Showing 39001 words to 42000 words out of 50455 words
Chapter 14 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf
wata qatuwar sabuwar mall da'aka bu'de itada
shanty duk da har lokacin ranta da zuciyarta kullum qara qonewa suke da baqin ciki da tsanarsa
akan gagarumar qiyayyar daya nuna Mata ta hanyar marinta Dan abin ya daki zuciyarta matuqa
Dan kwana tayi ta wuni tana kuka bayan mayen yasaketa ace mutumin dataso harta jefa kanta
cikin wannan mummunan rayuwar shine ya 'daga hannu ya mareta.
Doguwar gown ce ajikinta Ash kamar ta maza Amma tanada shape da aljihu na gaba Dana
gefe gefe tayi matuqar yimata kyau sbd kaskenta da kyawunta daya fito duk da tuni ta manta
wata kwalliya,,,
Facing cap tasaka akanta red duk da gashinta ba duka yashigeba Amma ko ajikinta sbd yanxu
ba komai take gane shine daidaiba.
Wayartace kawai ahannunta
Shanty ma dai goduwar rigarce Amma ita normal Arabian gown baqa Sai qaramin scarf yellow
'daure akanta.
Shanty ke 'daukar komai itadai Banda tunani ba abinda take duk da Tasha ka'dan kafin tafito
abin dai yau da 'dan sauki bazakace Tasha komaiba matuqar ba magana tafara ba.
Daf da zasu fita taji gabanta yayi mummunan fa'duwa sbd muryar dataji har abada bazata
mantataba...
Da sauri ta juyo tare jikinta har rawa yake tace,
Mahmud,,,,
Wat""""tafa'da da qarfi sbd ganin waye yake riqeda mahmud 'din...
Riqe yake hannun siyama tana tareda Khadija suna shopping cikin nisha'di hankali kwance...
Rantane yayi mummunan 6aci zuciyarta ta rufe ta qarasa gabansu batayi wata wata ba
yankawa siyama wani gigitaccen mari,
Arazane suka kallota Khadija ta zaro Ido zatayi magana a qule ta 'daga Mata hannu tareda Kai
hannu zata jawo 'danta taji anriqe Mata hannu tareda tureta baya cikin tsananin 6acin Rai ya
kalli siyama dake dafe da kumatu ya maida kallonsa kanta yace,
Don't you dare touch him with these dirty hands dasuke aikata sa6on Allah,,,just leave here
quitly sbd I won't tolerate your nonsense again so just leave..
Kallonsa tayi ido cikin Ido idanuwanta na cikowa da ruwa tace,
I hate you,,I hate you so very much,,I've never regretted anything the way I regret knowing you
in my life,,
You take away my son from me you cheat....
Riqeta shanty tayi da sauri sbd tuni tafara jawo musu attention 'din mutane..
Kallon Khadija dake kukan ganin mummunar rayuwar da ayshah ta tsinci kanta aciki yayi cikin
6acin Rai da takaici ya nuna ayshah yace,
See,,, see the woman you've been praising and talking about.,,
Girgixa Kai tayi cikin kuka tace,
Shaikh ayshah is a decent and.....
Will you please keep quiet,
If this is the kind of girl I once loved then I must say mum is right she's not the kind of girl I
should loved or married,,,,,
Kallonsa ayshah tayi da sauri idanuwanta na 6arewa da hawaye ta kalli Khadija tace,
I will never forgive your family for this,,,,
Juyawa yayi a fusace tareda riqo hannun siyama da Mahmud yabar gurin.
Duk yanda taso daurewa kasawa tayi ta durqushe a gurin tareda fashewa da kuka cikin qunar
zuciya.
Tabbas ba itaba ko shanty yau zuciyarta ta ta6u da abinda yayiwa ayshah..
Koda suka koma gida gabaki 'daya kukanta sabo yadawo Dan kuwa saiyau ta qara gane
kuskuran data tafka.
Kwana biyu duk yarasa gane kansa Dan duk yatuno abinda yafaru saiyaji ransa yayi
mummunan 6aci sbd hakanan wani gefe na zuciyarsa ke cewa bai kyautaba koba komai bai
kamata ace da aurensa akanta yabarta tacigaba da gantali agari Dole dai ya kawota gidansa ya
killace ko kuwa ya sauwaqe mata.
