Showing 51001 words to 54000 words out of 121560 words

Chapter 18 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3768

gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
A Daren Ayanah bata rintsa kona minti daya ba kwance kawai take amma babu ta inda bacci ya tinkaro idanuwanta sbd koda Yazo na iya ido ne babu kowane sauki da sassaucin dayake bawa ruhi da zuciyarta sbd a daidai wannan gabar ta rasa nutsuwa da farin ciki tareda walwala ko sakewa har abada sai kuma ranar data iya saka daya daga cikin jininta biyu da suke raye a idonta dan haka zata rayu ne kawai gangar jikinta na aiki amma Banda zuciya wadda itama bugawa kawai take amma duk abinda zata samu a duniyar nan yanzu bazai taba bata farin ciki Kona seconds ba sbd ta gama rufe babin rayuwarta babu farin cikin dazai shigo bayan qarasa rayuwa da qunci daddabe a ranta kuma a hakan zata bar duniya.

Daga Daren yau shima tana kwana a shimfidar ‘da namiji zata tashi daga AYANAH GHAZ dinta zuwa macen da batada Sauran amfani a duniya Bayan biyawa namiji buqata,
Zata tashi daga Ayanar Ammanta da Abaa dinta harma da Abaas dinta Wanda ya gwammaci mutuwansa akan ganin an keta haddinta Shiyasa ubangiji ya rabasu sbd kada yaga wannan mummunan ranar da Ayanaah bazata taba aure ba har abada,auren dayake fata tayi ya hada zuria da ita,auren dayake da mafi girman Buri akansa sbd shine yayi alkawarin bada aurenta ya karbi zinariya da azurfar sadakin aurenta a hannunsa koda yana qaninta wannan Alkawari ne daya dauka kuma mahaifinsu ma ya yaddar da cika masa wannan burin na shine zai bada auren Ayanah dinsa,

Duka wannan Buri kashe a iya mafarki da Buri zai tsaya,

Aurenta a matsayin ‘ya babba ga shugaban ANJOM kuma mace mafi kyau a GHAZ shine abinda garin ANJOM gabaki daya da ahalinta suke jira sbd sake daukaka darajarsa a garin gabaki daya,
Ashe kaddararta ma babu aure a cikinta kwata kwata Ayau gata zaa kaita a matsayin abar biyan buqata da sauke shaawa batareda daraja ko daya ba,

Ayau itace ranar yancin jiki da sunanta na qarshe sbd daga yau din bazata sake sunanta Ayanaah ba dayake da daraja sosai ga iyayenta da yan uwanta daga yau sedai a kirata da imebēti Ayanah har karshen rayuwarta,
Daga yau ta haramta ga kowane irin namiji har karshen rayuwarta dan haka aure sedai taji sunansa kokuma taga Ana yinsa……

Lumshe idanuwanta tayi ahankali radadin dayake cikinsu ya ratsa har zuciyarta yana sauka maqoshinta ta hadiyesa zuwa cikinta da babu komai a cikinsa sai tarin quncin da dashi zata mutu.

Har asuba bata rintsa ba bata kuma iya dogon Motsi sbd Sam hanayaniya ya dade da fita rayuwarta bare doguwar magana dan haka sai hakan yake sake qara mata kaman aji da nutsuwa,

Nafila tayi kafin lokacin sallar asubar yayi tayi sallah ta sake miqa dukkanin lamarinta ga ubangiji har gari ya waye sosai tana Zaune kanta akan kafafunta shiru idanuwanta Lumshe tamkar fresh fulawa sabon tsiro.

Karfe tara na safe aka shigo dakin nata aka sake hada mata wasu ruwa masu fitinanniyar qamshi da wani abu a cikinsu aka sakata cikinsu Zafin su na ratsata zuwa cikin jikinta take gashin jikinta suka miqe tanajin hatta kanta saida ya sara yayi mata nauyin daya sakata bude idanunwata data Lumshe ta rufe Bayan shigarta ruwan,

Ruwan ta kalla cikin sanyi kafin ta sauke Numfashi me dumi tana Ji suna sake shigarta sosai suna saka jikinta daukan dumi sosai,

Tsawon awa kusan biyu tayi a cikin ruwan kafin aka fiddo da ita aka fara shafe jikinta da Wani irin hadin danyar madarar datake hade da manshanu danye da baa rabasu ba,

Ahankali ake shafe jikinta Ana murzawa tamkar Ana gudun fatarta ta yage,

Ana gama shafe wa wani turaren hayaqi aka fara mata yana saka abinda aka Shafa mata kama fatarta da shiga tsigan jikinta dan kuwa hatta dogon gashinta saida aka shafe sa tas dashi,

Tenya ce da kanta ta shigo Ana biye da ita dauke da farar kakkaurar madarar shanu me Zafin gaske ta dauka da hannunta ta miqawa Ayanaah din wadda hannu kawai ta miqa batareda ta dago ba ta karba takai bakinta ba musu ba cewa komai ta fara sha a natse jikinta sanyaye.

