Showing 1 words to 3000 words out of 50455 words

Chapter 1 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2453

Compiled By Umar Dalha Funtua.


*_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*1*


_Bismillahir-rahmanirraheem_.


*B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,,

Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata,

Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki 'daya,

Ya rasu shida Mai 'dakinsa Fatima sunbar 'yaya hudu duka maza,,

Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa'da,
Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,

Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa
kowa dadiba.
yanada mata biyu inna hindatu da iya lami,

Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda 'yaya bakwai, _zayyanu, auwalu,
dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_.


Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu 'daya da baba malam
illai shi Yana da'dewa baiyi fadan ba,
Matarsa 'daya shi,mama salamatu Sai 'yaya biyar duk mata,hafsat, Amina, hajaru, zainab da

sumayya Kuma duk anyi musu aure.

Sai baba Yusuf Mai sanyin Hali da kawaici dakuma tsananin qaunar 'yanuwansa, shima
matarsa 'daya fatima da 'yaya biyu _*AYSHA*_ da nuratu.

Alh Bello shine qaraminsu Kuma fitnannensu Dan masifa da son kansa a fili yake sbd ya 'dan
taba yin arziki abaya Amma yanxu Babu shiyasa ko Abu ka'dan akai saiya maidasa babba akan
fitina da fa'dansa.
Matansa biyu mama bilki da umma sakina.,
'yayansa bakwai _ahmad, isah, Umar, abbakar Sai saudat Salma da husna_


Dukkaninsu a gida 'daya suke Sai dai kowa da shiyarsa Amma yaransu maza kaf 6angarensu
'daya hakama matan.

Asalinsu buzayen qasar nijar ne malanci yakawo mahaifinsu garin gombe harya gina gida
yazama mazauni.

Malamai ne kaf 'dinsu Kuma basuda wani aiki bayan malanta hakama ba wani arzikine dasuba
Sai rufin asiri.

A rayuwar gidan Sam basa auren na waje saidai atsakaninsu sbd yawa dakuma tsananin
kyamar wani yare daba nasuba na buzaye.

Qabilanci ne tsantsa acikin jinin kowane 'dan Adam dake rayuwa acikin gidan,
Basa qaunar ha'dawa da ko bahaushe bare wani yare har gwara Fulani.

Wannan aladace dasuka gado tun gurin iyaye da kakanni shiyasa duk kwa'dayi da maita ta
kyau da 'yayan gidan sukedashi ba'a tunkararsu da maganarso,

Qiyayyar dasuke fitowa suna nunawa ta rashin son ha'da zuria da wata qabila a qarara yake
Dan abin har tsoro da mamaki suke bawa na taredasu.


Yaran gidan kaf dinsu maza da mata ustazai ne kamilallu kullum jikinsu a rufe yake ruf ko
qafarsu baka gani fuskarsu ma wani sa'ilin suna rufewa idan zasu fita.,

Mazansu da matansu sun haddace alqur'ani akansu da sauran littafan addini.

Ka'dan ne daga cikinsu sukai karatun Boko sbd bai damesuba sunfi riqe addini shiyasa layin
gidan kullum acike yakeda motoci da mashina harda kekuna gurin 'daukar karatu a gidan.

Ayshah,husnah,saudat da Salma kusan sa'anin juna ne 'yan kimanin shekaru goma Sha takwas
zuwa Sha Tara.

A al'adar gidan mata basa wuce gaba da secondary aure suke musu Amma wannan karon
anbarsu Aysha sun wuce sbd ba'ayi Shirin aurensuba Amma antsayarwa kowaccensu da miji.

A university suke karatu yanxu suna two hundred level.,
Aysha medicine take karatu sukuma sauran gabaki 'daya Islamic sukeyi.


Yaya Umar shine Wanda aka ha'da Aysha dashi sbd sonta daya nuna yanayi qarara,

Ya Umar mutum ne Mai zafin Rai kamar iyayensu Dan kamarma ya zarcesu sbd baida hakuri ko
ka'dan ga saurin duka dayakedashi bayada kar6ar uzurinta ko ka'dan shiyasa kullum idan sukai
fira kwana kuka take sbd da fa'da suke rabuwa,

Sanyin halinta da sanyin jikinta tareda kasancewarta miskila Mara hayaniya shike wahalarda ita
ko acikinsu saudat bare gurin ya Umar.

