Showing 90001 words to 93000 words out of 121560 words
da suke Wani irin daukan Idon da shedar da ko waye a cikinsu zaman kansa yakeyi bana kowa ba,
Map location Kai tsaye sukai amfani dashi batareda an damar dashi da maganar komai suka doshi masarautar BOYEM a lokacin har anyi sallar asuba da sukai tin an airport dan haka gari ya fara haske sosai.
Tin daga nesa securities din gate na farko suka hango motocin a tafe suna daukan ido Kai da Kai kamar kumurcin maciji haka sukaga motocin na doso wa cikin wani irin rashin sauti a Jere da juna babu wani space dama ko mashin zai iya bi a tsakaninsu.
Suna gap da isowa motar farko ta qaro Wani irin gudu tayo gaba dan isar da sakon a bude gate kafin isowan Sauran motocin da baa buqatan tsayar wa dan basuda lokacin batawa a nan Hutu maigidansu ke buqata kawai.
Yanda motar ta doso da gudun ne ya saka securities miqewa suka jeru a kofa tareda daga mahaukatan bindigoginsu suna seta motar.
Tin kafin motar ta iso aka sauke glass tareda daga fiddo wata turar datake dauke da sunan LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM Baro Baro a jiki da saka hannun sultan YASAR Wanda itace shedar tabbatar dawowan magaji tin ranar da aka tafi dashi aka basa ita,
Ware idanuwa dakyau tarin securities din sukai tareda kafe idanuwansu Akan turar dake buqata iskan a sama da sunan NUAB Baro Baro take sukai qasa da bindigoginsu suna ja baya da cikin wata irin girmammiyar mamaki da kidimaa,
Cikin gaggawar da bata fi minti daya ba aka fara ware mahaukacin gate din suna bada hanya a Jere dan bayyanarda mafi girman girmamawansu ga me BOYEM daya dawo.
Haka motocin suka iso da gudu suna wucewa ciki kamar walkiya batareda tsayawaba
Kafin isarsu gate na biyu tini sako ya isa daga gate din farko ta wayar tsaro dan haka a gate na biyu yana isowa aka wangalesa tareda buga sautin qarar daya tashi masaurata ya isa kowane lungu da sako na isar da sakon dawowan LEUL NUAAB ALMAZZ BOYEM.
a daidai wannan lokacin HAILE na bacci cikin Nisan baccinta kunnuwanta suka jiyo mata sautin daya sakata bude idanuwanta a lokaci daya batareda ta motsa ba,
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
52
Cikin kunnuwan HAILE sautin qarar ke sake ratsawa tana shiga kunnuwanta zuwa qwaqwalwarta datake kokarin warware wa tinaninta menene yake faruwa,
Har lokacin bata motsaba daga kwancen datake idanuwan nata ne a bude tana kallan sama,
Duk inda kaji wannan sautinqarar ya tashi a masarautar ya karade ta to sanarwa ce ta ME BOYEN ya dawo maana sultan idan yayi tafiya kokuma ya fita masarautar to wannan sautin shine yake sanar da duk Wanda yake masarautar ya dawo yana cikinta,
Tsayawa cak idanuwanta sukai daga motsawan da sukeyi tana tashi Zaune cikin wani irin slow da kasa gasgata abinda kunnuwanta ke jiyo mata,
Sultan yana masarautar bai tafi koina,
Idan sultan na cikin Masarautar BOYEM wannan sautin yake tashi waye ya shigo masarautar da sautin dawowan jinin BOYEM yake tashi yana wargaza baccin dukkanin mai rai dayake masarautar ba bayi ba bamasu mulkinba……
Zuro kafafunta qasa tayi zata miqe tsaye Aslam da bata gani sosai sbd mummunan tashin hankalin data shiga da sanarwar da itamaa a cikin baccinta taji saukar sautin ta miqe tsaye zuciyarta na harbawa da Wani irin karfin gaske dan kuwa a yanzu kaf duniya idan ba sultan ba baa buga wannan qarar sai kuma Wanda yakeda matsayi da ikon mulkin BOYEM dan haka a duniya kaf yanzu ASIM ne kadai zaayi wa wannan karar sai kuma ‘dan da har abada bazai taba dawowa BOYEM ba,
To idan sultan da ASIM duka suna cikin masarautar waye zaa bugawa wannan sautin idan ba Wanda baya nan ba kenan shi dinne ‘dan mistress din BOYEM ya dawo Bayan shekaru masu yawa.