Sai data shanye kafin aka kawo ruwa masu zafi da kyau da qamshi aka fara zubawa a jikinta Ana wankewa tana Zaune cikin pool din da babu ruwa daga ita sai abinda iya nonuwanta kadai ya rufe sai wandon da shima baida banbanci da pant Wanda shima kusan har ciki an shafa komai,

Wanketa tas akai kafin aka bata damar wanka da ruwan sabulu masu tsananin tsada da qamshi,

Ta jima a ciki gurin wankan kafin ta fito sbd acan din kukane mai tsananin karfi da sosa zuciya tayi sosai kafin tayi wankan ta fito.

Komai da a yanzu ake kawo mata tana amfani dashi na musamman ne dan haka body lotions ne masu tsada hadin qasar BOYEM da body oils tareda turaren da ya gama kama jikinta dan kuwa ko bata shafa komai ba ko batai wanka ba wani qamshi ne yake fitowa a jikinta Wanda ya gama kama koina har gashin jikinta dan yanda ake turara Kayanta haka ake tirara ta.

Bayan ta gama shiryawa cikin wata doguwar rigar qasar kuwait black da mayafinta a kanta daure kalan daurin al’adar qasar breakfast aka kawo mata Sai a lokacin tayi tana gamawa lokacin sallah yayi tana sallah batasan lokacinda bacci ya dauketa ba a kwance kan lafiyayyan gadon dakin sbd madarar da ake bata akwai maganin saka bacci dan samun nutsuwar gangar jiki data Kai gashi duk tsayin Daren bata rintsa ba dan hakanne baccin ya samu daman dauketa sosai.

**********Karfe hudu na yammar ranar motoci sama da goma ne suka isa airport din BOYEM dan dauko SULTAN YASAR ALMAZ BOYEM Wanda a duka kaf motocin babu Wanda bata haura mahaukatan millions ba kudin siyanta,

Ko motocin securities din masarautar ba qanana bane dan haka kusan 30 min kafin saukar private jet dinsa suka isa airport aka zagaye koina na hanyar fitowa da securities masu tsananin gaske hakama daga lokacin da jirginsa ya sauka airport din babu motar da zata bar airport din sai motocinsa da securities dinsa sun wuce sbd matsayi da tsantsan ikon da Masarautar BOYEM take dashi take kuma bugawa kaf zamanin babu me matsayin dayake bugasa komai muqamin kasar dakake dashi.

Jirginsa na sauka ba bata lokaci motoci suka iso har bakin jirginsa suka daukesa aka bar airport dashi cikeda tsaro ba hayaniya zuwa Masarauta,

Tafiya bame tsayi sukai ba aka iso gida tin daga nesa securities sukai saurin bude gate suna mimmiqewa tsaye qame a jere kansu a qasa.

Haka motocin suka wuce ciki kaf har zuwa gate na biyu Wanda taron yan fadarsa suke duk matsayin su da muqaminsu da suke dashi na masarautar matiqar sarki yayi tafiya ya dawo dole ne suka tarbesa duk da baa dawowa dashi ya tsaya koina sai cikin tirakarsa sai daga baya yake fitowa fada koma Washe gari ko Bayan kwana biyu amma duk da hakan dole ke duk tafiyar da yayi ya dawo duk wani me matsayi a Masarautar BOYEM sai ya fito ya tarbesa,

Ana isa gate na uku mota biyu ce kadai ta wuce ciki wadda daga wadda yake ciki sai wadda babban amintaccensa da securities dinsa na hanyar tirakarsa suke ciki.

Motocin na shigewa gate din na uku aka rufesa ruf babu kuma mai iya ganin sultan din sai ranar daya gama hutawa ya fito iyalansa kadai ke suke da ikon ganinsa a wannan gabar dan haka koina ya sake daukan tsit me qasar BOYEM ya dawo komai nisan kilometers din dake tsakaninka da ina yake matiqar kana cikin BOYEM palace din to Ka tsananta nutsuwa da kama jikinka dan kuwa yana dawowa akwai sautin da ake bugawa Wanda kusan duka babban garin saiya dauka.

