Showing 6001 words to 9000 words out of 121560 words

Chapter 3 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3827

kwata kwata kafin Abaas din ya dago ya kalli Asamah kaman zai yi magana sai bai ce komaiba ya maida idanuwansa Akan Ammansa dake miqewa tabar gurin tana bin Bayan GHAZ Ayanah kuma hannu ta miqa masa ya Kama ya miqe suka nufi hanyar dakinsa tana cewa

‘Yankan qaramar wuqar cin tufa bazata girgiza jarumin anjom ba GHAZ din anjom me zuwa’

Yar dariya yayi yana kallan kafar tasa tareda cewa

‘Shekarun nawa basu Kai ba ai tukuna amma insha Allah idan nakai shekaru ashirin a duniya zan fara fita a matsayin jarumin na anjom wata ran harma na zama Garkuwa ga dukkaninku’

Har cikin ranta taji dadin abinda ya fada tana fatan hakan koda kuwa a mafarki ne.

Rakasa tayi dakinsa Wanda acan suka zauna ta tayasa fira sai ga su Zuhrah da Nurat sun taho suma sbd sunsan saiya kwana biyu kafin ya fito koina sbd tsaro da dokar GHAZ din tin asali duk Wanda yake jinin GHAZ yaji rauni har jininsa ya fita to saiya kwana biyu a killace batareda fito wa koina ba sai Raunin ya qame,

Hakan ne ya saka yan uwansa zuwa dan tayasa fira da debe kewa,

Kayan ciye ciye da dafaffiyar madarar raqumi me dumi aka kawo aka ajiya musu sunata firarsu da hutawarsu cikin kwanciyan hankali da nishadin farin cikin kansacewa da juna,

Anan suka wuni dan hatta ibadarsu anan sukayita,

Da yamma ma mahaifinsu shigowa yayi cikinsu cikeda Shakuwa da kaunar juna suka cigaba da farin cikinsu anan cikinsu yayi sallah tareda iyalansa har cikin dare tukuna dukkaninsu suka watse kowa ya nufi makwancinsa.

Ayanah na isa dakinta zare Kayan jikinta tayi ahankali tana rufe jikinta duka ruf da wata kakkaurar doguwar rigar wanka me Kama da alkyabba amma ita ta yadin saka me kyau.

Baiwarta Sakina ce take biye da ita dauke da wutar haskawa.

Gurin wankansu ta Nufa Wanda yake cike da ruwa masu tsafta da kullum ake sauyawa ta zare rigar tana zaunawa gaban ruwan tafara wanka a natse.

Sakina ajiye mata hasken tayi ta koma kofa ta tsaya daga waje tana jiran fitowarta.

Gama wankan tayi ta fito tana qamshin madarar flower me dadi.

Dakinta ta shiga ta zauna Sakina tana tayata goge jikknta harta gama ta shirya ta nufi lafiyayyan gadonta na sarauta ta haye.

Washe gari ma haka suka wuni gurin Abaas tareda iyayensu Wanda kwata kwata GHAZ ayau din bai fita koina ba yana cikin yayansa tausayin Abaas haka kawai yake shige masa zuciya sbd ganin kaman zuciyarsa tayi sanyin da bazai iya mulki ba idan ma yayi wahala zaisha sosai,

Akan ‘yayansa mata ya maida idanuwansa yana kallan yanda suke dariya suna Wasagu da juna sautin dariyarsu na shiga kunnuwansa zuciyarsa na na cikewa da tsananin kaunarsu yanajin kaman ya maidasu cikin Mahaifiyarsu sbd basu tsaro da kariya daga dukkanin wata cutar duniya da wahala.

Akan Ayanah ya tsayar da idanuwansa dariyarta na a bayyanarda asalin zallan Kyan da Allah yayi mata Wanda yasa Sam baa barinta fita daga GHAZ din itama,
Ayanah nada zuciya me sanyi da hakuri tareda juriya tareda jajircewa Akan ‘yan uwanta Wanda yasa yakejin kannenta sun dace dan kuwa tamkar uwarsu haka take kulawa dasu,

Akan Zuhrah ya maida idanuwansa yana kallan gashinta dayake sake zube a bayanta Wanda babu namijin da zai kalleta bata fizgi hankalinsa ba dan haka yake killace dukkanin wata al’aurarsu sam baya barin ko yatsar hannuwansu wani na waje na gani sbd a sujjarsa gabaki daya adduar ‘yayansa ne.

