Showing 15001 words to 18000 words out of 50455 words

Chapter 6 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2462

tashare bakin titin Dan Sam zuciyarta taqi barinta tafiya...

Juyawa tayi ta canza hanya zuwa bayan layin gidansu.

Bakin wani kangon gida ta tsaya da kusanma anmaidasa bola sbd dadewar da'akayi ba'a
cigaba da gininsaba.

Jujjuyawa tayi taga Babu mutane sosai agurin saitayi saurin shigewa gabanta na tsananta
fa'duwa Dan jikinta har rawa yake.

Cak ta tsaya tareda zubewa qasa ba shiri...

Kwance yake baisan inda kansa yakeba cikin jini duk gabaki 'daya kamannunsa sun canxa da
sbd duka da wahala.

Da rarrafe ta qarasa gurinsa tareda tallafosa jikinta ta fashe da kuka Mai qarfi tana Kiran
sunansa.

Kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan tabbas batasan sonsa yayiwa zuciyarta mugun
kamuba Sai yanxu data gansa cikin wannan mummunan halin....

Jin tayi kamar ya motsa tayi saurin 'dagowa suka ha'da ido sabbin hawaye suka gangaro Mata
ta fara girgixa Kai cikin kuka tace,

Why....why...why Nik,,,,why did you choose to make me suffer by seeing you like this????

Duk da a wahalce yake danko hannunsa bai iya motsawa Amma ganinta yakawo farin ciki
sosai acikin ransa barema dayaga halinda tashiga ganinsa haka..

Wani mugun yunqurin amai yayi saiga jini na fitowa ta bakinsa..

Zaro manyan idanuwanta dasukai ja tayi takalli jinin takuma maida kallonta kansa taga Yana
numfashi sama sama
Da gudu ta fito tareda mantawa da wani tsoron Kar aganta tasamo taxi itada mai taxi 'din suka
sakasa mota..

Baya tazauna taredashi duk da numfashinsa zuwa time 'din yakusa 'daukewa...

Damqe hannunta yayi cikin nasa hawayen wahala na gangaro Masa murya qasan maqoshi
yafada Mata sunan asibitin dazata kaisa.

Shihhhhhhhh don't talk pls""""''''''tace Masa qasa qasa cikin kunnensa tareda qara damqe
hannunsa tanajin zafi da ra'dadin ciwonsa na shiga zuciyarta.


Asibitin daya fa'da can takaisa suna zuwa akai emergency dashi Dr naganinsa yayi saurin zare
farin glass 'dinsa cikin tashin hankali da mamaki yace,

Oh my God,,Nik ne wanna ai...

Fitowa yayi tareda kallon nurse 'din data biyosa yace,,,

Waya kawo patient 'din dake ciki?

Ada sauri ta nuna Masa ayshah dake zaune ta sunkuyar dakai sbd kukanta dayaqi tsayawa
Dan yanda taga hankalin nurses 'din dasuka kar6esa ya tashi tasan ba qaramin Hali Nik 'din
yake ciki ba.

Qarasowa gabanta Dr yayi tareda kallonta dakyau kafin cikin mamaki yace,

Kece Kika kawo Nik?

Kai ta 'daga da sauri cikin tsoron Mai zaice yasamu Nik 'din.

Kallon tuhuma yakuma jifanta dashi kafin yace,

Ina muma 'dinsa da....

Bata Bari ya qarasaba cikin fargaba tace,

Please Dr kafadamin idan zaiji sauqi..

Yes zai zamu sauqi but....

Ok Dr ngd Amma Dan Allah idan kanada number mum 'dinsa kafa'da Mata.

Share hawayenta tayi tajuya batareda tabari yakuma wata magana ba.





Kwance take nurse 'din da'aka 'dauko Mata tun Daren jiya Dan kulada ita tana zare Mata drip
'din dake hannunta har lokacin idanuwanta dasukai mummunar kumbura Basu daina zubar da
hawayeba..
Finn ne akusada ita ya kwantarda kanta kan kafa'darsa Yana shafa kanta alamar rarrashi.

Mr Aiden ma daya iso da safen zaune yake kusada ita Davina na zaune kusadashi tashige
jikinsa...

Dukkaninsu kallo 'daya zakayi musu kasan mummunan alamarine yasamesu Mai kamada
mutuwa.

Waya Mr Aiden ya Kuma 'dagawa akaro na ba adadi yakuma Kiran police yayi Koda akwai wani
update Amma still Babu.


