Showing 81001 words to 84000 words out of 121560 words

Chapter 28 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3767

tsayawa ga duk abinda yakeji,
Matan sultan suna Qinta,
Yayan sultan suna qinta,
Imebētis din sultan suna qinta,
Yayan imebētis din sultan suna qinta,
Manyan fadar masarautar BOYEM suna qinta,
Shi kansa sultan din yana qinta…..

Hakan daya taso yana gani ne a bayyane ne ya saka zuciyarsa fara bushewa daga dukkanin wata kauna datake duniyar gabaki dayanta,
Ciwo yakeji mai Zafin gaske,
Radadi yake ji mai azabar gaske,
Fushi yake ji mai wutar gaske,
Rashin kauna yakeji ga kowa mai karfin gaske duka sbd Shi itace rayuwa da duniyarsa gabaki dayanta,

Bai damu da rashin kauna da shaquwan dake tsakanin sa da ubansa da duka wani jininsa ba sbd baya buqatan kauna ko soyayyar kowa a duniyarsa iya ta Amminsa da babu wata rai me daraja a gurinsa Bayan tata sun ishesa,

Mutum biyu ne rak a duniyar Bayan mahaifiyarsa daya cirewa hular Zafi da tiririn da kansa yake fitarwa sune Wainda su kadai ya taso da sanin masu kauna da kulawan Amminsa da zasu iya bada ransu akanta wato MAA TENYA dinsa da MAA SAKINAH Wainda su kadai ya taso ya gani a rayuwarsu shi da uwarsa,

‘Dan mistress yan uwansa suke kiransa Wanda shi hakan bai taba sosai ransa ba sbd hakan na nuna cikakken identity dinsa kenan da uwarsa wadda akanta shi sunan mistress yafi masa darajar sunan sultan me mulkin qasar gabaki daya,

Tin da qananun shekaru zafi da hayaqi sa ya bayyana ga duniyar masarautar BOYEM dan hakanne ya saka yan uwansa mata fara shakkarsa dan tamkar mahaukacin Zakin da baida hankali ko daya yake ga duk Wanda ya shiga huruminsa da baya buqatar kowa a cikinsa Bayan Mutum ukun nan da sune kadai ya saka a duniyarsa,

Zafi da tiririnsa ya saka zuciyar sultan shiga damuwan abinda zai iya zama sbd babu tsoro ko daya bare shakka a rayuwarsa,
Bai taba risinawa kowa ba a masarautar kaf dinta sbd har abada bazai taba risinawa duk Wanda baya kaunar mahaifiyarsa ba koda hakan na nufin bakin ransa to zai bada ran da hannunsa.

Ta bangare daya Li’ul ASIM ya taso mai tsananin tsoro da rashin wayo da dubara ko kadan,
Baida jarumta,jarumta baida kwazo baida jajircewa hakama baida dubara da tinani ko kadan duk abinda uwarsa ta dorasa haka yake hawa ba lissafi dan hakanne suka taso duniya biyu mabanbanta shi da LEUL kwata kwata duniyarsu bama iri daya bace dan shi hatta matan uban nasa mamaki da shakkar Zafin kasan da rashin tsoron sa sukeyi tareda fargaban abinda zai iya zamowa idan ya qarasa girma.

Da wannan tsoron sultan ya tattara sa yakai sa qasar RUSSIA karatu tareda bada umarnin bazai taba dawowa ba saiya gama karatunsa gabaki daya ya zama cikakken mutum tukuna zai sako Kafa a masarautar.

Wannan hukuncin ya masa Zafi da ciwo amma kuma sbd mahaifiyarsa da saiya tabbatarda tabar hannun sultan ta dawo hannunsa gabaki daya har qarshen rayuwarta ya Aminta ya tafi dan kafa duniyarsa da bayason ko kadan ta hadu data masarautar daya tsana a zuciyarsa fiyeda komai.

A hannun tenya da sakinah a tafi yabar mahaifiyarsa data kasa barinsa ta qanqamesa saida aka banbareta daqyar tana kukan da fiyeda shekara nawa bataiba sai yanzu da aka rabata da danta dan haka Bayan tafiyar sa rayuwarta ta sake komawa inda ta fito.

