Showing 84001 words to 87000 words out of 121560 words

Chapter 29 - HAYATEEM Hausa Novels By Mamuhgee.txt

10 Dec 2025

3757

kebance hankali kwance da nutsuwa,

Basu taba damuwa da komaiba a yanzu da komai na masarauta tinda komai baayi dasu sun koma kamar babu su,
Sultan ya yafe wishmah bata ma cikin masu zuwa tiraka tin shekarun da suka gabata hakama babu wata hidimar dake tasowa ta fito sbd yanayinta,
‘Danta da ake tinanin matsayinsa a Masarauta shima baya nan dan haka basa lissafi Sam idan ba tozartasu zaayi ba baama ambatar su dan haka suka zama bangaren dayafi kowane bangare shiru da rashin hayaniya,
Tenya tini ta rasa matsayinta sbd anrufe karban imebeti dan haka Kai tsaye ta koma tamkar yaya kuma jakadiyar wishmah da LEUL da babu ranar dawowansa.

Tinda NUAB ALMAZZ yabar qasar boyem tsawon shekarun sultan YASAR baitaba maganarsa da kowa ba kaman yanda bai taba Nemansa ba hakama NUAB din kansa bai taba Neman mahaifinsa ba sbd sun rabu Akan zazzafar zuciyar dake cin kowannesu ta jini daya dake yawo jikinsu,

NUAB ya tafi da Wani irin ciwon da har abada bazai barsa ba wato ciwon ganin idonsa yanda mahaifinsa ya wulaqanta masa mahaifiya batareda tinani da tausayin ciwon datake rayuwa a cikinsaba,

Ya tozartata ya bawa duniya da dabbobin dake duniyar harma da ‘yayan dabbobin tozartata,

Littafin tarihi ya buga sunanta a matsayin daba kowa ba face mistress din da batada kowane irin muhimmanci da daraja a Masarautar da a gurinsa takarmin Ammin tasa ya fita daraja a idonsa da zuciyarsa,
Duka wannan bai isa ba saida ya rabata da ‘danta tareda saka dokar karya taba dawowa masarautar saiya gama karatunsa duk sbd a quntata rayuwarta…..

Da wainnan abubuwan waye Sultan din da zaiyi fari a zuciyarsa?
Bayajin laifin mahaifiyarsa ne data zo a matsayin imebēti zuwa wishmah dan haka babu Wanda duniya ya isa ya wulaqanta masa uwa batareda ya takasa ya shayar da nasa dabbobin jininsa ba Bayan mahaifinsa Wanda shima daraja ce da girmansa na uban dayayi cikinsa aka haifesa yake ci amma kaf boyem babu Wanda bazai iya tara jininsa a pool yayi wanka dashiba indai Akan wishmah AYANAH GHAZ ne.

Bayan gama karatunsa sultan dayake biye da kowane irin motsinsa a rayuwa jiran dawowansa ya fara yi sbd ya zama abinda yakeson ya zama din wato mai cikakken tarin ilimi da rashin tsoro da Izzar dake yawo jininsa amma ga mamakin sultan mai girma NUAB ALMAZZ babu boyem a ransa ya shafeta kwata kwata har abada bai niyar dawowa dan babu ita a ransa ya cire,
BOYEM bata cikin abinda yake da shirin dawowa a tsari da qudirin rayuwarsa mai karfi daya shirya.

Wata irin rayuwa mai karfin gaske da power data fara saka zuciyar sultan nauyi NUAB ALMAZZ ya fara ginawa a Russia wadda ta fara bayyanar da irin karfi da power din dazaiyi wadda hakan zata ma iya zama hadari da boyem sbd babu ta yanda boyem zata zama Abokiyar gaba ko fada da ‘dan daya fito daga jininta.

A zuciyar NUAB ALMAZZ ya jima da goge boyem a rayuwarsa dan kuwa tabbas baida niya ko raayin komawa har abada aransa,
Baida kowa da komai da zai sakasa komawa Bayan Amminsa wadda yakeda kudirin daukota ya dawo da ita hannunsa itama tabar BOYEM kenan har abada,

Duk Wanda yake duniyarsa yasan alaqa daya ce ta rage wadda ta liqesa da Masarautar boyem wato mahaifiyarsa dake hannun masarautar haryanzu,
Buri da babban qudurinsa dazai qarasa yanke masa boyem a rayuwarsa shine Amminsa ta kasance a hannunsa to daga ranar ko sunan boyem bazai sake bayyana a cikin sunansa ba bare wata bayyananniyar alaqa…..