Siyama Kam duk inda hankalinta yake ya tashi sbd ba qaramin ka'duwa tayi da ganin ayshah
ba Dan kuwa Bata ta6a tsammanin tanada kyau ko ma'ana ba sbd Jin cewar kullum cikin hijab
take,,,indai har tana cikin hijab Deen yakamu da mugun sonta to kuwa yanxu ma data zare
hakan bazaiyi wuyaba itakuwa bazata ta6a yarda ko Bari ayshah tadawo rayuwar mijintaba Dan
tasan itace da rabon barinsa.
Khadija kuwa rayuwa tayi Mata zafi sbd muh'd daya fito fili ya nuna rashin sha'awar sonta
gareshi,
Nan komai ya dagule Mata ta rasa Ina zata saka kanta Dan har ciwo ta kwanta Amma qememe
yaqi ko zuwa dubota sbd har cikin ransa yakejin zafin abinda mum tayiwa ayshansa.
Su shanty tafara bi batareda sanin shaikh ba tun suna wulaqantata har shanty ta 'dorata akan
network ita kuwa ayshah cewa tayi ba ruwanta kowa tasa ta fishshesa....
Tun Abu na wasa saigashi zance ya bayyana har cikin jaridu cewar matar babban matashi
shaikh nuraddeen da qanwarsa sun kar6i number 'daya a fannen shaye shaye..
Ranar da jaridar ta fito kasa bacci yayi tuni ciwo yafara qoqarin kamasa sbd baqin ciki da
takaici,
Mum lokacinda taga abinda ke faruwa zubewa zaune tayi tana tsiyayar hawaye sbd inda
qaddarar Khadijar tafi muni ita harda maza sha'aninta takeyi.
Tun ranarda jaridar ta fito Bata dawo gidaba sbd tasan mummunan hukuncinsa dazata tarar Sai
kawai suka cigaba da sha'aninsu duk wannan sha'anin dasukeyi ayshah Bata ko kallon Khadija
bare Bata cika ko amsa maganartaba Dan duk wani Wanda ya danganci Deen ta tsanesa.
Yau zaune suke a garden din gidan suna shaqatawa su duka ukun,,
Shanty da khadeee Sai annashuwarsu suke ita kuwa wayarta take daddanawa duk da kallo
'daya zakayiwa ayshah kasan Sam ta manta da ya farin ciki yake,
Dogon pencil jeans blue ne ajikinta da Pink armless top ta 'daure gashinta tsakiyar kanta Yana
lilo...
Gate sukaga anbude hankinsu Yakoma can Banda ayshah dako 'dagowa batayiba taci gaba da
kallon wayarta.
Motar Deen khadee tagani ta miqe da sauri tareda Kiran sunansa.
Itadai ayshah banxa tayi dasu duk da taji abinda Khadijar tafada tacigaba da abinda takeyi.
Cikin takun qasaita da burgewa yake takowa fuskarnan a 'daure Amma kyawun fuskar ya Hana
aga mummunan 6acin Randa ke tattareda ita bayyana,
Tsayawa yayi gabansu tareda kallon Khadija Rai amatuqar 6ace ya nuna Mata mota.
Turo baki tayi cikin qunquni tayi cikin gida Dan dauko kayanta.
Har ya juya ya tsaya cak tareda juyowa ya kalli gefenta ahankali yaga Sam ko kallo duk Basu
ishetaba saima game 'dinta datakeyi...
Kayan dake jikinta ya kalla yaji ransa ya 6aci a qule yace,
You're also coming so just stop that rubbish and get up....
Rintse idanuwa tayi tana qoqarin danne hawayenta zuciyarta na karyewa tace,,,, why is he
doing this to me ya Allah,,i loved him more than anything is this the punishment for the mistake
I've done,,,he is always the reason for my tears...
Hawayen datake dannewa ne suka gangaro Mata ta miqe zuciya karye zatabar gurin baisan
sanda ya riqo hannunta ba sbd yaga hawayen dasuka gangaro Mata Kuma sunyi matuqar tasiri
a zuciyarsa ta yanda bazai iya tafiya yabarta ba.
Juyowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasuka ka'da cikin karyewar zuciya tace,
I'm not coming Deen,
Nida Kai yanxu akwai matuqar banbanci duk da ko awancen lokacin akwai banbancin Amma so
yarufemin Ido nakasa gani I don't want to repeat dsame mistake now,,
Kaci gaba naci baya so let's just end this now sbd bamai Sona yanxu bamai iya Zama Dani Dan
nazama abin kunya,abin gudu abin kyama...
Fixge hannunta tayi ta juya da sauri tabar gurin sbd kukan daya qwace Mata Dan kuwa tabbas
tana tausawa kanta duk ranar da shanty ta tattara takoma gurin iyayenta.
Harya shiga mota yaji bazai iya tafiyaba gwara ya 'dauketa ko gidan uwayenta yamayarda ita
maimakon wannan mummunar rayuwar datakeyi.
Kuka take ahankali zuciyarta na qara karyewa taji anriqo hannunta a hasale ta 'dago tareda
fixgewa Amma ba qaramin riqo yayi Mata ba yafara janta tana tirjewa harya saka mota ya rufe
yashiga yabar gidan da shanty tsaye tana hawaye..
Koda ya Isa gidansa dama part biyu ne Sai nasa atsakiya ya bu'de part 'din datun farko akayi da
sunanta sbd baisan haka halinta yakomaba ya jefata ciki tareda koma gate yabawa securities
gargadin karsu kuskura subarta fita Koda wasa tukuna ya juyo ya nufi part 'dinsa inda anan ya
tararda siyama zaune cikin ado tana kallo Mahmud kuwa dama Yana school.
Mamuhí ½í²‹
_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_í ¼í½’
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*31*
Tunda tazo gidan kwananta biyu Bata Kuma sakashi a Ido Bata damu ba Dan dama bashine a
gabanta ba hasalima iskancinta ta tsulawa a gidan son ranta sbd ganin take taken siyama data
'dauki tsana da kishi ta saka Mata,,
Abu 'daya ke damunta shine yanda tun ranar data dawo gidan ya 'dauke 'danta yamaida gurin
mum sbd wai karyaga munanan 'dabi'unta,,,,
Khadija ce kawai abokiyar firarta wani lokacin musamman yanda suke cikin tsananin kewar
kayan mayensu hardai ita ayshah Dan jitake kamar ta zare sbd rashinsu shiyasa kowa ya
ta6ata a gidan Bata raga Masa sbd takaicin rashin kayan caza kwakwalwa,..
Tunda ayshah tadawo gidan siyama take cikin baqin ciki da takaici tayi mitar harta gaji Amma
Yama qi sauraronta sbd idan har ayshah tabar gidan to gurin iyayenta zai maidata Amma ba
yanxu ba saita dawo cikakkiyar nutsuwarta sbd yasan suka ganta ahaka zuciyarsu bazatayi
dadiba,,,,
Kwance take cikin tsararen palonta ta qurawa tv Ido Amma ba kallon takeba tunani take ta
yanda zata samu ganin shanty Dan tayi kewarta da Kuma kayan korawa.,
Gajeran wando ne black ajikinta da vest itama black da 'dan adon white ajiki.,
Qofar palon taji anbude anshigo da qarfi tareda jeho Mata Kaya akai.
'dagowa tayi taga siyama tsaye Rai a6ace kamar zata fashe tace,
Ga kayanki Nan idan bazaki iya wankewa da kankiba to saiki hkr Amma Mai Mana aiki bazata
wanke wa'innan kayanba masu najasar giya da wama yasaniba ko harda najasar....
Wawan Mari ayshah tasakar Bata batareda tayi tsammaniba takuma tureta tareda fitowa daga
palon ta qwala Kiran Mai aikin dakeda suna Fatima.
Da sauri fatimar ta iso jikinta na rawa ayshah ta kalleta fuska a 'daure tace,
Wuce maza ki kwaso kayan Nan ki aje duk aikin dakike Kona waye ki wankemin su now..
Fitowa siyama tayi cikin zafin Rai da zafin Marin datasha ta kalli fatima ta daka Mata tsawa tuni
jikin yarinyar ya'dau rawa sbd ganin tana tsaka...