Ahankali jikinsa na mutuwa ya daga hannunsa ya miqa akan Zuhrah ya fara tattare gashinta cikin kulawa ya daure mata yana janye mayafinta me ado dayake gefenta ajiye ya rufe gashin nata.
#MAMUH
#GHAZ
#KUSRAH
#BOYEM
#ROYALTY
#BEST LOVE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

5
Dago Kai Zuhrah tayi ta kalli Abaa din tana Dora hannunta akanta ta taba mayafin daya rufe kanta dashi tana zubawa mahaifinta ido ta bude baki zatai magana ya Dora hannunsa daya akan bakinta ya girgiza mata Kai ya bude baki yace

‘Kanki ya kasance koda Yaushe a rufe Zuhrah ghaz’

Gyada kanta tayi batareda ta dauke idanuwanta daga Kansa ba sbd ganin wani irin kallan tsananin kaunar dayake mata.

Tsakiyar kanta ya sumbata yace

‘Albarkar Allah ta tabbata a rayuwanki Zuhrah koda yan uwanki duka’

‘Amin Abaa’ ta fada tana matsowa sosai jikinsa ta zauna.

Nurat ya maida idanuwansa ya kalla wadda take jikinta yayi sanyi sbd itace tafi kowa saurin kamuwa da yanayin da duk ya sauya,

Ta fisu saurin hawaye da zama emotional sbd tanada qawazuci sosai na iyayensu dan haka hannunsa ya miqa mata ta taso daga gefen Abaas ta dawo gefensa ta kallesa idanuwanta na raurau haka kawai.

Wani murmushi me sanyi da kyau ya dake yana Shafa fuskanta ya girgiza mata Kai yace

‘Jarumar ‘yata Nurat bata barin jikinta yayi sanyi a kowane yanayi’

Murmushi ta sake tana Kama hannunsa qamqam tace

‘Abaa ina fatan na kasance hakan daka fada koba yanzu ba’

‘Insha Allah Nurat zaki zama jajirtacciya dakakkiya bazaki taba gazawaba insha Allah’

Maganarsa ta saka Ammansu kallansa tana dan murmushi batareda tace komaiba.

Qarasa fitar da wunin sukai cikin tsananin kaunar dasuke Jin tafi ta koyaushe musamman da mahaifinsu yaketa yabonsu yana kasa dauke kallansa akansu cikeda kauna hakama Amma Jin takeyi tana sake kaunar mijinta sbd yanda ya tarbiyantar da ita da yayansu.

Da daddare Bayan sunyi sallah ishai Abinci da Kayan marmari aka kawo aka Jere musu tareda fitilun wutar ishen flower masu sanyin kamshi da aka kewaye gurin dasu suna basu haske tareda kamshi.

Dagowa GHAZ yayi ya kalli sakina baiwar Ayanah dake gefensa ya bude baki yace

‘Ina Asamah gabaki daya yau ban ganta ba’

Sunkuyar da Kai sakina tayi cikin girmamawa ta bude baki tace

‘Tin jiya bata fito ba babu Wanda ya ganta a yau sbd damuwan abinda ya faru da GHAZ Abaas’

Kallan Amma GHAZ yayi yana Neman qarin bayanin hakan

Kallansa tayi itama cikin kwantar masa da hankali tace

‘Tashiga damuwa sosai ne har dare jiya tana gurina tana kukan Neman Gafara da Afuwan abinda ya faru dan hakanne yau Kowa ya kyaleta ta dawo daidai’

Shiru yayi sbd bayason nuna damuwa ko fada a cikin iyalansa dan haka baice komaiba sbd duk tsawon shekarun nan bai taba dauke saka Idonsa da saka taka tsantsan sosai akan Asamah ba dan haka tin jiyan da jinin Abaas ya fita yake Jin rashin nutsuwa amma baya iya nunawa sbd yanzu suna cikin wani hali ne na kusrawa dake Neman kawo musu hari kowane lokaci suka samu damar hakan.

Abinci suka ci suna fira da nishadinsu har suka gama nanma suka ci gaba da firarsu har dare sosai kafin Abaa da Kansa ya raka kowacensu dakinta da Kansa kafin ya dawo ya tafi da Amma dakinsu itama tukuna ya fito ya dawo dakin Abaas sosai kafin ya fito ya shige shima.

Tsakiyar dare sosai Nurat dake kwance taba bacci cikin kwanciyan hankali da nutsuwa ta farka da karfi cikin mummunan faduwan gaba sbd mummunan mafarkin datai.