Jin Aslam tayi tana Neman rasa ganinta sbd shock da mamaki mai girma dan kuwa kwana da wuni sukeyi tareda kowace daqiqa ta rayuwarsu suna rokon Allah ya hanasa dawowa Masarautar da rayuwar sultan har abada dan haka ayanzu datake kasa yadda da shi dinne ya dawo doguwar Rigar sarauta me fadi da tsayi tareda adonta janyo ta Dora Akan Kayan baccin dake jikinta ta nufi kofa ta fice zuwa bangaren mahaifiyarta da a lokacin take tsaye tanason daga kafafunta zuwa toilet amma komai nata yayi nauyi takeji hakama kwata kwata kanta ya kasa dauka ko kawo tinanin LEUL BOYEM zai taba dawowa Masarautar BOYEM din sbd an tabbatar mata da babu alkhairi ko kadan a dawowansa gareta da zuriarta dan haka bata taba yin qasa a gurin aikin da har abada bazai taba dawowaba amma alamu sunata nuna hakan bazai samu ba dan haka aiki akeyi tuquru Akan mahaifiyarsa bazata taba shaawan dawowansa ba zataita hanasa dawowa duk kuwa yanda take Jin tsananin so da kewansa bazata iya bude Baki tace ya dawo ba dan haka wannan ya saka hankalin HAILE kwanciya koma dai menene su samu ASIM ALMAZZ ya hau mulkin BOYEM idan ya hau ko yaushe NUAB ya dawo din sun sai riga sun samu abinda suke so buri ya cika.
Aslam na isowa Kai tsaye bedroom din mahaifiyarta ta nufo jakadiya dake palon karshe na hutawan HAILE tana bawa masu gyaran palon umarnin tsarin da zaa sauya cikin girmamawa ta kalli Aslam din zata gaidata amma ko ganinta Aslam bataiba ta wuce ciki Kai tsaye daidai lokacin da HAILE ta isa kofar toilet din mai girma da tsari zata shiga,
Shigowan Aslam ya saka Hailen dakata wa cikeda mamaki mai dan girma idanuwanta Akan Aslman din sbd ganin lokacin da Aslam din ta taho
Bude Baki tayi zatai magana Aslam ta rigata da cewa
‘Ya dawo,
Shine ya dawo Bayan shekaru Mamee,
Ya dawo Masarautar BOYEM,
‘Dan mistress din Sultan ya dawo Mamee,
Ya dawo a daidai lokacinda muke kokarin ganin mun cimma burinmu kota yaya,
Mamee tayaya zaki kawar da sultan daga duniya ASIM ya hau mulki a yanzu wannan yana masarautar?
Tayaya zamuyi aure yanzu?
Tayaya komai zai tafi yanda mukeso a yanzu da wannan din ya dawo?
Tayaya sultan zai bar duni……..
Wani lafiyayyan mari HAILE ta sauke mata cikin kidima da rikicewa zuciyarta na wata irin rawa sbd gabaki daya Aslam wata irin mahaukaciyar zuciya ne da tinani da ita, matiqar zata shiga tsananin baqin ciki da bacin rai haka zata ringa tona asirin zuciyarta cikin tsananin baqin ciki da Zafin zuciya dayake fiddata hayyacinta dan hakanne ya saka haile bata barinta magana koina sbd zata iya aikata kuskuren da zaiyi karshen rayuwarsu gurin magana idan takai maqurar bacin rai,
Marin da HAILE tayi mata ita kanta hayyacinta barin jikinta yakeyi da abinda Aslam din ta fada dan kuwa bazai taba yiyiwa ace NUAB ALMAZZ ya dawo Masarautar BOYEM din ba dan haka tafi yadda da sultan ne ya fita kila ya dawo batareda saninsu ba dan haka Kai tsaye toilet ta fada kafafunta na dan rawa hakama zuciyarta na tsalle.
Alwalar sallar asuba zatai amma gabaki daya ta rikice hannuwanta rawa sukeyi bata Kama ruwa ba alwala tayi ta fito har lokacin kafafunta rawa sukeyi zuciyarta data kasa yadda da abinda Aslam ta fada amma sai bugawa takeyi sosai tana Jin batada Sauran nutsuwa idan zuwa tayi ta tabbatarda waye ya shigo akai wannan sanarwar.
Kallan Aslam dake Zaune cikin matsanancin yanayi tayi zuru ta bude Baki tace
‘Kije kiyi sallah zan tabbatarda me yake faruwa idan na kammala komai da kaina zan tafi gurin sultan dan tabbatarda komai.’