Barin NUAB ALMAZ qasar BOYEM ya bawa HAILE cikakkiyar damar fara yaqin maida danta cikakken jarumin da babu tsoro ko daya a zuciyarsa sbd sultan ya dorawa a mulkin dayake shakkar Dora NUAB ayanzu sbd zafinsa dayayi mummunan yawa,

A Morocco qasar iyayenta aka tura ASIM karatu amma shi yana zuwa Hutu a duk lokacinda yaso sbd Sam taqi yadda dayayi nisan dazai hanasa samun kusanci me karfi da sultan Wanda yasan a yanzu ne yaqi da qalubalen matsayin magajin BOYEM zai fara irin Wanda zai kawo fitina daban daban a tsakanin magajin biyu da duniyarsu ta banbanta,

Babban abinda yake saka zuciyar sultan girgiza shuke irin rayuwar da NUAB zaiyi a kusan shekaru masu yawan gaske batareda mahaifiyarsa da itace duniyarsa ba wadda shi kansa ayanzu bayajin har abada duk yanda zai shareta zai iya rabuwa ko barin ta fita hannunsa dan da itace zai iya riqe NUAB a hannunsa.

A ranar da NUAB ALMAZZ BOYEM yabar qasar a daidai wannan ranar aka bugo daga daular YUNAR dake kuwai imebeti zuhrah ta haifar masa yan biyu namiji da mace Wanda tukuicin haihuwan biyun a lokaci daya ya saka ya yantata tareda aurenta ya maidata cikakkiyar matarsa.

Koda labarin ya isowa su sakinah sujjada sukai cikeda tsanani farin cikin daya jima shekaru da barin rayuwarsu sbd Ayanah,

Kallan Ayanah sukai dake Zaune zuru suka fara fada mata amma bata ce komai batai reacting ko wane iri ba saima binsu takeyi da ido batareda ta tina matsayin Zuhrah akanta ba sedai suka gaji jiki a sanyaye suka kyaleta tinda dai ba haukacewa tayi ba memory kawai tayi loosing da walwala sai suke Jin sassauci a zuciyarsu hakama Bayan tafiyar NUAB babu ranar da baya video call da dukkaninsu yana magana da mahaifiyarsa da shi ne Wanda yake saka aji sautin muryanta Wanda a haka shekarun suka shude tamkar a mafarki.
#MAMUH
#THE BEGINNING
#THE GREAT LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

47
Masarautar BOYEM mai cikeda tarihi daya gabata na can baya qarni qarni da tarihin daya gabata a shekarun da basu Kai qarni qarni ba haryanzu tana cikin wadataccen arzikinta da daular datake sake ninkuwa ako Yaushe sbd arzikin da Allah yayi musu Wanda baya qasa koyaushe sedai gaba,

Shekarun da suka shude anyi su ne a cikin tinani da wasi wasin waye zai zama magaji a cikin jini biyu da sultan YASAR me mulki haryanzu daya haifa?

Akwai ‘dan asalin matarsa uwargidansa wato queen haile wadda take zuba taqama da ikon da kaf masarautar ake shakkarta Bayan sultan idan aka cire manyan fada wainda sune fada,
Itace macen datafi kowace mace daraja haryanxu a masarautar da wajen masarautar sbd tini aka shafe tarihin fada da tsantsar soyayyar da sultan yakewa wishmah dinsa wadda tarihinta yayi bacci gabaki daya bata cikin kowane lissafi,

Queen Haile ta karbi kowane irin iko,taqama da isar tsayawa ta tsayar da ‘danta ASIM ga zama cikakken mai jiran gado na karagar mulkin BOYEM kuma hakan ta Zaune dan kuwa masarautar da duniya gabaki daya sun gama shedar da hakan sun gama yadda da sanin ASIM ALMAZ ne Sarkin dazai mulki BOYEM Bayan sultan YASAR sbd shine a tareda mahaifinsa da qasar sa yanzu.