Kallon siyama ayshah tayi cikin takaici kafin ta juyo takalli Fatima Sai kawai takama hannun
fatimar tajata zuwa part 'din Deen.
Da sauri siyama tabi bayansu tana Kiran sunan fatimar a fusace,
Zaune yake a palon Yana waya sanye yakeda qananan Kaya sai wani qyallin kyau fatarsa take
Sai ganinta yayi gabansa ba zato,.
Kayan dake jikinta yafara kallo tunda sama har qasa ya dan tsuke fuska sbd fa'duwar da
gabansa yayi,,,
Maida kallonsa kan siyama dake cika tana batsewa yayi hankali kwance yace,
Ya akayi ne?
Cikin 'dage gira ayshah tace,
Nizaka kalla Dan nice zanyi magana,
Kan tv ya maida fuskarsa Yana cewa,
Then speak.
Cikin takaici tace,
Wannan me aikin waye yake biyanta agidan Nan?
Kallonta yayi cikin mamaki da takaici yace,
Idan baniba kece kike biyanta?
Just answer the question bance ka fadamin maganaba.
Yana kuma maida kallonsa ga tv yace,
Nine nake biyanta,.
Nikuma menene sunan matsayina agidan Nan?
Mata"""""yafada Kai tsaye batareda ya juyo ya kalletaba sbd yagano Sarai masifa takeji
shikuma bazai iyaba yanxu.
To hakan ne gud for nothing matarka takasa ganewa sbd she's insane so just tell her karta
Kuma shiga harkana daga yau sbd next time I won't be nice like this...ok..
Juyawa tayi tabar gurin yabita da kallon mamaki baki asake harta fice kafin yamaido kallonsa
kan siyama cikin 'daure fuska yace,
karki Kuma tsokanota Cox she's nothing but trouble so idan bazaki iya tsayawa gurinki ba
harsaikin je neman fa'da to karkiga laifina akan irin hukuncin dazan riqayi.
Miqewa yayi yashige bedroom dinsa yabarta tsaye kamar zatayi bindiga sbd baqin ciki da
takaici.
Itakuwa tana komawa fatima ta kwashi kayan tafice dasu jiki na rawa ita kuwa kasa Zama tayi a
palon ma tashige bedroom 'dinta ta kwanta.
Bayan two days da faruwar haka ta fito part 'dinta tana Shan waqar single ladies ta Beyonce a
wayarta ta nufi 'dakin Khadija dake kusada part 'din siyama.
Siyama dake zaune balcony 'dinta tana gyaran farce tahangota Nan take taji duk annurin
zuciyarta ya gushe sbd ganin baiwar kyawu da diri da ayshan takedashi,,
Gefen Deen takalla taga Yana zaune shima a balcony 'dinsa Yana karatu ga dukkan alama
shibaima lurada itaba hankalinsa nakan abinda yake karantawa,
Saurin tasowa tayi sbd Sam batason mijinta yaga ayshan ahaka,
Gabanta Tasha tareda jifanta da wani wulaqantancen kallo tundaga sama har qasa kafin tace,
Kindaisan Nan ba gidan gala bane dazaki ringa shigarda kikaga dama idanma kina tunanin
'daukar hankalin mijina ne then you're wasting your time sbd mijina bashida sha'awa akan
matan bariki hasalima kallon maza yake musu ba Mata ba so just go back inside and change
kafin ki Kuma fitowa.
Kashe wayarta tayi tareda sakata cikin aljihun jins 'din dake jikinta ta kalli siyamar taga kishi
qarara bayyane cikin idanuwanta cikin ranta tace,
Lallai ma wannan matar tacika Yar rainin wayo nida nakeda mijin tun farko na danne abinda
nakeji shine zata kawo min rainin hankali lallai kuwa Zan daidaita Mata sahu na koya Mata
hankali.
Murmushi tasaki na rainin wayo tace,
Kina tunanin inada abinda zanyi da wancan mijin naki?
Banda abinyi dashi Amma Zan nuna Miki Koda na lalace ahaka shi yanada abinyi Dani idanma
bayada Zan nuna Miki mijinki baida tabbas.