Miqewa Aslam tayi batareda tace komai ba sbd jikinta dayake matiqar a sanyaye babu kowace irin kuzari a tattare da ita dan kuwa a duniya babu abinda zai iya kashe zuciyarta lokaci daya ta buga irin ace bazata samu cikar burinta na aure ba Wanda shine maqasudin ragewansu Akan ASIM ALMAZZ ya hau mulki,
A yanzu rana tsaka idan NUAB ALMAZZ ya dawo BOYEM tabbas zasu samu babban katangar da zata iya shiga tsakaninsu da burinsu duk da bawai yadda zasuyiba zasu iya aikata komai Akan cikar burinsu ciki kuwa hadda kawar da rayukan wainda baa taba tinani ba.
Ficewa Aslam tayi zuciya da gangar jiki ba nutsuwa hakama HAILE tada sallarta tayi itama zuciyarta babu sukuni.
*****Motocin daya bayan daya suna zuwa can quryar harabar da iya jinin sarautar suke isa can a Jere suka fara Parkin daya bayan daya cikin tsarin da suka saba motar LEUL dince a tsakiya
Kai tsaye suka fara fitowa daya bayan daya aka bude kofar da LEUL BOYEM yake Zaune ya ziro kafafunsa cikin izza waje kafin ya fito gabaki dayansa yana shakar iskar Masarautar datake jininsa,
Lumshe fararen idanuwansa masu kyau da kwarjini me zafi yayi yana Jin Wani bangare na zuciyarsa yaja cikewa da gurbi me Zafin dayake ciki da wani sanyi me ratsa zuciyar sbd Ayau gashi inda mahaifiyarsa ke rayuwa yana shaqar iskar Numfashi daya da ita,
Gabaki dayansu a tsaye suke qyam babu alaman gajiya ko buqatan Hutu a tattare dasu ko kadan saima karfinsu mai daga hankali dayake sake bayyana.
Sarkin bayi ne cikin wata irin gaggawa ya iso gurin tareda tarin bayin da suka zube qasa gabaki dayansu kansu a qasa suna gaidasa batareda sanin yabar gurin ba Kai tsaye bai jira komai da kowaba ya doshi bangaren mahaifiyarsa shi daya tak sbd babu me hurumin shiga bangaren matan sarki idan ba ‘yayansu ba dan haka gabaki daya Yaransa suna tsaye a inda motocin su suke babu alaman sauki ko rahama ko daya a fuskarsu.
Aleey ne ya sanar da sarki bayi LEUL BOYEM ya Riga ya wuce bangaren mahaifiyarsa nasa bangaren suke buqatan a kaisu dan tabbatarda tsaronsa.
Babu bata lokaci Kai tsaye aka wuce dasu bangaren nasa me girma Wanda yake part guda mai tsari da kyau,
Duk da baya nan babu shekarar da baa sauya furnitures da komai na bangarensa sbd haka doka da kaidar take,
Komai na sauyin da ake masa ahankali ahankali yana tafiya ne da cigaban zamani da ake samu har zuwa yanzu da aka zuba duk wani luxury na rayuwa da zai basa Hutu da nutsuwa isasu,
Komai a tsare yake da duk abinda zai saka yaji kaman yana gidansa na Moscow kawai dai yar qura ce sosai itama a take Sarkin bayi ya fara bada umarnin a fara gyara.
Dakatar dashi Aleey yayi cikin nutsuwa da buqatar full control na kulawa da komai daya danganci lamarin LEUL komai qanqantarsa,
Babu abinda babu a Masarautar BOYEM na Jin dadi da biyan buqata dan haka take Aleey ya bada umarnin a fara sauya komai dake bangaren a cikin kankanin lokaci dan haka ba bata lokacin Sarkin bayi ya saka a fara fidda Kayan a fara shigo da wasu da suka fisu komai.
******Sultan YASAR a daidai lokacin da sautin qarar dawowan magajin dayayi shekaru yana jiran wannan ranar ta dawowansa a wannan lokacin wayar sa ne da wishmah ayanah ghaz wadda a tare sautin ya shiga kunnuwansu ya isa ga zuciyarsa yana sanyayar da wani gurbi me girma da yayi shekaru a zuciyarsa,
Ahankali sautin yake sake ratsashi ya rufe idanuwansa masu kyau da kwarjini yana jan wani Numfashi me dumi ya saukesa a hankali tareda bude idanuwansa Akan fuskar Ayanah dake bayyane kan screen dinsa shiru ta zuba masa ido a sanyaye bata iya cewa komai.