Rayuwa ta dawowa Masarautar BOYEM sabuwa dal da Kama hanyar cikar Buri sbd kowa abinda yake tsananin so ne yake ganin yana Kama hanyar samu musamman queen haile wadda komai datake tsananin so shine ta samu hawan ASIM ALMAZ kujeran BOYEM ne kadai ya rage mata Wanda shima a yanzu yanda take ganin kusancin ASIM din da sultan tasan bama zai taba Hana masa ba sbd ya manta cewan yanada wani magajin kwata kwata tinda bai taba yiwa kowa maganarsa ba tinda yabar masarautar da suke ganin kaman ma korarsa yayi amma aka boye cewan karatu ya tafi dan haka haile ta gama samun dukkanin abinda take so itada danta ASIM Wanda yake zuba nasa iko da mulkin a cikin masarautar sbd ganin shine sultan na gaba kuma hakan ne ya saka gabaki daya BOYEM shakkarsa akeyi da basa tsananin girma duk da babu tausayin Jamaa ko daya a ransa amma mahaifiyarsa ta koya masa boye hakan sbd sake samun damar haye matsayin da suke tsananin buri kuma a shirye suke tsaf da iya kashe kowace rai da zata shiga tsakaninsu da abinda suke so dan haka kowa yasha jinin jikinsa akansu,

MARAKI ma a yanzu ta rasa dukkanin power datake ita sbd haile ce me yaya take zuba iko da mulkin cikin gida,
Hakama imebētis kaf da yayansu da duk wani me matsayi a cikin gida tsananin tsoronta ya ninka a ransu sbd a yanzu itace uwa ga sultan na gaba dan haka babu me iya ko dago Kai ya kalleta komai na mulkin Masarautar ma ya qara tsanani da wasu irin dokar da bayi basuda shaqat ko kadan.

MARAKI duk da daman can kishin tsagwaron soyayyar data hango sultan yana yiwa wishmah da ‘danta ne suka sakota gaba ta sakawa zuciyarta zazzafar kiyayyar Ayanah da NUAB sbd bata taba kishin haile ba dan bata taba ganin soyayyarta data ‘yayanta a idanuwan sultan YASAR ALMAZZ kaman yanda taga wutar son Ayanah da danta naci a idanuwa da ruhinsa ba dan hakan a yanzu data shedar da sunyi tazarar da babu Sauran soyayya a tsakaninsu hankalinta ya dan kwanta ta tattara komai ta ajiye ta koma rayuwarta ta Hutu da kwanciyan hankali bata shiga matsalar da duk ba tata ba dan kuwa ko taya HAILE kishin nema wa danta mulki batajin zata iya sbd sanin ba lallai komai Yazo a sauki ba dan tayi imanin da idan ma sunyi nasarar cire Ayanah a idanuwan sultan to ba lallai sun cireta a zuciyarsa ba bare LEUL NUAB dayake jinin AYANAH GHAZ bazai taba fita a zuciyarsa ba dan haka ta cire kanta a wannan fadan iya abinda ta samu ya isheta ita a yanzu dan haka rayuwa sabuwa ta bude itama ta kwanciyan hankali da nutsuwa,

Imebētis din sultan kuwa da damansu ahankali ahankali sun rasa rayukansu a hannun uwar dakin tasu wadda a yanzu Bayan ita bata buqatan kowace mace a rayuwar sultan Wanda ya rufe shafin karban kowace imebētin a rayuwarsa tinda ya samu Ayanah ghaz kofar shaawansa ga kowace mace ta rufe kwata kwata matansa ne kadai suma haqqin su ne kadai yake saukewa gashi rayuwar ma tayi tsayi yanzu tsufa da manyanci ya taho musu,

A yanzu imebētinsa daya ce rak a raye itama ta jima da komawa tamkar baiwa ga haile ta zama kunnuwanta na dauko mata labarai da sirrin duk inda Hailen bata saniba dan hakanne take raye kamar fanko dan kuwa shi kansa sultan din tintini ya mance da ita baama maganarta a haka zata gama garari a masarautar ta tsufa ta mace,

MARAKI batada kowane irin amfani itama a gurin sultan Bayan na biyan buqatan sauke hakkin aure a ganin HAILE kenan Shiyasa bata damu da ita ba ta tattara ta watsar tinda batada ko ‘dan kanta a duniya kuma tanada daman daukan ‘ya daya ko biyu ma daga cikin yayan imebētis din sultan ta riqe tamkar ta haihu amma Sam batada raayin hakan tin acan baya da akwai Sauran yarinta bare yanzu da duka sun manyanta hakama yaran da yawansu gabaki daya an aurar dasu Masarautu manya masu daula da iko daban daban gabaki daya a yayan sultan din manyan yayansa ne kadai basuyi aure ba wato yayan Haile su biyu Aslm da meryam ta ukunsu neesat tayi aurenta sbd rayuwarta akwai sauki sabanin ta yan uwanta,

