Showing 42001 words to 45000 words out of 50455 words

Chapter 15 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2470


fatarta ke kyalli saidai tayi wata irin Rama duk da yamanta yanda take ada Amma yasan tabbas
wannan ramace,

Wayarta dake aljihun wandonta tafara haske alamar shigowar Kira ahankali yakai hannu yazaro
ya Duba dakyau saiyaga shanty ce ke kiranta Sai kawai yayi rejecting tareda blocking 'dinta ya
shiga contact 'dinta yayi wiping komai sbd karma tasamu damar Kiran wani akawo Mata kayan
mayen.
Miqewa yayi ya fice daga palon ya nufi motarsa yashiga yabar gidan.



Siyama kuwa tunda tashiga palonta takasa zama takasa tsayi Jin zuciyarta take kamar zata
bindige ta watse sbd baqin ciki da takaicin dake cinta.

Tabbas Dole tayi gaggawar 'daukarwa isakancin ayshah mataki tun kafin mijinta yafara son
ayshan ko yanxu Dan hakan na gaf da faruwa matuqar ayshah nacikin gidan,,,,Dole ne ayshah
tabar gidan Nan da gaggawa.,,,,,,tafada tana Zama kan kujera ranta na Dan saki sbd tunanin
daya fa'do Mata.


Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo tuni tabar 'dakin takoma part dinta tacigaba da
sha'anin gabanta.

Haryayi Shirin kwanciya ya kwanta siyama Bata shigoba tanacan tana fushi,

Fitowa yayi cikin kayan bacci na maza Ash color ya nufi part 'dinta.

Kwance take itama cikin kayan bacci tana ganinsa ta 'dan 'daure fuska ya lura Amma ya share
ya tsaya bakin gadon tareda zura hannunwansa cikin aljihun wandonsa yace,

Are you ok?

Yes"""""tace Masa Kai tsaye batareda ta saki fuska ba.

'daga kafada yayi yace,

Ok Saida safe.
Ya juya ya wucewarsa.

Sabon takaici ne yataso Mata ganin ya tafiyarsa da gske kenan bazai iya rarrashinta ba.

Qasa hakuri tayi ta sauko gadon tabi bayansa.

Shikuwa kasa komawa part 'dinsa yayi yasamu kansa dason zuwa yayiwa ayshah Saida safe
itama.

Cikin nutsuwa yashigo bu'de qofar yashiga,
Bata palon saidai kayan kallon palon a kunne suke musamman ma qararsu datayi yawa ya
girgixa Kai Yana cewa,

Problem queen.

Kashe kayan yayi harzai fice yaji sheahekar kuka na fito daga bedroom 'dinta.

Shiru yayi kamar ta tafiyarsa saikuma zuciyarsa takasa nutsuwa ya nufi bedroom 'din ahankali
ya shiga.


Zaune take qasa can qarshen gado ta cusa kanta tsakiyar qafafunta kuka take sosai kamar
ranta zai fita Wanda tunda rayuwarta ta ta6ar6are kullum komin dare saitayisa da hakan ne take
'dan rage nauyi da qunar zuciyarta.


Tsayawa yayi daga bakin qofar kansa na fara sarawa sbd qarar sautin kukan dake shiga
kunnuwansa na dawo Masa da sautin kukanta adah,

Rintse idanuwansa yayi da qarfi sbd kukan namatuqar motsa qwaqwalwarsa musamman yanda
abubuwa keson dawowa qwaqwalwansa da qarfi Nan take kansa yafara juyawa ya dafe kan da
qarfi Nan 'dakin yafara juyawa dashi Sai kawai ya yanke jiki agurin ya zube.

Qarar fa'duwarsa tasata 'dagowa ahankali saita gansa zube qasa kamar ba Rai ajikinsa.

Fa'duwa gabanta yayi mummunan yi ta taso jikinta na 6ari ta zube gabansa tareda Kiran sunan
Amma ba motsi
Yawu ta ha'diye cikin tsananin tashin hankali ta jijjigasa iya qarfinta bai motsaba da gudu ta
'debo ruwa toilet cikeda roba ta zuba Masa Dan tuni ta manta da yayyafa ruwan ake.

Wurgi tayi da robar ta zube qasa tareda kamosa jiki na rawa ta qara Kiran sunansa kuka na
su6uce Mata Nan tafara rera kuka ahankali Mai tattareda kashe jiki sbd Bata ta6a tunanin
sonda takewa Deen 'dinba haryanzu yananan kamarma kullum qaruwa yake,.