Sultan YASAR ya dade da sani da fahimtar hakan daga NUAB ALMAZZ dan haka shima yake a shirye tsaf da jiran wannan ranar da zai tinkari boyem da buqatan mahaifiyarsa wadda shima a nasa bangaren babu abinda har abada zai sakasa barin AYANAH GHAZ se mutuwarsa amma duk da hakan babbar dama ce daya tak Allah ya basa Akan ‘dan cikinsa daya zama Zakin da duk abokan Huldarsa da jamaar sa suke shakkar datake tamkar Sarkin dayake kere sarakunan gaske dan haka yana nan yana jiran ranar da dansa zai nemesa Akan hakan Bayan shekarun da suka dauka babu huldar komai a tsakaninsu.

**********
GHAZ VILLA
No 1148 Arbat Moscow Russia

Securities ne zagaye da villa din jefi jefi sbd security room din dake gefen gate din shigowa villa din a ciki suke bin security cameras din villa din da kallan tsaro akai akai Wanda hakan ne ya saka jefi kadan ne na securities dake zagaye da gidan kuma basada kowane irin barazana da suke fuskanta ko hadari dan haka duka securities din dake gate dana security room basa cikin hayaniya ko daya dan wannan tsari ne da dokar aikinsu da maigidansu baya buqata ko kadan wato hayaniya da tashin hankali dan hakanne koina na villa din tsit yake komai a natse ake yinsa ake kuma aikatawa,

Tin daga securities dake villa din har maids da cook da Madame din da kula da maaikan Vilar babu Wanda ba zallar nutsuwa ce yake aiki da ita ba sbd villa ce da babu inda ake buqatan garaje ko gaggawa a cikinta,
Villa ce da kaf maaikatanta sukeda ilimi me kyau da iya aiki dashi dan baa buqatan kowane aiki da babu ilimi a cikinsa,
Villa ce da duk Wanda yake cikinta yakeda yanci da sakewa a cikin masu aikinta amma kuma hatta takawansu a tsari da ilimi sukeyinta ko a gurin aikin nasu dan hakanne duk wani mai aikin GHAZ villa nutsuwansa ta musamman ce duk da akwai lokutan da suke sakewa a tsakaninsu suyi raha da dariya da sakewa sosai amma idan mai villa din kanta yana gida atmosphere din na musamman ne,

Kudi da rayuwa me nutsuwa da tsaron da yake tabbatar musu da sun gama samun Saar rayuwa duk wani maaikacin villa din suke samu Wanda ya saka suke sake Jin babu wata rayuwar gata data fi musu zama masu aiki a karkashin NUAB ALMAZZ har qarshen rayuwarsu,

NUAB ALMAZZ me GHAZ villa da GHAZ Empire gabaki dayanta dake buga lokaci da daukaka a qasar da wajen qasar harma da qasashe da dama a bangaren harkar business da kuma qera jirage,

NUAB ALMAZZ Wanda yake cikin shekarunsa na daukaka da suna ya tsayu ya kafu ya kuma kafar da duniyarsa da babu Wanda zai iya girgizata idan ba Allah daya kafasaba,
Tarin dukiya da daukaka da arzikin dayake nuni da shi din jinin boyem ne ba matsalar datake gabansa bace dan kuwa ya tara dukiyar da Bayama lissafa wa hakama babu ta yanda zuriar sa shima zasuyi talauci har qarshen rayuwarsu insha Allah dan kuwa Allah ya tsaya masa Akan kowace huldarsa da businesses nasa,

Shi din dan business ne kuma shugaba ne na tsayayyun matasan da basu da gata harm da qananun yara maza wainda da uwansu sun rasa iyaye sun fada wata rayuwar da batada kyau,

Bayan zamansa babban tsayayyen business tycoon a qasar da wasu qasashen kallan riqaqqen mafia boss ake masa wato shugaban yan taadda sbd kasancewansa jarumin daya zama cikakken gatan duk wani dan taadda da rayuwarsa ta lalace kuma ya zame musu tamkar uba yana kawo sauyi a rayuwarsu ,