Rashin aurensu nada nasaba ne da rashin shaawan auren da basu da shi sbd raayin hakan da mahaifiyarsu ta cusa musu sbd batason su taba aure Masarautar da batai ko kusan matsayin ta mahaifinsu ba,

Duk masarautun da ake aurar da yayan masarautar BOYEM basuyi ikon Masarautar boyem dinba sbd ta boyem din itace wadda babu kamarta dan hakanne dole sai wadda bata kaitaba amma suma Masarautun baa baya sukeba ko kadan ga tarin arziki da dukiyar da bata Jin kashewa tareda iko da mulki me karfi ta qasashe daban daban amma duk da hakan HAILE ta kasa barin yayanta su zaba ko daya daga cikin duk masauratun da ake kawo musu tayin aure gashi a al’adar BOYEM sukuma mazan ne kadai basada ikon auren macen daba jinin ahalin ba amma matan Ana aurar dasu wani gurin kuma Sam baa taba yiwa macen datake jinin BOYEM auren tilas saida cikakken raayinta sbd zataje ne qasar daba tata ba idan akai mata tilas zata rasa ahalinta kuma taje tayi qunci dan haka basa tilas tin farko ga matan boyem,

Wannan dalilin ne ya saka yayan nata suke Zaune masarautar mahaifinsu haryanzu hakama a tsaye suke qyam Akan tabbatarda karban mulkin dan uwansu Wanda tsufa ya kamasu a gida batareda sun ankare ba takai sultan ya rufe kofar Neman aurensu kwata kwata hukuncin su sai ranar da aka nada sabon sultan a Masarautar BOYEM shine zai bude musu kofar Neman aurensu daya rufe,

Hukuncin ya rikitar da rayuwarsu kwata kwata ta juye ta zama baqin cikin da babu Sauran hasken sauki a cikinsu sai zallar rashin imanin yadda da hakura daga abinda suke so dan kuwa indai wannan hukuncin dake kansu zasu jira to ko zasu kashe rai nawa suma saisun tabbatarda ASIM ne ya zama sultan dan kuwa idan ba shidinba ya hau babu me dauke wannan hukuncin zasu tsufa su mutu ne ba aure dan haka babban burinsu na rayuwa Akan tasu dalilin na tsananin son aure ya karfafa kudirinsu Akan hawan ASIM boyem dan yanzu wannan ne ma babban dalilinsu na jajircewa,

Ita kanta queen HAILE wannan shine dalili na biyu me karfi daya sakata tsayuwa Akan qudiri daya na tabbatar da ASIM ya karbi mulkin boyem sbd ganin yayanta zasu suna shirin tsufa su mutu babu aure ga qanwarsu neesat dake aure Masarautar Malaysia yayanta hudu babban ‘danta ma yana kokarin shiga university amma su Sauran suna gida manyanci yana sako musu Kai dan kuwa shekaru ashirin ake magana yanzu ko Bayan Barin NUAB ALMAZZ kasar idan aka hada da shekarunsu na baya ma suna hararar shekarun da suke Neman na wuce aure ma.

*******wishmah Ayanah tinda ‘danta hasken idaniyarta da zuciyarta ya tafi bata taba sake walwala ba a tsayin shekarun nan,
Bata taba manta tsananin soyayya da kaunar datake masa ba kona daqiqa daya,
Bata taba manta kamanninsa ba,
Bata taba dena kewa da tsananin son ganinsa ba duk da babu ranar da baya wuni kiransu akai akai yana video call da itaba sbd tsananin kauna da soyayyar dayake mata wadda ta zarta rayuwarsa da babu komai a ciki sai emptiness da Wani irin Zafin jinin sarauta dayake yawo a jininsa fiyeda mahaifinsa,

Wishmah a hankali taci gaba da manta komai da kowa harta gama mance komai a rayuwarta bata tina komai da kowa Bayan mutane biyar da sune rayuwarta,sune ji da ganinta a yanzu datake tamkar sabuwar haihuwa,
Qunci da baqin cikinta sun wanke babusu a zuciyarta sbd Manta komai datai dan haka rayuwarta take simple fayau ba damuwa da tashin hankali Bayan damuwan rashin HAYATEEM dinta da baya tareda ita Wanda shima hakanan koyaushe take rasa dalilin daya saka bakinta yake furta masa kada ya dawo qasar BOYEM Wanda shi kansa NUAB din wannan furucin nata ne ya hanasa dawowa qasar wadda har abada ya fitar da ita cikin ransa baida niyar dawowa rayuwa a cikinta.