Ahankali ya bu'de idanuwansa tareda 'daga hannu da qyar ya dafe kansa saiyaji jikinsa yayi
tsananin mutuwa na wani mugun tausayinta sbd kukan dayaga tanayi sosai sbd ganin halinda
yashiga,

Murya qasan maqoshi yakira sunanta kawai saita miqe da gudu tabar gurin sabon kuka na
zuwar Mata na yanda ko yaushe dai sonsa keyiwa zuciyarta galaba Wanda Kuma taga illar
hakan yakamata ace takoyi darasi Amma gashinan cikin mintuna qalilan ta manta halinda take
ciki duk akansa ta rikice ganin halinda yashiga yanxu.
Kasa barin 'dakin yayi ya zauna bakin gadonta jikinsa na rawar sanyin ruwan data jiqasa tsaf
dasu ga sanyin ac.,

Lafewa yayi jikinsa amatuqar mace Dan tabbas kukanta ya ta6a zuciyarsa.


Har tsakiyar dare tana Palo rakube tana kuka saidataji shiru ta miqe jiki a sanyaye ta nufi
bedroom 'din,

Kwance yake bacci ya 'daukesa ya takure guri 'daya alamar sanyi.

Qarasowa tayi bakin gadon ta zauna tana kallon face 'dinsa hawaye nacigaba da gangaro Mata
tajawo bargo ta rufa Masa cikin sanyin muryar kuka tace,

Deen na yarda da soyayyarka itace qaddata,
Banta6a tunanin zuciyata zata so wani Abu duniya kamar yanda take sonkaba,
Duk wata tarbiyata da alada ta iyayena da kakanni na asuli na zubar na za6i soyayyarka sbd
Kaine farin ciki Ashe bansaniba Kuma Kaine baqin cikina,
Tabbas Dana tankwara zuciyata nabi za6in iyayena na auri ya Umar da duk wahalarda zansha
arayuwa inada ladar hakurinta sbd iyayena nakewa biyayya,

Deen banyi Dana saninkaba arayuwa sbd har yanxu zuciyata takasa yimin adalcin cireka
acikinta musamman ma yanxu danake ganin qiyayyata qarara a idanuwanka Wanda hakan ba
qaramin karya zuciyata yayiba Dan kuwa na tabbata hasararriyar data rasa komai.,

Mahmud 'dina danake ganin shine 'dan farin cikin daya saura arayuwata shima karabani dashi
sbd kaima kana gudun 'danka yayi irin halina sbd na Zama abar gudu ga kowa,
Ka rabani da iyayena,
karabani da farin cikina,
Ka tarwatse rayuwata,
Qarshe ka rabani da kanka but still zuciyata kaitake so why deen.?

Kukane yaci qarfinta tayi shiru zuciyarta na tsananin zafi da qunar halinda take ciki...

Da sauri ta miqe sbd kukanta daya fara sauti Dan karta tadashi Wanda ita Bata saniba duk
abinda take fa'da yanaji
Jikinsa yayi matuqar sanyi Dan baita6a tunanin haka take sonsaba Sai yanxu,
After what all happened she really wants to give his love a chance...

Rintse idanuwansa yayi jijiyoyin kansa na tashi tausayinta da sonta na shigarsa lokaci 'daya
musamman yanda yakejin 'dacin rabata 'da 'danta da akayi lokaci 'daya kenan wanine ya
'dauke mahmud yakawo Masa ba itace takaisa da kantaba.

I'm the reason for all her pains and sorrows,
I've been acting to harsh towards her,
I've insulted her for no reason,

Rintse idanu yayi zafin abubuwan na shigarsa kamar yayi kuka,
Ayshah kukanki yazo qarshe insha Allah..
From tomorrow i will give you your full right as a lovely respected first wife.

Har akayi asuba idonsa biyu cikin tsananin tunani Nan take Sai kansa yafara wani mummunan
ciwo Wanda baita6a irinsa ba musamman yanda kaman tunaninsa ke neman dawowa da qarfi
out of control.

Da qayar ya iya fitowa yaje masallacin gidansa sallar asuba.

Akan idon siyama ya fito hawayen datake dannewa suka silalo Mata kenan dai agurin ayshar ya
kwana.

