikeda bacin rai kafin yace
‘Nan fadar BOYEM ce ba gurin wankanka ba dan haka umarni ne ka koma Ka sake shiryawa fada zata sake nemanka amma Ka sani hakan da kayi na yanke maka fita Masarautar BOYEM bisa umarni me karfi sai Bayan wata daya zan buqaci ganinka’
Da mamaki me karfi da shakkar dake cikeda zukatan yan fadar kowa ya dago ya kalli sultan sbd zazzafan furuci suke jira daga garesa da hukunci me Zafin gaske amma suma tsananin shock da mamakin da suka kasa fitowa a cikinsa na ganin tantirancin karshe ganin idonsu ya saka suka bazasu iya cewa komai ba ko yin komai sai tinani da nutsuwansu ya dawo daidai jikinsu tukuna dan haka barin fadar a watse meeting din suke buqata yanzu suje su sako tinani,
NUAB kuwa juyowa yayi cikin nutsuwa da sabuwar tafasar datake cin ransa zai kalli sultan sai kuma ya fasa ya juya yana barin gurin sbd bayason jijjiga duniya da ikon sultan din a gaban mutanen da ikonsa yafi komai a duniyarsu.
Yana Juyawa gabaki daya bayi da securities din fadar suka sake zubewa qasa suna sauke kansu jikin bayi na tsima,
Su aleey ma Juyawa sukai suna bin bayansa sultan ya zubawa Bayan NUAB din idanuwansa yana kallan sunan GHAZ din dayake Baro Baro bayyane a tsakiyar bayansa daga sama.
Kaman yanda ya taho haka aka daga masa umbrella ta basa kariya daga Zafin rana hakama shades dinsa na rage masa hasken rana ne da zai keto a cikinta,
Har suka fice sukai nisa babu Wanda ya motsa saida suka bace wa fadar gabaki daya tukuna aka ringa sauke Numfashi me Zafi da bacin rai me tsanani musamman ASIM daya kasa motsawa daga kallan inda suka wuce din idanuwansa jajir da sbd tsananin ja da bacin rai da baqin cikin dayake ciki har wasu ruwa ruwa suka cike idanuwan fuskarsa tayi jajir hannuwansa na dan rawa ya saukesu yana juyowa ahankali ya fara bin palace officials din wato manyan fada da kallo daya bayan daya yana debe musu albarka a zuciyarsa tareda Jin zazzafar tsanarsu da baqin cikin ganinsu ma a gabansa sbd shiga rudin da sukai har suna kasa cewa komai a fadar da sun isa su yankewa ‘dan mistress kowane irin hukunci,
Wasu yawu masu daci na baqin ciki ya Hadiye yana dauke idanuwansa daga kansu ya dawo da kallansa kan sultan Wanda tin kafin ASIM din yayi magana yace ya tada zaman fadar na yau sai kuma wani lokacin.
Cikeda girmamawa da son barin fadar su shaqi iskan nutsuwa a waje kowa dake fadar suka zube qasa a hankali suna masa a huta lafiya.
Koda ASIM ya zube qasan shima zuciyarsa kaman zata fado yake jinta tsabar baqin cikin sultan da duk Wanda yake fadar dan haka har sultan ya bar fadar ta kofar da shi kadai yake bi ASIM bai dago ba,
Sultan na ficewa aka fara ficewa daya bayan daya daga fadar babu Wanda ya samu cewa dan uwansa komai har suka watse,
ASIM ne yayi na qarshen fitowa tareda babban yaronsa Salman Wanda shima zuciyarsa taje cikeda baqin cikin dayake kusan na ubangidansa haka suka bar fadar Kai tsaye suna nufar bangaren HAILE.
A kofar bangaren da babu me wucewa sai jinin BOYEM da bayinsu mata kadai,
Tinda ya tinkaro bayin dake bangaren suka ringa zubewa qasa kansu a qasa suna masa Barka da shigowa amma babu Wanda ya kalla zuciyarsa gap take da bugawa ya isa palon hutawar mahaifiyarsa inda ya tadda su a tsaye dukkaninsu Banda meryam dake Zaune itama tana dafe da goshinta
Aslam da HAILE kuwa a tsaye suke qyam kowannensu abinda ya faru a fadar yake son ji dan kuwa suna tsammanin jin zazzafan hukuncin da zai saka NUAB zuciya ya sake barin qasar gabaki daya.