Halin umminta ne ta 'dauko Zak harma ta zartata sanyin halin shiyasa mahaifinta da ummin ke
tsananin qaunarta da tausayinta sbd ganin kawaici da hakurinta sa6abin qanwarta nuratu dake
da masifa ba'a ta6ata ko ka'dan.

Aysha kyakkyawace Mai kyan jiki Dana fata ko acikin gidan tafisu hasken fata da kyau sbd
tafisu rashin son fita duk da dama kulle ake musu basa fita.




***********
Yau tun 6 na safe tafara shiri sbd anyi shifting lectures 'dinsu zuwa sabon site 'din university
Wanda bakowane course ake maidawa can ba gashi yanxu an rabata dasu husnah dansu
yanxu tsohon site suke.

Hakanan batajin dadin rabata dasu da'akai sbd batasan ya can 'din takeba,.

Tsaf tashirya cikin doguwar rigar atampha red Mai adon dark blue saita saka dogon hijab dark
blue daya sauka har qasa yanaja danko kalar atampharta ba'a gani bare qafafuwanta,
Jakarta ta 'dauka tareda ficewa taje tagaida iyayensu kowane 6angare kafin tadawo 'dakinsu
suka fito taredasu husnah.


A qofa suka hadu da ya Umar da ya Ahmad zasu shigo,

Har qasa suka durqusa su duka suka gaidasu
Ahmed ne ya kar6a Yana shigewa cikin gidan
Ya Umar ne ya amsa tareda kallon ayshah

Qasa tayi da kanta Tana wasa da Jakarta su husna kuwa tuni suka wuce sbd Umar 'din Sam
baya wasa yanxune zasuji ruwan bala'i.

Kallonta yakumayi dakyau ahankali yace,

Meyasa baki saka safa ba?

Cikin sanyin murya kanta na qasa tace,

Sunyi dattine na wanke na shanya ruwan da'akayi da dare sun hanasu bushewa.

'daure fuska yayi yace,

Toki tabbatarda kin dawo kan lokaci.

To''''' tace a hankali tareda wucewa cikin sanyinta.


Ajiyar zuciya ya saki ahankali bayan ta wuce Dan hakanan yakejin Sam hankalinsa yakasa
kwanciya da karatun Aysha sbd jiyake kamar zai rasata ne duk dayasan bazata kula kowaba.



A bus stop suka rabu dasu husnah ita ta nufi new site Banda faduwa ba abinda gabanta keyi
sbd ita mutum ce Mai tsoron shiga jama'a batareda Wanda tasaniba.

Koda ta Isa kai tsaye hall 'din dazasuyi lectures ta nufa kanta a qasa cikin nutsuwarta take
takawa Dan duk a takure take sbd yanayin students 'din data gani anan 'din kamarma 'yan iskan
makarantar ne aka kwaso aka dawo Nan dasu Dan dukanin alamu sun nuna kusan hakan ne,


Lectures suke Amma Sam takasa samun nutsuwarda zata fahimci lectures 'din Dan wasu
samari dake kusada ita suna dariyar shigarta.


Sai kusan six suka fito daqyar taga tafito ta iso gida Dan har wani zuru zuru tayi na fargaba data
yini yau aciki.

Tana Isa gida ta tu6e tayi wanka tareda sallah kafin tazauna cin abinci Tana fira da umminta
tareda Bata labarin wani fa'da dataga anayi kan hanyarta ta dawowa.






********

Babban gidane dayaji komai najin da'din duniya sbd girma,kyau dakuma haduwarsa..

Babbar mace ce 'yar gayu da hutu tareda ilimin Boko dayagama ratsata yasa manyancinta qin
bayyanuwa sosai,

Babbar justice ce a babbar federal high court dake garin hakama Mai tsananin roqoce da
addininta na christian Dan har muqami gareta a church sbd riqoda addininta Dan dukda
zamanta babbar Mai kudi hakan bai hanata halarta da kula da aikin church ba kullum.. _justice
queen aiden Bellamy_ kenan.
'yayanta uku rak a duniya,
*FINN* shine babba mum's boy kenan sbd shine ya 'daukota sawu da sawu Dan shima law ya
karanta yanxu lawyer ne kullum tare suke zuwa office sudawo tare suje church tare,
Duk wani Hali nata ya 'dauko Dan harma ya zartata musamman yanda ta tsani kowace qabila
da addini idan ba nataba toshima haka.