Daga masallaci part 'dinsa ya wuce Kai tsaye ya kwanta sbd har time 'din jiyake kaman kansa
zai buga Dan har wani jiri ya ke gani.

Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
[7/29, 10:07 AM] +234 902 378 7901: *_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_



*33*



Qarfe bakwai na safe motar muh'd tashigo harabar gidan badan yasoba sbd tun ranarda Deen
yamaido ayshah gidan ya yafe gidan gabaki sbd zuciyarsa bazata ta6a iya 'daukar ganin
ayshah da waninsa ba.,
Amma yau dolece sbd tun jiya mum ke Kiran Deen Bata samunsa shine takirashi ta sanardashi
mutuwar Finn cikin tsananin kuka da tashin hankali gashi daddynsu tuni Yakoma Madina da
Zama saidai yakan ziyarceta time to time.,
Ga Deen da Khadija basanan tayi kuka harta gaji shine ta yanke shawara ta sallami duka masu
aikinta da zarah Mai kulada mahmud tayo Nigeria gurin 'yayanta danta gaji da muguwar
rayuwar ka'daicin datake ciki tana buqatar 'yayanta atareda ita Koda hakan na nufin saita
musulunta infact she's ready to become Muslim kamar mijinta da yaranta musamman ma
Mahmud shiyasa tana dirowa qasar takira muh'd yazo ya 'dauketa.


Bu'de qofa yayi yafito riqeda mahmud ya zagayo ya bu'de Mata qofar ta fito tun anan jikinta yayi
mugun sanyi sbd ganin baiwa da 'daukakar da Allah yayiwa 'danta ta hanyar musulunci.

Tundaga nesa Khadija ta hango mum 'din da gudu ta fito ta rungume mahaifiyarta tareda sakin
kuka ahankali sbd tana tsananin tausayin kanta da mum 'dinsu sbd suna cikin tsananin ka'daicin

rayuwa musamman yanxu da iyakacinta cikin daki ko gate Deen ya hanata kaiwa bare ta fita.

Lafiyayyen 'dakin Khadija mum tasauka shikuwa muh'd palon Deen yaje ya zauna Yana cigaba
da kiransa a waya sbd ko alamar siyama baiganiba bare tafadowa Deen 'din.


Mahmud kuwa da gudu ya nufi bedroom 'din daddynsa Yana kwala Kiran sunansa cikin farin
ciki.

'dago Kai yayi daqyar yana ganin Mahmud 'din ya saki murmushin qarfin hali da farin cikin ganin
'dansa ya tashi zaune ya rungumesa.

Assalamualaikum daddy""""yafada Yana tashi daga jikin daddyn nasa tareda miqa Masa 'dan
qaramin hannunsa.

Wa'alaikm Salam my boy'""""yafada Yana miqa Masa hannu kafin ya miqe tsaye ya fito dashi
Palo Yana ganin muh'd a zaune ya qara sakin fuska tareda miqa Masa hannu suka gaisa ya
zauna nan muh'd yafada Masa abinda ke faruwa.

Shiru yayi Yana maimaita innalillahi cikeda tausayin 'dan uwansa sbd ya mutu bai samu arzikin
musuluntaba.

Miqewa yayi suka fito suka nufi gurin mum 'din muh'd kuwa noqewa yayi ya tafiyarsa sbd ko
ganin Khadija ko ayshah baya son yayi.


Mum na ganinsa ta taso da sauri ta rungumesa tareda sakin kuka ahankali.

Bubbuga bayanta yariqa yi Yana cewa it's ok mum, everything will be fine insha Allah.

Zaunar da ita yayi bakin gado tareda riqo hannayenta biyu yace,

Mum ayshah is here and....

Da sauri ta 'dago ta kallesa yayi shiru taredayin qasa da Kai.

Murmushi tasaki tareda 'dago fuskarsa tace,

I'm happy to hear that sweetheart,,
Your happiness is always my happiness, she won't face anything from me I promise afterall
she's my sweet little Mahmud's mother,,,and I'm really sorry for....

Girgixa Mata Kai yayi tareda cewa,

Mother's don't apologise to their children.

I love you my sweet boy.

I love you too mum.

Wayarsa ya fitar ya Danna Kiran siyama don ayi gaggawar shiryawa mum 'din abinci.

Saidata Kusa katsewa ta 'dauka a daqile tayi sallama,,
Shima a qasan maqoshi ya amsa tareda cewa tazo ta gaida mum yanzu a 6angaren Khadija.