NUAB ALMAZZ ya zamo uban marasa gatan da rayuwarsu ta lalace ne sakamakon Tsintar matashin da aka kashewa uwa da uba da Kanwa aka cinye masa gadonsa duka sbd son zuciya irin ta dangan mahaifinsa sanadin hakan ya fada harkar taaddanci mai karfi a haka aka kamasa aka shiga kotu dashi aka yanke masa shekaru biyar gidan yari tin yana da Sauran kuruciya,

Shekaru biyar yana fitowa gidan yari NUAB ya daukesa ya tsayawa rayuwarsa tsaf saida ya tabbatarda ya samu adalcin daya kamaci iyayens da basa duniya.
#MAMUH
#LEUL BOYEM

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

49
Tin daga wannan lokacinda ALEEY KUAS ya zama babban yaron da babu kamarsa a gurin NU'AB Almazz,
Aleey ya sadaukar da rayuwarsa ga kowane hukuncin NU'AB ALMAZZ da zai iya sadaukar da rayuwarsa ya bada ita batareda kowace irin second tinani ba indai Akan NUAB ne,
NUAB ya Inganta rayuwarsa ta hanyar sakasa ya qarasa karatun da bai qarasa ba ya hada takardunsa ya zama cikakken mutum da ayanzu ilimin sa yake daukan businesses da mahaukanta kudin da bai taba tinanin a rayuwa zai taba iya ko lissafowa a mafarkinsa ba,
Ya tsayu ya kafu a cikin manyan businesses na qasashe daban daban yana tsayuwa a gaban mutanen da bai taba tinanin zai iya ganinsu idan ba a news paper ba ko tv amma a yanzu a gabansa yake ganinsu tareda boss dinsa harma kusan shine yake gabatar da abubuwa da dama na haduwar da businesses din dan haka rayuwarsa tayi Wani hawa da saman da badai masu qananun matsayibama sedai manyan duniya duk ta Sanadin Ubangidansa da ko rai yace ya dauka to tabbas bazai qara mintina biyu batareda ya cika umarnin ba,

Duk abinda NUAB ALMAZZ yake so ko menene shi aleey yake so ba me kyau bane kuwa hakama abinda NUAB ALMAZZ yakeso to aleey yana sonsa da dukkanin rayuwarsa dan hakanne burin Ammi ya zama qudurarren burinsu da dukkanin Wanda yake qarqashinsu na Neman Abaas a duk duniyar dayake koda hakan na nufi zasu juya nahiyoyi da dama.

Tin daga kan aleey NUAB ALMAZZ ya zama gatan kowane mara gatan,

Sama da daruruwan yan taaddan qasashe daban daban da kaddara ta sakasu fadawa taadanci da shaye shaye NUAB ya tallafi rayuwarsu ya sakasu jikinsu ya kawo sauyi a rayuwarsu suka zama Yaransa cikin sauyawa zuwa masu abin yi,

Duk Wanda bai gama karatu a cikinsu yana sakasa ya qarasa karatunsa ya fara aiki a qarqashin sa wainda kuma Sam basuyi karatun ba suma aikin da zasu iya a duniyarsa yake sakasu dan haka kusan duka wainda suke a qarqashinsa ire irensu ne amma kuma ilimin sosai suke samu dayake ratsa su sun zama yan business din gaske da kamar da saa kowannesu yake yawo dan kuwa tako ina cigaban GHAZ empire ake samu,

Tamkar zakuna suke a cikin duniyar manyan business tycoons sbd tsananin ilimi da saarsu harma da qwanjinsu dayake bayyane Akan zasu iya komai akai ubangidansu da ayanzu kusan koina duniya ta sansa sbd tarin yan amanarsa kuma yan taaddansa dan duk da sun sauya rayuwa sun taka matsayin cigaban rayuwa wannan rayuwar ta rashin sauki da rashin tsoro yana nan a tattare dasu,

Ilimi da kudi tareda power da suke samu daga shugabansu NUAB ALMAZ ya qarawa rashin tsoro da zuciyarsu kafin gaske da basa shakkar komai da kowa a duniya idan ba shi dinba da babu Wanda baya sauke masa Kai idan ya fito sbd girmamawa dan shine ya jasu cikin jikinsa da dukiyrsa ya maidasu mutanen da kowa yake shakka a yanxu dan haka duk da wasu sun girmesa wasu kuma tsarin shekarunsa ne da wainda ma ya girma gabaki dayansu a uban dayafi kowane uba daraja kimar da zasu iya tasa yaqin duniya akansa suke kallansa,

Tsoronsu akeyi shakkar su akeyi sosai sbd uba gidansu yana dukiyar da suke juya duniyar yanda suke so,
Kusan dukkanin yaran nasa babu Wanda baiyi zaman gidan yari ba sbd rashin adalcin sharia amma ayanzu sun Kai sun taka matsayin da koda a gaban mutane zasuyi Kisa babu Wanda zai dago ya kallesu amma kuma ba irin rayuwar suke yiba yanzu dan kuwa business suke me tsafta da class da tsari amma duk da hakan kallan yan taadda masu karfin gaske ake musu Ana tsananin shakkarsu.