Idan akace Aljannar duniya gurin tsara bangaren sultan YASAR to an taqaita ne kawai sbd Kai tsaye kana shiga tin daga hanyar da zata kaika palon farko na isa tirakarsa zakaji jikinka ya mutu ko kafafunka sai kayi daqyar kake dagawa,

Doguwar hanya ce datake tsit tiles din da zaka Dora kafafunka kayi tafiya ya dauki Wani irin sanyin da duk Taku kake jinsa har cikin qwaqwalwarka,

Qamshi da zakaji yana ratsa hancinka zuwa qwaqwalwarka haka zaka jisa yana shigarka cikin nutsuwa tamkar umarni ake basa sbd nutsuwar kamshin datai yawa,

Komai dayake hanyar fari da golden ne dayake daukan ido yana sakaka sanin Kai ba kowa bane a qasar BOYEM ma gabaki dayanta bare masarautar ita kanta,
Tsit gurin yake ba motsi ba hayaniya securities ne tin a karfon kofar da wata security camera datake bin motsi duk inda yayi amma iya kofar shigowa ne kadai securities din suke kana shigo doguwar hanyar tsit kawai sai mutuwan jiki,

Idan Ka wuce doguwar hanyar palon farko zaka iso wanda kana shigar sa Ajiyan zuciya ce zata kufce maka me sanyi itama da nutsuwa sbd komai na palon ladabtarwa kawai yakeyi dan asalin dukiyar duniya ce a cikinsa,
Komai na palon brown and golden ne Wanda idan Ka jima a ciki Kai tsaye zaka iya yadda da labarin da ake bawa duniya n cewan komai dayake cikin masarautar BOYEM indai Golden ne zinariya ce kawai sbd kusan akwai guraren da adon nasu da gaske akwai zinari a cikinsu.

Wasu luxury leather Turkish royal sofas ne brown da suke daukan ido sun dauki sanyin ac da wani sanyayyan qamshi har sun gaji,

Premium luxury winter velvet curtains ne a palon da suka sake maidasa tamkar ba a duniyar mutane ba sai Sauran abubuwan dake palon masu tabbatar da duniyar masu arziki daban take ko a ina ne,

Kana wucesa yar qaramar tafiya ce da bata wuce Taku hudu zuwa hudu Ka isa palon dake gabansa Wanda shima tsaruwarsa ta wuce na farkon sedai shi komai na cikinsa milk da golden ne Wanda shi nasa tsarin English settin ne ba kamar na farkon dayake komai na royalty ne,

Kana wucesa qaramin palo ne a karshen Wanda komai nasa yafi zama mai sanyin tsari da nutsuwan kala dan kuwa milk sky blue ne da golden mara Kala sosai hakama baida kaya sosai sai burgewa da zallan class,anan asalin lafiyayyan bedroom din sultan YASAR me BOYEM yake Wanda fadar tsaruwarsa bata lokaci dan kuwa gadonsa kadai dayake tsakar tsakiyar dakin ya isa ya sakaka tsayawa kallansa dan kuwa komai na dakin coffee brown da golden ne dayake nuna asali da ainihin tsarin royalty dan hatta wani tsadadden smart automatic curtains dake zagaye da gadonsa da baa ganin Wanda yake ciki sedai Inuwansa abin kallo da daukan hankali ne harma da tsoron dukiyar datai yawa a masarautar.

Qamshi da sanyin dayake fara sauka a Fuskanka zuwa hancinka na daban ne idan Ka sako Kai dakin Wanda duk duniya babu me shigarsa idan ba matansa ba suma sai kuma macen da zai kwanta da ita Wanda yake tamkar saar duniya garesu.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

31
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
Masu aikin bangaren Sultan daban suke gurinsu daban yake Sam baa hadasu da kowa hakama koyaushe cikin kiyaye lafiyar su ake akai akai sbd tsaro da bawa komai daya gangancesa tsaro da kariya daga koman qanqantar cuta.

Ayau din daya dawo daga doguwar tafiyar kwanaki da satika harm da wata gabaki daya matansa harma da wasu daga cikin imebētinsa sun shirya sosai sunci burin samun gayyata zuwa shimfidarsa sbd dole bazaa rasa tarin buqatar mace daya dawo da ita ba tinda tsawon lokaci baya tareda mace,

Matansa su biyu sunsan dole ne zuwa turakarsa yi masa Barka da dawowa harma da kwana acan amma ba lallai su samu yaji buqatan kwanciya dasu ba dan saukewa Kai buqata haka dan hakanne kusan kowacensu tayi shiri tana fatar ta kasance itace wadda Ayau zai saukewa buqatarsa.

Daga matansa harma da imebētis dinsa gabaki dayansu sun san an shirya masa wasu sabbin imebētin wainda zai samu nutsuwa dasu sosai amma duk da hakan basu cire ran samun gayyatarsa dan haka a ranar babu macen data fito sbd tsima kansu da sukai da Qamshi da abubuwa daban daban.

Wanka yayi a cikin ruwan da aka hada masa masu zafi da qamshin itatuwa masu sanya nutsuwa tsawon lokaci a cikin ruwan saida yar gajiyansa ta sake ta wartsake kafin ya fita ruwan yayi wanka da shower da ruwan dumi har suna fidda hayaqi tukuna ya dauro towel me kauri da girma ya fito wani irin qamshi na biyosa daga toilet din.