Fuska ka 'daure sosai kamar zatayi kuka cikin baqin ciki tace,

Another problem has arrived mitswww.

Abinda Bata saniba shine yaji abinda tafada ransa yayi mummunan 6aci Amma saiya qyale
kawai.


Saidata share kusan rabin awa kafin ta iso tashigo fuska ba walwala ta gaida mum 'din.

Baki mum tasaki ganin irin gaisuwar rainin wayo da siyamar tayi Mata Nan take ta 'daure fuska
zata yiwa siyamar kaca kaca saita tunoda tayi alqawarin Kama girmanta sbd Deen 'din ta amsa
tana qaqalo murmushi Amma cikin zuciyarta tsana da takaicin siyamar ne fal.


Qoqarin juyawa take cikin 'daurewar fuska yace,

Prepare something for mum to eat yanxu.

Danne takaicinta tayi takallesa cikin Ido tace,

Inaga wannan ba aikina bane sbd banice da girki ba idan ka manta jiya agurin tsintacciyar
matarka ka kwana.

Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka 'dan bayyana yace,

Yes you're right na mantane you can leave Zan kirata ita tayi.

Haushinsa ne ya qara turnuqeta ta Fice cikin takaici kamar zata daki iska.

Daqyar ta tashi tayi wanka fuskarta duk a kumbure sbd kukan data kwanayi wannan karon
doguwar rigace ajikinta Mara hannu ta jawo qaramar hula tasaka duk gashinta a waje sbd Bata
kamasaba Kai tsaye 'dakin Khadija ta nufa sbd number shanty takeso ta duba wayarta taga
komai ya goge.

Dai dai kusan qofar Khadija Nan sukaci karo da siyama ta fito afusace.,

'dauke Kai tayi zata wucewarta siyama tace,

I will never live peacefully with these three around,the great madam queen,the mental so called
first wife and the stubborn son of great time mitswww...

Kasa qyaleta tayi ta kalleta a wulaqance tace,

And who are you calling mental?

You""""tafada Kai tsaye tana gyara tsayuwa.

Murmushi ayshah tasaki tareda kallonta up and down tace,

Do you know you're completely crazy and foolish?

Qara hasala siyama tayi zuciyarta ta rufe ta 'daga hannu zata sakarwa ayshar Mari taji anriqe
hannunta ta baya.

Atared suka juyo Dan ganin waye dukkaninsu idanuwansu suka sauka kan mum.

Wurgar da hannun siyama tayi ta 'daga nata hannun zata Mari siyamar ayshah da idanuwanta
suka ka'da Nan take sbd ganin mum 'din ta riqe hannun mum 'din idanuwanta na bayyana
tsantsar qiyayyarta da mum cikin 'daga murya tace,

And who are you to interfere in this.?

A razane dukkaninsu suka kalli Ayshan sbd ba qaramin bazata zancenta yayi musuba.

'daure fuska ta sakeyi tareda 'dage gira 'daya tace,

This is between me and her and I can fight for myself I don't ask or need anyone's interference
coz I don't tolerate crazy old ladies now.....

A matuqar zuciye ya 'daga hannu zai Mari ayshar mum tayi saurin riqeshi tana girgixa Masa Kai

idanuwanta na kawo ruwa sbd ta tabbatarda abinda tayiwa ayshar Dole ta fuskanci haka.

Cikin 6acin Rai ya kallesu fuska a 'daure tareda daka musu tsawa yace su bar gurin.


Wani kallo ayshah ta watsa musu kafin tabar gurin tana cewa,

Dama me mutum ze tsayayi tunda masifa ta iso gidan.

Kasa kallon mum da jikinta yayi matuqar sanyi yayi yawuce part 'dinsa direct zuciyarsa na quna
dan kuwa mummunan mataki zai 'dauka akansu duka indai akan mum ne.

Daf da zata shiga palonta taji anrungumeta ta baya da sauri ta juyo tana ganin Mahmud 'dinta ta
'daukesa da sauri tareda qanqamesa tana hawayen farin ciki koba komai ta yanke shawarar
tafiya sbd har abada bazata iya Zama gida 'daya da mum ba 'dauke 'danta zatayi ta tafiyarta
inda bamai Kuma jinsu bare yagansu.