Bude idanuwanta tayi ahankali tana sauke ajiyan zuciya a sanyaye kafin ta tashi Zaune tana Jin rashin nutsuwa,

Shiru tayi tana Dora hannunta kan kirjinta dake bugawa sosai cikin rashin Jin dadi,

Koma wa tayi ahankali tana kokarin kwanciya taji motsi me karfi daga waje dan haka gabanta ya sake faduwa ta zuro kafafunta qasa da sauri tana saukowa gadon tareda daukan mayafi tana Daurawa akanta ta nufo kofa tana bude kofar ta fito Kai tsaye batareda tsoron duhun Daren ba.

Takawa tayi Kai tsaye ta nufi dakin Ayanah sedai kafin ta isa dakin wani irin jan haske taga yana gauraye saman garin na alamar wuta.

Saman ta ringa kalla tana nufar dakin sai kuma hayaniyar tashin qara daga nesa Wanda ya sakata qarasawa dakin da sauri tanajin tsoro na shigarta.

Tura dakin tayi ta shiga da sauri ta qarasa gadon Ayanah ta haye gadon tana shigewa jikinta ta qanqameta.

Cikin bacci Ayanah taji Nurat cikin jikinta wadda tasan itace Kai tsaye sbd itace Kai tsaye take zuwa lokuta da dama cikin dare gurinta idan ta kasa bacci.

Numfashi da ajiyan zuciya Ayanah ta sauke tana Shafa kan Nurat din sedai kafin ta bude baki tayi magana aka sake turo dakin cikin wani irin sauri da karfi.

A tare suka miqe Zaune cikin faduwan gaba da mamaki,

‘Abaa’ Ayanah ta Ambaci sunan mahaifinsu dake shigowa da qaramin hasken wuta a hannunsa.

Nurat ma cikin fargaba tace

‘Abaa’

Qarasowa yayi da sauri batareda ya amsa su ba Amma na gefensa da hasken itama jikinta na tsananin rawan mummunan tashin hankalin da basu taba samun kansu a ciki ba tsawon tarihin GHAZ.

Riga me tsananin kauri ya janyo a cikin Kayan Ayanah ya miqa mata cikin kokarin hana mummunan tashin hankalinsa fita sbd kada su firgita yace

‘Saka wannan Ayanah’

Karba tayi hannuwanta na dan rawa tana sakawa akan kayanta tace

‘Abaa meya faru ne?’

Bai amsata ba ya janyo wata rigar ya saka a hannun Nurat dake sake shiga rikici idanuwanta na raurau

Amma ce ta taimakawa Nurat din gurin saka rigar Abaa ya Kama hannunsu su biyun ya nufo kofa dasu wannan Karan Amma ce riqe da hasken gaba daya.

Dakin Zuhrah suka isa wadda take bacci sosai hankali kwance

Cak Abaa ya tadata Zaune Wanda ya sakata bude ido tana sake lumshewa zata zame ta sake komawa kwance ya miqar da ita gabaki daya yana cewa

‘Ayanah samo mata Riga me nauyi sbd sanyi’

Da sauri Ayanah ta nufi Kayan Zuhrah din ta dauko Riga da sauri ta kawo tana miqa masa

Da Kansa ya sakawa Zuhrah din yana Kama hannunta itama suka fito.

Dakin Abaas suke kokarin nufa wani irin kuka da Ihun mutane mara dadin saurare ya sake tsananta yana gauraye garin tareda qaruwar hasken wutar dake cin garin sosai.

Sai a lokacin bacci gabaki daya ya sake su Ayanah suka shiga tsoro da faduwan gaba me tsanani suna kasa ma tambayan meya ke faruwa.

Abaas ma baccin yake Ayanah ce tayi saurin isa gurinsa ta tadashi da sauri dukkanin jikinta na rawa.

Fitowa sukai Abaa yaja su zuwa kofar baya ta fita gidan ya tura su wani daki tareda dukkanin bayin gidan mata ya kalli Amma batareda yace komaiba ya qanqame hannunta ya kalli Ayanah itama yace

‘Ku kula karku fito saina dawo
Idan kuma kunji shiru ban dawoba ku fita ta baya akwai hanyar dana tanadar muku ta barin gari ku bi karku tsaya sai kun fita ruwa gabaki daya kun fada nahiyar yom acan zaku samu rayuwan kwanciyan hankali idan har kuka fadawa sarkin garin ku GHAZ ne.