Yana shigowa suka zuba masa ido dukkaninsu suna jiran jin bayani a bakinsa amma ganin yana yinsa ya saka jikin meryam da Aslam sanyi suka zauna batareda sun furta komaiba sedai HAILE ne tace
‘Meya faru?
Yaya akai a fadar?
Wane hukunci sultan ya zartar masa?
Zai bar qasar dai ko?
Zazzafan fushi me tsananin zafi ne ya taso masa ya saka hannuwansa biyu ya dauki table din dayake gurin cikeda Kayan marmari da Kayan ciye ciye ya daga sama ya buga qasa da karfi komai ya fashe da karfi tareda watsewa da kara me karfi.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
56
HAILE data ga hakan take zuciyarta ta tabbatar mata da basu samu abinda suke so ba kenan,
NUAB bai karba kowane hukunci ba daga sultan kenan,
Matsalarsu akwai yiyuwar zata fara ne daga yanzu matiqar NUAB yana nan,
Kallan ASIM da idanunwansa suka mugun jajir tayi tana bude Baki zatai magana ya Katseta da cewa
‘Ba dan taadda kadai bane mahaukaci ne,haukace da kanta take kwance a cikin jininsa bawai a cikin kansa bama,ya tabbatarda shine bastard son da sultan YASAR me BOYEM yakeda shi a Idon duniya’
Aslam da duka ba wannan take son ji ba dan bata jin kowace hauka ce akansa zai gagaresu su da suke su hudu ga kuma manyan fada a bayansu hakama ASIM ALMAZZ shi BOYEM ta sani a matsayin ‘dan sultan dayake tareda shi kawai ita hukuncin da akaiwa NUAB din takeson ji dan jin hukuncin ne zaisa su sani ko NUAB din zai tafi ne yanzu ko zaman qasar.
Meryam kuwa da tsananin quncinta da rufewan Idon son cikar burinta ta samu abinda takeso to ita koma waye se hau mulkin BOYEM yanzu indai zai janye musu hukuncin dake kansu babu abinda ya shafeta muradinta kawai tayi auren kada ta qare a haka ta mutu a hakan tsufa na cimmusu a ba aure bare ‘yaya.
HAILE kuwa guri ta nema ta zauna haka shima ASIM din zaunawa yayi yana zayyana musu abinda ya faru a fadar tas.
Shiru Aslam da meryam sukai kafin suka dago suka kalli juna meryam na shaqar Wani Numfashi me zafi sbd tabbas ita kam yanzu takai karshe bazata yadda a fara wannan sabon rikicin da zai zama babban al’amariba a lalata Sauran lokacin da suke tinanin suna dashi na samun abinda suke so dan kuwa komai rikice zeyi yaqin Neman mulkin ya dawo sabo duk suna nan suna jiran a gama me hawa ya hau ita kam yayi mata tsayin da tabbas ba lallai ta iya jira ba dan haka duk inda taga alamar nasara da gaggawa wlh can zata koma ba bata lokaci koda kuwa hakan na nufin tabar ‘dan uwanta uwa daya uba daya ta zabi bastard son din.
Aslam ma Zurfi tayi a tinanin da babu alkhairi ko daya a cikin ranta dan ita kam ko zata qara shekara nawa batajin zata taba kaunar ko Inuwar Wanda ma yake kaunar Ayanah da NUAB.