*_NIK_*,,,,Niklaus kenan, shine nabiyu Wanda shida qanwarsu *DAVINA* kwata kwata
halayensu sunyi hannun Riga Dana mahaifiyarsu sbd Sam su Babu ruwansu da wani riqo da
addini bare zuwa church,,

Nik 'dan gayune na qarshe daya ha'du iya ha'duwa sbd tun farko a hannun dad 'dinsu yake a
qasar Germany danshi Sam bayason takura yanason yayi rayuwarsa a sake shiyasa yaqi biyo
mum 'din dazata dawo Sai daga baya ta matsa tareda 'daga hankalinta akan saiya dawo
Nigeria.
Gabaki 'dayansu suma farare ne tas bama kamarshi dayafisu son hutawa akoda yaushe kamar
mace.

Davina ma kusan kamarsa take 'yar gayu kullum Tana tareda friends ana gurin shopping ko
gurin hutawa..

Hutu da gata tareda dukiya sun ratsasu sosai shiyasa kullum cikin qara kyau Nik yake,
Duk wani son life 'dinsa mata basa burgesa tunda yadawo Nigeria sbd Sam bazai iya ko

kallonsu ba bare ya iya kulasu yan matansa nacan sunfi burgesa sbd sune sukafi sakasa
nisha'di.



Tsaf take cikin kayanta na aiki ta fito ta hawo sama bedroom 'dinsa Dan shika'dai ne 'dakinsa
yake sama sbd tsananin so data fili ta nuna qarara tafisonsa fiyeda sauran 'yayan nata.

Tura qofar tayi ahankali sanyin ac da qamshin turarensa na signature hugo ya daki hancin takai
kallonta kan lafiyayyan gadon dayake kwance Yana bacci dunqule cikin falin bargo qal.

Takowa tayi ta Isa bakin gadon tareda durqusawa ta rintse ido tafara kwararo masa adduarsu ta
church Wanda kullum saitayi Masa kafin tafita office hakama da daddare komai Daren dazaiyi
awaje saita jira yadawo tayimasa sbd ba qaramin so takeyiwa 'dan nataba.


Ahankali ya 'daga hannunsa 'daya ya janyo dayan pilonsa batareda ya bu'de idanuba ya toshe
kunnensa dashi sbd damun baccinsa da mum din keyi da addua.

Jin ta qara 'daga murya tana fa'din,

Ohhhh Lord I pray for..........Jesu....


Cikin muryar bacci Yana qara tora kansa cikin pillow yace,

Mum pls I hate this...

Miqewa tayi bayan tagama tareda 'duqawa ta shafi fuskarsa bayan ta janye pillon cikeda kulawa
tace,

Nik can pls promise me you'll......

Katseta yayi cikin qosawa yace,

Yes I promise I will.

Thank you sweetheart'''' tace tareda miqewa tafice tana murmushi.

'dakin Davina tanufa Kai tsaye daganan.

Kwance take tana bacci itama Amma ki'da ke tashi a hankali cikin 'dakin sbd ita Bata iya bacci
Saida kida qaidarta ne.

Tada ita tayi itama kafin tafito ta tsaya Saida masu aiki suka jera komai na breakfast 'dinsu Nik
idan sun tashi kafin takalli Finn dake shirye Yana jiranta suka wuce office.


WANNNAN KENAN.



Mamuh💋


_Dont forget to follow,vote and comments_ _@mamuhgee_..
*_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*2*


Yauma a sanyaye ta iso makarantar sbd duk jinta take a takure badan tana tsananin son
karatunba da batajin zata iya cigaba da zuwa sbd wannan new site 'din yafi qarfin abinda
qwaqwalwarta zata iya 'dauka.


Lectures biyu tayi yau Dan haka da wuri tagama Tana fitowa hall ta fiddo niqaf 'dinta ta rufe
kyakkyawar fuskarta sbd kallo dayayi mata yawa Wanda tasan bai wuce na suturartaba sbd har
ja hijabinta keyi.