Wayar mum ce tafara ringing Amma ko qyafta idanuwanta batayiba bare ta motsa...

Finn ne yayi qarfin halin 'dauka tareda saka loudspeaker...

Gabaki 'dayansu atare suka zabura Jin abinda Dr yafada mum kuwa tuni takai qofa jiri na 'dan
'dibarta Amma batajin zata iya jira.

Da sauri Finn ya riqota suka 'dunguma mota gabaki 'daya Sai asibitin.


Tashin farko da mum taga halinda Nik 'dinta ke ciki Sai ganin sukayi ta yanke jiki Saida dadinsu
yayi saurin riqota ta fashe da kuka tana kallon yanda Nik dinta ke numfashi cikin azaba da
wahala duk da har lokacin tashiba.

Saidata shaqi kukanta kafin ta miqe Finn ya Kama hannunta suka nufi office 'din Dr suka bar

dad da Davina a room 'din.

Dogon bayani Dr yayi musu akan Yana tunanin mummunan dukane akayiwa Nik 'din Wanda
harya ja Masa internal bleeding Dan qila andaki kansa.

Share hawayenta tayi ta Kuma kallon Dr tace,

Where did you find him I mean who brought him here?

It was a lady,,, she was all covered by.....I think she's a Muslim.

Tafasa zuciyar mum tafara Nan take 6acin ranta da baqin cikinta suka danne damuwar dayake
ciki...

Miqewa tayi tareda kallon Finn dashima yacika yayi fam dajin cewar ninja lady ce tayiwa Nik
wannan mummunan aikin.


Kallon Finn tayi bayan sunbar office 'din cikin tuquqin da zuciyarta keyi tace,

I want them to pay double for wat they've done to my poor darling boy...make them cry and
regret their lives.

Yes mum""""yafada Yana fiddo wayarsa aljihu Dan making call.

Da daddare ya farka Nan dukkanin familyn suka kewayesa suna basa kulawa cikin so da qauna
musamman mum da kamar tayi ihu takeji duk ya motsa taga ya rintse Ido alamar azaba.

Da daddare bayan Finn da Dad 'dinsa sun taimaka Masa yayi wanka ya saka kayan bacci ya
kwanta mum ta lullu6esa ya lumshe idanu alamar bacci duk suka fito Dan tafiya gida.

Lumshe idanuwansa yayi tareda sakin murmushin da iyakacinsa zuciya ya tuno baby face da
fararen idanuwanta lokacinda take kuka tana Kiran sunansa.

Ahankali cikin maqoshinsa yace'
I love you my sweet ninja lady...





Washe gari ma data fito kasa wucewa makaranta tayi saita samu kanta dabin umarnin zuciyarta
ta nufi asibiti gabanta na tsananta fa'duwa Amma ba yanda ta iya Dan batajin zata iya Kai

yamma batareda taga halinda yake ciki ba..


Baba alhaji da baba shehu tareda Yaya Ahmad da Yaya abbakar ne suka dawo daga gurin wani
taron fatawa...

Daf dazasu Kai anguwarsu wata baqar mota Tasha gaban taxi 'din dasuke ciki kafin suyi want
motsi qartin maza majiya qarf suka fito da bindigogi suka tasa qeyoyinsu baba alhaji dayaso
gardama aka 'dibesa wani mummunan Marin dayasashi ha'diye maganar dayaso yi sukabar
gurin da mugun speed.



Kodata isa asibitin Kai tsaye emergency ta nufa cikin sauqi saiga 'daya daga nurses 'din dasuka
kar6esa a jiyan ta tareta cikin sanyin murya ta tambayeta room 'din dayake.
Nuna Mata tayi ta nufi 'dakin gabanta na tsananin bugawa.

Nesa ka'dan da 'dakin ta tsaya tareda qurawa qofar 'dakin ido tana qoqarin controlling
matsuwarta tason ganinsa.

nurses biyu taga sun fito 'dakin mace da namiji tayi saurin qarasawa ta tare macen cikin sanyi
tace,

Please patient 'din dake ciki yaji sauqi kuwa?

Kallon up and down tayi Mata kafin tace,

Eh Amma dai yanxu mun Hana kowa shiga gurinsa har family 'din sbd munason yasamu
isashen hutu.

Bin bayan nurse 'din tayi da kallo bayan ta wuce tana tunanin kenan ba kowa a 'dakin.

For the first time taji wani farin ciki bayan tsawon lokaci..