Shiru sukai dukkaninsu Banda Ayanah da Amma da suka riqe hannunsa suna girgiza kai,

Nurat da Zuhrah tareda Abaas kuwa cikin tsananin tashin hankali da wani irin firgici suka ce

‘Abaa ina zaka?
Karka fita dan Allah kazo mu tafi din bama sai mun jira ba dan Allah Abaa’

Girgiza kai yayi yana kallansu da jajayen idanuwansa da suke rine da tsananin ‘daci da baqin ciki yace

‘Ni shugaba ne ta yaya zan tafi nabar mutane na batareda nasan meya ke faruwa a garin ba……..

Katsesa Amma tayi cikin wani irin mugun tashin hankali muryanta na rawa zufa na tsiyayo mata da cewa

‘Koma menene ba alkhairi bane sbd Ihu da kukan da garin gabaki daya ya dauka ya tabbatarda hakan,
Masifa ce da balai a garin yau karka tafi dan Allah ka tsaya’

Zare hannunsa yayi cikin nata idanuwansa na sake kada wa jajir.

Cafke hannunsa Ayanah tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa wasu hawayen tashin hankali me tsanani suna kufce mata a rikice tace

‘Abaa dan Allah karka tafi mu tafi mubar garin tare bazamu iya tafiya koina babu kai ba’

Nurat ma qanqamesa tayi Zuhrah ta fada jikin Amma tana qanqameta Abaas ma Abaan ya riqe yana wani irin rawar jikin tashin hankali da tsoro take ya fasa kukan daya saka Abaan kallansa yanajin tsananin tausayinsa.

Banbare Ayanah da Nurat yake a jikinsa suna qanqamesa Ayanah tayi fashewa da wani irin kukan da bata taba sakewaba a rayuwarta tana ambatar sunan Abaan.

Fincikesu yayi da qarfi yana hana zuciyarsa karyewa ya turasu jikin Amma ya fice da sauri yana janyo marufin dakin.

Rawa da kuka sukeyi sosai Wanda gabaki daya gurin yayi tsit sai sautin kukansu dake tashi ahankali cikin mummunan tsoro,fargaba da tashin hankali.


Masifa,balai da kaddara ne suka saukarwa garin ANJOM a cikin Daren dayake na farko a tarihinsu da wannan masifar ta fadowa garin,

Wuta ce take ci tako ina zagaye da garin Wanda saida kusrawa suka gama cinnawa zagayen garin wuta sosai koina ya Kama sannan suka shigo cikin silalowa suka sakawa koina wuta a cikin garin kafin suka afkawa garin da wata irin mummunan kisan da take jini yafara fesuwa koina na mutane.

Ihun da kukan Neman agaji da ceto mutane suka fara Wanda ya saka gabaki daya garin daukan hayaniyan Data saka kowa fitowa Ana gudun Neman ceto sedai yawa da karfin da kusrawan ke dashi ya saka munin lamarin yayi yawan da komai ya lalace.

Kukan kananun yara dana mata da dabbobi ma dake gudun cetan rayuwansu ne yake gauraye gari da dajin ANJOM dayake amsa wa cikin sauti mara dadi da karya zuciya tareda tsananin tausayi.

Wuta kuwa haka take cin wasu mutane harma da dabbobi sbd gobara sosai garin ya dauka kowane gida sakawa wuta sukeyi sbd kada ma mutane su samu gurin boye dan haka komai ya zama tashin hankali mara misali lokaci daya.

GHAZ da fadawansa da askarawansa koda suka fito dan bada ceto ga jamaar gari lamarin ya gama munanar da babu abinda zasu iya sbd Angama cinye garin ANJOM da wuta da jinin mutane dan haka take suka fara cetan wainda zasu iya cikin azabar wuta da tashin hankalin munin gawawwakin mutane da suke tsallakewa da takawa.
#MAMUH
#ROYALTY
#SLAVERY
#BEST LOVE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070


6

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********


**********
Wani irin zufane yake jiqa Dukkaninsu zuciyoyinsu kaman zasu fado sbd munin tashin hankalin dasuke ciki,

Cikin duhun hasken wutar daya kusa cinyewa Ammah ta dago Idanuwanta da sukai jajir da hawaye masu karya zuciya ta kalli Ayanah kafin ta maida kallanta kan Sauran ‘yayan daya bayan tana hana hawayenta saukowa fuskanta sbd zuciyoyinsu duka a karya suke batason qarasa karyasu gabaki daya.

