Showing 9001 words to 12000 words out of 121560 words
mata
Bude bakinta batareda maganarta takai ga fita ba wani irin mashi mai tsinin gaske ya keta wuyanta ya shiga makoshinta ya fita ta baya.
Cak GHAZ daya kawo daf da ita ya tsaya yana cin wani irin birki idanuwansa a kafe sbd mummunan tashin hankali da firgici mafi munin rayuwansa.
Sakin yaran hannunsa yayi yana tarota da sauri ta fado jikinsa babu rai idanuwanta a bude…..
Jininta ne ya fara gangarowa daga wuyanta zuwa tafukan hannunsa dake tallafe da ita,
Mummunan rawa dukkanin jikinsa keyi daya kasa riqeta din ta zame daga jikinsa.
Rufewa idanuwansa sukai baya gani amma a hakan ya miqe ya sunkuceta ya Dora a kafadarsa ya Kama hannuwan yaran da hannunsa daya suka bar gurin da wani irin mummunan tashin hankali sbd gari kam an gama cinyesa wutar ta kawo gurin su sosai dan haka yake tsananta gudu.
Gida ya nufa da tsananin tashin hankali sabo sbd dai dole yabar garin da yayansa sbd kowane lokaci zaa iya kashe su ko kamawa sbd wutar harta fara shigowa gidan nasa sosai.
Yana shigowa ajiye gawar Amma yayi daga gefen dakin ya fizge rigarsa ta sama me dan kaurin saqi ya rufeta da ita.
Ihun shigowan mutane dake Neman hanyar tsira ne da Ihun wainda wuta ke ci ne ta cike gidan nasa dan haka da gaggawa idanuwansa jajir fuskansa duk jinin Amma daya dauko koina ya bata fuskansa hakama hannuwansa da jikinsa koina jini ne.
Tura kofar dakin yayi da karfi Wanda ya saka dukkaninsu miqewa tsaye cikin tsananin firgici da tsoro,
Nurat ce ta fara cewa ‘ABAA’ cikin mummunan tashin hankali Tana nufosa da gudun gaske ta fada jikinsa.
Abaas ya miqawa hannu ya Kama ya janyosa hakama Zuhrah koina jikinta wani irin mazari ya dauka ta fara ja da baya tana fita hayyacinta,
Ayanah ma jinin jikinsa da fuskansa take kallo Tana kasa hawaye ma sai rawan jiki da jajayen ido,
Fizgo Zuhrah Abaa din yayi yana cewa Ayanah
‘Muje,ku fita da sauri,Kuyi sauri ba lokaci’
Daqyar Ayanah ta iya bude bakinta daya bushe qayau sbd masifar tashin hankali tace
‘Abaa Amma bata nan,taje nemanka,
Ina zamu ba tareda ta dawo ba?
Qin kallanta Abaan yayi ya Kamo hannunta itama da karfi ya fito dasu Sauran mutanen da zasu samu kubuta tareda su suna biye dasu.
Nurat dake da kokarin wucewa kaman ance ta juya idanuwanta suka sauka akan gawar Amma dake shimfide fuskanta kawai ne a rufe abin hannunta ta gane take ta tsaya cak tareda cewa ‘AMMA’ cikin wani irin sanyi da mutuwan jikin kasa yadda.
Ayanah ce ta kalli gurin da sauri itama Tana Jin jininta na Neman kafewa,
Abaas ne ya kwace daga riqon mahaifinsa ya nufi gurin da gudun gaske yana isa ya yaye rufar take ya some a gurin,
Nurat ma silalewa tayi a gurin some sbd kasa dauka da zuciyar su tayi
Ayanah ma salalewa qasa tayi zuciyarta na Neman bugawa ganinta yana disashewa Abaa yayi saurin dagota da karfin gaske shima zuciyarsa radadin gaske take kaman zata Dena bugawa amma sbd su bazai iya karyewa a lokacin ba sbd kubutar da rayuwarsu daga garin,
Girgizata yayi da karfi tareda ambatar sunanta yana danne abinda yake Ji a kirjinsa na bugawan zuciyan dayake kokarin samu yace
‘Ayanah karki karye ke uwa ce a yanxu da babu Amma,
Kece zaki zama garkuwan yan uwanki,
Kece Amma yanzu,
Kece madubi fitilar da zata haske hanyar da rayuwanku zatabi,
Karki karye kiyi jarumta ba yanzune lokacin kukan rashin Amma ba,
Ki dake zuciyarki ki kubutar da yan uwanki daga nan Allah ya Riga ya karbi Amma karki Bari burinta na kubutar da rayuwanku ya tashi a banza.’