'dakin ta dosa gabanta nacigaba da fa'duwa.

Tsayawa tayi bakin qofa tareda rintse ido tasaki numfashi ahankali tareda tattaro Yar nutsuwa ta
tura qofar ahankali.


Cak ta tsaya sbd idanuwanta dasuka sauka cikin nasa Yana kwance ya qurawa qofar Ido kamar
Daman yasan itace zata shigo..

Tashi zaune yayi batareda ya 'dauke idanuwansa cikin nataba..

Har ya iso gabanta Bata motsaba sbd garkuwar jikinta da idanuwansa suka kaririya..

Hannunta ya riqo ya jawota ciki ya rufe qofar har time 'din batayi wani qwaqwaran motsiba.

Zaunar da ita yayi bakin gadonsa tareda durqusawa gabanta idonsa cikin nata yace,

Ayeeshah did you came to hia see?

'daga Masa Kai tayi sbd batada kuzarin magana..

Wani qayataccen Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka bayyana ka'dan..

Tasowa yayi ya zauna kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta da wata kasalalliyar murya
yace,

Did you love me ayeeshah?

Shiru tayi tareda sunkuyar dakai qasa.

Murmushi yakuma saki yace,

Please talk to me ayeeshah..

Juyarda Kai tayi still batace qalaba.

Murmushi yayi tareda zubewa qasa ya riqe kansa Yana juye juye cikin tsananin azaba.

A ki'dime ta sauko gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali da tsoro Amma saitaga
Yana qara mimmiqewa saikuma yayi dif ba alamar numfashi ataredashi.

Kansa ta rungumo batareda tasaniba tafara kuka tareda Kiran sunansa...
_*I love you Nik*_,,,pls wake up..
_*I love you so very much*_.....

Miqewa tayi da sauri Dan kirawo Dr taji anriqo hannunta tayi saurin juyowa sukai Ido biyu Yana
sakar Mata wani hot smiling...

Kallon mamaki take Masa da sauran guntayen hawayenta Dan tagano da gangan yayi hakan
Dan ta fa'di abinda yake son ji..
Wata fitinanniyar kunyace ta rufeta tayi saurin juya Masa baya tana sauke numfashi ahankali...

Zagayowa yayi tareda matsota sosai danshi Sam bai 'dauki hakan komai ba...

Matsota sosai yayi jikin bango tareda duqo da fuskarsa daf da Tata har numfashinsa na mugun
ha'duwa ya 'daga hannu ahankali ya cire Mata niqaf tai saurin rintse ido... fuskarta na bayyana
wani sahirtaccen murmushin daya Kuma tafiya dashi.

Bakinsa yakai daidai kunnenta cikin wata kasalalliyar murya yace,,

You finally said it my love...

Sake tamke idanuwanta tayi sbd Jin kalar muryar dayayi amfani da ita ba qaramin shigarta
tayiba.

Kallon dogayen eye lashes 'dinta yayi yace,

Will you marry me ayeeshah...

'daga Masa Kai tayi ahankali sbd tuni ta manta da wani banbancin yare da addininsu.




Su baba alhaji kuwa wani qaton gida aka kaisu suna shiga aka 'daddauresu tareda jiqasu tsaf
da ruwan qanqara kafin aka fara jibgarsu baji ba gani.





Mamuh💋
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_

*21*


Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo
ya kalli tiger yayi Masa alama da ido...

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma 'debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu
tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da
dai Suma su baban ba a raga musu ba...


Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya
'daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da'di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka 'daukosu a watsar..




Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon
dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us...

'dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik...I can't marry you without my family's approval.. besides that I'm Muslim you're Chris.....

Katseta yayi da cewa,

I'm ready to convert my love....I want to become Muslim too...

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin
yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu...Dan tasan
gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah...

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi
maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na
fa'duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths 'dinsa qasa qasa
yace,

Wait hia...

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli
yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin
kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice 'dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta
tako ina.
Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.


Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa'duwa ta qarasa a
darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan
gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..

Yawu ta ha'diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma
harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba'a fa'daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da'di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani
qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba'ai zancen komaiba kan al'amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro
da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin
ya jikinsa yakeba..


Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..
Matuqar zafi gidan kusan kowa ya 'dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba
malam ya 'dau zafi matuqa....

Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..

Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,

Ayshah Kinga abinda wa'innan mutanen sukayi Mana ko?

Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..