Sauri takeyi ta tafi gida duk da niqaf 'din data saka kanta a qasa yake bazaka ta6a cewa sauri
takeyiba sbd cikin nutsuwa take tafiyar kaman yanda addini ya koyar.

Tsayawa tayi cak tareda juyowa ahankali sbd sunanta dataji ankira daga bayanta.

Ajiyar zuciya tasaki sbd ganin wata ayshar ce ake Kira ba itaba.

Juyawa tayi zata wuce batareda sanin isowa mutumba sukai wani irin karon dayasa wayar
hannunsa da car keys 'dinsa zubewa qasa.

Ya salam'' tafada ahankali cikin sauri tareda ja da baya jikinta na matuqar rawa sbd jikinsu daya
'dan ha'du Wanda wannan shine karo na farko da jikinta ya ta6a ha'duwa da jikin wani 'da
namiji.

Tsayawa kallonta yayi sbd ganin yanda jikinta ke tsananin rawa abin dayafi basa takaici ma
kenan,

Samanta zawa qasanta ya kalla cikin qyanqyamin shigarta sannan shibaiji baqin cikin ha'duwar
jikinsuba shida yakeda komai na rayuwa musamman kyawunsa dake fuzgar mata Sai itace da
fuskarta ke rufe qilama nakasasshiyace shiyasa ta rufe fuskar.

Dafasa abokinsa Murphy yayi bayan ya 'dauko Masa kayansa dasuka zube Yana cewa,

Let's go Nik we're getting more late..

Wucewa yayi tareda qara juyowa ya kalleta yana 6ata fuska.

Hawayen datake dannewa ne suka gangaro mata ta 'dago Kai ahankali takalli inda sukabi dai
dai yakuma juyowa manyan idanuwansu suka ha'du da juna.

Atare gabansu ya Fadi yayi saurin 'dauke Kai sbd tsoro da idanuwanta suka bashi danshi
mutum ne Mai tsoron mutane sbd bai cikason ko kallon wasu mutanen ba.

Ita ma cikeda tsoro ta juya jikinta na tsananta rawa ta fice tabar makarantar.

Harta Isa gida nutsuwarta bata gama daidaita.

A qofar farko ta ha'du da ya Umar gabanta yakuma yankewa ya Fadi sbd ganin Yana qureta da
kallo tai saurin tattaro nutsuwa tareda qaqalo murmushi cikin sanyin murya tace,

Ya Umar ina yini?

Cikin Jin da'di da tsananin qaunarta ya amsa tareda cewa,

Ayshah da gani kin 'debo gajiya ko?

Eh'''tace tana sauke Kai qasa.

Bata hanya yayi ta wuce batareda yakuma wat maganarba.

A 'dakin umminta ta yada zango ta cire hijab 'dinta tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.



Washe gari jiki a sanyaye ta shirya ta nufi makarantar duk da yau ya Umar da kansa ya rakota
har bus stop tashiga mota.


Tunda suka shiga first lecture 'dinsu taga tamuqar ba tattaro nutsuwa tayiba to bazata fahimci
komaiba shiyasa ta 'dan nutsu ta karanto addua tareda maida hankali saigashi tana fahimtar
komai.


Sai four suka fito a gajiye take sosai ga yunwa datakeji sbd Sam basa cin abinci a waje komai
rintsi shiyasa ko ruwan makarantar Bata ta6a siya tashaba.

Sam bazaka kalleta kace yunwa takejiba sbd acikin nutsuwarta take tafiya.


Saukowa take daga sama Dan hall din dasukai lectures yau a sama yake.

Wasu samari ta hango qasa a tsaye suna sheqa dariya suna nunota
Tasan da ita suke Dan idan da sabo yakamata ace tasaba da tsokanarsu Dan kullum idan zata
fita Sai sun tsokaneta suna kiranta da ninja lady Wanda sunan tuni yafara binda acikin
makarantar Dan gabaki 'daya yanxu ba Wanda yasan fuskarta sbd kullum rufe fuskarta take
cikin niqaf,, Ba kalar mummunar halittar daba'a kiranta da ita sbd kawai ta cire niqaf 'din aga fuskarta Amma
Sam ta danne duk da sau tari idan an mata tana Jin zafi harda hawaye musamman idan
matane sukai mata.