Wata irin jijjiga jikin Ayanah keyi taba girgiza kai kuka me tsananin gaske na zuwar mata tace
‘Abaa bazan iya ba,
Abaa ina buqatan kai da Amma a gurin zamtowa uwa garesu,
Abaa kune hasken rayuwanmu,kune garkuwanmu,
Abaa kune rayuwarmu tayaya zan iya babu dayanku?’
Rungumeta yayi jikinsa da karfin gaske yana rintse idanuwansa da a Karan farko rayuwansa suka zubewa hawaye ya kasa cewa komai yana sake qanqameta a jikinsa Tana wani irin kuka me tsananin karfin gaske hannuwanta na kakkarwa.
Sakinta Abaan yayi ya janyo Zuhrah datai mutuwan tsaye bata ko motsawa jikinsa itama ya qanqameta yana hanasu ganin hawayensa.
Sakinta yayi sbd da alama an shigo gidan nasa dan haka Abaas da Nurat ya zubawa ruwan dake gurin da suka fara daukan dumin wuta suna bude ido ya fizgesu tsaye
Da gudu Ayanah tazo gaban gawar Amma ta saka hannu ta shafe idanuwanta suka rufe hannuwanta na tsananta kakkarwa ta saka hannunta cikin na Amman ta zare abin hannunta na zallan azurfa Wanda yake dauke da sunan Amma din tayi mata addua hakama Sauran adduar sukai mata a tsaye Abaa ya fizgesu suna kuka me tsananin gaske na tashin hankali.
Turasu wata qaramar hanya dake baya yayi cikin sauri yana waiwaye sbd yana jiyowa sun shigo gidan da yawansu.
Kirjinsa wani irin radadi da ciwo yake masa Wanda yakejin bazai iya Nisaba amma ko yayane zai tabbatarda ‘yayansu sun tsira,
A bayansu yafara Jin takunsu me karfi da tsanani dan haka cikin sauri ya juya ya kalli hanyar kafin ya kalli gabansu da akwai Sauran tafiya kafin su bulla daji harma su isa bakin ruwa gashi sunada yawa fa qananun yara.
Tsayawa yayi tareda kamo hannun Ayanah ya kalleta taje dukkaninsu suka tsaya cak kowa ya zuba masa ido,
Ganin irin kallan dayake mata ya saka Ayanah fizge hannunta tareda ja baya Tana rintse idanuwanta Tana girgiza kai da karfi Tana fita hayyacinta gabaki daya.
#MAMUH
#SLAVERY
#ROYALTY
#BEST LOVE
#GHAZ
#BOYEM
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070
7
*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********
*************
Matsota Abaa yayi tayi saurin sake yin baya da karfi tana fasa kuka me karfin gaske numfashinta na sarkewa.
Abaas da Zuhrah da Nurat kuwa gabaki daya riqe Abaan sukai kowannesu jikinsa na rawa suna tsananin rokonsa akan ya biyo su su tafi karya sauya hakan.
Zafafan hawayensa ne masu tsananin zafi suka Riga akan fuskan Abaas dake jikinsa ya sauke Kansa yana banbaresu daga jikinsa yace suyi sauri subar gurin shi zai rufe hanyar kafin kusrawa su qaraso sunyi nisa zai biyo su daga baya.
Girgiza kai dukkaninsu suka hau Ayanah kuma tsananta kukanta yayi tana Jin kirjinta na wani irin radadi me tsananin gaske.
Harbin mashi suka fara Ji tako ina ba tsammani take suka fara gudu dukkaninsu wasu kuma kibiyar na samun su dan haka suka shiga firgici me firgitarwa suna Neman rarrabewa amma Abaa ya kasa barin hakan ya taresu ta baya suna gudu me tsanani batareda sunsan inda suke jefa kafafunsu ba.