Mutane biyar da su kadai ne a zuciya da kwakwalwan wishmah sune,
Shi kansa HAYATEEM din nata sai Mahaifinsa sultan data kasa cirewa a cikin kanta Wanda duk tsawon shekarun nan babu ranar da shima baya video call da ita kowace asuba sedai bata cewa komai haka zai kira ya zuba mata idanuwansa yana kallanta tana masa shiru batareda cewa komaiba itama tana kallansa harta gaji ta kife wayar tayi kwanciyarta tenya tazo ta dauki wayar ta fice da ita Wanda hakan wani sirri ne da babu Wanda ya sani a duniya daga sultan din se tenya wadda itama ta rasa dalilin sa na hakan a kowace asubar bayan kuma ya Riga ya nunawa duniya wishmah da ‘danta basa gabansa.
#MAMUH
#LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM
#BOYEM LEUL
#ALMAZZ NUAB

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

48
Bayan NUAB da sultan YASAR dake zuciyar Ayanah ABAAS ne Wanda bakinta bai taba qasa da kasa fada ba hakama zuciyarta bata taba mantawa da tsananin sonsa da kaunarsa ba hakama bakinta bai taba gazawa da fadawa NUAB yayi mata alkawarin kawo mata Abaas kada ta mutu bata gansa ba ta sake rungumar sa a jikin taba Wanda ba ita kadaiba zuwa yanzu babban kudurinsa na rayuwa ya zama na bawa mahaifiyarsa abinda takeso,

Sauran mutum da sukafi kowa zamowa rayuwarta ta yau da kullum Bayan ‘danta da Abaas sune sakinah da tenya da suka sadaukar da rayuwarsu tin daga Sauran yarinta da suke da ita har zuwa yanzu da manyanci ya Kama su dukan sun tsaya da lafiyarsu da lokacinsu da rayuwarsu sun bata kariya da kulawa kuma sun shirya hakan har qarshen rayuwarsu data rage musu dan haka itama duk da a yanayi na rashin memory da rashin nutsuwa da lafiyar tinani sune wainda ta sani kadai a rayuwarta datake jinsu har jini da ruhinta da suka zame jininta koda basu hada jinin ba a yanzu sune asalin jininta datake kalla dan a lokuta da dama idan dan tinaninta da ya hau daidai takan zauna ta qura musu ido ta ringa kiransu da Zuhrah da Nurat tana hawaye tana rintse ido sbd ciwo da radadin na taso mata a kirji da baa son kwata kwata taba tinawa da wannan kuncin sbd lafiyarta da kome zai iya faruwa idan wannan quncin da baqin cikin ya dawo mata cikin kwakwalwa dan hakanne kwata kwata Bayan kokarin kulawa da sake mantar da ita komai babu abinda su tenya ke kokarin yi,

Baa iya zuciyar wishmah sukeda matsayi me girma ba a zuciyar NUAB ALMAZZ su din taurari biyu ne da bazai taba iya biya ba har qarshen rayuwarsa,
Su din haske ne a rayuwarsa da suka bawa halittar datafi komai na duniyarsa daraja kulawa da tattalin datake buqata a lokacin da bata kowa a duniya Bayan shi kadai kuma aka rabasa da ita,

Sun kular masa da ita tin baizo duniya ba harma Yazo duniyar ya zama abinda ya zama yanzu Amma haryanxu sune suke tsaye akanta Bayan Wanda take full responsibility yayi watsi da rayuwarta batada amfanin komai a rayuwarsa baya buqatanta bayin matarsa ma sunfita daraja.

Bayan zallar kauna mai girma da darajar su dayake gani matsayin iyaye mata da tamkar sune suka haifesa yake basu dan hakanne kowacensu takejin sa Aranta tamkar itace ta haifesa musamman sakinah da bata taba sanin menene namiji ma bare haihuwa dan haka take Jin LEUL NUAB tamkar dan data haifa da cikinta hakama tenya dake da yaya biyu mata da tini sukai aure basa masarautar jinsa tamkar ‘da namiji da Allah bai bata ba,

Da wannan rayuwar bangaren wishmah AYANAH samun nutsuwa da kwanciyan hankali a tsakaninsu da bayinsu gida bakwai dake hidimar bangaren komai nasu a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login