A natse cikin sanyin nutsuwa ya sauke ajiyan zuciya datake dauke da shirin zartarwa da shirin fuskarta abubuwa da dama a masarautar da wainda suke cikin masarautar dan kuwa wannan ranar yake jira Wanda NUAB ALMAZZ zai kawo kansa masarautar da kansa amma kuma fitarsa da kansa ya rasa kenan saida umarnin sa dan kuwa shine yake riqe da cokalin juya rayuwarsa yanda yaso har sai ya cika masa burinsa daya dauka akansa tin daga ranar daya diro duniya,
Burinsa daya saka ya banzatar da abinda yakeso fiyeda komai da rayuwarsa.
Kallan Ayanah yayi a natse ya Lumshe ido akanta ya sake budesu akanta kafin ya bude Baki cikin mulkin dayake yawo jininsa shima da sautin daya shigeta yace
‘HAYATEEM dinki Zaki me BOYEM ya dawo gareki a matsayin cikakken namijin da BOYEM ke buqata’
Motsa idanuwanta tayi akansa tana Jin maganar tasa ta sauka cikin hankali da tinaninta harma da gangar jikinta dan haka ta motsa tana tashi Zaune da kyau duk da bata karfi ko kadan sbd rashin lafiyan datake cinta,
Juya kanta tayi ahankali zuwa kofar ficewa bedroom din nata datake ciki daidai nan sultan ya kashe wayar yana jinginar da bayansa ga lafiyayyar kujeran dayake Zaune ta bedroom dinsa tareda dake rufe idanuwansa ahankali zuciyarsa na yin dum tareda shiga tinanika da dama.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
53
Ahankali tafara Takawa tana nufar kofar bedroom din nata idanuwanta na kafe kofar da idanuwanta tanajin jikinta na qara rasa karfinsa da kuzari,
Duk takunta daya nauyi kirjinta qaruwa yakeyi ta daga hannunta da baida karfi ta Dora a kirjinta tana dafe sa sbd kaman gangar jikinta bazata iya daukan nauyinba Wanda tsawon shekarun tana jinsa amma Ayau yayi tsananin da jikinta ke sake sakewa ta isa kofar ta zubawa hannun kofar idanuwanta da sukai jajir a take batareda tasan menene takejiba a yanxu kuma,
NUAB kuwa tinda ya doso bangaren bayin dake hanyar gabaki dayansu suke zube qasa kansu na yin qasa dan idanuwansu basuyi darajar da zasu kallesa ba dan haka ko motsi me sauti babu me yi tsit hanyar ta dauka badan babu mutane ba Sedan tsananin bada girma ga jinin BOYEM.
Tinda ya tinkaro din shima kowane takunsa dawo masa da kowane Taku da yayi a ranar barin masarautar yake,dawo masa da takun da yayi a ranar daya rabu da mahaifiyarsa,rayuwarsa sanyi da hasken idaniyarsa wadda se yau ze sake haduwa da ita,
Babu hanyar da zata isar da shi bangaren mahaifiyarsa ko daya data bace masa duk da akwai manyan gyare gyare da sauyi da aka samu me yawa amma dai mahaifiyarsa na nan inda ya barta dan haka babu jiran komai Kai tsaye gurinta yake nufa.
Koda ya iso kofar bangarenta dayake dauke da sunan wishmah Baro Baro a jiki wani irin Numfashi me sanyi ya sauke yana dawo da kallansa kan Maa sakinah datake fitowa a hankali cikeda mutuwan jiki da mamaki idanuwanta na sauyawa da wani irin kallan datake masa zuciyarta na sake narkewa dan kamannin jinin GHAZ dayake bayyane a fuskarsa musamman Abaas Wanda yafi Kama da Ayanah sak dan haka kasa cigaba da kallansa sakinah tayi tana qasa da idanunwata hawaye na taruwa a cikinsu,
Maa tenya ma a sanyaye take fitowa dan tarbansa a matsayinta na jakadiyar Amminsa dan haka saukar da idanuwanta qasa tayi daga kallansa tana jinin Wani irin girmammen farin ciki da mutuwar jiki a lokaci daya dan haka bude Baki tayi zata fara gaisuwa da kirarin dayake dolenta…..