Yaransa sune yan uwansa,
Sune danginsa,
Sune yake shiga cikinsu yayi nutsuwa ko babu hayaniya sune ahalin da suka cike gurbin ahali da dangin da baida kaman yanda shima shine ya cike gurbin iyaye da yan uwan jini da suka rasa dan haka Bayan komai akwai kauna mai tsananin karfi a tsakaninsu dasuke wa juna su dashi,

Iya kafuwa da tsayuwa GHAZ empire ta tsayu,
Manyan qasashe da Masarautu ne da manyan tycoons na karshe ne abokan huldarta dan hakkanne NUAB ALMAZ yayi suna da fice a duniya da yake da Wani irin matsayi da girman gaske a idanuwan duk wani marasa karfi da galihu,
A cikin abokan huldarsa kuka shi din Zakin dayake yawo ne da saa a rayuwarsa,
A gurin tarin yaransa da uwansu ya kere na Masarautu da dama shi sarki ne da a duniyar nan idan yace A to A dince idan yace kuma B ce to dince kawai ko uban kowa ya yadda ko kada ya yadda,
Shi sarki ne da ko masarautar ubansa yace su tayar bazaa kwana ba saisun saka jini gudana a cikinta ta shefe kaman baayi kowa a cikinta ba.

Duk suna da tambarin da ake masa Akan zamowa gatan yan taadda bai taba bawa ko yan jarida daman fira dashi ba Akan hakan sbd baya buqatan yiwa kowa a duniya bayani kawai dai yasan yana samun feelings na nutsuwa daga sauya musu rayuwan da yayi hakama kusan yanajin radadin daya sauya rayuwarsu zuwa ga illa sbd yasan ciwo da radadin abubuwa ire iren wainda suke tinda shima tin da qananun shekaru aka rabasa da tasa uwar da haryanzu baiji dumin jikintaba taji nasa,

Fushi ne a zuciyarsa da haryanzu bai huceba,
Zafi ne a cikin kansa da haryanzu wutarsa bata mutu ba,
Qiyayya ce me karfin gaske dayake wa jamaar Masarautar BOYEM da haryanzu bai sauka ba sai ranar da mahaifiyarsa ta shigo hannunsa ne kadai komai zai iya fara sassautowa.

Duk wani Zafi da fushinsa a zuciyoyi da kan Yaransa take ci batareda sun San menene a ransa ba dan haka iya gane menene zuciyarsa amma dai tinda suka sansa sukasan da wannan wutar dake ci a cikin idanuwansa dan haka tasu zuciyar da ruhin basu taba Dena ci da wutar Zafi ba da jiran kowane umarnin sa Akan koma menene ba.

Duka wannan rashin tsoron da rashin shakkar da GHAZs kaman yanda ake ambatar su sbd sunan komai nasa daya mallaka a rayuwarsa sunan mahaifiyarsa ne amma iya GHAZ din suke dashi sun samo izzar hakan ne daga ubangayyarsu LEUL NUAB ALMAZZ da babu sunan shakka ko tsoro bare fargaba a cikin littafin rayuwarsa datake tsaye cak kaman mashi,

Komai Zafi da rashin saukewa kowa Kai a duniya idan ba shi ba basu kamo sa ba ya dame dukansu ya shanye babu Wanda kaf duniyar baya iya dagowa ya kalla da idanuwansa idan ba iyayensa mata ba sai kuma ubansa dabai San yaya zai kallesaba tinda basa tare shekaru.

Izzar dayake bugawa da iko tareda taqama da tsananin power dayake Juyawa da ita sun hadu hade ne da jinin dayake yawo a jikinsa na sarautar BOYEM,

Duk wannan shekarun yayi su ne yana jiran ranar da Amminsa zata furta masa ya taho ta janye kamalanta na kada ya dawo,

Daga ranar da Amminsa ta furta masa tana son zuwansa to tabbas a ranar bazai kwana ba sai jirginsa ya saukesa qasar BOYEM hakama bazai Baro ba saiya tabbatarda uwarsa ta dawo hannunsa.