Ranar da 'danta takwana cikin farin ciki da Jin 'dadin data Jima batayiba.,
Shikansa mahmud yayi kewar mummynsa sosai shiyasa Sai lafe Mata yake Yan shagwa6a.

Acikin Daren ta ha'da kayanta tsaf asuba nayi tayi sallah ta fa'da wanka jiki na rawa.


Daga masallaci direct part 'dinta ya nufo daf dazai shiga yaga fitowar wani qaton namiji da gudu
riqeda rigarsa a hannu yayi bayan part 'din nata..

Mummunar fa'duwa gabansa yayi kansa ya Sara harsaida wani mugun jiri ya 'dibesa yayi saurin
dafa bango.

What namiji cikin gidana?
Wani qarfi ne yazo Masa tareda 6acin Rai sa zafin zuciya yabi bayan mutumin Amma bai
ganshiba gate yakoma da sauri yacewa securities karsu Bari kowa yafita Koda matansa ne
kafin yadawo zuciyarsa na tafasa a zafafe ya banka qofar bedroom 'dinta dai dai fitowarta
wanka 'daureda 'dan wani munafikin towel dayayi Mata ka'dan danko hadewa bayayi sosai.

Fa'duwa gabanta yayi jikinta ya'dan fara rawa Amma tafara qoqarin dakewa Dan ita tunaninta
yagano guduwar dazatayi.

Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita
Ya rintse idanuwansa cikin zafi da karyewar zuciya ya damqota tareda matseta ya jijjigata da
qarfi yace,

Why,why ayshah?
Duk abinda kikayi baya da aurena is not enough saikin kawomin cikin gidana,,,

Cikeda mamaki da tsoro take kallonsa tana qoqarin kwacewa sbd zafin riqon dayayi Mata,.

Tureta yayi da qarfi harsaida ta fa'di har kanta ya bugu goshinta ya fashe a zafafe zuciya na
tafasa yace,

Ayshah Nima ayau na tabbatarda kece qaddarata,
Nasoki abaya so Mai tsanani,
Yanxuma Dana manta komai still zuciyata saidata kamu da sabon sonki nakuma tabbatarda
dazan Kuma samun wani memory loss 'din I will still fall for you but wannan shine sakayyar....

Rintse idanuwansa yayi ga mamakinsa saiga hawaye na tsiyayo Masa ya girgixa Kai zuciyarsa
na qara 'daci yace,

Ayshah go, leave, I don't want to see you again.

Tashi tsaye tayi cikin tsananin zafi da qunar Rai tana kallon tsakiyar idanuwansa hawaye na
qoqarin sauko mata tace,

Deen me kake zargi dashi?

'dauke Kai yayi yace,

Just leave,.

Juyosa tayi da qarfi cikin kuka tace,

Deen ni kake zargi da wani?
Ni ayshah kana tunanin Zan iya rayuwa da wani namijin bayan kai.?
Deen do you really hate me that much da har kakemin wannan zargin after all the years danayi
batareda kaiba Amma na tsare mutunci aurenka.?

Wannan shine nawa sakamakon?
Deen when will you stop hurting me and ruining my life?

Girgixa Kai tayi cikin hawaye idanuwanta na kadawa jajir sbd wannan shine Abu mafi Muni
dayayi Mata arayuwa and this mark the end of their relationship.

Share hawayenta tayi tace,
Bazan ta6a manta wannan ranarba sbd itace ranarda na datse duk wani sauran hope na

tsakanina dakai,
Nagama dakai Deen.

Juyawa yayi ya fice a fusace hawayensa na qara 6allewa.

Zubewa tayi bakin gado tareda sakin kuka ahankali zuciyarta na Kara karyewa tace,

Baba kuyi hkr gida Zan dawo wlh zuciyata fashewa zatayi Ina cikin tsananin rayuwa Ina
buqatarku ku yafemin.


Har time 'din mahmud bai tashi bacci ba hakanan ta tadashi ta saka Masa Kaya ko wanka
batayi masaba suka fito.

Mum da Khadija tagani bakin qofar palonta jiki asanyaye Khadija kuwa kuka takeyi sosai.

Kallon Khadija tayi itama idanuwanta na sake 6arewa da hawaye tace,

Khadija mum yau ta qara tabbatarminda Bata qaunata and she will never do sbd nasan she's
behind all this,,, anyways dama I should be ready for even more of these since she's here
Amma komai yariga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login