Koda yayi fito HAILE na dakin ta iso tana Zaune haskenta na daukan ido qamshinta me sanyi ya gauraye dakin daya sakasa dan Lumshe ido yana qarasowa ya zauna a kujeran dake gaban dresser Sai a lokacin ya dago fararen idanuwansa tas masu girma da tsananin kwarjinn dayake tsinkar da duk Wanda ya kallesu ya sauke a fuskarta ya mata kallan nutsuwa yana sake yadda da babu mace mai kyanta duk da babu soyayya a ransa ta kowace mace amma yadda da HAILE itace mace mafi daraja a Masarautar BOYEM yanzu.

Bude baki yayi ya amsa gaisuwarta a taqaice yana maida kallansa ga madubin dake gabansu ta saka towel ahankali tana goge masa jikinsa a natse da kulawa tareda tsananin sonsa datake Jin koyaushe kaman zai kasheta,

A rayuwarta bata taba rasa komai datake so ba,
Babu abinda batada dashi a rayuwarta tin daga kan dukiya da mulki da kyau da iko amma sultan YASAR BOYEM shine abinda ta kasa mallaka ita kadai yanda take so,
Shine Wanda takejin tana yiwa so kamar ma fiyeda yayanta sbd babu namiji a cikinsu,
Shine Wanda take iya yin komai a Kansa ciki kuwa harda daukan rayukan mutane datake Jin ba komaiba,
Shine Wanda bazata iya taba barin ya San soyayya ba idan ba akanta ba dan kuwa ita kanta haryanxu tasani sultan yasar bai taba son kowace mace ba harsu da suke matansa babu asalin soyayya a tsakaninsu kawai dai yana aurensu kuma yana samun yanda yake so a tattare dasu hakama yana tareda dasu ne sbd sanin kowane sarki baya taba cika ko zama Sarkin saida mata da iyali a kansa,

Idan har sultan Yasar ba ita ze so ba har abada bazata taba barin ya dandana menene soyayyar gaskia da gaskia dan kuwa a littafinta baa ma haifi macen da duk duniya sultan Yasar zai so ba Bayan ita.

Harta gama goge jikinsa ta dauki mai me Laushi da qamshi tana shafa masa bata Dena kallansa ba kaman zata hadiyesa kaman zata bude zuciyarta ta sakasa ta rufe kowa a duniya ya Dena ganinsa Bayan ita kadai.

Cikin Kayan Shan iska da hutawa ya shirya ya Dora jallabiya milk me kyau da tsada tareda santsi ya nufi gurin sallar dake cikin dakinsa ya tada sallar laasar,

Yana idarwa abincin dayafi karfin cikin kusan Mutum goma aka kawo aka jere reras a makeken dining table din dake palon sa na biyu acan ya isa yaci abinci daidai cikinsa,

Yana gamawa Maraki na shigowa itama da tata hidimar dole HAILE ta fice tabar bangaren,

Baccin nutsuwa da sake samun wartsakewa yayi nai dadin gaske har yamma sosai tukuna ya farka yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya mai duhu da wata black and golden kyabba mara nauyi data fito da haske da zallan kyansa na asalin jinin BOYEM.

Sallar magrib ya fito a babban masalaccin dayake cikin fadarsa Wanda securities ne dashi shima masalaccin hakama manyan Masarauta ne suke sallah a cikinsa,

Koda ya fita baya dawowa ciki sai yayi sallan ishai Wanda yana shigewa kuma babu me sake ganinsa sai wata safiyar.

Karfe takwas da rabi harma da mintina ya shige kuma yana shigewa ake rufe kowane gate na Masarauta babu shiga babu fita sai kuma Washe gari dan haka koina y sake kamuwa da nutsuwan tsit dan kuwa dole kowa ya gama abinda yake ya shige ba hayaniya koda kuwa kana nesa ne.

****Adaidai wannan lokacin Ayanah ce a cikin pool din da zatai wankan zuwa tirakar Sultan a daren,
Bayi sama da hudu ne a kanta suna zuba mata ruwan dumi da qamshi a hankali tin daga kanta suna sauka kan fuskarta da gangarowa jikinta da santsi sbd fatarta datai Wani irin Laushi da santsi me yawan gaske,

Idanuwanta a rufe suke bata iya budewa ba sbd bata buqatan kallo ko ganin komai da ake mata,

Sakinah na cikin masu gagarumin shirin nata Wanda dukkanin kowane motsin sakinar jinsa takeyi yana yanka da Sosa zuciyarta sbd ganin yanda Ayanaah ta gama mutuwa daga gangar jiki har zuciya babu abinda ya rage hakama daga daren yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login