Kallon kanta tayi taga dogon pencil jeans ne blue daya matse 'yan cinyoyinta sosai red top Mara
hannu Sai 'yar jacket Mara nauyi data 'dora akai ko 'dankwali Babu akanta,
Murmushin mugunta tasaki tareda kashe Mata ido 'days ta nuna Deen da idanu tace,
Just wait and watch...
Jacket 'din jikinta ta zare tabar taciki ta nufi gurinsa tana zare ribbon 'din data 'daure kanta
dashi.
Saidata Kusa Isa gurinsa ta tasaki qara tareda qarasawa gurinsa da sauri tana ihu...
'dagowa yayi da sauri tareda miqewa tsaye kafin yayi wani motsi ta shige jikinsa ta cukuikuye
tana ihun Kiran scorpion.
A tsorace ya 'dago da ita daga jikinsa Amma Sai qara shigewa jikinsa take tana ihun kuka
kamar da gaske....
Rintse idanuwansa yayi kansa na sarawa sbd hoton ranar da irin haka tafaru a tsakaninsu can
baya ya dawo masa.
Girgixasa tana sakin kukan qarya yayi saurin 'dagota cikin kasala Yana kallon cikin idanuwanta
wasu abubuwa na qoqarin dawo masa yace,
Calm down ayshah ba wani scorpion anan.,,,
'dagowa tayi ta kallesa sbd Jin kasalalliyar muryar dayayi magana da ita tace,
Akwai scorpion anan'''""" ta fa'da cikin shagwa6a tana nuna cikin rigarta,.
Hannuwansa dake riqe da ita ya 'daga 'daya ya nufi cikin rigar ahankali jikinsa na tsananta
mutuwa.
Gefen siyama dake daskare cikin tsananin mamaki da takaici tareda baqin ciki ta kalla tasakar
Mata wani mugun murmushin mugunta Jin hannunsa ya sauka cikin rigarta yasa tayi saurin
zamewa tana ha'de fuska Amma ganin siyama ta nufosu a zuciye saitayi saurin komawa jikinsa
tana cewa,
Ba anan yakamata acire scorpion 'dinba we need some privacy.
Hakanan yakasa Musa Mata ta jasa suka shige part 'dinsa ta turo qoafar da qafarta sukabar
siyama tsaye sake da baki jiri na neman zubarda ita.
Suna shiga ta fixge jikinta tareda harararsa tana qarasawa tsakiyar palon ta kwanta a 'daya
daga royal kushins dake palon ta canxa Tasha zuwa boomtv.
Mamuhí ½í²‹
_dont forget to follow, vote and comment_
[7/29, 10:07 AM] +234 902 378 7901: *_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_í ¼í½’
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*32*
Qarasowa yayi tsakiyar palon ahankali sbd jikinsa daduk ya mutu Dan ba qaramin yamutsa
tunaninsa tayiba musamman yanda yaji kansa na sarawa da alamun dawowar tunaninsa,,,
Har cikinta ransa baya qaunar bu'de idanuwa yakallleta badan komaiba Sai Dan halayenta na
yanxu musamman mashi dayaga kamar tafi rainasa sbd haushinsa datakeji.
Bedroom 'dinsa ya wuce yaje ya zauna bakin gado Yana qara tunano 'dan tunaninsa na baya
daya 'dan shigo kansa adazun.,,
A 'dazun da tunanin ke shigarsa ji yayi kamar numfashinsa zai fuzge ya bar jikinsa sbd wani
zazzafan sonta daya shigesa acikin tunanin,,,
Kenan shima akwai lokacinda scorpion ta shige Masa Riga...oh Allah please help me remember
komai da komai coz I want to feel that love,the happiness and possession Dana shiga duka
akanta koba komai I can see in her eyes she's completely broken and lonely she's just trying to
endure the pain ne batareda ta nunaba but he can see it all around her kawai she's fighting it ne
sbd taci gaba da rayuwarta koba kowa,..
Miqewa yayi ya dawo palon for the first time yanason yaji everything daga bakinta,,,
Cak ya tsaya akanta sbd bacci daya tarar tayi abinta hankali akwance,
Zama yayi kusada ita tareda qurawa face 'dinta Ido Yana kallon natural beauty da kuma yanda