Wannan kiran shine kiran dayake jira daga mahaifiyarsa kowace daqiqa dan haka aleey ma koyaushe a shirye yake tsaf da jiran kiran ya shirya saukar su BOYEM da me BOYEM din gabaki dayanta duk da baya buqatan mulkinta.

Villa dins datake kamar gari guda kusan fiyeda rabin Yaransa dake Russia suna cikinta bangare daban daban Sauran yaran nasa kuwa suna qasa daban daban inda yake da companies dan haka villa din akwai tsaro mai tsari da rashin hayaniya,

Duk Wanda yake karkashin GHAZss baya cikin wahala ko talauci Bayan kwanciyan hankali da rashin hayaniya sai zallar iko da rashin tsoro dan Sam baya kaunar lusari ko sakaran namijin da bazai iya tsayawa namiji ya cire tsoro a zuciyarsa ba a karkashinsa dan hakanne ya kasance duk Wanda yake karkashin GHAZss babu Wanda ba tsayayyen namiji mai zarra ba hakan ne ya saka koina suke kwarjinsu daban yake bare ace uban kwarjinin nasu na guri.

*******
Hayaqi ne da qamshi yake fitarwa me nutsuwa yake cike da gauraye toilet din  mai tsananin girman da koina daukan ido yakeyi sbd kyallin tsaddan luxury vinyl tiles da komai na Duravits toilets dayake tsare a toilet yana saka jikin duk Wanda ya kalla mutuwa,

Qarar shower ce yake tashi a cikin luxury steam and sauna shower room dake cikin toilet alamar wanka akeyi da ruwan dumin da hayaqinsu yake bada qamshin shower gel dinsa na the Noir,

Tsawon mintina a ciki kafin ya kammala
Hannunsa me tsananin haske da lafiyar fata ya bude kofar kafin kafafunsa suka fito ya fito gabaki dayansaa ruwa na gangarowa daga lafiyayyar farar fatarsa da Hutu da lafiya kawai take bayyana wa tana daukan ido,
Ruwan ko zama basa yi a farar fatarsa Kal sbd santsi da lafiyarta gangarowa sukeyi kawai suna sauka qasa.

Gurin da towels suke a Jere a tsare kaman bundles na kudi ya nufa ya miqa hannunsa daya ya dauko daya ya daura a kuqunsa kafin ya sake daukan daya a natse cikin asalin nutsuwan sarauta dake yawo a jininsa ya Dora a kan gashin kansa dayake tamkar na mahaifiyarsa yafara gogewa ahankali kafin ya fito sanye da fararen soft sole bedroom slippers yana nufar makeken dresser mirror din dayake closet dinsa mai girman dayafi na daki biyu dan kuwa tarin sutura ce a Jere da basada adadi babu kalar designer din data amsa sunanta da babu a gurin tin daga kan bangaren agogunansa da suke bugun mahaukatan dollars har zuwa kan takarman sakawansa da suke cin manyan kudi da bangaren wandunada shirts da suits da underwears hatta ties na wuyansa da socks dinsa kowanne da bangarensa daban inda aka jerasa.

Ga turaruka suma da pins da combs nasa suna kowanne baida adadin number dan babu abinda ake siya kadan hakama akai akai ake qaro wasu Ana jibgawa.

Cikin nutsuwa da rashin hayaniya ya shirya tsaf a cikin navy blue loro pianas vicuña polo shirt da Michael kors trousers fari tas ya komai na jikinsa na fidda wani tsadadden qamshin Gaultier elixir na yana gauraye niimar duk inda ya wuce da inda yake tinkara a cikin sanyi.

Palonsa na hutawansa y wuce Kai tsaye cikin nutsuwa zuwa palon da dining room dinsa yake inda zaiyi breakfast da aka gama cike dining din a tsare da aji,

Tin daya doso qamshin sa ya sanar da aleey fitowan sa dan haka ya miqe daga Zaunen dayake riqe da iPad me girma dayake wani aikin report da aka turo daga kamfaninsu dake Brazil.

Ajiye iPad din yayi yana dago Kansa ahankali ya sauke Akan hanyar da NUAB ALMAZZ din daya fito kwarjinsa da Kyansa dayake sake cika idanuwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login