Shiru sukai dukkaninsu suna tinanin ta inda zasu fara wannan sabon yaqin da suke ganin kaman yana tinkaro su batareda sunyi tsammanin Wanda sukewa kallan baida banbanci da almajirin yan taaddan shine taaddancin ma da kansa,
Kuma idan har zai iya tsayuwa a gaban sultan me BOYEM da babu dan Adam din dayake BOYEM da zai ita tsayawa gaban idonsa ya kallesa bama bare tsayuwa ba kaya daga shi zai towel a gaban dukkanin manya fada da suma iya karshen rashin girmamawan rayuwa sun samesa a hakan da yayi musu to tayaya suke expecting akwai abinda zai girgiza sa,
Numfashi HAILE ta sake me Zafin gaske kafin ta dago ta kalli ASIM da idanuwanta da sukai jajir itama ta bude Baki tace
‘Ka saka salman yayi kwakwaran binciken qarshe Akan NUAB din ya binciko waye shi da wainda yake tare da huldodinsa da matsayin dayake tinanin yanada shi dan da alama akwai Wanda ya tsaya masa,
Hakama ta Dayan bangaren babban abinda zai kawo sassauci a wannan yaqin da zaayi dashi nasarar mu ta zarce tasa shine tabbatarda qiyayyarsa da sultan bame warware wa bace har abada hakama Ka tabbatarda an gano menene abinda yafi so da’
Shiru ASIM yayi baice komaiba sai idanuwansa jajir daya kafe Hailen dasu yana sauraronta dan kuwa ta hakan zai fara tabbas yana buqatan sanin komai Akan NUAB sbd abinda aka fara musu akansa ba shuke idanuwansu suka gane masu akansa ba.
******Sultan kuwa tinda ya bar fadar yake Zaune palon sa cikin nutsuwa Zaune yana jin tinanikansa da burikansa suna gauraraya da warware wa da saqawa sbd duka burinsa Akan NUAB ya zama tsayayyen Zakin BOYEM ne da zai riqe uwa da qasar da Amana amma hakan ya budewa alaqarsu sabuwar babbar alaqar nisanta da juna tareda zama Wanda fushinsa da zafinsa yayi yawan dabai tsammata dan haka ya basa umarnin tsayawa cikin masarautar ne batareda ya fita koina sbd ya samu lokaci isashe me tsayi da nutsuwa tareda mahaifiyarsa kafin ya basa umarnin dayake ransa na shekaru Akan amsar mulkin BOYEM cikin lumana dan kuwa ana fara wannan yaqin bazai samu irin wannan nutsuwan kulawa da mahaifiyarsa ba dan tako Ina fitina ce zata bude kofa musamman ga wainda suke jiran amsar mulkin da manyan fada dan shi koma menene NUAB din ya zama shi shine yake son ya zama mai mulkin BOYEM bayansa kota halin yaya ya shiryawa kowannensu a tsakanin shi NUAB din da bazai karba ta lalama ba da wainda zasu tada hankalin baa basu ba da manyan fada da duka zasu iya kasa Aminta da hakan a shirye yake da kowa.
******a bangaren LEUL kuwa koda suka koma saida ya sake sabon wanka ya shirya cikin ash Rb wears da suka zauna jikinsa a natse qamshinsa me sanyi na tashi ya fito palonsa inda aka kawo abincin rana daga bangaren Amminsa aka cika dining din a Jere babu kalan fruits din da babu Bayan lafiyayyan abinci Kala uku.
Zaunawa yayi a natse batareda damuwan komai a ransa ba duk da har lokacin zuciyarsa daukan dumi takeyi idan ya Tina rashin daar da aka nuna ta aiko bayin mahaifiyarsa kiransa,
Bai damu da hukuncin sultan akansa ba sbd bayajin akwai dalilin daya isa ya hanasa fita idan ya tashi fitar musamman da Ayau din ya basa umarnin aleey ya fara shirin tafiyarsu da Amminsa barin qasar gabaki daya Wanda da kansa a shirye yake da samun sultan ya fada masa da Amminsa zai tafi Kai tsaye idan shirye shiryen suka kammala kenan.
Tareda Yaransa gabaki daya suka ci abinci a dining din Wanda hakan ke qara musu kaunarsa da tsayuwa Akan kowane lamarin sa dan babu kyama ko nuna banbancin matsayi a tsakanin sa dasu,
Cikin kulawa da sakewa sukaci abincin aleey na sake koro masa bayanin manyan fada guda nawa ne a tarihin Masarautar hakama guda nawa ne suka Halarta taron yau din da dukkanin yanayinsu daya nuna a fuskarsa tareda sunayensu babu Wanda bai dauko komai akansa ba tsaf dan haka kwakwalwansa take tamkar computer.