Biyosu kusrawa sama da arbain sukai suna harbosu da kibiya tako ina suna wani irin ihu dake girgiza duk wani me sauraro.
Duhun dajin suke bi suna gudu sosai Wanda kusan da yawan wainda suke tareda su suna Jin yanda suke mutuwa amma babu daman tsayawa wa hakama Abaa cikin tsananin tashin hankali ya hanasu juyawa su waiwaiya baya yace suyita gudu karsu tsaya.
Cikin gudu da tsananin ciwon dayakeji a kirjinsa na tsananta yace
‘Ayanah duk tsanani kada ku tsaye kuyita gudu harsai kun tsira’
Sanyi jikinta yayi zata juyo cikin karfin hali da daga murya yace karki juyo Kuyita gudu Ayanah.
Muryansa da bataji daidai ba ya sakata juyowa da sauri idanuwanta suka akan kibiyar data bullo gefen kirjinsa ta bayansa da aka harbo
Tsayawa zatai Ya fizgeta da karfi yana turata yace
‘Ku tafi karku tsaya,
Ku tafi Ayanah,
Ki tafi dasu karki Bari kowa ya juyo bare tsayawa’
Kasa wa tayi ta juyo tareda riqe hannunsa suna gudu tare yana turata daga jikinsa zuwa gaba yana cewa ta tafi ta kula da yan uwanta ta tabbatarda sun tsira sun kubuta sun Gina rayuwa me kyau.
Fara gazawa yayi dan haka turata da karfin gaske tana kokarin dawowa ya dago idanuwansa jajir yace
‘Ban Aminta ki tsaya ba bare dawowa gareni ki tafi Allah zai zama gatanku insha Allah,
Burina burin Ammanku shine ku tsira dan haka Ayanah ku tafi ku cika mana wannan burin ku rayu,
Duk rintsi ku hada kai karku rabu da juna’
Sake turata yayi sa karfi tana qara riqosa amma ina jini sosai yake fita a kirjinsa harma da bakin sa take kafafunsa suka kasa daukansa ya durqushe a gurin ta kira sunansa da karfi tana kokarin durqusawa Kaman daga sama taji bayanta an riqeta.
Cikin tsananin azaba ya dago idanuwansa ya kalli Asamah wadda bata hayyacinta sbd kukan baqin ciki da danasanin datake ciki tareda fatan tayi mummunan mutuwan data jawa rayukan dake ANJOM.
Daqyar ya bude baki jini na fita sosai yana kallan Asamah yace
‘Ki tseratar dasu,
Karki bari kowannesu ya tsaya bare dawowa ANJOM ‘
Janta Asamah tayi tana Hana su Zuhrah dawowa suka fara ihu ganin halinda Abaansu ya shiga ransa na kokarin barin kirjinsa sbd wani irin jinin dake fita bakinsa.
Kaman daga sama sai ganin Mutum biyu sukai akansa ba Imani a tare suka soka wuqa biyu a wuyansa idanuwansa na kan yayansa dake Ihun gaske suna Neman zarewa sbd mummunan tashin hankalin sheda mutuwan mahaifinsu akan idonsu.
Asamah cigaba da turasu tayi suka kutsa dajin suna tsananta gudu hannun Ayanah yana cikin na Abaas hakama Nurat da zuhrah suma hannuwansu na riqe dana juna.
Biyo su akai wannan Karan an Dena harbin da alama da rai ake sonsu.
Kuka sosai sukeyi suna tsananta gudunsu Banda Ayanah datake Jin zuciyarta na kokarin nema bugawa hakama idanuwanta basa ganin komai jefa kafa kawai takeyi.
Dukkaninsu sun kasa yadda a awannin da basu wuce uku ba sun rasa iyayensu duka cikin dare daya a Masifa da mummunan kaddara daya,
Neman sarewa sukeyi amma Sam Asamah ta kasa Bari saima hanya data sauya musu sbd an kusa kamosu dan haka cikin wani irin qazantaccen rami ta turasu suka shige suka boye tareda sakina wadda take riqe da Zuhrah a yanzu.