Katseta yayi Kai tsaye da muryansa data saka bayin dake bangaren sake Shan jinin jikinsu kansu a qasa,
‘Na dawo Maa’ ya fada a natse Kai tsaye yana kallansu su biyun zuciyarsa cikeda kauna da girmansu,
Tenya ce kauna da matsayin dayake dashi a cikin ranta ya danne matsayinta na jakadiyar sa data mahaifiyarsa ta dago tana fidda Wani murmushin farin ciki mai sanyi tace
‘Barka da dawowan me BOYEM da kansa,
Barka da dawowan Hayateem me zuciyar uwa da uba,
Barka da dawowan Zakin mazan boyem,
Barka da dawowan me jinin boyem da ghaz,
Barka da dawowan magajin asali na BOYEM,
Barka da dawowan LEUL me uwa uku’
Numfashi kawai ya isa saukewa yana kallan Maa sakinah da adduoin tsari kawai take jero masa a zuciyarta da ko bata bayyana ba ya sani haka take ita koyaushe bakinta a cikin adduar basa kariya da tsari daga kowane Sharri take kuma baa fili ba,
Ciki suka juyo suna qarasowa suna gaba yana bayansu dan yi masa iso ga inda mahaifiyarsa take,
A babban palon suka tsaya dukansu suna basa hanyar wucewa palo na gaba shi kadai dan isa ga mahaifiyarsa,
A natse ya wuce ya isa kofar ya saka hannunsa ya bude tareda saka kafarsa ciki idanuwansa na dagowa kallan kofar dakinta data bude itama tana fitowa da tsananin sanyin kafafu idanuwanta da sukai ja suna sauka akansa batareda ta kyafta ba
Shi kansa idanuwansa jajir suka a lokacinda ya kafeta dasu yana mata kallan da kowace gabar jikinsa ke amsa tsananin kaunar dayake mata.
Kasa motsawa tayi daga inda take cak duniyarta na Wani irin Juyawa sbd kasa yadda da abinda idanuwanta ke gani,
Da gaske ne NUAB dinta ne a gabanta kokuwa ire iren gizon da yake mata ne shi da Abaas,
Shi kansa mutuwar tsaye yayi a gurin dayake yake din yana kallan kowane yanayi da mahaifiyarsa ta koma Wanda hadda manyanci dayake nuna tsufa Yazo a tattare da ita ga ciwo fa qunci da damuwa da kadaici tareda rashin cikakken tinin kanta dan haka kan idanunwansa suke sake yin ja radadin rashin lokutan mahaifiyarsa da aka rabasa dasu tin kuruciya suna dawo masa dan kuwa an hanata yarintar ‘danta kaman yanda aka hanasa yarinta a gaban mahaifiyarsa,
An hanasa samun kulawa da tattalin a lokutan ciwonsa da baqin cikinsa kaman yanda kowane ‘da yake samu daga mahaifiya ko mahaifansa,
Shi shikadai yake ciwo yayi jinyar kansa ya kula da kansa ya tsayawa kansa yayiwa kansa komai tamkar marayan da baida uwa baida uba baida gata,
A lokutan ciwo mai tsanani da dama yayi kukan rashin mahaifiyarsa da dumin jikinta kadai zai iya basa warakar dayake nema da sassaucin kowace irin azaba amma duka an hanasa samun hakan an hana mahaifiyansa samun basa hakan daga karshe dai Bayan shekaru Ayau Allah ya hadasu haduwan da mutuwa ce yanzu kadai zata rabasa da ita badai kowane ‘dan Adam ba komai matsayinsa kuwa a duniya.
‘HAYATEEM’ bakinta ya bude ya furta a hankali cikin wani irin sautin daya saka gabaki daya tsigar jikinsa tashi ya tako bai tsaye komaiba ya janyota jikinsa ya rungume da Wani irin karfi yana rintse idanuwansa da har wani radadin yaji suke masa.
Sake ambatar sunansa tayi da sautin daya sake tada duk wata tsigar jikinsa tana Qanqamesa ta fasa wani irin kuka mai qarami da sanyayar sauti tana Jin nauyin kirjinta yana fadawa qasa ahankali ta sake qanqamesa tana ambatar sunansa.
Dagota yayi ya Kama fuskarta da tafukan hannuwansa biyu yakai bakinsa tsakiyar kanta yayi kissing cikeda tsananin kaunarta ya sake juya gefen fuskarta yai kissing ya dago hannuwanta duba biyu yayi kissing kowanne ya sake rungumeta jikinsa tsamtsam yana Jin kaman bazai taba iya rayuwa ba daga ranar da wani