Ihu suka 'dauka suna Kiran,

Here comes our ninja lady..hahhhhhhh

Sunkuyar da Kai tayi tacigaba da saukowarta sbd Bata ta6a kulasuba.

'daya daga cikinsu mace taci ado ta matse cikin qananun Kaya kamarba musulma ba ta 'daga
musu hannu tareda miqewa tsaye cikin 'daga murya tace,

Yau dai Kam dole muga fuskar ninja lady sbd bamusaniba Koda aljana muke tare,,wat do you

say guys????

Ihu suka 'dauka cikin shewa suna cewa,,

Yesss ohhhh..

Cak ta tsaya gabanta na tsananta fa'duwa ganin yarinyar ta nufota ana mata kirari gurin na
da'da 'daukar ihu sbd kowa dakeson ganin fuskarta ta.

Ayshah mutumce Mai tsananin tsoro da rashin qwarin zuciya sbd Sam batada kuzarin dazata
iya qwatar kanta Sai kawai tafara hawaye ahankali tareda rintse idonta tadan ja baya daidai
lokacinda yarinyar takai hannu zata bu'de mata niqaf taja baya ka'dan cikin rashin sa'a Ashe
takai bakin qarfen stairs 'din ta fa'da.
A tsorace kowa gurin ya 'dau ihu..



Sanye yake cikin wasu tsadaddun designers qananun Kaya blue jins da blue shirt datayiwa
farar fatarsa kyau bazaka kallesa kallo 'daya kace christian ne ba sbd yamafi Kama da akirasa
bafulatani sbd komai nasa Mai kyawu ne.,

Shigowarsa kenan tareda amininsa nako yaushe Murphy.,Sai Davina dasuka ha'du yanxu cikin
school 'din ta maqale Masa wai wani lecturer 'dinsu ya hanata shiga lectures yau shine suka
shigo department 'din yayiwa lecturer 'din magana sbd baya tsoron kowane lecturer shi duk da
shima student ne Yana final year 'dinsa...Amma ba ruwansa duk Wanda yatakasa takashi yake
sbd gata da sakewa daya samu daga uwarsa.


Ba zato yaji saukar mutum akansa saigasu sun zube qasa atare..

Holy Christ...yace da qarfi daidai itama tace,

Ya salam''''..

Da sauri Murphy da Davina sukayo kansa ya miqe Yana yarfa cikin tsananin azaba yace,

Oh God she broke hand..

Wat'''''Davina tafada tana yamutsa fuska.


Zafi yakeji sosai Nan danan student 'yan neman fada suka 'dauko kujera aka zaunar dashi

Sambatu yake sbd jiyake baitaba Jin azaba irin wannan ba duk da ba wani ciwo bane.

Mum Davina takira tana 'dauka tace,

Hello my little princess,,,,,

Mum your Nik meet wit an accident his hand and leg got sprained....

Wat,,,, where and how?

One stupid ninja lady fell on him,her face was covered she probably doesn't see where she was
going so......

Take him to hospital now I will be there soon.

Kamasa sukayi zasu fice ya juyo cikin azaba yacewa murphy hand her to school authorities
she did it on purpose.


'dagowa tayi idanuwanta sunyi jajir sbd kuka Dan tunda tafado takasa tashi sbd qafarta da
hannunta sun bugu matuqa Amma ba'a ganiba zaa miqata ga hukumar makaranta sbd
tafadowa 'dan gata.

Hannu ta zura cikin niqaf dinta ta share hawayenta tareda dafawa ta miqe tabi securities
dasukazo tafiya da ita.


Sai gaf da magriba ta iso gida sbd tajima kafin subarta tatafi dukda sun mata gargadi Mai kyau
akan karta Kuma ko lallon hanyarda Nik yabi bare takuma karyasa Dan mum 'dinsa tace next
time aka qara bazata yarda ba.


Kodata dawo gida hankalin 'yan gidan tashi yayi dasuka ganta tana 'dingisawa..

Karo na farko data fara qarya arayuwarta kenan Dan cewa tayi 'dan adaidaita ya fa'di da ita.



Zazzafan zazza6i tayi tareda 'yar qaramar jinyar qafarta Dan satinta kusan 'daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login