Suna shigewa Asamah ce ta saka hannuwanta ta toshe bakin Nurat da Abaas ita kuma sakina ta rufe na Zuhrah sbd yanda suke kuka suna wata irin jijjiga.
Ayanah ta kasa komai ta koma tamkar marasa hankali da kwakwalwa kwata kwata dan haka batace komai bare kukan Wanda ya kasa fitowa tsabar muni da girman tashin hankalin datake ciki.
Suna Ji kusrawan na wucewa da gudu da karfi suna ihu me ban tsoro amma basu motsa ba har saida suka Ji sun gama wuce kafin Asamah ta zare hannunta a Bakinsu Sai a lokacin Nurat ta fasa wani irin kukan daya saka Idon sakina fara zubar hawaye
Asamah kuwa kukan itama ta fasa me tsananin ciwo tana rungume Zuhrah dake jijjiga kaman me wani ciwo.
Rintse idanuwa Ayanah tayi tareda sunkuyar da kai tana fasa kuka mai tsima zuciya da girgiza kowa.
Babu Wanda yace komai a cikinsu dukkaninsu kuka ne sukeyi mara dadin Ji bame rarrashin wani sbd kaddarar tayi musu nauyin da zuciyarsu take kasa dauka,
Ayanah hannu ta Dora Akan kirjinta tana duka kukanta na sake tsananta sbd kirjinta ya toshe Jin takeyi kaman ta mutu tabi iyayenta.
Har asuba tayi gari ya fara haske suna cikin ramin idanuwansu sunyi wani irin kumbura da ja babu me iya dogon motsi sbd mutuwa da jikinsu yayi rayuwan gabaki daya ta fice musu arai sbd basu San ta ina zasu fara rayuwa babu daya daga cikin iyayensu ba,
Basu San koinaba,basu taba fita ANJOM ba tinda aka haifesu,
Basu saba da kowa ba Bayan junansu fa iyayensu,
Basu taba jagorantar lamarin su ba da kansu komai iyayesu ne ke tafiyar musu dashi,
Abinci ma basu taba Cinsa batareda iyayensu ba,
Ayau dare daya sun tsinci kansu a mummunan kaddarar da basuma San ina zasu ba,
Gurin wa zasu?
Tayaya zasu fara rayuwa?
Yaya rayuwa zatai dasu bare Wanda zai tsaya ga lamarinsu dan haka Ayanah kukanta ke karuwa sbd batasan ta ina zata fara zamowa uwa da iyayenta suke fada Akan kannanta kawai dai abu daya ta sani a yanzu zata iya rasa rayuwarta akan wani abu ya samesu sbd sune rayuwanta.
Sakina ce takeda dan Sauran kuzari a jikinta sbd itama Asamah a cikin mummunan yanayi take samun tabbacin mutuwan mijinta tin shekarun baya hakama a Daren itama daqyar Tasha sbd umarnin a kasheta da shugaban kusra ya bayar.
Fitowa sukai daga ramin babu me gani sosai sbd kumburin ido.
Sakina ce ta Kama hannuwansu daya bayan daya suka gama fitowa suna kallan filin dajin da hayaqi yake tashi sbd wutar garin da har lokacin ci takeyi sosai hakama koina yayi tsit ko kukan dabbobi babu.
Hanya suka jijjuyawa suna Neman gurin bi sbd sun riga sun sauka daga kan hanyar da Abaa ya dorasu da zata kaisu inda yace kuma bazasu maida kansu hanyar komawaba bare su sake hawa hanyar daga can.
Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangaro daga idanuwan Ayanah ta sake riqe hannun Abaas dake cikin nata gefe daya kuma Nurat na riqe da ita Zuhrah na riqe da Asamah suka Kama hanya ba tareda sunsan inda zasu ba suka cigaba da nutsuwa cikin dajin.
Tafiya sukeyi bame cewa komai ba kuma me kuzari dan haka har rana ta fara ketowa zafi na ratsa su ga babu me takarma a kafa dan haka wahala ta faro sako kai amma duk da hakan babu Wanda yace komai har lokacin.
Wuni guda sukai suna tafiya sai gab da magrib suka fara hango ruwa daga nesa dan haka suka dan sauke ajiyan zuciya kadan Sai a lokacin Ayanah ta kalli kafafun yan uwanta taga kowa kafarsa ya fashe sosai jini sukeyi dan haka tace su zauna su huta.