Juya kanta tayi ta kalli kofar dakin zuciyarta na kasa jurewa ta juyo ta sake kallan Ayanah wadda tayi saurin riqeta cikin mummunan tashin hankali ta bude baki da wata irin murya mara karfi cikin yarensu tace

‘Aāyi Amma, ātadirigi Amma, dan Allah Amma karkiyi hakan, āyi Amma.’

Hawayen da Amman ke riqewa ne suka gangaro cikin tsananin karyewan zuciya ta kalli Ayanah din tace

‘Ayanah dole zan dubosa sbd da hakan zamu tsira gabaki dayanmu’

Wani irin rikitaccen kukan tashin hankali me tsanani Ayanah ta sake tana rintse idanuwanta tareda sake qanqame hannun Amman tana girgiza akai ko magana ta kasa,

Nurat datake qame tin Bayan biyar Abaansu riqe hannun Amman daya tayi Tana girgiza kai itama hawaye masu tsananin zafi na gangarowa daga idanuwanta.

Abaas dake rungume dashi da Zuhrah saurin fadawa jikin Amman yayi ya rungumeta shima dukkanin jikinsa na rawa yace

‘Amma babu inda zaki tafi’

A rufe murya na rawa Zuhrah tace

‘Abaa ya tafi zai dawo Amma mu jirasa dan Allah karki tafi,
Idan kin tafi zan biki mu dubosa tare’

Turesu tayi daga jikinta tana kasa kallan kowannesu tace

‘Ku jira zan dawo,
Ayanah ki kula dasu karki Bari kowa ya biyo koda ban gansa ba zan dawo’

Sake riqeta Ayanah tayi Tana girgiza kai hannunta na rawa sosai muryanta na sake mutuwa kukanta na bayyana tace

‘Amma bazan iya ba dan Allah karki fita,
Amma bazan iya ba,
Āyi Amma dan Allah’

Zare hannu Amman tayi tace

‘Ayanah zaki iya yanzu fa zan dawo,
Nima idan na dade ku tafi kawai zamu taho daga baya ni dashi mu sameku acan
Kawai ki tabbatarda kin kula dasu sbd kece uwa a cikinsu kinji?’

Kasa cewa komai Ayanah din tayi kukanta na qaruwa tana girgiza kai jikinta na rawa sosai,

Su Zuhrah ma kuka sukeyi sosai suna qanqame Amman hankalinsu a tsananin tashe tsoronsu na sake bayyana.

Sake daukan Ihun tashin hankali da tsananin tsoro garin ke dauka hakama wuta tako ina Wanda ya saka Amman kasa riqe kanta sbd tana buqatan janyo GHAZ subar garin dan kuwa ba lallai su tsira ba hakan kawai ya hakura su tafi kawai dan tseratar da ahalinsu.

Tsoronta cirewa yayi tana Jin tsananin buqatan dawowansa su bar garin ta qwace daga riqon da yayanta sukai mata ta fice tareda janyo kofar da sauri ta rufe tana cewa bayin dake ciki tareda su suriqe su karsu Bari kowa ya fito.

Kai tsaye Amman na fitowa gidan taga masifar fata saka kafafunta daukan wata irin rawar tsoro da firgici zuciyarta na Neman bugawa da sauri ta dafa bango sbd jirin daya debeta na ganin wuta koina da jini kaman bana mutane ba.

Bangon dafa jini ne taji a tafin hannunta da sauri ta janye hannunta jikinta na sake daukan rawa.

Juyawa tafara yi kafafunta na Neman kasa daukanta tafara baza ido Tana kwada kiran GHAZ Wanda bazai taba jinta ba koda yana kusa sbd karfi da qarar wuta da Ihun mutane da gurnanin rayukan da basu gama fita kirjin mutane ba,

Taku kadan tayi Tana kutsa hanyar da mutane ke fitowa suna gudu baa hayyacinsu ba Ana ture juna,

Bata ganin komai sai hayaqi da tsananin hasken wuta dake Kama mutane Tana kashe idanuwanta ga wani irin Zafin azabar da basu taba Ji ba dan haka ja da baya ta fara Tana wani irin Ihun kiran GHAZ.

Gadan gadan kusrawa sukayo bangaren suna sarar mutane tako ina Ana gudu da Ihun mafi munin tashin hankali.

Bude baki tayi Tana sake yin baya da sauri Tana kokarin ambatar GHAZ data hango yana fitowa gurin da gudun shima dauke da wasu yara qananu guda biyu duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login