Bayanin full binciken rayuwar ASIM daya hada da abinda ya qara karanta tattare da yanayi sa na yau din shima ya fara koro bayanin a tsare dalla dalla cikin ilimi da tabbaci tin daga kan karatunsa na primary har zuwa yanxu dayake da har masters da Sauran ilimin wasu abubuwan tas.
Dakatar dashi NUAB yayi daidai lokacin da zai zayyana bayanin su Aslam da mahaifiyarsu tas sbd baya buqatan sanin kowa da komai a masarautar tinda baida alaqa dasu bakuma zama zaiyiba bare rayuwa a cikinsu.
Sai yamma Bayan magrib ya sake komawa gurin Amminsa wadda take jiransa zuciyarta cikeda ‘doki dan haka tare suka ci abincin dare tana jin kaman zata maidasa ciki sbd tsananin kaina shi kuwa kowane motsinta kashe jikinsa yakeyi sbd yanayinta dake nuna she’s very weak hakama fatarta kaman tanayin pale.
Sai dare sosai Bayan ya tabbatarda tayi bacci kafin ya Baro bangaren ya koma nasa,
Wanka yayi ya saka Kayan baccin James plebe ya daure gashinsa tsakiyar kansa ya dauki wayar sa ya kunna ya Nemo numbern likitansa dayake Greece ya sanar masa da yana buqatan qwararrin likitan zuciya da kwakwalwa su shirya su hadu a qasa daya ko Greece din dazai kawo mahaifiyarsa a duba masa lafiyarta cikakkiya.
Washe gari haka ya dake tafiya gurin mahaifiyarsa ya wuni tareda ita yana bata lokacinsa da rayuwarsa gabaki daya ta wannan lokacin kafin sbd ganin hakan na taimakawa gurin samun kuzarinta.
Kaf masarautar haryanxu bame samun damar ganinsa dan kuwa duk lokacinda zai fito daga bangarensa zuwa na mahaifiyarsa watsewa kowa keyi sbd Yaransa dake tare hanyar sbd tsaro,
HAILE da ‘yayanta kuwa baqin cikin jiran wata Dayan ta cika ya hanasu kowane irin motsi tinda dole dik shirinsu su jira wata dayan tayi su ji me sultan zai yanke akansa,
Fada ma gabaki daya sun kasa sakewa sbd shakka da zullumin me wata Dayan zata haifar idan ta cika,
Duk tsawon wannan lokacin NUAB bai taba zuwa gurin sultan ba dan haka basu sake haduwa ba bakuma su da niyar haduwar kowa da abinda yake ransa Akan haduwar tasu sbd NUAB jiran komai ya kammala yakeyi ya samu sultan din ya tsaya a gabansa da kansa ba sako ba ya sanar masa zai tafi da mahaifiyarsa.
Shi kuwa sultan ranar yake jira sbd yana sane da dole bazaa rasa dalilin da zai saka NUAB zuwa garesa ba indai Ayanah tana raye dan haka ranar shima yake jira.
********koina masarautar ta fara daukan zafi sbd watan nan daya tafiya yakeyi amma kamar shekaru suke jinsa ganin baya gudu dan kuwa Kai tsaye su HAILE sun gama yankewa da tsayar da sabuwar shawara me karfi Akan NUAB na barin BOYEM zasu kawar da abinda ya rage masa kadai a BOYEM
Wanda zai sakasa dawowa koba yanzu ba wato uwarsa dan kuwa tana barin duniya sunsan bazai taba dawowa BOYEM ba,
Wannan sabon burin ya kafu ne a ransu sbd zuciyarsu kaf data rasa nutsuwarta sakamakon tarihin LEUL BOYEM tas da suka samu daga kwakwaran bincikensu Wanda ya gigita kwakwalwansu da sanin cewa su idan a boye zasu iya daukan ran mutane shi a tasa duniyar a bayyane