Guri suka nema suka zauna babu me kuzari a jiki,
Nurat da Zuhrah ne suka kwantar da kansu a kafadunta suna rufe idanuwansu hawaye masu dumi suna gangarowa daga ciki,
Abaas kuwa gefe ya zauna tareda sunkuyar da Kansa yana kafawa qasa jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumburi.
Har duhun dare yayi suna Zaune gurin salla ma a haka sukai da taimama ba ruwa,
Nurat ce me tsoron cikinsu dan haka duhu na qarawa hankalinsa yana sake tashi dan haka dole suka miqe a hakan suka sake bin hanya cikin hudun dare babu motsin komai koda kuwa na dabba ne daman hakan dajin yake shiru babu motsin komai gwanin tsoro da firgita.
Tafiya sosai sukai har dare ya sake tsalawa sosai karfinsu gabaki daya ya qare ga yunwa da azaba Zuhrah Amanta uku a hanya.
Duk wannan tafiyar da sukeyi suna maqale da juna sun kasa sake juna,
Fitsari Nurat tace zatai dan haka suka tsaya ta dan matsa gefe kadan ta durqusa tayi ta gama kenan tana miqewa taji Mutum ya cafkota gabaki dayanta batasan lokacinda ta fasa wani irin mummunan ihu me karfin gaske ba daya saka Sauran kusrawan dake gurin tahowa gurin da sauri suna ihun daya saka fitsari kufcewa Sakina.
Cikin mummunan tashin hankali da tsananin tsoro Su Ayanah sukayo gurin sedai Asamah da sakinah riqe su sukai da karfi suna hanasu tafiya sbd kada Ayi biyu,
Sama kusrawan su shida sukai da Nurat suna dariyar farin ciki suna tsalle tana ihu da wani irin kukan mafi tashin hankalin rayuwanta.
Kwacewa Ayanah ta fara yi tareda bude baki zata kwala kiran Nurat Asamah suka rufe musu baki take suka fara kokawan kwacewa sbd ganin zaa tafi da Nurat batareda an gansu ba dan haka Abaas ya bude baki ya kira sunan Nurat din karfi sbd sunfi son a tafi dasu dukansu koma inane da a dauke dayansu abar saura su rabu.
Cikin rashin Imani kuwa kusrawan suka juyo tareda biyo su Ayanah din wainda da kansu suka fito suna nufar Nurat da gudu suka rungume junansu su hudun suna fashewa da kuka.
#MAMUH
#ROYALTY
#BEST LOVE
#BOYEM
#BOYEM PALACE
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070
8
*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********
************
Wani irin kuka mai tsananin ratsa kunnuwa Ayanah ta fasa itada Nurat a lokaci daya suna rungume juna da tsananin karfin gaske jikinsu na wata irin rawa mummunan tsoron da basu taba shiga ba,
Abaas da Zuhrah ma dukansu kukan sukeyi suna rungume junansu gabaki dayansu kowannensu jikinsa kakkarwa yakeyi musamman Nurat datafi shiga matsanancin tsoron dayake Neman juyar da kanta ita data shiga hannun kusrawan,
Asamah da sakina ma qarasowa sukai da gudu suna kasa barinsu suka rungumesu kowannensu kuka yakeyi sosai sbd sanin rayuwa kuma ta tsaya musu daga wannan daqiqar.
Magana Nurat ke son yi amma yanda jikinta ke fizga bakinta na kasa budewa sbd bata hayyacinta gabaki daya yasa Ayanah dake wani irin kuka mai tsanani itama jikin na rawa sake qanqameta jikinta tana kasa maganar itama,
Hannunta daya ta saka ta sake qanqamo su Abaas da Zuhrah tana ambatar sunan Abaansu da karfi tareda Neman dauki daga ubangiji sbd bazasu iya rayuwan nan me cikeda tsoro ba basuda kowa a duniyar.
Wata irin dariyar Jin dadi me karfi da ban tsoro tareda firgitarwa kusrawan sukeyi suna zagaye su tareda wani irin tsalle kaman sunga nama.
Duk dan Adam din dazai