Cigaba yayi da cewa,

Duk bazanyi wani tashin zanceba ko dogon zance auren Umar da ayshah nasaka Nanda wata
biyu kowa yaje yafara shiryawa Kuma nijar zasu koma bayan auren nagama magana kowa zai
iya tafiya.

Takaici ne ya turniqe Yaya Umar Dan so yayi ace Nanda sati 'daya a 'daura auren..

Iyayensu da sauran 'yan gidan kaf sunyi na'am da hukuncin baba malam 'din Dan tsoron abinda
zai iya biyowa baya.

Ayshah kuwa jitayi hankalinta yayi mummunan tashi hawaye yaciko idanuwanta jikinta har rawa
yake ta miqe ko gani batayi sosai tabar palon.

Kuka take sosai cikin qaramin sauti zuciyarta na tsananta shiga qunci..
Kamar munafuka takoma cikin gidan ko fitowa Bata cikayiba..hakama zuciyarta a matse take
dason ganinsa.

Zaune take akan carpet 'din sallah kaman kullum tayi shiru idanuwanta a lumshe..

Zama kusada ita taji anyi ta bu'de idanuwanta ahankali ta sauke kan nuratu...

Qasa qasa da murya nuratu tace,
Anty ayshah jiya Da ina dawowa daga makaranta nagansa acikin anguwar Nan..yauma Dana
dawo nagansa.

Qurawa nuratu jajayen idanuwanta tayi gabanta na duka da qarfi....

Muryarta na rawa tace,

Kinfa'dawa wani kingansa?

Girgixa Kai tayi tana kallon ayshahn tace,

Anty ayshah kina sonsane?

Hawayen dasuka gangaro Mata ta goge da bayan hannu tace,

Ina sonsa nuratu..

Dafata nuratun tayi cikin danne mamakin da tausayawa tace,

Anty ayshah karki Bari zuciya da shai'dan suyi galaba akan tarbiyar da iyayenmu sukai shekaru
suna bamu.

Cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta ta bawa hawayen datake dannewa Daman kwarara..


Washe gari shiryawa tayi a sanyaye Dan batada tabbacin za'a barta cigaba da karatun duk da
tuni ya fara wargajewa.

Cikin ikon Allah ba'a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen
titi nanta ha'diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar
gida suna Shirin fitowa...

Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui
Masa Mai kyauba.


Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron
wani qaramin gida..

Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare
dasuba.

Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi...

Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin 'dinsa ya saitashi ya jefa Masa
Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya 'dago lazy eyes 'dinsa
dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya
batareda yau ya gano gidansuba.

Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.

Azafafe yace,

Uban me kakeyi anan?

Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa'daba..

Mari Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..
Yace,

He said wat are you doing hia you monkey fool.

Kallon Umar 'din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani 'dan Adam Kai tsaye yace,

I came hia to see my love.

Ture sani Umar yayi da qarfi ya shaqo wuyan Nik 'din yace,

Wh...wh..who is your love?

Ayeeshah''''""ya fa'da Kai tsaye ba tsoro a idanuwansa.

Hannu ya dunqule yakaiwa Nik wani mugun duka Saida bakinsa ya fashe.

Wani dattijo ayshah tagani zai wuce tayi saurin Shan gabansa tana hawaye tace,

Baba Dan Allah kaga wasu can suna fa'da Dan Allah ka hanasu karka Bari ayi fitina.

Juyawa yayi ya kalli gurin daidai sun nanna'de rigunansu zasu cire takaicin dukan daakayiwa
iyayensu dattijon yayi saurin tarewa tareda matsarda Nik dake tsaye baida alamar motsawa
gefe yace,

Haba Kuna 'yayan musulmai 'yayan manyan malamai zakuyi Abu irin na jahilai...
Meyayi zafi haka dabazaku Kira hukuma ba Zaku 'dauki mataki da hannunku...

Fa'da yahau yi musu sosai suka basa hkr tareda barin gurin sbd duk zafin ransu sunada
tarbiyar girmama babba sosai Koda basusanshiba.


Juyowa yayi ya kalli Nik yace,

Kaima ka wuce tunda Suma sun tafi..

Juyawa yayi ahankali yabi bayansu duk da baisan abinda mutumin yafadaba...shidai yau
alqawarine yayiwa zuciyarsa saiyaganta Dan haka zaibi bayansu saiyaga gidansu..

Daf dazai shiga kwanar yaji anriqo rigarsa ta baya yayi saurin juyowa sukai Ido biyu ta juya
yabiyota da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login